2015/01/05

RANAR DA MIJIN KE KOKARIN ZAMA MATAR, ITA KUMA MATAR KE KOKARIN ZAMA MIJIN !!

استَوْنَق الجملُ، واستدْيَكَت الدجاجةُ
ME ZAI KASANCE RANAR DA MIJIN KE KOKARIN ZAMA MATAR, ITA KUMA MATAR KE KOKARIN ZAMA MIJIN?
Amsa: Lallai mace tana da matsayi mai girma a musulunce; don itace: uwar gida, da yara, kuma taushi da soyayya, rahama ga miji da 'ya'ya (don haka, itace: jagora kuma abun koyi ga harkokin cikin gida).
Haka kuma shima miji yana da babba matsayi kuma da mafi girma, saboda kasancewar mazaje tsayayyu kuma shugabanni akan mata da daukacin iyalai (don haka: mazaje sune abun dogaro ga daukacin harkokin wajen gida). Wannan shine rabo na adalci da musulunci yazo da shi.
Bayan kason da Allah s w t yayi, ya bawa mata matsayinsu, haka suma mazaje, to kuma sai Allah da hikimarsa da buwayarsa ya daidaita su wajen hakkoki tare da bada daraja ta musamman wa maza akan mata a cikin fadinsa:
(وَلَهُنَّ مِثْلُ الَّذِي عَلَيْهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ، وَلِلرِّجَالِ عَلَيْهِنَّ دَرَجَةٌ) سورة البقرة: 228).
Ma'ana: (Lallai su mata suna da kwatankwacin abin da ke kansu na hakkoki, da kyautatawa. Kuma lallai mazaje suna da wata daraja mai girma akan mata).
          kamar yadda kuma Allah mai girma, cikin hikimarsa sai ya hani sashe (mata) yin burin samun abinda Allah ya fifita sashe (maza) akan shashen (matan) da shi, cikin fadinsa:
(وَلا تَتَمَنَّوْا مَا فَضَّلَ اللَّهُ بِهِ بَعْضَكُمْ عَلَى بَعْضٍ، لِلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِمَّا اكْتَسَبُوا، وَلِلنِّسَاءِ نَصِيبٌ مِمَّا اكْتَسَبْنَ، وَاسْأَلُوا اللَّهَ مِنْ فَضْلِهِ) (سورة النساء: 32).
Ma'ana: (Kuma kada kuyi burin abinda Allah ya fifita sashinku da shi akan sashi, mazaje suna da rabo da sakamako na daga abinda suka aikata, suma mata suna da rabo da sakamakon abinda suka aikata. Ku dai ku roki Allah daga falalarsa) maimakon burin samun abinda Allah ta'alah ya fifita sashinku da shi.
To bayan wannan, a nan ne tambayarmu zata fado: MENENE ZAI KASANCE LOKACIN DA MIJIN YA ZAMTO MATAR, ITA KUMA MATAR TA ZAMA MIJIN?
Lallai abun mamaki ne ka samu namiji a gidansa -koma a wajen gidan- yayo kasa da darajarsa yayi koyi da mata cikin ayyukansu da sifofinsa, Shi yasa wani mawaki ke cewa:
وما عجَبٌ أنّ النساء ترجَّلَتْ ## ولكنّ تأنيثَ الرجال عُجابُ
Ma'anar maganar ita ce: (Ba abun mamaki ba ne: mata su yi kokarin komawa maza, Sai dai abun mamakin shine: Maza su yi kokarin komawa mata!). Ta'aliki a nan: Duka neman zama hakan kuskure ne.
Wannan kuma shi yasa larabawa su ke da Karin-magana da take cewa:
استَوْنَقَ الجمَلُ، واسْتَدْيَكَتِ الدّجاجة
Ma'ana: (Rakuma na kokarin zama namijin rakumi, kaza kuma na neman zamowa zakara).
          Sukan kuma buga wannan Karin-maganar ne: don su yi bayanin: Saukan maza daga matsayin lokacin da suka nemi kamantacceniya da mata, da kuma neman hawan mata matsayin maza a yayin da suke neman yin kama da mazaje. Dukkan hali biyun abun zargi ne kuma abun kyama, sai dai wanda yafi muni shine: Na bangaren mazaje; saboda daga cikin sifofin mata akwai rauni da gajen hakuri, namiji kuma juriya da karfi; saboda haka: Mai karfi ya matsa lamba cewa sai ya zama mai rauni, mai kuma hakuri da juriya ya dawo baya = babban abun mamaki ne, sannan kuma abun ki!
Dama kuma Manzon Allah (s a w) ya la'anci namijin dake kamantacceniya da mata, da kuma matan dake neman zama maza, Yazo a cikin Sahihul Bukhari (5885) Abdullahi bn Abbas –r a- yace:
(لَعَنَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْمُتَشَبِّهِينَ مِنْ الرِّجَالِ بِالنِّسَاءِ، وَالْمُتَشَبِّهَاتِ مِنْ النِّسَاءِ بِالرِّجَالِ(
A wannan zamanin kuwa zamanin fitina Mata na dage tufa, kamar su aka umurta da abinda aka umurci maza, kai harma su bude kirji da gashi da sauransu. Yayin da su kuwa mazan ke take wando da tsawaita tufa, irin yadda aka umarci mata da shi, Allah dai ya kiyashe mu.
Lallai-lallai za a samu babban koma baya, kuma tarbiyar 'diya maza, da 'yan mata zai rikide kana ya rikice lokacin da miji yayi sake har matarsa ta dawo matsayin mijin, saboda su mata a gida aka sansu, saboda a lokacin da mace ta fita kasuwa, da titi ba tare da lalura ba, shi kuma namiji ya zama maras ra'ayin da ba zai iya sayan lemo ko atumatur ba sai matar ta nuna masa; dauki wannan, dauki wancan, ma'ana: ya kai makura wajen lalacewar ra'ayi; matsayinsa a gidansa ya zama bai wuce na neman kudi, da tuka matarsa izuwa bukatunsu ba, Lallai a irin wannan yanayin: 'YA'YANSU MATA –BA TARE DA SUN FADAKA BA- ZASU YI KOKARIN KOMAWA MAZA, SU KUMA YARANSU MAZA ZASU TAFI CAN KASA; SU KWAIKWAYI MATA; Wal'iyazu billahi; saboda a 'dabi'ar 'ya mace –kamar yadda maluman da suka san halayyar 'dan adam ke bayyanawa- ta kan yi koyi ne da wanda yafi rauni a gidansu, a yayin da abubuwa suka juya; aka samu mijin (ubanta kenan) shi yafi rauni, to sai 'yarsa tayi koyi da shi, a garin kuma 'daukar halayyansa sai kaga ta 'dauki wassu halayya da sifofin maza, SAI KAGA TANA SAMUN MATSALA A CIKIN RAYUWAR AURENTA.
Haka shi kuma 'da namiji yakan yi koyi ne da wanda yafi karfi a gidansu; don haka a yayin da uwarsa ko matar gidan da ya tashi ta kwace matsayin mijin to zai yi koyi da ita ne a wannan yanayin –in ba taimakon Allah ya samu ba- sai wannan yaron ya samu wassu daga cikin halayya ko 'dabi'un mata ta yadda bai sani ba! Akwai kuma matsaloli masu yawa da za su hayayyafa akan wannan. Abin daya gabata kawai misali ne na irin wadannan matsalolin,
Wannan kuma shi ya sanya shari'a ta yi umarni ga miji da matarsa, da kuma namiji da mace, da cewa su tsaya –kowa- akan matsayin da aka ijiye shi, don samar da maslaha, tare kuma da kawar da mafsada, kamar yadda shari'ar ta ke yin hanin aikata sabanin haka, a cikin dalilan da suka gabata, saboda in dai hakan ya kasance; tofa lallai an kaddamar da jela ko bindi (wutsiya) dake can karshe akan kai da ke sama, kana kuma an juya ma'auni, kamar yadda wani mawakin ke cewa:
قد قُدّمَ العَجْبُ على الرُّوَيس ### وشارَف الوَهدُ أبا قُبَيس
وطاوَلَ البقْلُ فُرُوع المَيس ### وهبَّت العنزُ لِقَرعِ التيْسِ
وادَّعَت الرومُ أبًا في قيسِ ### واختلَط الناس اختلاطَ الحيْسِ
إذْ قرأ القاضِي حليفُ الكيسِ ### معانِي الشعر على العُبَيسي
Yara maza su yi kokari komawa mata, haka kuma su 'ya'ya mata su yi kama da yara maza shine abinda zai kasance idan abinda aka ambata cikin tambayar da ta gabata ya faru. Allah ya sauwaka.
Allah ne masani!
Reprence:
Na tsotso wannan ma'anar daga littatafa guda biyun da ke tafe, kana na rubuta wannan makalar:

-
من أخطائنا في تربية أولادنا وطرق علاجها في الإسلام، د. محمد بن عبد الله بن صالح السحيم.

- العدل في الشريعة الإسلامية وليست في الديمقراطية المزعومة، للشيخ عبد المحسن العباد البدر.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...