HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 08/SAFAR/1437h
Daidai da 20 /11/2015m
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI HUSAIN XAN ABDUL'AZIZ ALUSH SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta
tabbata ga Allah; wanda ya sanya yin biyayya a gare shi ya zama sababi na samun
alkhairori, da kuma saukan albarkoki, Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah; Ubangijin qasa da sammai, Kuma ina shaidawa lallai annabinmu
Muhammadu bawanSa ne kuma Manzonsa; Mafificin halittu, Ya Allah ka yi salati da
sallama da albarka a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa, har zuwa ranar
mutuwa.
Bayan
haka;
Ya ku Musulmai!
Ina yin
wasici a gare ku da ni kaina da kiyaye dokokin Allah mabuwayi da xaukaka,
saboda da taqawar Allah ne ni'imomi suke sauka, kuma ake tunkuxe bala'oi.
'Yan'uwan
Musulunci!
Halin da
Musulmai suka samu kansu a wurare dayawa yana tada hankali kuma yana vata rai,
musamman tare da bayyanar fitintinu masu makantarwa, da nau'ukan jarabawa mabanbanta,
waxanda suka janyo wa Musulmai halaka da rushe-rushe da nau'ukan varna; a cikin
ADDINI da RAYUKA da MUTUNCI da DUKIYOYI da GIDADDAJI, Bamu da damar juya hakan,
kuma bamu da qarfi idan ba mun koma zuwa ga Allah ba (Wannan kuma shine
ma'anar: لا حول ولا قوة إلا بالله).
Kuma
lallai babban sababi, dangane da abinda ya sauka wa Musulmai na tashin hankali
da fitintinu da kuma jarrabawa da musibobi shine: Nisantar Addinin Allah, da
hanyar Annabi, a vangarorin rayuwa mabanbanta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk abinda ya same ku na musiba to
sakamakon abinda hannayenku suka aikata ne, kuma (Allah) yana yafe abu dayawa", [Shura: 30].
Kuma yana cewa:
"Varna ta bayyana a sarari da teku, saboda
abinda hannayen Mutane suka aikata, don ya xanxana musu sashin abinda suka
aikata, la'alla ko za su koma", [Rum: 41]. Kuma Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Kuma matuqar shugabanninsu basu yi
aiki da abinda Allah ya saukar a cikin littafinsa ba, face Allah ya sanya
yaqinsu a tsakaninsu". Kuma Aliyu (رضي الله
عنه) yace:
"Bala'i baya sauka sai in anyi zunubi, Kuma ba a xauke bala'i sai idan an
tuba".
Don
haka; Aikata munanan aiyuka, da sassavawa Ubangijin qasa da sammai = Suna gusar
da ni'imomin da ake rayuwa a cikinsu, kuma suna yanke ni'imomi masu zuwa.
Ibnul-Qayyim yana cewa: Bayani akan
wannan a cikin Alqur'ani ya zo a fiye da wuri 1000 .
Kuma haqiqa fitintinun da suke sabbaba zubar
da jini da kisa basu yi ta kai-komo, suka yawaita ga musulmai ba, Sai sakamakon
yadda suka bayyanar da savawa karantarwar wahayin Alqur'ani da Hadisi. Ya zo a cikin littafin (Musnad na Imam Ahmad)
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Idan savo suka bayyana a cikin
al'ummata, to sai Allah ya game su da uquba daga wurinsa".
To
idan wannan lamari na gaskiya; wanda ya vuya ga zukata dayawa; musamman waxanda
suka yi nisa daga karantarwar Alqur'ani da Sunnah = ya tabbata a zukata, To mu
sani! Lallai akwai wassu GINSHIQAI MASU GIRMA, waxanda idan Musulmai
suka fahimce su, suka yi aiki da su,
sannan suka yi kwaxayin ganin tabbatuwansu, To lallai zasu kuvuta daga
na'ukan sharri mabanbanta, da kuma kaiton da fitintinu da jarrabawa suke
jawowa;
GINSHIQI
NA FARKO: Tuba ta gaskiya zuwa ga Allah; ta hanyar komawa zuwa ga hanyar
Allah, da yin aiki da shari'arSa, da bin umurninSa da kuma umurnin ManzonSa (صلى الله عليه وسلم);
Wannan
kuma, kasancewar da aikata tuba ne kawai, gyara cikin qasa ke tabbatuwa, a kuma
yi aikin bunqasa rayuwa, sannan a tunkuxe nau'ukan sharri da fitintinu da
musibu da bala'oi ga Mutane, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya, Ya ku
Muminai, da fatan zaku samu rabo", [Nur: 31].
Kuma Allah yana faxa dangane da AnnabinSa
Hudu:
"Ya ku Mutanena! Ku nemi gafarar
Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi, Zai saki ruwan sama akanku mamako,
kuma ya yi qarin qarfi a gare ku akan qarfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu
laifi" [Hudu: 51].
Saboda
haka; Alkhairi da dukkan nau'ukansa yana
nan ne akan tuba, Kamar yadda shima kawo
gyara da dukkan shakalinsa yake rataya akanta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Idan suka tuba zai zama alkhairi a gare su,
Idan kuma suka juya baya, Allah zai azabta su azama mai raxaxi, a duniya da
lahira, Kuma a cikin qasa basu da wani masoyi ko wani mataimaki" [Tauba:
74 ].
Kuma
tuba zuwa ga Allah; ta hanyar gyara abinda ya lalace, na barin wajibai, da
aikata abubuwan haramun sababi ne na xauke bala'i, da tunkuxe musiba, Allah (تعالى) yana cewa:
"Allah bai kasance zai azabta su, alhalin
kana cikinsu ba, kuma Allah bai kasance mai azabta su ba, alhalin suna neman
gafara" [Anfal: 33].
Hasalima tuba ta kan zama sababin saukar
alkhairori mabanbanta, da samuwar ababen farin ciki masu yawa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan
ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku daxi jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani
lokaci ambatacce, kuma ya bai wa dukkan ma'abucin girma girmarsa"
[Hudu: 3].
Kuma Allah yana faxa ta harshen Annabi Nuhu:
"Sai nace: Ku nemi gafarar Ubangijinku;
lallai shi ya kasance mai yawar gafara
* Zai saki ruwan sama akanku
mamako *
Kuma ya qarfafe ku da dukiya da 'ya'ya, kuma ya sanya muku lanbuna, kuma
ya sanya muku qoramai" [Nuhu: 10-12].
GINSHIQI
NA BIYU: Yawaita aikata aiyukan xa'a, da sauran ababen qara kusantar Allah;
Saboda
da aikata haka, ake tunkuxe bala'oi, ake kuma jawo ni'imomi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda ya kiyaye dokokin Allah zai
sanya masa mafita * Kuma ya azurta shi ta inda baya tsammani,
Kuma duk wanda ya dogara ga Allah, to shi, ya isar masa" [Xalaq:
2-3 ].
Ibnul-qayyim
yana cewa:
"Shi mai kyautatawa mai yin sadaka: Yana
amfani ne da runduna da mayaqan da suke yaqi a madadinsa, alhalin yana cikin
barcinsa akan shumfuxinsa. Shi kuma wanda bashi da wata runduna ko mayaqa gashi
kuma yana da maqiya, to lallai maqiyan nasa sun yi kusa su ci nasara akansa,
koda kuwa lokacin hakan ya yi jinkiri. Allah ne mai taimako".
Kuma ma'abuta
Imani masu aiki da xa'ar Allah, da hanuwa da haninsa, Suna da wata kula ta musamman
daga Allah, da kuma cikakkiyar kiyayewa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai ne, Allah yana bada kariya ga
waxanda suka yi imani" [Hajji: 38].
GINSHIQI
NA UKU: Lokacin da gajimaren fitintinu suka lulluve sararin samaniyar
wannan al'umma, kuma kumfar bala'oi suka kasance sune suke tuqa kwale-kwalenta
= To a lokacin buqatuwar wannan al'ummar na ta zauna; ta zana hanyar tsiranta;
don ta samu ta kai ga tudun tsira, ko gavar samun aminci , buqatuwarta zuwa ga
haka Ya kan qara girma.
Kuma
lallai ba za ta tava samun hanyar hakan ba matuqar bata magance mushkilolinta
da cutukan da suka addabe ta da hasken Alqur'ani mai girma, da kuma sunnar
Annabi mai karaici ba.
Kuma
idan kayan baqanta rai da musibu, suka zama suna xakar fiskar wannan al'ummar,
a cikin kowani kwari, To lallai babu abinda aka fi fatan samun mafita daga gare
su fiye da neman warwaran waxannan matsalolin daga cikin wahayin Alqur'ani da
Sunnah, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya,
kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103]. kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa mun saukar da littafi zuwa gare
ku, a cikinsa akwai ambatonku, Ashe ba za ku hankalta ba", [Anbiya'i:
10]; Yana nufin: A cikinsa akwai xaukakarku da buwayarku, da kasancewanku
shugabanni.
Kuma
Imamu Malik ya fitar a cikin (Muwaxxansa) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai shi yace:
"Na bari a cikinku al'amari guda biyu; ba za ku vata ba matuqar kun yi riqo
da su; Littafin Allah, da sunnar AnnabinSa".
Kuma Abu-dawud ya fitar a cikin (Sunan,
xinsa)| daga hadisin Irbadh xan Sariyah, Yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yayi mana sallah, sa'annan ya fiskanto
mu, yayi mana wa'azi; irin wa’azi mai isarwa (mai ratsa jiki); wanda zukata
suka tsorata, Idanu kuma suka zubar da hawaye daga gare ta. Sai muka ce: Ya
Manzon Allah (s.a.w) kamar wa’azin mai bankwana; to kayi mana wasici, Sai yace,
"Ina yin wasici akanku
da bin dokokin Allah, da kuma ji da bi, ko da bawa ne ya zama shugaba a kanku,
lallai wanda ya rayu a cikinku da sannu zai ga savani dayawa, Na umarce ku da
yin riqo da sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu. Ku riqe ta da haqoranku
(Fiqa), kuma ku kiyaye fararrun ala’mura; domin kowace, bidi’a vata ce".
Saboda
riqo da wahayin Alqur'ani dana Sunnah a lokacin fitina, da kuma yin aiki da su
a halin jayayya da savani, da neman hukunci a cikinsu a kowace rabewar kai da
jayayya da husuma = su ne kaxai hanya guda xaya kwara; da za ta tunkuxe sharri,
da nau'ukan vata, da tashin hankali masu yawa mabanbanta, da rashin nitsuwar da
ta yaxu a duniyar Musulmai; ta yau.
GINSHIQI
NA HUXU: Aminci abun nema ne ga kowace al'umma, kuma gaya ce, da kowace
qasa take neman cimma sa, Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yace:
"Wanda ya wayi gari a cikinku, da aminci ko rashin tsoro a cikin kansa da
jama'arsa (wato: iyalansa), ko hanyarsa, Da kuma lafiya a cikin jikinsa, A
wurinsa akwai abincinsa na yininsa = To kamar an tattara masa Duniya ne
gabaxayanta", Tirmiziy da Ibnu-Majah suka ruwaito shi, da isnadi
mai kyau (hasan).
Kuma
lallai shi AMINCI yana dogara ne, akan haqqaqa ko tabbatar da gangariyar
Imani da Allah mabuwayi da xaukaka, cikin aqida, da zantuka, da aiyuka. Kuma
shi aminci asasinsa yana ginuwa ne akan yin aiki da umurnin da suka zo a cikin
Alqur'ani, da kuma tarin faxakarwar da suka zo daga Annabi, tare da yin aiki da
shari'ar Musulunci, cikin kowani sha'ani, daga cikin sha'anin rayuwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Waxanda suka yi Imani, kuma basu gauraya
imaninsu da zalunci ba, Waxannan, sune suke da cikakken aminci, kuma sune
shiryayyu" [An'am: 82].
Kuma
duk lokacin da wassu garurruka suka kauce wa shari'ar Allah, suka kuma bi
abubuwan da zukatansu suke so, sai tsarinsu mummuna ya jagorance su = To sai su
rasa amincin da suke fatan samu, sa'annan tsoro da firgici da rashin kwanciyar
hankali ya maye gurbin aminci, Allah (تعالى)
yana cewa:
"Kuma Allah ya buga misalin wata alqarya,
wacce ta kasance amintacciya natsattsiya; arziqinta yana zuwa mata a wadace daga
kowani wuri, Sai ta kafirta da ni'imomin Allah; Sai Allah ya xanxana mata tufafin
yunwa da tsoro saboda abinda suka kasance suna aikatawa" [Nahli:
112].
GINSHIQI
NA BIYAR: Lallai mafi muhimmanci daga cikin sabbuban da suke sanya al'umma
ta yi qarfi sune: Taimakakkeniya a tsakanin Mutane; akan biyayyar Allah da
taqawa, da haxa kai akan alkhairi da shiriya, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gabaxaya,
kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103].
Kuma
lallai yana daga cikin manya-manyan musibun da aka jarrabi al'ummar Musulmai da
su, kuma suka raunata qarfinta, suka kuma yasar da tutotin xaukakarta: Savani
da rarrabuwar kai da husuma da jayayya, wanda mulkin mallakan da ya gabata a
qarnonin da suka shuxe ya haifar da su ; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma kada ku yi jayayya sai ku raunana, sai
qarfinku ya tafi, Kuma ku yi haquri; lallai Allah yana tare da masu haquri" [Anfal:
46].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Kada ku yi qiyayya , kada ku yi hassada wa juna, kuma kada ku juya wa juna
baya, Ku kasance bayin Allah 'yan'uwan juna, Baya halatta Musulmi ya qaurace wa
xan'uwansa fiye da yini uku", Ahmad ya ruwaito shi, Amma asalin
hadisin yana wajen Imam Muslim.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ya ku Mutane! Na hore ku, da lazimtar jama'a, kuma ina hana ku rarraba
kai. Ya faxi wannan har sau uku", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma
lallai abubuwan da suka auku a tarihi dalilai ne manya da suke nuna cewa lallai
rarrabuwar kai halaka ne, kuma sababi ne na zagwanyewar al'umma da rushewarta;
(Wani MAWAQI yana cewa dangane da qasar
Andalus wacce hakan ya same ta, a shekaru darurrukan da suka gabata, a yayin da
aka samu rarrabuwar kai, da yawaitan qananan Sarakuna da masarautu):
Daga cikin abubuwan da suke sanya ni guje wa
qasar "Andalus",
(مما يُزهِّدني في
أرض أندلسٍ)
Sunayen "Mu'utadidu" a cikinta, da
"Mu'utamidu".
(أسماءُ مُعْتضِدٍ
فيها، ومُعْتَمِد).
A matsayin;
Laquban masarautu; waxanda aka sanya su, ba a
gurbinsu ba.
(ألقاب مملكة في غير
موضِعها).
Kamar muzurun da ke kumbura don ya kwaikwayi
tuben Zaki.
(كالهِرّ يَحْكِي
انتفاخًا صَوْلةَ الأسد).
Wajibi ne
akan Musulmai su kiyaye dokokin Allah, kuma kada su samu rarraba alhalin
littafin Allah yana cikinsu; yana hukunci, da karantar da su, salon rayuwa.
Sunnar ManzonSa kuma (صلى الله عليه وسلم) tana haskaka musu, tana basu shiriya.
Tarihin halifofin Annabi shiryayyu shi kuma
yana, abin koyi, kuma misali rayayye.
Kuma duk lokacin da suka karkace daga wannan
hanya, to halinsu zai kasance kamar faxar mai faxi:
Kowa yana ganin wani ra'ayi, Yana kuma
taimakon maganarsa
(كلٌّ يرى رأيًا
وينصُرُ قولَه).
Kuma akanSa, yake adawa da sauran 'yan'uwa
(وله، يعادي سائر
الإخوان).
Dadai ace, Su, a lokacin jayayya, za a datar
da su,
(ولو أنهم عند
التنازع وُفِّقوا).
Da miqa hukuncinsu zuwa ga Allah, ba tare da
wani saivi ba.
(لتحاكموا لله، دون
توان).
Kuma da sun wayi gari –bayan husuma- suna
masoyan juna,
(ولأصبحوا –بعد
الخصام- أحبةً).
Suna masu baqanta ran maqiya, waxanda kuma Shexan
ke qara qasqanta da su.
(غيظ العدا، ومذلة
الشيطان).
Amma duk lokacin da kansu ya rarraba, suke ta
yin husuma da jayayya to kawai za su zama loma ce mai daxin lankwamewa a wajen
maqiyansu da kuma Shexan.
Kuma shin –Ya kai Mai gani- Tare da
girman abinda ya samu Musulman Duniya, Shin za su dawo zuwa ga shiriyarsu, su
kuma sake haxuwa qarqashin tuta guda xaya (wato jagoransu a duniya ya zama
Mutum xaya!),
Kundin xaukar salon rayuwarsu Wahayin Allah
guda biyu (Alqur'ani, da sunnar Manzo?),
Me musu hukunci kuma shari'ar mai rahama
(Allah)?
Muna roqon Allah ya tabbatar da haka,
kusa-kusa; ba nesa ba. Lallai shi mai amsar addu'a ne.
NA
QARSHEN WAXANNAN GINSHIQAN SHINE: Mutane a lokacin bayyanar fitintinu su lazimci
hanyoyin shari'a, da karantarwar Alqur'ani, da sunnar Annabi; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan wani lamari na tsoro ko aminci ya
zo a gare su, sai su watsa shi, Kuma da za su mayar da shi zuwa ga Manzo, da
kuma ma'abuta al'amari daga cikinsu, da waxanda suke bincikensa daga cikinsu za
su san shi" [Nisa'i: 83]. Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Yin ibada a lokacin kashe-kashe kamar yin hijira ne zuwa gare ni".
Kuma
Musulmai –a lokacin fitintinu- dole su sani cewa lallai sha'anin HARSHE, da ALQALAMI
(wato: yin magana, ko rubutu) yana da hatsari wajen tada fitina ko qara ruruta wutarta,
kuma a lokacin fitina, lokaci ne da ake zaton zamewar qafa da yin kuskure,
Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin da kuke marabarsa da harsunanku, kuma
kuke faxa da bakunanku abinda baku da ilimi akansa, kuma kuna zatonsa mai
sauqi, alhalin kuwa Shi, a warin Allah mai girma ne" [Nur:
15].
Kuma
lallai MALAMAI da SHUGABANNI, da WAYAYYU, da MASU AIKIN WATSA LABARU wajibin
dake kansu –musamman a wannan zamanin- yana da girma, wajen bin diddigi da
qoqarin tabbatar da abu, a lokacin fitina, tare da rashin tunzuruwa ko faxar
duk wani abinda zai haifar da fitina, ko
qara ruruta wutarta.
Kuma duk wanda ya bibiyi fitintinun da suka yi
ta aukuwa a qasashen Musulmai, a shekarun baya zuwa yau = Zai san gaskiyar
abinda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya
bada labara akansa, kuma zuciyarsa zata samu yaqini; Cikin wani hadisin da wassu Maluma suka
raunata shi, Wassu kuma suka nuna cewa
zai iya zama hadisi hasan (mai kyau), Saidai kuma ma'anar da hadisin ke
xauke da ita ta zo cikin qa'idodin shari'a, da kuma nassoshi kevantattu da
gamammu. Wannan kuma shine hadisin da Annabi (صلى الله
عليه وسلم) yake cewa:
"Wata fitina, kurmiya, bebiya, makauniya zata kasance, Wanda ya nemi ya leqa
ta to zata kama shi, Kuma tsoma baki a cikinta kamar aukar da tokobi ne",
Abu-dawud ne ya rawaito shi.
Kuma a tarihi gabaxaya babu wata fitina da ta
auku face tushenta maganar baka ne, ko rubuta, Wannan kuma shine dalilin da ya
sa Abdullahi xan Abbas yake cewa:
"Lallai fitina da harshe take, Fitina
bada hannu take ba".
Kuma abinda Musulmai suka gani na fitintinun
wannan zamanin; waxanda sharrinsu yayi girma, cutarwarsu kuma tayi ta yaxuwa
= Na qara tabbatar da wannan maganar.
Allah shine mai taimako.
Allah
ya sanya mana albarka cikin wahayi guda biyu, ya kuma amfanar da mu da shiriyar
da take cikinsu.
Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman
gafarar Allah a ni da ku, da kuma sauran Musulmai, Ku nemi gafararSa; lallai
shi, Mai gafara ne Mai rahama.
HUXUBA TA BIYU:
Ina yabon Ubangijina kuma Ina gode
masa, Kuma ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai
yake bashi da abokin tarayya, Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu
bawansa ne kuma Manzonsa ne. Ya Allah
ka yi salati da sallama a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa.
Bayan
haka;
Ya
ku Musulmai!
Lallai yana
daga mafi alkhairin aiyuka, waxanda suka fi tsarki: Yawaita yin salati da
sallama ga Annabi mai karimci; saboda yin salati a gare shi da yawaita hakan
sababi ne na sauqar albarka a bayan qasa, kuma sababi ne na tunkuxe bala'oi,
Sai ku yawaita aikata hakan musamman a ranar Juma'a da darenta.
Kuma lallai
ne Mu, a qasar harami guda biyu masu xaukaka, An ni'imtar da mu da ni'imomi
masu girma,
Mafifitansu kuma sune: Aiki da shari'a mai
tsarki da yin hukunci da ita, da samun dunqulewa tsakanin shugabanni da waxanda
ake shugabanta, wanda hakan kuma, suka haxu, suka sabbaba samun aminci da
nitsuwa da kwanciyar hankali da wadaci,
Don haka;
Wajibi ne akan Mutanen wannan qasa da mazauna
cikinta, da kuma sauran Musulmai, muyi godiya akan waxannan ni'imomin, mu kuma
nisanci fushin Allah, da kuma yin aiki tuquru don neman yardarSa, da kuma
kwaxayin tabbatuwan danqon alaqa tsakanin shugaba da waxanda ake shugabanta,
akan gaskiya da shiriya.
Kuma
lallai wajibi ne akanmudangane da addininmu, da kuma Annabinmu: Mu bayyana wa
Duniya girman Musulunci; Mu nuna musu cewa lallai addinin Musulunci addinin jin
qai ne, da kyautatawa, da adalci, da kuma sauqi da tausasawa, da haxin
kai. Sannan kuma Duniya ta ga cewa
lallai shi Musulunci shine yake samar da mafi girman al'umma ta fiskar wayewa
da bunqasa, wanda suke rayuwa ko ni'imtuwa cikin walwala da wadaci da jin daxi
da aminci, da soyayya da taimakakkeniya, da sauran ma'anoni masu girma
maxaukaka, waxanda kowani halitta ke fatan dacewa da rabauta da su. Yin haka
kuma wajibi ne; wanda Allah ya wajabta shi akanmu, dangane da addininmu.
Ya Allah! Lallai Mu,
muna roqonka –Ya Ubangijinmu, Ya abun bautarmu- muna roqonka ka bada buwaya ga
addininka, kuma ka xaukaka kalmarka. Kuma ka haxa kan Musulmai akan alkhairi.
Ya Allah ka haxa kan Musulmai akan
alkhairi da shiriya.
Ya Allah! Ka gyara halinmu da halin
Musulmai.
Ya Allah! Ka yaye baqin ciki, ka
kore ababen vacin rai.
Ya Allah! Ka tseratar da bayinka
Musulmai daga kowani ibtila'i da fitina.
Ya Allah! Ka yi maganin maqiyan
Musulmai; Lallai su, basu gagare ka ba, Ya Mai girma!
Ya Allah! Ka kiyaye 'yan'uwanmu
Musulmai a kowani wuri, Ya Allah ka kasance mai taimako a gare su; Ya
Mabuwayi ya Mai matsanancin qarfi.
Ya Allah! Ka datar da Mai hidiman
Masallatan harami guda biyu zuwa ga abinda kake sonsa, kuma ka yarda da shi, Ya
Allah ka taimaki addini da shi, kuma ka xaukaka kalmar Musulmai da shi.
Ya Allah! Ka gafarta wa Musulmai maza
da Musulamai mata; rayayyu daga cikinsu da kuma matattu.
Ya Allah! Ka bamu mai kyau a Duniya,
a Lahira itama mai kyau, kuma ka kare mu daga azabar Wuta.
Bayin Allah!
Ku ambaci Allah ambato mai yawa,
Ku yi masa tasbihi safiya da maraice;
Qarshen addu'armu itace:
الحمد لله
رب العالمين
No comments:
Post a Comment