Tambaya:
Mutum ne ya yi sallah guda xaya
ma gawa har guda biyar (5), to shin yana da "kiyraaxi
guda" ne akan kowace gawa xaya?
ko kuma kiyraaxin" ana samunsa ne gwargwadon yawan sallolin?
Amsa: Ana
masa fatan ya samu tarin lada da ake kiransa "karaariyxa"
gwargwadon yawan gawawwakin, saboda faxin
annabi (saw):
«مَنْ صَلَّى عَلَى جَنَازَةٍ
وَلَمْ يَتْبَعْهَا فَلَهُ قِيرَاطٌ، فَإِنْ تَبِعَهَا فَلَهُ قِيرَاطَانِ».
Ma'ana: "Duk wanda ya yi
sallah ma gawa, sai kuma bai raka ta zuwa makwancinta ba to yana da lada –kiyraxi
guda xaya-, in kuma ya raka ta har aka bunne ta to yana da kiyraaxi
guda biyu"([2]). Da kuma saboda abin da ya zo na
hadisai da suke dauke da irin wannan ma'anar, kuma dukkaninsu suna nuna cewa
lallai shi lada na kiyraaxi yana
yawaituwa da yawan gawawwakin. Don haka; wanda ya yi sallah kaxai
ga gawa yana da "kiyraaxi",
shima wanda ya raka ta har aka bunne ta yana da nasa "kiyraadin",
wanda kuma ya mata sallah, sa'annan ya raka ta har zuwa a bunne ta to shi kuma
yana da "kiyraaxi" ne guda biyu. Wannan kuma yana daga cikin falalar
Allah (swt) da qyautarsa ko kuma baiwarsa ga bayinsa. Don haka; yabo da
godiya duka nasa ne, babu abun bauta da gaskiya, kuma babu ubangiji sai shi,
Allah kuma shi ne majivincin dacewa!
Tambaya:
Yaya yanayin sallah ma gawa ya ke, tare da faxaxa
zance, kuma shin dole ne ba a yinta (sallar gawa) sai da tsarki? ([3])
Amsa: Sallah
ma gawa lallai ba makawa sai da tsarki, saboda kasancewar manzon Allah (saw) ya
sanya mata suna sallah, don haka; itama sallah ce da ta ke da: buxewa
da yin kabbara, kana kuma ta ke da sallama, don haka; wajibi ne a yi ta da
tsarki, haka kuma wajibi ne a yi karatun fatiha a cikinta, da kuma yin addu'a
ga mamaci, sai kuma salati ga annabi (saw). Duk kuma mutumin da ya yi sallah ba
tare da ya yi tsarki ba, sallarsa bata inganta ba. Kuma abin da aka shar'anta a
cikinta su ne:
Mutum ya yi
kabbara (kabbararsa ta harama) daga farko, sa'annan sai ya karanta
fatihah da abin da ya sauwaqa a
bayanta.
Sa'annan sai ya
yi kabbara ta biyu, sai kuma ya yi salati ma
annabi (saw); irin salatin annabi Ibrahim (sanannen salati);
"اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى
مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وعَلَى آلِ
إِبْرَاهِيمَ فِي الْعَالَمِين إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَـارِكْ
عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وعَلَى
آلِ إِبْرَاهِيمَ فِي الْعَالَمِين إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيد".
"ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WA ALA AALI MUHAMMADIN,
KAMA SALLAITA ALA AALI IBRAHIMA WA ALA AALI IBRAHIMA FIL ALAMINA INNAKA HAMIDUN
MAJIID, ALLAHUMMA BARIK ALA MUHAMMADIN WA ALA AALI MUHAMMADIN, KAMA BARAKTA ALA
IBRAHIMA WA ALA AALI IBRAHIMA FIL AALAMINA INNAKA HAMIDUN MAJIID"([4]).
Sa'annan sai ya
yi kabbara ta uku; yana mai addu'a; Ya ce:
«اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِحَيِّنَا
وَمَيِّتِنَا، وَصَغِيرِنَا وَكَبِيرِنَا، وَذَكَرِنَا وَأُنْثَانَا، وَشَاهِدِنَا
وَغَائِــبِنَا، اللَّهُمَّ مَنْ أَحْيَـــــيْتَهُ مــــــنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى
الْإِيمَانِ، وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَّا فَتَوَفَّهُ عَلَى الْإِسْلَامِ،
اللَّهُمَّ لَا تَحْــــــرِمْنَا أَجْـــــرَهُ، وَلَا تُضِــــلَّنَا بَــعْدَهُ».
«اللهُمَّ، اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ
نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَــرَدِ،
وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا نَقَّيْتَ
الثَّوْبَ الْأَبْيَضَ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَـيْرًا
مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلًا خَيْرًا مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجًــــــا خَــيْـــــرًا مِـــنْ زَوْجِــهِ، وَأَدْخِـــلْـــهُ
الْجَــنَّةَ وَأَعِــــــذْهُ مِـــنْ عَــــذَابِ الْقَـــبْرِ -أَوْ مِــــنْ
عَـــــذَابِ الـــنَّـــارِ-». «وَافْـــسَــحْ لَــهُ فِي قَـــبْـــرِهِ، وَنَــوِّرْ
لَــهُ فِــيهِ».
Ma'ana: "Ya Allah ka
gafarta wa rayayyunmu da matattunmu, da qanananmu
da manyanmu, da mazanmu da matanmu, da halarceccenmu da wanda baya nan daga
cikinmu, Ya Allah duk wanda ka raya shi daga cikinmu to ka raya shi akan imani,
wanda kuma za ka kashe shi to ka kashe shi akan musulunci, Ya Allah kada ka
hana mu ladansa, kuma kada ka batar da mu a bayansa"([5]).
Ya Allah ka gafarta masa ka yi
masa rahama, ka bashi lafiya, ka kuma yi masa afuwa, ka karrama liyafarsa, ka
yalwata mashigarsa –kabarinsa-, ka wanke shi da ruwa, tare da kankara kanana da
manya, ka tsaftace shi daga laifuka kamar yadda ka ke tsaftace farar tufa daga
dauxa, ka canza masa gidan da ya fi nasa alheri, da iyalan da su
ka fi nasa alheri, da matar da tafi matarsa alheri, kuma ka shigar da shi
aljannah, ka tsare shi daga azabar kabari, -ko kuma ya ce: Daga azabar
wuta-"([6]).
Sa'annan sai ya
yi kabbararsa ta hudu; Sai
ya xan tsaya kaxan,
sannan ya yi sallama guda xaya ta
hannun damansa. Kuma mustahabbi ne ya riqa
xaga hannayensa a lokacin kowace kabbara.
Idan kuma gawar ta mace ce to
sai ya ce:
«اللهُمَّ، اغْفِرْ لَها ...».
Ma'ana: "Ya Allah ka
gafarta mata…". Idan kuma mutum biyu ne to sai ya ce:
«اللهُمَّ، اغْفِرْ لَهما ... ».
Ma'ana: "Ya Allah ka
gafarta musu su biyu…". Idan kuma adadin yafi haka to sai ya ce:
«اللهُمَّ، اغْفِرْ لَهم... ».
Ma'ana: "Ya Allah ka gafarta
musu…". Idan kuma gawar ta yaro ne ko yarinya tamace to sai ya ce:
«اللَّهُمَّ اجْعَلْهُ فَرَطًا
وَذُخْرًا لوالديه، وشفيعًا مُجابًا، اللهم ثقل به موازينــــــــــــــهـــما،
وأعظم به أجورهـــــمـــــــــــــــــا، وألحقه بصالح المؤمنين، واجعله في كفالة
إبراهيم u، وقِهِ برحمتك عذابَ الجحيم».
Ma'ana: "Ya Allah ka
sanya shi ya zamto rigayen kirki, mai tanadi ga iyayensa guda biyu, kuma mai
ceton da ake amsa masa, Ya Allah ka nauyaya ma'aunansu da shi, ka kuma girmama
ladansu da shi. A riskar da shi da salihan muminai, ka sanya shi daga cikin
renon annabi Ibrahima (as), ka kuma tsare shi –da rahamarka- daga azabar wutar
Jahim"([8]).
Kuma sunnah ne liman ya tsaya daidai da kan gawa namiji, mace
kuma daidai da tsakiyanta; saboda tabbatuwan hakan daga annabi (saw), a cikin
hadisin Anas xan Malik, da hadisin Jundub (ra) ([9]).
Amma zancen wassu maluma da ke cewa: Lallai sunnah ita ce
liman ya tsaya a daidai da qirjin gawa
namiji, wannan zance ne mai rauni, wanda bamu san wani dalili akansa ba.
Kuma mamaci a lokacin yi masa sallah zai kasance an fiskantar
da shi izuwa ga alqiblah, saboda faxin
annabi (saw) dangane da xakin ka'abah
cewa lallai ita:
«قِبْلَتكُمْ أَحْيَاءً
وَأَمْوَاتًا».
An so gawar mutum namiji ta kasance a kusa da liman in
gawawwakin suna da yawa, ita kuma mace ta gaba; bangaren alqiblah,
in kuma aqwai gawawwakin yara to sai a fara gabatar da gawan yaro
namiji akan ta mace, sa'annan sai gawar mace, sai kuma ta qaramar
yarinya mace. Sai kuma a sanya kan yaro qarami
ya zamto daidai da kan babban mutum, sai shi kuma tsakiyan mace ya zama yana
daidai da kan namiji, haka itama karamar yarinya mace; ana so ya zama kanta
yana daidai da kan babbar mace, shi kuma tsakiyanta yana daidai da kan namiji.
Su kuma masu sallah gabaxayansu sai
su zama dukkansu a ta bayan liman, Sai dai in mutum bai samu bayan liman ba to
a nan zai iya tsayawa ta dama da shi.
$/&/$
([7]) Muslim
ne ya rawaito shi, daga hadisin Ummu-salamah, a qissar rasuwar
Abu-salamah, Ya zo a cikinsa:
«اللهُمَّ
اغْفِرْ لِأَبِي سَلَمَةَ وَارْفَعْ دَرَجَتَهُ فِي الْمَهْدِيِّينَ، وَاخْلُفْهُ
فِي عَقِبِهِ فِي الْغَابِرِينَ، وَاغْفِرْ لَنَا وَلَهُ يَا رَبَّ الْعَالَمِينَ».
Ma'ana: "Ya Allah ka gafarta wa
Abu-salamah, ka kuma xaga
darajarsa, ka kawo masa mai mayewa a cikin zuriyarsa daga cikin waxanda su ka
saura, ka gafarta mana mu da shi ya Ubanijin talikai". (lamba: 920).
([8]) Bangarorin wannan an rawaito daga Abdullahi bn Abbas, da
Abu-hurairah, Abdurrazak ne kuma ya rawaito shi a cikin littafinsa (Almusannaf:
3/492, lamba: 6439), da Ibnu-Abiy shaibah (3/ 136, lamba: 3). Kuma abin da ya
fi shahara shi ne wannan addu'ar tana daga cikin maganar ALHASAN BN ALIYU,
kamar yadda su ka rawaito hakan a cikin "musannaf" xinsu guda
biyu (Abdurrazak: 3/529, lamba: 6588, da Ibnu-abiy shaibah, 3/136, lamba: 3).
No comments:
Post a Comment