الأسئلة العشرة عن برنامج "الخلفاء الأربعة الراشدين" بقلم: أبو بكر حمزة
(1)
TAMBAYA: Menene dalilin yin laƙabi
ga Abubakar (RA) da "As-siddiq"?
AMSA: Saboda yawan gaskata
manzon Allah (SAW).
(2)
TAMBAYA: Menene sunan mutane hudu (4) da haifayya ce
tsakaninsu, waɗanda
kuma dukkanninsu sun shiga "musulunci"?
AMSA: 1- Abdullah bn Usman
(Abubakar Siddiq -RA-), 2-
Usman bn Amir (Mahaifin Abubakar Siddiq), 3- Asma'u Bnt Abubakar Siddiq ('Yar uwar A'ishah), 4- Abdullahi bn Az-zubair bn
Al-awwam (Jikan Abubakar Siddiq ta wajen 'yarsa Asma'u).
(3)
TAMBAYA: Wanne malami ne yace: falalolin Abubakar Siddiq
(RA) galibinsu "KHASA'IS" ne; Ma'ana: Sauran sahabbai basu yi tarayya
da shi a cikinsu ba?
AMSA: Shekhul Islam Ahmad bn
Abdulhalim (Ibnu taimiyyah).
(4)
TAMBAYA: Menene sunan matar manzon Allah (SAW) kuma 'ya ga
Umar bn Al-khaɗɗab?
AMSA: Sunanta shine: Hafsah
bnt Umar (RA).
(5)
TAMBAYA: Menene sunan mutumin da ya kashe Umar bn Al-khaɗɗab (RA); Ma'ana: ya zama
sababin shahadarsa?
AMSA: Fairuz (laƙabinsa:
Abu-lu'ulu'ah Almajuwsiy).
(6)
TAMBAYA: Wane mutum ne ya kama kafadar Abdullahi bn Abbas
(RA) a lokacin da suke tsaye akan gawarsa (Umar bn Al-khaddab -RA-); yake kuma ta
yabonsa (Umar) da yi masa addu'o'i?
AMSA: Aliyu bn Abiy-ɗalib (RA).
(7)
TAMBAYA: Menene sunan matan Usman bn Affan (RA) guda biyu
wanda ya samu laƙabin "zun-nuuraini"
saboda auransu da ya yi, kuma 'ya'ya ne ga Manzon Allah (SAW)?
AMSA: Sunansu shi ne 1-
Rukayyah (RA), da 2- Ummu Kulsuum (RA).
(8)
Aliyu bn Abiy-ɗalib (RA) yace: "Mafi
alherin mutane bayan Manzon Allah (SAW) shi ne: Abubakar, Sa'annan sai
Umar" Sai 'dansa yace: Sai naji tsoron kar yace: Sai Usman; Sai nace:
Sa'annan sai kai? Sai yace: Ni ba kowa bane face: 'Daya daga cikin
musulmai". TAMBAYA: Menene
sunan 'dan Aliyu da ya masa wannan tambayar?
AMSA: Sunansa shine Muhammad (ƙani
ne ga Al-hasan da Al-husain, laƙabinsa kuma: Ibnul-hanafiyyah).
(9)
TAMBAYA: Menene sunan 'yar Aliyu bn Abiy-ɗalib (RA); da ya aurar da
ita ga Umar bn Alkhaɗɗab (RA)?
AMSA: Sunanta shine:
Ummu-kulsuum (jika ce ga manzon Allah -SAW- ta wajen 'yarsa: Faɗimah)?
(10)
TAMBAYA: Menene sunan mutumin da ya kashe Aliyu bn
Abiy-ɗalib
(RA); Ma'ana: ya zama sababin shahadarsa?
AMSA: Sunansa shine:
Abdurrahman bn Muljim Almuradiy (ɗaya daga cikin khawarijawa).
No comments:
Post a Comment