2015/01/04

صفة صلاة النبي صلى الله عليه وسلم من قبل التكبير إلى ما بعد السلام

SIFFAR SALLAR ANNABI (SAW) ([1])
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah shi kaxai, Salati da sallama su qara tabbata ga bawansa kuma manzonsa; annabinmu Muhammad da Iyalansa da Sahabbansa, Bayan haka:
Waxannan yan kalmomi ne takaitattu da suke bayanin siffar sallar annabi (SAW) mun yi nufin gabatar da su ga xaukacin musulmai maza da mata; domin duk wanda ya leka abin da ke cikin takardun ya yi iya qoqarinsa wajen koyi da annabi (SAW) cikin haka; saboda faxinsa (SAW):
«صَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِي أُصَلِّي».
Ma'ana: "Ku yi sallah kamar yadda ku ka ganni nake sallah"([2]). Bukhari ne ya rawaito shi.
GA BAYANIN HAKAN GA MAKARANCI:
Musulmi dole ya cika alwalarsa: Wannan kuma shi ne ya yi alwala kamar yadda Allah ya umurce shi; yana mai aiki da faxinsa maxaukakin sarki:
(يا أيها الذين ءامنوا إذا قمتم إلى الصلاة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم إلى المرافق وامسحوا برؤوسكم وأرجلكم إلى الكعبين)  المائدة: ٦
Ma'ana: "Ya ku waxanda suka yi imani idan kuka tashi izuwa ga sallah sai ku wanke fiskokinku da hannayenku zuwa guiwoyin hannu, ku shafi kayukanku, kafofinku kuma ku wanke su zuwa idon sawu guda biyu", [Ma'idah: 6]. Da kuma aiki da faxin annabi (SAW):
«لا يَقْبَلُ اللَّه صَلاةً بِغَيْرِ طُهُورٍ».
Ma'ana: "Allah baya karbar sallar da aka yi ta babu tsarkaka"([3]). Da kuma fadinsa ga Mutumin da ya munana sallarsa:
«إِذَا قُمْتَ إِلَى الصَّلاَةِ فَأَسْبِغِ الوُضُوءَ».
Ma'ana: "Idan ka tashi izuwa ga sallah sai ka cika alwala"([4]).
Sai mai sallah ya fiskanci alqiblah; -Wacce: ita ce ka'abah- Zai fiskance ta a ko-ina ya ke a cikin duniya, da xaukacin jikinsa, yana mai nufan sallar da ya ke nufi; ta nafila ce ko ta farilla da zuciyarsa, amma ba zai furta niyyarsa ba da harshensa; saboda furta niyyah ba shari'a ba ne; dalili kuwa shine annabi (SAW) da sahabbansa (RA) basu furta ta ba. Sai kuma ya sanya "SITRAH" a gaba gare shi; ya yi sallah zuwa gare ta; in ya kasance liman ne ko kuma mutumin da ke sallarsa shi kaxai. Shi kuma fiskantar alqiblah a cikin sallah yana daga cikin sarruxanta (ma'ana: abubuwan da in ba a aikata su ba sallah bata inganta), Sai dai a wassu halaye sanannu da aka togace, waxanda aka yi bayaninsu a cikin littatafan ma'abota ilimi.
Sai kuma ya yi kabbarar harama; Yana mai cewa: "ALLAHU AKBAR", yana mai dubin gurbin sujjadarsa da ganinsa.
Yana mai xago hannayensa guda biyu a lokacin kabbararsa daidai da (setin) kafaxunsa guda biyu, ko kuma daura da kunnuwansu guda biyu.
Zai kuma xora hannayensa guda biyu akan qirjinsa; tafin hannun dama kuma akan tafin hagu; saboda tabbatan hakan daga annabi (SAW).
Sunna ne ya karanta addu'ar buxe sallah (istiftah); Wacce kuma ita ce:
«اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبِ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنَ الــــخَطَايَا كَـمَا يُنَــــــــــقَّى الثَّوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللَّهُمَّ اغْسِلْ خَطَايَايَ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالبَرَد»([5]).
In kuma yaso sai ya ce: 
«سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ، وَتَعَالَى جَدُّكَ، وَلَا إِلَهَ غَيْرُك»([6]).
Idan kuma ya karanta wanin addu'oin nan guda biyu daga cikin addu'oin buxe sallah, da suka tabbata daga annabi (SAW) to hakan ya yi qyau. Sai dai kuma mafificin abu shi ne ya aikata wannan addu'an a wannan lokacin, wancan kuma a wani lokacin na daban; saboda yin hakan shi ke nuna "cikakken koyi da manzon Allah".
Sa'annan sai ya ce: "A'UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIIM, BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIIM.
Sanannan sai ya karanta "FATIHAH" gabaxayanta, saboda faxinsa (SAW):
«لا صَلاةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ الْكِتَاب».
Ma'ana: "Babu sallah ga mutumin da bai karanta FATIHAH ba"([7]).
Sai kuma ya ce: "Aamin" bayan ya gama karanta ta; a bayyane a sallar da ake bayyana karatu a cikinta.
Sa'annan sai ya karanta duk abin da ya sauwaqa na daga ayoyi ko surorin alqur'ani.
Daga nan sai ya yi ruku'i yana mai yin kabbara, tare da xago hannayensa daidai da kafaxunsa, ko kunnuwansa guda biyu; yana mai sanya kansa daidai da bayansa, hannayensa guda biyu kuma akan guiwowinsa, tare da bubbuxe tsakanin yatsunsa.
Dole ne kuma ya nitsu a cikin ruku'insa.
Yana mai cewa: "SUBHANA RABBIYAL AZIIM", Anso ya maimaita haka sau uku ko fiye da haka. kuma mustahabbi ne ya qara akan haka da faxinsa: "SUBHANAKAL LAHUMMA RABBANA WA BIHAMDIKA ALLAHUMMA IGFIR LIY".
Sai ya xago kansa daga ruku'i, yana mai xago hannayensa guda biyu daidai da kafaxunsa guda biyu ko kunnuwansa, yana mai faxin: "Sami'al lahu liman hamidah"; Idan liman ne ko kuma mai sallah shi kaxai. Bayan kuma ya riga ya gama tsayuwa sai ya ce: " RABBANA WA LAKAL HAMD, HAMDAN KASIRAN DAYYIBAN MUBARAKAN FIYHI, MIL'AS SAMAWAATI WA MIL'AL ARDI WA MIL'A MA BAINAHUMA WA MIL'A MA SHI'TA MIN SHAI'IN BA'AD".
Amma idan kuma mamu ne to shi a lokacin xagowarsa daga ruku'i zai ce: "RABBANA WA LAKAL HAMD; HAMDAN KASIRAN XAYYIBAN MUBARAKAN FIYHI, MIL'AS SAMAWAATI WA MIL'AL ARDI WA MIL'A MA BAINAHUMA WA MIL'A MIN SHAI'IN BA'AD".
Kuma mustahabbi ne ga kowanne daga cikin liman da mamu su sanya hannayensu akan qirazansu, kamar yadda suka aikata hakan a cikin tsayuwarsu; gabanin su yi ruku'i; saboda tabbatan abin da ke nuna hakan daga annabi (SAW); a hadisin Wa'il xan Hujr, da Sahl xan Sa'ad (RA).
Sai kuma ya yi sujjada, yana mai fara ajiye guiwowin qafofinsa akan qasa gabanin hannayensa; idan hakan ya sauqaqa masa; in kuma aikata hakan ya wahalar da shi to sai ya fara gabatar da hannayensa gabanin guiwowinsa, yana mai fiskantar alqiblah da kan yatsun qafofinsa da hannayensa, tare da haxe tsakanin yatsun hannayensa.
Kuma mutum zai yi sujjada ne akan gabbai guda bakwai; goshinsa tare da hanci, hannaye guda biyu, da guiwowi biyu, da cikin 'yan yatsun qafofi guda biyu.
Sai kuma ya ce: "SUBHANA RABBIYAL A'ALAH", zai maimaita hakan har sau uku ko fiye da haka.
Kuma mustahabbi ne ya qara da cewa: "SUBHANAKAL LAHUMMA RABBANA WA BI HAMDIKA, ALLAHUMMA IGFIR LIY". Sai ya yawaita addu'oi; saboda faxinsa (SAW):
«فَأَمَّا الرُّكُوعُ فَعَظِّمُوا فِيهِ الرَّبَّ عَزَّ وَجَلَّ، وَأَمَّا السُّجُودُ فَاجْتَهِدُوا فِي الدُّعَاءِ، فَقَمِنٌ أَنْ يُسْتَجَابَ لَكُمْ».
Ma'ana: "Amma shi ruku'i to sai ku girmama ubangiji a cikinsa, Shi kuma sujjada ku yi qoqarin addu'oi a cikinsa; ya cancanci a amsa muku"([8]). Sai mutum ya roqi ubangijinsa alkhairin duniya dana lahira, sawa'un sallar ta farilla ce ko ta nafila.
Sannan ya kuma nisantar da damatsunsa daga kuivinsa, ya nisanta cikinsa ga cinyoyinsa, suma cinyoyin sai ya nisanta su daga kwabrin qafofinsa guda biyu, yana mai xage zira'insa daga qasa; saboda faxin annabi (SAW):
«اعْتَدِلُوا فِي السُّجُودِ، وَلا يَبْسُط أَحَدُكُمْ ذِرَاعَيْهِ انْبِسَاطَ الْكَلْبِ».
Ma'ana: "Ku daidaita a  cikin sujjadarku, kada xayanku ya shumfuxa zira'insa kamar yadda kare ke shumfuxawa"([9]).
Sai kuma ya xago kansa daga sujjada, tare da faxin "ALLAHU AKBAR" yana mai shumfuxa dugadugin qafarsa ta hagun tare da zaunawa akanta, ya kuma kafe qafarsa ta dama, sai kuma ya xora tafukansa guda biyu akan cinyoyinsa guda biyu da guiwarsu, yana mai cewa:
«رَبِّ اغْفِرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَارْزُقْنِي، وَعَافِنِي وَاجْبُرْنِي»([10]).
RABBI IGFIR LIY, WARHAMNIY, WARZUQNIY, WA AFINIY, WAJBURNIY.
Wajibi ne mutum ya nitsu a cikin wannan zaman.
Sa'annan sai ya yi sujjada ta biyu, tare da faxin "ALLAHU AKBAR", Zai aikata kwatankwacin abin da ya aikata a cikin sujjadarsa ta farko.
Sa'annan sai ya xago kansa yana mai yin kabbara, Sai kuma ya yi zama takaitacce kamar irin zaman da ke kasancewa tsakanin sujjada, ana kiran wannan zama "JILSATUL ISTIRAHA", hukuncin aikata hakan kuma mustahabbi ne, ta yadda idan da bawa zai bar aikatata to da ba komai akansa, kuma ba a yin wani"zikiri ko addu'a a cikin wannan zama".
Daga nan sai mutum ya zabura izuwa ga raka'a ta biyu, yana mai dogara -a lokacin tashinsa- akan guiwowinsa guda biyu, in hakan ya yi masa sauqi, in kuma da wahala to sai ya dogara akan qasa. Sa'annan sai ya karanta "FATIHA" da kuma abin da ya sauwaka na alqur'ani bayan fatihar.
Sa'annan sai ya aikata kwatankwacin abin da ya aikata a raka'ar farko.
Idan sallar raka'a biyu take da su, kamar sallar asuba da juma'a da idin azumi ko layya To sai ya zauna bayan xagowarsa daga sujjada ta biyu, yana mai kafe kafarsa ta dama, tare da shumfuxa kafarsa ta hagu, yana mai xora hannunsa na dama akan cinyarsa ta dama, da dunkule 'yan yatsunsa gabaxayansu in banda manuniyar yatsa; yana mai nuni da ita zuwa ga tauhidi, idan kuma da zai damqe qaramar yatsa da wacce ta ke biye da ita, sai kuma ya lankwashe babbar yatsarsa tare da ta tsakiya, sai kuma ya yi nuni da manuniya to hakan ya yi qyau; saboda dukkan sifofin guda biyu sun tabbata daga annabi (SAW). Amma mafificin abu shi ne ya aikata wannan a wannan lokaci, dayan kuma a wani lokacin na daban. Sai kuma ya sanya hannunsa na hagu akan cinyarsa ta hagu da guiwarsa, Sa'annan ya yi "TAHIYA" a wannan zaman, wanda kuma shi ne: "ATTAHIYYATU LIL LAHI WAS-SALAWATU WAX-XAYYIBATU, ASSALAMU ALAIKA AYYUHAN NABIYYU WA RAHMATUL LAHI WA BARAKATUHU, ASSALAMU ALAINA WA ALA IBADIL LAHIS SALIHINA, ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUH"([11]).
Sa'annan sai mutum ya ce: "ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMA SALLAITA ALA IBRAHIMA WA ALI IBRAHIMA; INNAKA HAMIDUN MAJID, WA BARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMADIN KAMA BARAKTA ALA IBRAHIMA WA ALI IBRAHIMA; INNAKA HAMIDUN MAJID"([12]).
Sa'annan sai ya nemi tsarin Allah daga munanan abubuwa guda huxu; ya ce:
«اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَـرِّ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ».
Ma'ana: "Allah ina neman tsarinka daga azabar jahannama, da kuma azabar kabari, da kuma fitinar rayuwa da ta mutuwa, da kuma fitinar mai shararren ido; dujjal".
Sa'annan sai ya yi duk addu'ar da ya ga dama; na alherorin duniya da lahira. Kuma idan da zai yi addu'a ga iyayensa ko kuma ga waninsu daga cikin musulmai to da haka ya yi qyau; sawa'un sallar ta farilla ce ko ta nafila; saboda gamewar faxinsa (SAW) a cikin hadisin Abdullahi xan Mas'ud a yayin da ya koya masa "TAHIYA":
«ثُمَّ لِيَتَخَيَّرْ مِنَ الدُّعَاءِ أَعْجَبَهُ إِلَيْهِ فَيَدْعُو به».
Ma'ana: "Sannan sai ya zavi abin da ya burge shi na addu'a; sai ya yi addu'a da shi"([13]). A wani lafazin kuwa:
«ثُمَّ يَتَخَيَّرُ مِنَ الْمَسْأَلَةِ مَا شَاءَ».
Ma'ana: "Sannan sai ya zabi abin da ya so na addu'a"([14]). Wannan kuma ya game dukkan abin da zai amfanar da bawa a rayuwarsa ta duniya da kuma ta lahira.
Daga nan sai ya yi sallama, ta bangarensa na dama, dana hagu, yana mai cewa: AS-SALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAHI, AS-SALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAH,
In kuma sallar tasa mai raka'a uku ce, kamar sallar magriba, ko hudu kamar sallar azahar da la'asar da ishah, To a nan zai karanta TAHIYAR da ta gabata, sannan ya yi SALATI ga manzon Allah (saw). Daga nan sai ya miqe a tsaye, yana dogara akan guiwowinsa, tare da xaga hannayensa daidai da kafaxunsa yana mai cewa: ALLAHU AKBAR, Sai kuma ya xora su akan qirjinsa, kamar yadda ya gabata. Sai ya karanta surar FATIHA kawai. In kuma a wassu lokuta ya karanta wassu sashin surori bayan fatihar, to ba laifi; saboda ya tabbata cewa wani lokaci annabi (saw) yana karanta "sura" a waxannan raka'oin bayan fatiha, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Abu-sa'id (ra) ([15]).
Idan kuma da mutum zai bar yin salati ga annabi a tahiyar farko to ba komai; saboda yinsa a tahiyar farko mustahabbi ne ba wajibi ba.
Sa'annan sai ya yi tahiya bayan raka'a ta uku, a sallar magriba, da kuma bayan ta hudu a sallar azahar da la'asar da isha'i, kamar yadda hakan ya gabata a sallah mai raka'oi guda biyu.
Sa'annan sai ya yi sallama ta dama da shi da kuma ta hagu.
Sannan sai ya ce: ASTAGFIRULLAH, sau uku.
Sai kuma ya ce:
«اللهُمَّ أَنْتَ السَّلاَمُ، وَمِنْكَ السَّلاَمُ، تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالإِكْرَامِ».
"ALLAHUMMA ANTAS SALAMU, WA MINKAS SALAMU, TABARAKTA YA ZAL JALALI WAL IKRAAM"([16]).
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ».
"LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR"([17]).
«اللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَيْتَ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدّ».
"ALHUMMA LA MANI'A LIMA A'AXAITA, WALA MU'UXIYA LIMA MANA'ATA, WALA YANFA'U ZAL JADDI MINKAL JADDU"([18])
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ، وَلَهُ الْفَضْلُ، وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ».
LA ILAHA ILLAL LAHU; WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR. LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH, WALA NA'ABUDU ILLA IYYAH, LAHUN NI'IMATU WA LAHUL FADL, WA LAHUS SANA'UL HASAN, LA ILAHA ILLAL LAHU, MUKHLISIYNA LAHUD DINA, WA LAU KARIHAL KAFIRUUNA"([19]).
Sannan ka yi SUBHANAL LAHI sau talatin da uku (33).
Ka ce ALHAMDU LIL LAHI sau talatin da uku (33).
Sai kuma ka ce ALLAHU AKBAR sau talatin da uku (33).
Sannan sai ka fadi cikon darin: LA ILAHA ILLAL LAHU; WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR.
Sai kuma ya karanta "ayatul kursiyyi", da KUL HUWAL LAHU AHAD, da KUL A'UZU BI RABBIL FALAQ, da KUL A'UZU BI RABBIN NAAS. Bayan kowace sallah.
Kuma mustahabbi ne ya maimaita surorin nan guda uku, sau uku, bayan sallar asuba da magriba, saboda hadisi ingantacce ya zo akan haka, daga manzon Allah (saw) ([20]).
Kamar yadda kuma mustahabbi ne, ya yi qari akan zikirin da ya gabata, bayan sallar magriba da asuba, ta hanyar faxin:
LA ILAHA ILLAL LAHU; WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, YUHYI WA YUMIYTU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR. Saboda tabbatan hakan daga manzon Allah (saw).
Idan liman ne an so bayan ya yi ASTAGFIRULLAHI sau uku, ya kuma fadi "ALLAHUMMA ANTAS SALAMU WA MINKAS…"([21]) mustahabbi ne a gare shi ya juya zuwa ga mutane, yana mai fiskantarsu Sa'annan sai ya zo da sauran zikirorin da su ka gabata, kamar yadda hadisai da yawa daga annabi (saw) su ka yi nuni akan haka, Daga cikinsu akwai hadisin A'ishah (ra) a cikin sahihu Muslim([22]).
Su kuma waxannan zikirorin dukkansu sunnoni ne babu farilla.
Kuma an shar'anta wa kowani musulmi namiji da mace da su yi raka'a guda hudu gabanin sallar la'asar, da raka'a biyu bayanta, bayan sallar magriba kuma raka'a biyu, bayan isha'i raka'a biyu, haka kuma gabanin sallar asuba raka'a biyu, gabaxaya za su zama raka'a goma sha biyu (12), waxannan raka'oin kuma ana kiransu sallolin RAWATIB, saboda annabi (saw) ya kasance yana aikata su a halin zaman gari, amma a halin kasancewarsa matafiyi kuma ya kan bar aikata su, in banda raka'oi guda biyu na sunnar alfijir (da ake yinsu bayan ketowarsa) da kuma witiri, waxannan biyun kam annabi (saw) ya kasance yana kiyaye su a halin zaman gida da kuma yanayi na tafiya.
Kuma abun da ya fi falala shi ne a yi sallolin rawatib da witiri a cikin gidaje, amma idan da mutum zai yi su a cikin masallaci to ba laifi akan haka, saboda fadin annabi (saw):
«أَفْضَل الصَّلاَة صَلاَة الْمَرْءِ فِى بَيْتِهِ إِلاَّ الْمَكْتُوبَةَ».
Ma'ana: "Mafificin sallar mutum shi ne sallarsa a cikin gidansa in banda ta farilla"([23]).
            Kiyaye yin aiki da waxannan nafilolin yana daga sabbuban shiga aljannah, saboda faxin annabi (saw):
«مَنْ صَلَّى اثنْتَيْ عَشْرَةَ رَكْعَةً فِي يَوْمه وَلَيْلَته تَطَوُّعًا، بنى الله لَهُ بَيْتًا فِي الْجَنَّة».
Ma'ana: "Duk wanda ya kiyaye raka'oi guda goma sha biyu (12) cikin yininsa da darensa na nafila, Allah zai gina masa gida a cikin gidan aljannah"([24]). Muslim ya rawaito shi a cikin "sahihinsa".
            Idan da kuma mutum zai yi raka'oi guda hudu gabanin yin sallar la'asar, da raka'oi biyu gabanin magriba, da wassu biyun bayan isha to hakan ya yi kyau, saboda abin da ke nuni akan hakan ya tabbata daga annabi (saw).
            Haka kuma da zai sallaci raka'oi guda hudu bayan azahar, da wassu hudun gabaninta to wannan shima ya yi qyau, saboda faxinsa (saw):
«مَنْ حَافَظَ عَلَى أَرْبَعِ رَكَعَاتٍ قَبْلَ الظُّهْرِ، وَأَرْبَعٍ بَعْدَهَا، حَرُمَ عَلَى النَّارِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya kiyaye raka'oi guda hudu gabanin azahar, da guda hudu bayanta, to ya haramta ga wuta"([25]). Imam Ahmad ne da ma'abota littafan sunan (Abu-dawud, Tirmiziy, Nasa'iy da Ibnu-majah) su ka rawaito shi da isnadi ingantacce, daga Ummu-habibah (ra). Ma'ana a nan shi ne: Bawa zai yi qarin raka'oi guda biyu bayan "sunna ratiba" da ake yinta raka'a biyu bayan azahar, domin sunna ratibar ita ce a yi raka'a hudu gabanin azahar da kuma biyu bayanta; don haka idan ya kara biyu akan haka sai abin da aka ambata cikin wannan hadisin da Ummu-habibah (ra) ta rawaito ya samu.
            Allah shi ne majivincin dacewa!
Salati da sallama su qara tabbata ga annabinmu Muhammadu xan Abdullahi, da kuma iyalansa, da sahabbansa, da waxanda su ka bi su da qyautatawa zuwa ranar sakamako.
$/&/$



([1]) MAJMU'U FATAWA IBNU-BAAZ, (11/1-17).
([2]) Bukhariy ya rawaito shi, daga hadisin Malik xan Alhuwairs, (lamba: 631).
([3]) Muslim ya rawaito shi, daga Abdullahi xan Umar (ra), (lamba: 224).
([4]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 757), da Muslim (lamba: 397) daga hadisin Abu-hurairah (ra).
([5]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 744), da Muslim (lamba: 598) daga hadisin Abu-hurairah (ra).
([6]) Wannan lafazi ya zo daga maganar annabi (saw, da ake masa laqabi da: marfu'i), ta hanyar Abu-sa'id da A'ishah (ra), a wajen Abu-dawud, (lamba: 775, 776), Shi kuma Imam Muslim ya fitar da shi daga maganar Umar bn Alkhaxxab –ra- (wato: Mauqufi, da lamba: 399) daga hadisin Abu-hurairah (ra).
([7]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 756), da Muslim (lamba: 394) daga hadisin Ubadah bn  Samit (ra).
([8]) Hadisin Wa'il (ra) Muslim ne ya rawaito shi a cikin "sahihinsa", (lamba: 401). Shi kuma hadisin Sahal xan Sa'ad (ra) Bukhariy ne ya rawaito shi (740).
([9]) Muslim ne ya rawaito shi, (lamba: 497), daga hadisin Abdullahi xan Abbas (ra).
([10]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 532), da Muslim (lamba: 493) daga hadisin Anas (ra).
([11]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 831), da Muslim (lamba: 402) daga hadisin Abdullahi xan Mas'ud (ra).
([12]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 3379), da Muslim (lamba: 493) daga hadisin Ka'ab bn Ujrah (ra).
([13]) Wannan riwaya ce a cikin "sunan Abiy-dawud", (lamba: 968).
([14]) Bayanin wanene ya rawaito wannan hadisin ya gabata cikin hadisin Abdullahi xan Mas'ud (ra) da ke magana kan sigar tahiyoyi, wanda Imam Muslim ya rawaito.
([15]) La'alla malam a nan yana nufin hadisin da Imam Muslim ya rawaito daga hadisin Abu-sa'id (ra), (mai lamba: 451) .
([16]) Muslim ya rawaito shi daga hadisin Sauban da A'ishah (ra), (lamba: 591, 592).
([17]) Daidai wannan wuri a cikin wannan hadisi, Bukhariy da Muslim duka sun rawaito shi (Bukhariy, lamba: 808, Muslim, lamba: 593) daga hadisin Mugiyrah xan Shu'ubah (ra).
([18]) Muslim ne ya rawaito shi, (lamba: 594) daga hadisin Abdullahi xan Az-zubair (ra).
([19]) Muslim ne ya rawaito shi, (lamba: 595) daga hadisin Abu-hurairah (ra).
([20]) Wato hadisin Abdullahi xan Habib. Bayani kan wani malami ne ya ambace shi; daga cikin maluman hadisai, a littatafansu, zai zo, a lokacin ambato: ZIKRORIN SAFE DA MARAICE, da lamba: (4) .
([21]) Bayani akan wanene ya ambato wannan hadisin a cikin littafinsa, ya gabata. (Muslim, lamba: 592).
([22]) Wannan magana mun ciro ta daga littafin TUHFATUL IKHWAAN, Na Ibnu-baaz, (shafi: 13), da kuma MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH, (11/ 188, da 26/ 24).
([23]) Bukhariy ne ya rawaito shi, (lamba: 731), da Muslim (lamba: 781) daga hadisin Zaid xan Sabit (ra).
([24]) Muslim ya rawaito shi, (lamba: 728) daga hadisin Ummu-habiybah bint Abu-sufyan (ra).
([25]) Ahmad ya rawaito shi (6/236), da abu-dawud (lamba: 1269), da Tirmiziy (lamba: 427), ya ce: hadisi ne mai qyau (hasan), da Nasa'iy (lamba: 1415), da Ibnu-majah (lamba: 1160).

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...