ABUBUWA (20) DA SUKE
TAIMAKO
KAN
HAQURI BISA GA
CUTARWAR HALITTU
(عشرون أمرًا تعين في الصبر على أذى الخلق)
TANADAR
SHEIKHUL ISLAM AHMAD XAN ABDULHALIM XAN ABDUSSALAM IBNU-TAIMIYYAH
FASSARAR
Abubakar Hamza
بسم
الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah,
Salati da sallama su qara tabbata ga Manzon Allah,
da iyalansa da sahabbansa da duk wanda ya bi Allah,
Bayan haka:
Lalli rayuwa jarabawa ce, kuma Bawa a cikinta ka iya fiskantar dangin
cutarwa mabanbanta daga 'yan'uwansa halittu, Saidai akwai abubuwa masu yawa;
waxanda suke taimakon Mutum kan haquri bisa ga cutarwar 'yan'uwasa halittu. Sheikul
Islam Ahmad xan Abdulhlim Ibnu-Taimiyyah (wanda ya rasu, a shekarar hijira
ta 728) a cikin littafinsa mai muhimmanci QA'IDATUN FIY ASSABAR (قاعدة
في الصبر) wanda yake magana kan HAQURI (daga shafi na 94-103), ya ambaci
abubuwa guda ashirin (20) kamar haka; a inda yake cewa:
ويعينُ العبدَ على هذا الصبر عدةُ أشياء:
Ma'ana:
"Abubuwa dayawa za su taimaki bawa, akan wannan nau'i na
haquri".
Sai ya ambaci guda
ashirin (20) daga cikinsu, kamar haka, Yace:
أحدها:
أنْ يَشْهَدَ
أنَّ الله -سبحانه وتعالى- خالِقُ أفعالِ العِبَاد؛ حركاتِهِم
وسكناتِهم وإراداتِهم، فما شاءَ الله كان، وما لم يشَأْ لم يَكُن، فلا يتحرك في
العالم العلويّ والسفليّ ذَرَّةٌ إلا بإذنه، ومشيئتِه، والعباد آلة، فانظر إلى
الذي سلَّطهم عليك، ولا تنظُرْ إلى فِعلهم بَكَ، تستريحُ مِنَ الْهمِّ والغمِّ
والحزن.
NA XAYA:
Mutum (a zuciyarsa) ya ji cewa lallai Allah (سبحانه
وتعالى)
shine ke halitta aiyukan bayi (gabaxaya); motsawansu, da yin shirunsu, da
nufinsu; Kuma duk abinda Allah ya yi nufi shi yake kasancewa, Wanda kuma bai
nufa ba, shi kuma ba zai kasance ba. Akan haka; Daidai da kwayar zarra a cikin
duniyar sama ko qasa ba za ta motsa ba face da izininSa da nufinSa, Su kuma
bayi kamar kayan aiki ne. Don haka; Sai ka yi dubi zuwa ga wanda ya xora su
akanka, kada ka yi dubi zuwa ga aikin da suka aikata maka; Sai ka huta daga
baqin ciki da tashin hankali da vacin rai.
الثاني:
أنْ يشهد ذنوبه، وأن الله إنما سلّطهم عليه بذنبه، كما قال تعالى: {وَمَا أَصَابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِمَا
كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ}؛ فإذا شهد العبدُ أنَّ جميع ما يناله مِن المكروه فسببُه ذنوبُه، اشتغَلَ
بالتوبة والاستغفار مِن الذنوب التي سلَّطهم عليه، عن ذمِّهم ولَومِهم والوقيعة فيهم،
وإذا رأيت العبد يقَعُ في الناس إذا آذَوْه ولا يرجِع إلى نفسه باللوم والاستغفار:
فاعلم أنَّ مصيبتَه مصيبةٌ حقيقيةٌ، وإذا تاب واستغفر، وقال: هذا بذنوبي، صارت في
حقه نعمة.
قال علي بن أبي طالب -رضي الله
عنه - كلمة من جواهر الكلام: لا يَرْجُوَنّ عبدٌ إلا ربَّه، ولا يخافَنّ عبدٌ إلا ذنبه. وروي عنه وعن غيره: ما نزل بلاءٌ إلا بذنب، ولا رُفع إلا
بتوبةٍ.
NA BIYU:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da zunubansa, yana mai jin cewa
lallai Allah bai xora su akansa ba sai da zunubansa; kamar yadda Allah (تعالى) yace:
"Kuma babu abinda yake samunku na musiba face da sababin abinda
hannayenku suka aikata, kuma yana yafe dayawa" [Shurah: ???].
Akan haka; Idan bawa yaji cewa dukkan abinda ya same shi na
abin qi, sababinsa shine zunubinsa, to sai ya shagalta da yin tuba da neman
gafara; daga waxannan zunuban da suka zama sababin xora Mutane akansa, Ya bar kuma aibanta su da zarginsu, da cin
mutuncinsu. Kuma idan ka ga yana kutsawa cikin mutuncin mutane idan suka cutar
da shi, baya kuma komawa ga kansa da zargi, da neman gafara to ka sani lallai
musibarsa musiba ce ta haqiqa. Idan kuma ya tuba ya kuma nemi gafara, sannan
yace: Abinda ya same ni saboda zunubai na ne, to musibarsa ta zama ni'ima a haqqinsa.
Aliyu xan Abiy-xalib (رضي الله عنه) ya faxi wata magana
wacce take cikin maganganu masu tsada, cewa:
"Kada bawa yayi fatan wani idan ba Ubangijinsa ba, kuma kada ya
ji tsoron wani abu idan ba zunubinsa ba".
Kuma an ruwaito daga gare shi, da kuma waninsa cewa:
"Bala'i baya sauka sai da zunubi, kuma ba a xauke shi sai da tuba".
الثالث:
أنْ يشْهَدَ العبدُ حُسن الثواب الذي وعَدَه الله لِمَنْ عَفَى وصبَر، كما
قال تعالى: {وَجَزَاءُ
سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِثْلُهَا، فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ،
إِنَّهُ لا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ}. ولما كان الناس عند مقابلة الأذى ثلاثة أقسام: ظالم يأخذُ فوق حقه،
ومقتصد يأخذُ بقدر حقه، ومحسن يعفو ويترك حقه. ذكر الأقسام الثلاثة في هذه الآية؛
فأولها للمقتصدين، ووسطها للسابقين، وآخرها للظالمين.
ويشهد نداء المنادي يوم القيامة: ألا لِيَقُمْ مَن وَجَب أجرُه على الله، فلا يقوم إلا من عفى وأصلح.
وإذا شهد مع ذلك فَوت الأجر بالانتقام والاستيفاء سَهُل عليه الصبر والعفو.
NA UKU:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da kyakkyawan ladan da Allah yayi
alkawarinsa ga wanda yayi yafiya kuma yayi haquri; a cikin faxinsa:
"Kuma sakamakon mummuna mummuna ne kwatankwacinsa, Wanda kuma yayi
yafiya, yayi sulhu to ladansa yana kan Allah, Lallai shi (Allah) baya son
azzalumai"
[].
Kuma yayin da Mutane suka kasance a lokacin fiskantar cutarwar
da aka yi a gare su, suke karkasuwa kashi uku; Azzalumi; wanda da yake xaukan
fiye da haqqinsa, da Mai tsakaitawa; wanda shi kuma ke xaukan gwargwadon
haqqinsa, da Mai kyautatawa; wanda shi kuma yake yafewa sannan ya bar haqqinsa
= to sai Allah – a cikin wannan ayar- ya ambaci waxannan Kason guda uku, Sai
farkon ayar ya zama na Masu tsakaitawa, Tsakiyanta kuma na Waxanda suke yin
gaba cikin aiyukan alkhairi, Qarshenta kuma na Waxanda suke yin zalunci.
Kuma sai bawa (a cikin zuciyarsa) ya halarto kiran da mai kira
zai yi a ranar tashin kiyama, cewa:
Ku saurara!
Wanda ladansa
ya tabbata
akan Allah
ya taso,
Babu kuma
wanda zai taso a lokacin sai wanda yayi yafiya, yayi sulhu.
Kuma idan bawa (a cikin zuciyarsa) ya halarto da cewa: Wannan ladan,
zai kuvuce masa idan har ya xau fansa ko ya dawo da haqqinsa gabaxaya to yin
haquri da afuwa sai ka ga yayi sauqi a gare shi.
الرابع:
أنْ يَشْهَد
أنه إذا عفى وأحْسَن أوْرَثه ذلك مِن سلامة القلب لإخوانه، ونقائه من الغِشّ، والْغِلّ،
وطلب الانتقام، وإرادة الشَّرّ، وحصل له مِن حلاوة العفو ما يَزيدُ لَذَّتَه
ومنفعتَه عاجلا وآجلا على المنفعة الحاصلة له بالانتقام
أضعافًا مضاعفة. ويدخُل في قوله تعالى: {وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ}، فيصير محبوبًا لله، ويصير حالُه حالَ من أُخِذَ
منه دراهمٌ فَعُوِّضَ عنها ألوفًا من الدنانير، فحينئذ يَفْرَح بما مَنَّ الله
عليه أعظم فرحٍ ما يكون.
NA HUXU:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da cewa: Idan har yayi afuwa, ya
kuma kyautata sai hakan ya gadar masa da tsarkin zuciya ga 'yan'uwansa, da
kuvutar zuciya daga alqus, da qulle mutum, da neman xaukar fansa, da yin nufin
sharri, Sai kuma ya samu xanxanon zaqin da ake samu idan aka yi afuwa, wanda
zai qara masa jin daxi da amfani a duniya da lahira, fiye da amfanin da ya samu
lokacin xaukar fansa ninkin ba-ninkiya. Sai kuma ya shiga cikin faxin Allah (تعالى):
"Kuma Allah yana son masu kyautatawa" []; Sai ya zama abin
so ga Allah, daga nana sai halinsa ya zama kamar wanda aka xauka masa dirhami
guda xaya, Sai kuma aka yi masa canzi da dubban dinari, Kuma a lokacin ne, zai
yi farin ciki da abinda Allah yayi masa baiwa da shi, mafi girman farin ciki .
الخامس:
أنْ يَعْلَمَ
أنَّه ما انتَقَمَ أحَدٌ قطّ لنفسه إلا أوْرَثَه ذلك ذُلاً يجده في نفسه، فإذا عفى
أعَزَّه الله. وهذا مما أخبر به الصادق المصدوق حيث يقول: "ما زاد الله عبدًا بعفوٍ إلا عزًّا"، فالعِزّ الحاصل له بالعفو أحبُّ إليه وأنفعُ
له مِن العِزّ الحاصل له بالانتقام، فإنَّ هذا عِزٌّ في الظاهر وهو يُورث في
الباطن ذُلاً، والعفوُ ذُلٌّ في الباطن وهو يُورثُ العز باطنًا وظاهرًا.
NA BIYAR:
Mutum ya sani cewa: Lallai babu wanda zai xau fansa wa kansa
face Allah ya gadar masa da qasqancin da zai ji shi a cikin ransa, Idan kuma
yayi afuwa sai Allah ya xaukaka shi, Wannan kuma yana daga cikin abinda Manzon
Allah; Mai gaskiya abun gaskatawa ya bayyana a inda yake cewa:
"Allah bai yi qari ga wani bawa, kan afuwar da ya yi ba, face
xaukaka".
Wannan kuma saboda xaukakar da ake samu idan aka yi afuwa shi yafi sayuwa a
gare shi, kuma shine yafi amfani, fiye da xaukakar da ake samu idan aka xauki
fansa; saboda na qarshen izza ce ta zahiri, amma kuma tana gadar da qasqanci a
baxini, yayin da shi kuma yin afuwa qasqanci ne a baxini, saidai kuma ya kan
gadar da izza a baxini da zahiri.
السادس -
وهي من أعظم الفوائد -:
أن يشهد أن
الجزاء من جنس العمل، وأنه نفسه ظالمٌ مذنبٌ، وأنَّ مَن عفى عن الناس عفى الله
عنه، ومن غفر غفر الله له، فإذا شهد أن عفوه عنهم وصفحه وإحسانه مع إساءتهم إليه،
سبب لأن يجزيه الله كذلك من جنس عمله؛ فيعفو عنه ويصفح ويحسن إليه على ذنوبه،
ويسهل عليه عفوه وصبره ويكفي العاقل هذه الفائدة.
NA SHIDA –Wannan kuma yana cikin manya-manyan fa'idodi-:
Bawa (a zuciyarsa) ya halarto da cewa: Lallai sakayya ya kan
kasance daga jinsin aiki, Kuma lallai shima a karan-kansa mai zaluntar kansa
ne, mai zunubi, kuma lallai duk wanda yayi afuwa ga Mutane sai Allah yayi masa
afuwa, Wanda ya gafarta sai Allah yayi masa gafara, Don haka; idan bawa ya halarto
da cewa: Lallai yafiyar da zai yi musu, da rangwantawarsa, da kyautatawarsa, a
tare da munanawansu = sababi ne, na Allah ya sakanta masa daga jinsin aikinsa;
sai yayi afuwa a gare shi, ya rangwanta masa, ya kyautata masa, tare da
zunubansa, A haka; Sai yin afuwa da haquri yayi masa sauqi. Wannan fa'idar kuma
ta ishi mai hankali!
السابع:
أنْ يعلَم أنّه إذا اشتغَلَتْ نفسُه بالانتقام وطلَبِ المقابلة ضاع عليه زمانُه، وتفرَّق عليه قلبُه، وفاتَه مِن مصالحه ما لا يمكن استدراكُه،
ولعل هذا يكون أعظم عليه من المصيبة التي نالَتْه مِن جهتهم، فإذا عفى وصفح فرغ
قلبُه وجسمُه لمصالحه التي هي أهمُّ عنده مِن الانتقام.
NA BAKWAI:
Bawa ya san cewa: Lallai shi idan har ransa ta shagalta da
neman xaukar fansa, ko sakayya to sai lokacinsa ya tozarta, kuma zuciyarsa ta rarraba,
sannan maslahohinsa da ba zai iya riskarsu ba, sai su wuce masa, kuma la'alla
wannan yafi girman muni a wurinsa fiye da musibar da ta shafe shi daga
vangarensu. Amma idan kuma yayi afuwa, ya rangwanta to sai zuciyarsa da jikinsa
su tafi zuwa ga maslahohinsa waxanda sun fi muhimmanci a gare shi fiye da
xaukar fansa.
الثامن:
أنَّ انتقامَه واستيفاءَه وانتصارَه لنفسه وانتقامَه لها، فإنَّ رسولَ الله
صلى الله عليه وسلم ما انتقم لنفسه قط، فإذا كان هذا خيرُ خلق الله وأكرمُهم على
الله لم يكن ينتقم لنفسه مع أنَّ أذاه أذى لله، ويتعلق به حقوق الدين، ونفسُه أشرفُ
الأنفس، وأزكاها، وأبرُّها وأبعدُها من كل خُلقٍ مذمومٍ، وأحقُها بكلّ خُلقٍ جميل،
ومع هذا فلم يكن ينتقم لها. فكيف ينتقم أحدُنا لنفسه التي هو أعلم بها وبما فيها
من العيوب والشرور، بل الرجل العارف لا تساوي نفسُه عنده أن ينتقم لها، ولا قدر
لها عنده يوجبُ عليه انتصارُه لها.
NA TAKWAS:
Bawa ya ji cewa, Lallai xaukar fansansa da qoqarin maido da
haqqoqinsa da neman ya ci nasara yana yi ne wa Ransa, kuma xaukar fansan shima
wa ita yake yi, alhalin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) bai tava xaukar
fansa ga kansa ba, daxai, To, idan wannan shine xabi'ar mafi alheri daga cikin
halittun Allah, wanda kuma ya fi su, matsayi a wurin Allah: ya zama baya xaukar
fansa ga kansa, tare da cewa lallai cutar da shi, cutar da Allah ne, kuma
haqqoqi na addini suna rataya akan haka, kuma ransa itace tafi dukkan rayuka
xaukaka, kuma ita ta fi su tsarki, da biyayya, kuma itace tafi nisantar kowace
xabi'a abar zargi, kuma tafi cancantar kowani hali mai kyau, amma tare da haka;
Bai kasance yana xaukar mata fansa ba! To, ta yaya xayanmu zai xauki fansa ga
kansa, wanda shine yafi kowa sanin abinda take xauke da su na aibuka da
sharrori.
Kai, lallai shi Mutum masani ransa a wurinsa bata kai ya xauka
mata fansa ba, kuma bata da matsayi a wirinsa da zai wajabta masa neman kwato
mata haqqinta.
التاسع:
إنْ أوذي على ما فعله لله أو على ما أمَرَه به مِن طاعته ونهى عنه مِن
معصيته وجب عليه الصبر ولم يكن له الانتقام، فإنه قد أوذي في الله، فأجرُه على
الله، ولهذا لما كان المجاهدون في سبيل الله ذهبت دماؤهم وأموالهم في الله لم تكن مضمونة، فإنّ الله -تعالى- اشترى منهم أنفسَهم وأموالَهم، فالثَّمَنُ على الله لا على
الخلق، فمَن طلب الثمن منهم لم يكن له على الله ثمَنٌ، فإنه من كان في الله تلَفُه
كان على الله خلَفُه.
وإن كان قد أوذي على معصية، فليرجع باللوم على نفسه، ويكون في لومه لها شغل
عن لومه لمن آذاه.
وإن كان قد أوذي على حظٍّ، فليُوطِّن نفسَه على الصبر، فإن نيل الحظوظ دونه
أَمْرٌ أَمَرُّ من الصبر، فمن لم يصبر على حر الهواجر، والأمطار، والثلوج، ومشقة
الأسفار، ولصوص الطريق، وإلا فلا حاجة له في المتاجر، وهذا أمر معلوم عند الناس أن
من صدق في طلب شيء من الأشياء بذل من الصبر في تحصيله بقدر صدقه في طلبه.
NA TARA:
Idan har ya zama an cutar da shi ne akan wani aikin da ya
aikata shi don Allah, ko akan wani abinda ya umurce shin a xa'arSa, ko wanda ya
hana shin a savonSa to wajibi ne akansa ya yi haquri, kuma haramun ne akansa ya
xauki fansa; saboda an cutar da shi ne a wannan yanayin akan Allah, kuma
ladansa yana kan Allah; Wannan kuma shi ya sanya masu jihadi fiysabilil lahi,
idan rayukansu da dukiyarsu suka tafi don Allah, ba a biyan fansansu, wannan
kuma saboda Allah (تعالى) ya sayi rayukansu da dukiyoyinsu daga
gare su; don haka; ladan yana kan Allah ne ba a kan halittu ba, kuma duk wani
daga cikinsu da ya nemi kuxinsa to bashi da wani kuxi akan Allah; saboda DUK
WANDA LALACEWAN ABUNSA YA ZAMA A HANYAR ALLAH NE, TO, MAYAR MASA DA GURBIN
WANNAN ABUN YA KAN KASANCE AKAN ALLAH NE.
In kuma ya zama an cutar da shi ne akan wani savo; to sai ya
dawo da zargi ko aibantawa ga kansa, sai kuma zarginsa ga kansa ya shagaltar da
shi ga barin zargin wanda ya cutar da shi.
In kuma an cutar da shi ne, akan wani rabo (na duniya) to sai
ya horar da kansa akan yin haquri; wannan kuma saboda samun rabo gabaninsa
akwai lamarin da yafi haquri daci, kuma duk wanda bai yi haquri akan zafin
rana, ko ruwan sama, ko qanqara, da wahalhalun tafiye-tafiye, ko varayin kan
hanya ba, to, lallai bashi da buqatar yin kasuwanci. Wannan kuma sanannen abu
ne a wurin Mutane; cewa: Duk wanda yayi gaskiya wajen neman wani abu, to ya kan
yi haquri cikin nemansa gwargwadon gaskiyarsa cikin nemansa.
العاشر:
أن يشهد معية الله معه إذا صبر، ومحبة الله له ورضاه، ومن كان الله معه دفع
عنه من أنواع الأذى والمضرات ما لا يدفع عنه أحد من خلقه، قال الله تعالى: {وَاصْبِرُوا إِنَّ اللَّهَ مَعَ
الصَّابِرِينَ}، وقال: {وَاللَّهُ يُحِبُّ الصَّابِرِينَ}.
NA GOMA:
Bawa ya ji cewa, Lallai Allah yana tare da shi idan yayi
haquri, kuma zai samu soyayyar Allah da yardarSa, Duk kuma wanda Allah yake
tare da shi to zai tunkuxe masa nau'ukan cutuka, da dukkan abubuwan da zasu
cutar da shi, irin abinda wani daga cikin halittunSa ba zai iya tunkuxe masa
ba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku yi haquri; lallai Allah yana tare da masu haquri" []. Kuma yace:
"Kuma Allah yana son masu haquri" [].
الحادي عشر:
أنْ يشهد أنَّ الصبر نصفُ الإيمان، فلا يَبذُل مِن إيمانه جُزءًا في نُصرة
نفسِه، فإنْ صبَر فقد أحرز إيمانَه وصانه من النقص، والله -تعالى- يدفَعُ عن الذين آمنوا.
NA GOMA SHA XAYA:
Bawa (a cikin zuciyarsa) ya ji cewa, Lallai haquri rabin imani ne,
Don haka; ba zai bayar da sashin imaninsa wajen taimakon kansa ba, Idan kuma har
yayi haquri to ya kiyaye imaninsa daga wata naqasa. Kuma lallai Allah -تعالى- yana bada kariya ga
waxanda suka yi Imani.
الثاني عشر:
أنْ يشهَدَ أنَّ صَبْرَه حُكم منه على نفسه، وقَهْرٍ لها، وغَلَبَةٍ لها،
فمتى كانت النفسُ مقهورةً معه مغلوبةً، لم تطمع في استرقاقه وأَسْرِه، وإلقائه في
المهالك. ومتى كان مطيعًا لها، سامعًا منها، مقهورًا معها: لم تزل به حتى تُهْلِكه،
أو تتداركه رحمةٌ مِن ربّه. فلو لم يكن في الصبر إلا قهره لنفسه ولشيطانه، فحينئذ
يظهر سلطان القلب وتثبت جنوده، فيفرح ويقوى ويطرد العدو عنه.
NA GOMA SH BIYU:
A (cikin zuciyarsa) bawa ya ji cewa, Lallai haqurin da zai yi,
cin nasararsa ne akan Ransa, da rinjayarta, da cin galaba akanta, kuma duk
lokacin da Rai ta zama an rinjaye ta, an kuma yi galaba akanta, to, baza ta yi
kwaxayin mayar da shi bawan da zata riqa bautar da shi ba, ko kuma jefa shi
cikin abubuwan da za su halakar da shi. Yayin da kuma duk lokacin da Mutum ya
zama mai yin xa'a ga Ransa, mai jin maganarta, wanda ta rinjaye shi, to ba za
ta kyale shi ba har sai ta halaka shi, idan ba wata rahama ce ta fiskance shi
daga wajen Ubangiji ba.
Kuma da haquri bashi da wata fa'ida sai yadda Mutum zai
lankwasa Ransa, da Shexaninsa (to ya ishe shi). Kuma a lokacin ne qarfin zuciya
zai yi rinjaye, kuma rundunoninsa za su tabbata, sai ya yi farin ciki, yayi
qarfi, har ya iya korar maqiyansa daga gare shi.
الثالث
عشر:
أنْ يعلم
أنَّه إنْ صبَر فالله ناصرُه ولا بد، فإنَّ الله وكيلُ مَن صبَر وأحال ظالمَه
عليه، ومَن انتصر بنفسه لنفسه وكَّله الله إلى نفسِه، فكان هو الناصر لها، فأين من
ناصرُه الله خيرُ الناصرين، إلى مَن ناصرُه نفسُه أعجزُ الناصرين وأضعفه.
NA GOMA SHA UKU:
Bawa ya sani cewa, Lallai idan yayi haquri to Allah zai taimake
shi, babu makawa, saboda Allah ya kan wakilci wanda yayi haquri; sa'annan ya
mayar da lamarin wanda ya zlunce shi zuwa ga Allah, Shi kuma wanda ya nemi ya
taimakawa kansa da karan-kansa sai Allah ya jivintar da shi zuwa ga kansa, Sai
ya kasance shine mai taimakawa Ransa, Shin kuma zaka haxa wanda mai taimakonsa
shine (Allah) mafi alkhairin masu taimako, da wanda mai taimakonsa shine Ransa,
gajiyeyyen mai tamako, kuma mafi rauni.
الرابع
عشر:
أنَّ صبْرَه
على من آذاه واحتماله له يوجبُ رجوعَ خصمه عن ظلمه وندامته واعتذاره، ولوْم الناس
له: فيعود بعد إيذائه له مستحييا منه، نادمًا على ما فعله، بل يصير مواليًا له،
وهذا معنى قوله: {ادْفَعْ
بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ فَإِذَا الَّذِي بَيْنَكَ وَبَيْنَهُ عَدَاوَةٌ كَأَنَّهُ
وَلِيٌّ حَمِيمٌ وَمَا يُلَقَّاهَا إِلاَّ الَّذِينَ صَبَرُوا وَمَا يُلَقَّاهَا
إِلاَّ ذُو حَظٍّ عَظِيمٍ}.
NA GOMA SHA HUXU:
Lallai haqurinsa kan cutarwansa, da jurewansa yana hukunta
denawar abokin husumarsa daga zaluntarsa, d yin nadamarsa, da bada uzuri, da
aibantawa dga wajen Mutane, a gare shi; Sai abokin husumarsa ya dawo –bayan cutarwar
da yayi a gare shi- yana jin kunyarsa, yana nadam akan abinda ya aikata masa, Kai!
Sai ya komo ya zama masoyi a gare shi, Wannan kuma shine ma'anar faxin Allah:
"Ka tunkuxe da abinda yafi kyau, Sai wanda a tsakaninka da tsakaninsa
akwai adawa ya zama kamar wani masoyi makusanci * Kuma
babu wanda ake bashi su sai waxanda suka yi haquri, kuma babu wanda ake bashi
su face ma'abocin wani rabo mai girma" [Fussilat: 34-35].
الخامس عشر:
ربما كان انتقامه ومقابلته سببًا لزيادة شر خصمه وقوة نفسه وفكرته في أنواع
الأذى التي يوصلها إليه كما هو المشاهد، فإذا صبر وعفى أمن من هذا الضرر. والعاقل
لا يختار أعظم الضررين بدفع أدناهما. وكم قد
جَلَب الانتقامُ والمقابلةُ مِن شرٍّ عجَزَ صاحبُه عن دفعه؟ وكم قد ذهبت به نفوس
ورياسات وأموال وممالك؟ لو عفى المظلوم لبقيت عليه.
NA GOMA SHA BIYAR:
Kuma zai yiwu xaukar fansansa da zai yi da qoqarin maida
martaninsa ya zama sababin qaruwar sharrin abokin husumarsa, da qarin qarfin
ransa, da sake tunanin yadda zai isar da dangogin cutarwa mabanbanta zuwa gare shi, kamar yadda ake
ganin hakan a rayuwr mutane. Amma idn ya yi haquri, ya yafe to sai ya aminta
daga wannan cutarwar. Kuma lallai mai hankali ba zai zavi mafi girma daga cikin
nau'ukan cutarwa guda biyu; ta hanyar tunkuxe wacce tafi qaranci ba. Kuma sau
nawa neman xaukar fansa da bqoqarin ramuko ya jawo sharrin da ma'abocinsa ya
gagara tunkuxe shi. Kuma sau nawa da hakan rayuka da mulki da dukiyoyi da
masarautu suka tafi, Wanda da mutumin da aka zalunta ya yi yafiya, da
abubuwansa sun wanzu tare da shi?
السادس عشر:
أن من اعتاد الانتقام ولم يصبر، لا بد أن يقع في الظلم، فإن النفس لا تقتصر
على قدر العدل الواجب لها، لا علما، ولا إرادة، وربما عجزت عن الاقتصار على قدر الحق،
فإن الغضب يخرج بصاحبه إلى حَدٍّ لا يعقل ما يقول وما يفعل. فبين هو مظلوم ينتظر
النصر والعز، إذ انقلب ظالماً ينتظر المقت والعقوبة.
NA GOMA SHA SHIDA:
Lallai wanda ya saba xaukar fansa; baya yin haquri to babu
makawa dole zai auka cikin zalunci, saboda kasancewar Rai ba za ta taqaita ga
gwargwado na adalci da ta cancance shi ba; ta fiskar saninsa, ko yin nufinsa,
kuma wani lokacin zata gaza taqaitawa akan gwargwadon gaskiyan ne, saboda fushi
yak an fitar da ma'abocinsa zuwa ga yanayin da baya sanin abinda yake faxa ko
yake aikatawa ba. Sai mutumin da ya samu kansa a matsayin wanda aka zalunta;
mai neman taimako da izza daga Allah, sai katsam ya wayi-gari ya juye ya zama
shine mai zalunci; wanda ke jiran fushin Allah da uqubarsa.
السابع عشر:
أن هذه المظلمة التي قد ظُلمها هي سبب إما لتكفير سيئة، أو رفع درجة، فإذا
انتقم ولم يصبر لم تكن مكفرة لسيئته ولا رافعة لدرجته.
NA GOMA SHA BAKWAI:
Wannan zaluncin da aka yi masa, ko dai ya zama sababi ne
kankare masa zunubi, ko xaukaka darajara, Idan kuma har ya xauki fansa, bai yi
haquri ba, to lallai ba za ta kasance mai kankare masa zunubi ba, haka ba za ta
xaga darajarsa ba.
الثامن عشر:
أنَّ عفوَه وصبْرَه من أكبر الجُند له على خصمه، فإنَّ مَن صبر وعفا كان
صبرُه وعفوُه موجبًا لذُلِّ عدوِّه، وخوفه وخشيتِه منه ومِن الناس، فإنّ الناس لا
يسكتون عن خصْمِه وإنْ سكَتَ هو، فإذا انتقم زال ذلك كله، ولهذا تجد كثيرًا من
الناس إذا شتَمَ غيرَه أو آذاه يُحبُّ أنْ يستوفيَ منه، فإذا قابله استراح وألقى عنه ثقلاً كان يجده.
NA GOMA SHA TAKWAS:
Lallai yafiyarsa da yin haqurinsa suna daga mafi girmar
rundunar yaqar waxanda yake husuma da su, saboda Mutumin da yayi haquri yayi
afuwa to haqurinsa da afuwarsa sukan hukunta qasqancin maqiyansa, da kuma jin
tsoronsa da tsoron mutane, wannan kuma saboda su mutane ba za su yi shiru akan
abokin husumar tasa ba; koda kuwa shi ya yi shiru. Idan kuma ya xauki fansa to
wannan gabaxayansa ya gushe. Kuma don haka ne; ka ke samu dayawa daga cikin
mutane idan har ya zagi waninsa, ko ya cutar da shi = ya ke son wanda ya
zaluntar ya yi qoqarin dawo da haqqinsa daga gare shi, kuma idan har ya raman
to sai ya ji ya huta, kuma ya sauke wani nauyin da ya ke ji akansa.
التاسع عشر:
أنه إذا عفى عن خصمه، استشعرت نفس خصمه أنه فوقه، وأنه قد ربح عليه، فلا
يزال يرى نفسه دونه، وكفى بهذا فضلاً وشرفًا للعفو.
NA GOMA SHA TARA:
Lallai idan yayi afuwa ga wanda yake husuma da shi, Sai Ran wanda
suke husumar da shi ya ji cewa, lallai mai yin afuwar yana sama da shi, kuma ya
ci riba akansa, Kuma ba zai gushe yana ganin kansa a qasa da shi ba. Kuma
wannan ya ishi afuwa falala da xaukaka.
العشرون:
أنه إذا عفا وصفح كانت هذه حسنة، فتولد له حسنة أخرى، وتلك الأخرى تولد
أخرى، وهلم جرا، فلا تزال حسناته في مزيد، فإن من ثواب الحسنة الحسنة، كما أن من
عقاب السيئة السيئة بعدها، وربما كان هذا سببًا لنجاته وسعادته الأبدية، فإذا
انتقم وانتصر زال ذلك.
NA ASHIRIN:
Lallai idan yayi afuwa, ya kuma yi rangwame sai hakan ya
kasance lada a gare shi, sai ladan ta haifa masa wata ladan ta daban, sai itama
waccar ta haifa masa wata, da sauransu; sai ya zama ladansa ba za su gushe ba
suna ta qaruwa; saboda yana cikin ladan aikata aiki mai kyau, sake aikata wani
aikin mai kyau, kamar yadda yana cikin uqubar aikata aiki mummuna, bawa ya sake
aikata wata mummunan bayanta. kuma tayuwu hakan ya zama sababin samun tsiransa
da rabutarsa ta har abada. Amma idan ya xauki fansan kuma, ya nemi samar wa
kansa nasara sai hakan ya gushe.
وصلى الله على سيدنا محمد وآله وصحبه وسلم.
Kammalawa/ 19/ Safar/ 1437h,
Daidai da 01/ Disamba/ 2015m.
A garin Madinar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم).
No comments:
Post a Comment