بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على عبد الله ورسوله نبينا
محمد وآله وصحبه، وبعد:
GABATAR DA LITTAFIN
Yabo da
godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin
halittu.
Tsira da
aminci su qara tabbata ga wanda babu wani annabi a
bayansa; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa bakixaya.
Bayan haka; Lallai abubuwan da aka jingina su
ga ma'aikin Allah annabi Muhammadu s a w na hadisai ingantattu sune suka qunshi addini na gangariya –tare da littafin Allah; alqur'ani-; kamar yadda kuma sune wahayi na kai tsaye wanda Allah
ta'alah ya yi wa Manzonsa don su zama bayani ga abinda subhanahu ya sassaukar a
gare shi na littafinsa; alqur'ani. Don haka; Duk wanda ya yi riqo da hadisin Annabi tare da alqur'ani to haqiqa ya yi riqo da igiyar Allah mai qarfi wacce bata tsinkewa, haka kuma wanda ya kama alqur'ani kana ya sake hadisi, ko ya sake dukkan biyun (alqur'ani da hadisi) to irin wannan ya vata vata mai nisa, kuma ya yi asara mabayyaniya.
Shi kuma littafin alqur'ani da xaukacin hadisan Manzo (s a w) ba su iso wa ga mutanen da suka zo daga baya ba; Sai
ta hanyar wassu zarata; waxanda Allah ta'alah ya halicce su don su sadaukar da rayuwarsu baki xayanta wajen koyan wannan addinin daga bakin Manzon Allah (s a
w), da kuma kare shi, tare da tallata shi ga sauran al'ummar duniya; Waxannan mutanen kuma su ne iyalen Annabi (s a w) da su ka rayu
da shi da kuma sahabbansa maxaukaka. Lallai waxannan jarumai, mazajen
fama, alarammomi mahaddata addinin Allah sun bauta wa Allah kamar yadda Manzonsa
ya koyar da su, kana kuma sun so wannan Manzon da abinda ya zo da shi fiye da
sonsu ga iyayensu, 'ya'yansu da sauran mutane baki-xaya, kamar yadda su ka bada kariya ga Ma'aiki da kuma addinin
Allah a cikin rayuwar manzo da bayan rasuwarsa, Musamman kuma mutane guda huxu ko biyar da su ka zama khalifofinsa, bayan komawarsa
zuwa ga mahaliccinsa; Allah ta'alah.
Kuma kasancewar sanin rayuwar sahabban Manzon
Allah; musamman manya-manyansu, da fahimtar yadda su ka bada gudumawa ga wannan
addini= ya kan qara fahimtar da Mutum
matsayin waxannan Mutanen a
cikin addini, da kuma wurin Manzo, wanda kuma hakan ya kan haifar da qarin sonsu a cikin zukata.
Kuma kasancewar shi tarihi akwai ingantacce,
akwai kuma qirqirarrun
qissoshi
da labarai a cikinsa.
Sa'annan kasancewar an samu wassu da su ka vace daga
hanyar Allah miqaqqiya dangane
da sahabban Annabi; xaukacinsu, ko kuma
sashinsu; musamman kuma manyansu Abubakar, Umar da Usman –r a- har ma WANI
WANDA AKE CE MASA Aliyu xan Abdil-aliy al-amiliy alkarkiy wallafa
littafi ya yi sukutum mai suna "nafahaatu al-lahuti fi la'ani aljibti wax-xaguti (نفحات اللاهوت في لعن الجبت والطاغوت)" don tsinuwa ga wanda ake musu laqabi da
''aljibtu wax-xagutu'' a
addinin shi'a, (wato: Abubakar as-siddiq, da Umar al-khaxxab –r a-).
Shi wannan xan shi'an ya
kawo a cikin littafinsa dana ambata "p3/a'', Haka kuma Wanda ake kira ni'imatul-lahi
Al-jaza'iriy a cikin littafinsa ''al'anwaar annu'umaniyya, 1/ p53'' = Sun
kawo maganar da ta ke tafe don nuna wa mabiyansu cikin aqida ('yan
shi'a) cewa Abubakar kafiri ne:
«كان
يصلي خلف رسول الله عليه وآله والصنم معلَّقٌ في عُنُقه يسجد له».
Ma'ana:
(Wai Abubakar ya kasance yana yin salla a bayan Manzon Allah -s a w- alhalin
gunki na rataye a wuyansa; yana yin sujjada
a gare shi).
Shi kuma
Malaminsu mai suna Almajlisiy; Muhammad Baqir a cikin
littafinsa ''jala'u al'uyun, p 45'' kafirta Umar xan Al-khaxxab yayi, a inda yake cewa:
«لا مجال لعاقلٍ أنْ يشكّ في كفر عُمر، فلعنة
الله ورسوله عليه، وعلى كلّ مَن اعتبره مسلمًا، وعلى كلّ مَن يكفّ عن لعنه».
Ma'ana:
(Wai: Mutum mai hankali ba shi da damar ya yi shakka kan kafircin Umar, tsinuwar
Allah da Manzonsa su tabbata akansa –wai akan umar-, da kuma akan duk wanda ya xauki Umar a
matsayin musulmi, haka ta sake tabbata
ga wanda ya kame bakinsa; daga la'antar Umar).
–haka ya faxa!
Haka Shi kuma ''alkarkiy''
da ya gabata a cikin littafinsa da ambatonsa ya gabata (p57/ a) ya sake kafirta
Usman xan Affan –r a- inda ya ce:
«إنّ مَن لم يجد في قلبه عداوة لعثمان، ولم يستحلَّ عرضه، ولم
يعتقد كفره: فهو عدو لله ورسوله، كافرٌ بما أنزل الله».
Ma'ana:
(Lallai wanda bai ji wani irin adawa a zuciyarsa akan Usman ba, bai kuma
halatta cin mutuncinsa ba, Bai kuma qudurta cewa shi kafiri ba ne a cikin
zuciyarsa: To, shi maqiyin Allah da
manzonsa ne, kuma ya kafirce wa abin da Allah ya saukar). –haka shima wannan ya faxa!
To saboda waxancan dalilan naga wajabcin karantar da
al'ummar musulmai tarihin halifofin Annabi -s a w- guda huxu ko biyar;
wato: Abubakar, Umar, Usman, Aliyu, da Alhasan xan Aliyu –r a-, ta fiskar KHILAFANCINSU
DA FALALARSU, Na kuma sanya taken rubutun: HADISAI HAMSIN KAN KHILAFANCIN
HALIFOFIN MANZON ALLAH -S A W- DA FALALOLINSU. Kamar kuma yadda na sharxanta wa kaina;
saboda abin da na ambata na matsalar rashin
ingancin wassu tarihohin; cewa ba zan ambaci ''hadisi ko asari'' ba Sai
wanda maluma su ka ce ingantacce ne; ma'ana: wanda ya wajaba a qudurce shi ko
ayi aiki da shi.
Fatana; Itace Allah ya sanya albarka
cikin wannan aiki; ta yadda za a rike shi a matsayin ''manhajar karatun tarihin
khalifofin Manzon Allah'' a makarantu, da majalis na karance-karance da su ke
masallatai ko zauruka. Ya kuma amfanar da musulmai da zasu bibiyi karatunsa ta
kafofi mabanbanta.
Rufewa: Kafin na
qarqare muqaddimata Ya kamata
a san cewa shi asalin wannan rubutu ya kasance ne da harshen larabci; ta fiskar
kulla ''babi'', sa'annan na Ambato ''hadisi ko asar'' a qarqashin wannan
babi, sai kuma na rufe da yin ta'aliqi
da zai fito da manufar ambaton wancan ''hadisin'' a wancan ''babin'', Ganin
muhimmancin a samu wannan rubutun da harshen hausa ya sanya yanzu nayi azamar
fassara shi izuwa ga ''harshen Hausa''.
Ya Allah ina roqonka da
sifofinka maxaukaka da ka qara xaukaka darajar
sahabban Manzonka; Annabi Muhammadu –صلى
الله عليه وسلم-; musamman
kuma manya-manyansu; Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, ya kuma yarda da su, ya
yardar da su ga xaukacin musulmai,
Sannan Muna roqon Allah da
ya azurta mu da sonsu, ya kuma haxa
mu da su da kuma Manzonmu Muhammadu -s a w- a cikin aljannar Firdausi
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا
محمد وآله وصحبه أجمعين.
Marubuci: Abubakar Hamza Zakaria
4 / Shawwal /1434h daidai 11/08/2013 miladiyya.
No comments:
Post a Comment