HADISAI
HAMSIN KAN
KHILAFANCIN HALIFOFIN MANZON ALLAH (S A W)
DA
FALALOLINSU
TATTARAWA DA FASSARAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على عبد الله ورسوله نبينا
محمد وآله وصحبه، وبعد:
GABATARWA
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
Tsira da aminci su qara tabbata ga wanda babu wani annabi a
bayansa; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa bakixaya.
Bayan haka; Lallai abubuwan da aka
jingina su ga ma'aikin Allah annabi Muhammadu s a w na hadisai ingantattu sune
suka qunshi addini na gangariya
–tare da littafin Allah; alqur'ani-; kamar yadda kuma sune wahayi na kai tsaye wanda Allah ta'alah ya yi wa Manzonsa
don su zama bayani ga abinda subhanahu ya sassaukar a gare shi na littafinsa; alqur'ani. Don haka; Duk wanda ya yi riqo da hadisin Annabi tare da alqur'ani to haqiqa ya yi riqo da igiyar
Allah mai qarfi wacce bata tsinkewa,
haka kuma wanda ya kama alqur'ani kana ya sake hadisi, ko ya sake dukkan biyun (alqur'ani da hadisi) to irin wannan ya vata vata mai nisa, kuma ya yi asara mabayyaniya.
Shi kuma littafin alqur'ani da xaukacin hadisan Manzo (s a w) ba su iso wa ga mutanen da suka zo daga baya ba; Sai
ta hanyar wassu zarata; waxanda Allah ta'alah ya halicce su don su sadaukar da rayuwarsu baki xayanta wajen koyan wannan addinin daga bakin Manzon Allah (s a
w), da kuma kare shi, tare da tallata shi ga sauran al'ummar duniya; Waxannan mutanen kuma su ne iyalen Annabi (s a w) da su ka rayu
da shi da kuma sahabbansa maxaukaka. Lallai waxannan jarumai, mazajen
fama, alarammomi mahaddata addinin Allah sun bauta wa Allah kamar yadda Manzonsa
ya koyar da su, kana kuma sun so wannan Manzon da abinda ya zo da shi fiye da
sonsu ga iyayensu, 'ya'yansu da sauran mutane baki-xaya, kamar yadda su ka bada kariya ga Ma'aiki da kuma addinin
Allah a cikin rayuwar manzo da bayan rasuwarsa, Musamman kuma mutane guda huxu ko biyar da su ka zama khalifofinsa, bayan komawarsa
zuwa ga mahaliccinsa; Allah ta'alah.
Kuma kasancewar sanin rayuwar
sahabban Manzon Allah; musamman manya-manyansu, da fahimtar yadda su ka bada
gudumawa ga wannan addini= ya kan qara fahimtar da Mutum matsayin waxannan Mutanen a cikin addini, da kuma wurin Manzo, wanda kuma hakan ya kan haifar da qarin sonsu a cikin zukata.
Kuma kasancewar shi tarihi akwai
ingantacce, akwai kuma qirqirarrun
qissoshi
da labarai a cikinsa.
Sa'annan kasancewar an samu wassu
da su ka vace daga
hanyar Allah miqaqqiya dangane
da sahabban Annabi; xaukacinsu, ko kuma
sashinsu; musamman kuma manyansu Abubakar, Umar da Usman –r a- har ma WANI
WANDA AKE CE MASA Aliyu xan Abdil-aliy al-amiliy alkarkiy wallafa
littafi ya yi sukutum mai suna "nafahaatu al-lahuti fi la'ani aljibti wax-xaguti (نفحات اللاهوت في لعن الجبت والطاغوت)" don tsinuwa ga wanda ake musu laqabi da
''aljibtu wax-xagutu'' a
addinin shi'a, (wato: Abubakar as-siddiq, da Umar al-khaxxab –r a-).
Shi wannan xan shi'an ya
kawo a cikin littafinsa dana ambata "p3/a'', Haka kuma Wanda ake kira ni'imatul-lahi
Al-jaza'iriy a cikin littafinsa ''al'anwaar annu'umaniyya, 1/ p53'' = Sun
kawo maganar da ta ke tafe don nuna wa mabiyansu cikin aqida ('yan
shi'a) cewa Abubakar kafiri ne:
«كان
يصلي خلف رسول الله عليه وآله والصنم معلَّقٌ في عُنُقه يسجد له».
Ma'ana:
(Wai Abubakar ya kasance yana yin salla a bayan Manzon Allah -s a w- alhalin
gunki na rataye a wuyansa; yana yin sujjada
a gare shi).
Shi kuma
Malaminsu mai suna Almajlisiy; Muhammad Baqir a cikin
littafinsa ''jala'u al'uyun, p 45'' kafirta Umar xan Al-khaxxab yayi, a inda yake cewa:
«لا مجال لعاقلٍ أنْ يشكّ في كفر عُمر، فلعنة
الله ورسوله عليه، وعلى كلّ مَن اعتبره مسلمًا، وعلى كلّ مَن يكفّ عن لعنه».
Ma'ana:
(Wai: Mutum mai hankali ba shi da damar ya yi shakka kan kafircin Umar, tsinuwar
Allah da Manzonsa su tabbata akansa –wai akan umar-, da kuma akan duk wanda ya xauki Umar a
matsayin musulmi, haka ta sake tabbata
ga wanda ya kame bakinsa; daga la'antar Umar).
–haka ya faxa!
Haka Shi
kuma ''alkarkiy'' da ya gabata a cikin littafinsa da ambatonsa ya gabata
(p57/ a) ya sake kafirta Usman xan Affan –r a- inda ya ce:
«إنّ مَن لم يجد في قلبه عداوة لعثمان، ولم يستحلَّ عرضه، ولم
يعتقد كفره: فهو عدو لله ورسوله، كافرٌ بما أنزل الله».
Ma'ana: (Lallai wanda bai ji wani irin adawa a
zuciyarsa akan Usman ba, bai kuma halatta cin mutuncinsa ba, Bai kuma qudurta cewa shi
kafiri ba ne a cikin zuciyarsa: To, shi maqiyin Allah da manzonsa ne, kuma ya
kafirce wa abin da Allah ya saukar).
–haka shima wannan ya faxa!
To saboda waxancan dalilan naga wajabcin karantar da
al'ummar musulmai tarihin halifofin Annabi -s a w- guda huxu ko biyar;
wato: Abubakar, Umar, Usman, Aliyu, da Alhasan xan Aliyu –r a-, ta fiskar KHILAFANCINSU
DA FALALARSU, Na kuma sanya taken rubutun: HADISAI HAMSIN KAN KHILAFANCIN
HALIFOFIN MANZON ALLAH -S A W- DA FALALOLINSU. Kamar kuma yadda na sharxanta wa kaina;
saboda abin da na ambata na matsalar rashin
ingancin wassu tarihohin; cewa ba zan ambaci ''hadisi ko asari'' ba Sai
wanda maluma su ka ce ingantacce ne; ma'ana: wanda ya wajaba a qudurce shi ko
ayi aiki da shi.
Fatana; Itace Allah ya sanya albarka
cikin wannan aiki; ta yadda za a rike shi a matsayin ''manhajar karatun tarihin
khalifofin Manzon Allah'' a makarantu, da majalis na karance-karance da su ke
masallatai ko zauruka. Ya kuma amfanar da musulmai da zasu bibiyi karatunsa ta
kafofi mabanbanta.
Rufewa: Kafin na
qarqare muqaddimata Ya kamata
a san cewa shi asalin wannan rubutu ya kasance ne da harshen larabci; ta fiskar
kulla ''babi'', sa'annan na Ambato ''hadisi ko asar'' a qarqashin wannan
babi, sai kuma na rufe da yin ta'aliqi
da zai fito da manufar ambaton wancan ''hadisin'' a wancan ''babin'', Ganin
muhimmancin a samu wannan rubutun da harshen hausa ya sanya yanzu nayi azamar
fassara shi izuwa ga ''harshen Hausa''.
Ya Allah ina roqonka da
sifofinka maxaukaka da ka qara xaukaka darajar
sahabban Manzonka; Annabi Muhammadu –صلى
الله عليه وسلم-; musamman
kuma manya-manyansu; Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, ya kuma yarda da su, ya
yardar da su ga xaukacin musulmai,
Sannan Muna roqon Allah da
ya azurta mu da sonsu, ya kuma haxa
mu da su da kuma Manzonmu Muhammadu -s a w- a cikin aljannar Firdausi
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا
محمد وآله وصحبه أجمعين.
Marubuci: Abubakar Hamza Zakaria
4 / Shawwal /1434h daidai 11/08/2013
miladiyya.
HADISI
(NA 1 ): WANDA KE MAGANA KAN ''KHILAFANCIN ANNABTA'' BAYAN MANZON ALLAH (S A W);
(a)
LAFAZIN
HADISIN DA RIWAYOYINSA:
عَنْ سعيد بن جُمهان، عن سَفِينَةَ مولى
رسول الله r، قَالَ: «قَالَ رَسُولُ اللَّهِ r: "خِلافَةُ
النُّبُوَّةِ ثَلاثُونَ سَنَةً، ثُمَّ يُؤْتِي اللَّهُ الْمُلْكَ، أَوْ مُلْكَهُ
مَنْ يَشَاءُ".
وفي لفظ الترمذي: ثُمَّ قَالَ لِي سَفِينَةُ: أَمْسِكْ خِلاَفَةَ
أَبِي بَكْرٍ، وَخِلاَفَةَ عُمَرَ، وَخِلاَفَةَ عُثْمَانَ، ثُمَّ قَالَ لِي: أَمْسِكْ
خِلاَفَةَ عَلِيٍّ، قَالَ: فَوَجَدْنَاهَا ثَلاَثِينَ سَنَةً.
وفي لفظ أبي داود: قَالَ سَعِيدٌ قَالَ
لِي سَفِينَةُ: «أَمْسِكْ عَلَيْكَ أَبَا بَكْرٍ سَنَتَيْنِ، وَعُمَرُ عَشْرًا، وَعُثْمَانُ
اثْنَتَيْ عَشْرَةَ، وَعَلِيٌّ كَذَا»، وفي رواية: (ستّ سنين).
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya
zo daga Sa'idu bn Jumhaan, daga Safinatu –'yantaccen bawan Manzon Allah
s a w- (Allah ya yarda da shi) Ya ce: Manzon Allah (s a w) ya ce: "Khilafancin
annabta shekaru talatin ne, Sa'annan sai Allah ya bada mulkinsa ga wanda ya
nufa''.
A
lafazin tirmiziy (Sai Safinatu ya ce wa xalibinsa: Riqe! Khalifancin Abubakar, da
khalifancin Umar, da khalifancin Usman, sa'annan ya ce: riqe! Khilafancin
Aliyu. Xalibin ya ce:
Sai mu ka lissafa muka samu khilifancin nasu shekaru talatin ne).
Amma
a lafazin Abu-dawud haka lafazin ya zo: (Sa'id bn Jumhaan, ya ce: Sai Safinatu
ya ce mini: Qirga wannan!
Abubakar da khilafancinsa shekaru biyu, Umar goma, Usmanu goma sha biyu, Aliyu
kuma kaza), a wata riwaya: shekaru shida.
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SU KA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Wannan hadisin maluman sunna dayawa sun
ruwaito shi a cikin littatafansu, daga cikinsu Imam Abu-dawud a cikin
littafinsa ''as-sunan'', lamba: 4646 da 4647, da Abu-isa At-tirmiziy a
cikin ''jami'i'', lamba: 2226, kuma ya ce: hadisi ne hasan. Alhafiz Ibnu-hajar
a cikin littafinsa ''fat-hul bariy, [2/ p2677] '' ya ce: (Ma'abuta ''sunan''
sun ruwaito wannan hadisin, kuma Ibnu-hibbana da waninsa sun inganta shi).
Ibnu-taimiyyata a cikin littafinsa ''minhajus
sunnan nabawiyyah, [7/ p50]'' ya ce: (Wassu maluma sun raunata wannan hadisin,
Saidai kuma Imam Ahmad da wassunsa sun ce hadisi ne tabbatacce. Kuma wannan shine
madogararsu daga cikin nassoshi kan tabbatar da khilafancin Aliyu).
Lallai shi wannan hadisin ta hanyar ''Sahabi Safinatu
(r a)'' da ya gabata hadisi ne ''hasan'', Saidai kuma hadisin ya zo ta hanyoyin
wassu sahabbai guda biyu; wadanda sune: Jabir bn Abdullahi, da Abubakrata
as-sakafiy (r a); don haka hadisin ''sahihi'' ne da waxannan
''shawahid''.
[Ka duba: littafin ''silsilatu al-ahadisi as-
sahihati na Albaniy, -2/ p823- lamba: 459]. Kuma shi ''Albaniy'' ya kawo maluma
goma da su ka inganta wannan hadisin.
(d)
ABUN DA HADISIN KE
KARANTARWA:
Lallai
wannan hadisin Na daga cikin hadisan da su ke qara tabbatar da annabcin Annabi
Muhammadu (s a w); saboda haka maluma dadama su ka ambace shi a littatafansu a
babuka da su ke bayanin dalilan annabtaka ''a'alamun nubuwati''; wannan kuma kasancewar
''bada labari kan abinda zai faru a gaba; sa'annan kuma abun ya faru kamar
yadda labarin ya shaidar'' xaya
ne daga cikin alamomin annabta; Manzon Allah (s a w) kuma ya bada labarai
dubbai kan abubuwan da za su faru a wassu lokuta da suke tafe; sai hakan ya
faru kamar yadda ya labarta.
Kamar
yadda ya gabata xaya daga
cikin maruwaitan hadisin daga cikin sahabbai wato; Safinatu (r a) ya ambaci khilafancin
khalifofi huxu; wato
Abubakar, Umar, Usman da Aliyu (r a) a matsayin cewa su suka cike shekaru
talatin na bayan Manzo, wanda ake laqabi wa jagoranci a cikinsu da laqabin ''khalifancin annabta''.
Saidai
kuma wassu masu bin diddigi daga cikin maluma sun lissafa lamarin; ta hanyar
lissafa shekaru da watanni da satuka da kwanaki na khalifancin kowani khalifa
daga cikin khalifofin nan guda huxu,
sai suka samu cewa bayan qarewar khalifancinsu
akwai kamar watanni shida da suka rage a cikin shekarun nan ''talatin''; wanda
kuma su ne mutanen garin ''kufa'' su ka yi mubaya'a wa Alhasan bn Aliyu bn
Abiy-xalib, har zuwa
lokacin da ya je ya zare hannunsa kan khilafanci ya kuma yi mubaya'a ga Mu'awyah
bn Abiy-sufyan wanda shine farkon ''sarakunan Musulmai'' (r a); don haka irin waxannan maluman
suke cewa: Shugabannin musulmai da za a kira jagorancinsu da ''khilafancin
annabta'' su biyar ne, Na qarshensu shi ne: ''Alhasan'', Shi kuma ''Mu'awuyah''
shi ne farkon sarakunan musulmai.
''Ibnu
taimiyyata'' yana cewa: (Rasuwar Annabi –s a w- ya kasance a watan uku –rabi'u
al'auwal- a shekara ta goma sha xaya bayan hijirarsa zuwa garin Madina,
bayan nan kuma zuwa shekara talatin shi ne aka samu sulhu da xan Manzon
Allah –s a w- a tsakanin vangarori guda biyu
na muminai; wato Shugaba Alhasan bn Aliyu; a lokacin da ya yi ''murabus'' ya
barwa Mu'awuyah; shekara ta 41 a watan 5 –jumada al-akhirah, kuma lallai an
kira wannan shekarar da ''shekarar haxewar jama'a''; saboda dukkan mutane a
wannan shekarar sun haxe wajen yin
mubaya'a ga Mu'awiyatu –r a-, kuma shi ne: ''sarkin Musulmai na farko'').
[majmu'u al-fatawa, 35/ p19].
Ya
zo cikin littatafa da su ka yi wa hadisin da ya gabata sharha, kamar littafin
''aunul ma'abuud, [p2020]'', da ''tuhfatul ahwaziy [2/ p1798]'' maganar
''Al-alkamiy'' da ya ke cewa: (A shekara talatin da su ke bayansa –s a w- ba a samu shugabancin wani idan
banda na khalifofi guda huxu, da kuma
watannin Al-hasan … kwanakin khilafancin Abubakar su ne: shekaru biyu, da wata
uku, da kwana goma … ''Nawawiy'' ya faxa a cikin littafin: ''tahzibu
al-asma'i wallugaat'' cewa: khilafancin Umar shekaru goma ne da watanni biyar
da kuma kwana ashirin da xaya. Usman
kuma shekaru goma sha biyu; in banda kwana shida. Aliyu kuma shekaru biyar, A
wani qaulin kuma
shekaru biyar ba wassu 'yan watanni, Sai kuma Al-hasan wata bakwai … ). Wallahu
a'alam!
(e)
BANBANCI TSAKANIN ''KHILAFANCIN
ANNABTA'' DA KUMA ''MULKI'':
A
cikin wannan hadisin lallai Annabi (s a w) ya bayyana cewa bayan tafiyarsa
da shekaru talatin duk jagorancin da ya kasance a wannan tsukin to ''khilafancin
annabta'' ne. Bayan haka kuma sai ''mulki''; To shin akwai banbanci ne tsakanin
lamura biyun?
Amsa
ita ce: Kamar yadda Allah ya kasantar da annabawansa kashi biyu, wassu a
matsayin ''annabawa kuma masu sarauta –mulki-'' kamar yadda Allah ya bai wa
iyalan annabi Ibrahim mulki mai girma da annabci; sai su ka zama
annabawan Allah kuma cikin daula, wato kamar su annabi Yusuf, haka kuma annabi
Dawud da xansa Sulaiman
suma Allah ya shaida cewa ya basu mulki mai fadi; kamar shi annabi Sulaiman Allah
ya hore masa iska, da shexanu don su
masa gine-gine, da shiga cikin ruwa don kwaso albarkatun da ke ciki, da
sauransu.
Kaso
na biyun kuma sune ''Manzannin Allah a matsayin bayi; masu cikakkiyar bauta a
gare shi; ba daula''; Wannan kuma shi ne zavin annabinmu; annabi Muhammadu
lokacin da Allah ya turo masa Mala'ika ya tambaye shi; shin so ya ke yi ya zama
''Annabi mai mulki, ko kuma Manzo bawa?'' Sai ya ce: Na zavi na zama
''Manzo kuma bawa; na samu abinci na ci yau, gobe kuma na rasa; idan na qoshi sai in
gode maka, idan kuma naji yunwa sai in roqe ka!''
To
haka lamarin ya ke dangane da ''khilafancin annabta'' ba shugabanci ne na daula,
ko kuma gadar da mulkin ga 'ya'ya suke kasancewa a gaban waxannan
khalifofin ba, Savanin masu
mulki; waxanda cikin
sarakunan musulmai Mu'awuyah bn Abiy-Sufyan (r a)'' shi ne ya kasance na farkonsu.
Ana shan daula, sai dai shi Mu'awuyah an yi daula ne cikin halal.
Kuma
lallai su masu mulki su kan yi qoqarin
su gadar da ''sarautar'' tasu ga
'ya'yansu.
Idan
aka nazarci tarihin khilafancin waxancan khalifofi guda biyar za a ga ba
fantamawa ce, ko daula, ko zurfafawa cikin tufa ko abinci ko mallakar dawakai
na alfarma da sauransu su ke gaban
jagororin ba; saidai kawai addini. Yayin da ''sarakuna'' a bayansu har zuwa yau
labarinsu dangane da abinci na alfarma, abubuwan sha, tufa, abubuwan hawa, ba
boyayyen abu ne a wurin mutane ba. Shi
yasa lamarinmatakin farkon shi yafi soyuwa a wajen Allah.
Manufa dai anan: ita ce:
''khalifancin annabta'' na qoqarin
tabbatar da muradun ''annabta'' ne bakixaya, ba gina duniya ko kuma morarta
ba, yayin da shi kuma ''mulki'' gwargwadon mai mulkin ya ke kasancewa; idan ''na
Allah ne'' sai ka ga ya taqaita wajen
morar mulki ga halal kawai, sa'annan ya kula da muradun annabta, in kuma ba
haka ba; to sai yawan zalunci da sharholiya da budun-buduma cikin morar duniya
ta kowace hanya. Wallahu a'alam.
Wanda ke buqatar qarin bayani kan fiskoki masu yawa da
su ka banbance ''mulki'' da ''annabta'', da ''khilafanci annabta'' duk da cewa:
da mai mulki da annabi dama waxanda
suka khalifance shi: mabiya su kan yi musu xa'a. {To sai ya duba Majmu'u fatawa
ibni taimiyya' [35/ p17-32], da kuma p33-35}. Allah ta'alah ya fahimtar da mu
addininsa, amin!
مجموع الفتاوى (ج35/ ص19)
وَوَفَاةُ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَتْ فِي شَهْرِ
رَبِيعٍ الأَوَّلِ سَنَةَ إحْدَى عَشْرَةَ مِنْ هِجْرَتِهِ وَإِلَى عَامِ ثَلَاثِينَ
سَنَةَ كَانَ إصْلَاحُ ابْنِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْحَسَنِ
بْنِ عَلِيٍّ السَّيِّدِ بَيْنَ فِئَتَيْنِ مِنْ الْمُؤْمِنِينَ بِنُزُولِهِ عَنْ الْأَمْرِ
عَامَ إحْدَى وَأَرْبَعِينَ فِي شَهْرِ جُمَادَى الْأُولَى وَسُمِّيَ " عَامَ
الْجَمَاعَةِ " لِاجْتِمَاعِ النَّاسِ عَلَى " مُعَاوِيَةَ " وَهُوَ
أَوَّلُ الْمُلُوك
قال الإمام أحمد في رواية حمدان بن علي : " ما كان في القوم أوكد بيعة
من عثمان كانت بإجماعهم (ج1/ ص532-533)
قال غير واحد من السلف والأئمة كأيوب السختياني وأحمد [بن حنبل]، والدارقطني،
وغيرهم: من لم يقدم عثمان على علي فقد أزرى بالمهاجرين والأنصار (ج1/ ص534).
كما قال غير واحد من الأئمة، منهم أيوب السختياني وغيره: من قدم عليا على عثمان
فقد أزرى بالمهاجرين والأنصار] (ج6/
152-153).
قال الإمام أحمد: " لم يجتمعوا على بيعة أحد ما اجتمعوا على بيعة عثمان
" (ج6/ ص154).
أحمد بن حنبل، مع أنه أعلم أهل زمانه بالحديث، احتج على إمامة علي بالحديث الذي
في السنن: " «تكون خلافة النبوة ثلاثين سنة، ثم تصير ملكا». وبعض الناس ضعف هذا
الحديث، لكن أحمد وغيره يثبتونه، فهذا عمدتهم من النصوص على خلافة علي
(ج7/ ص50).
قال الحافظ ابن حجر في تقريب التهذيب
وهو يترجم لسعيد: سعيد بن جُمهان -بضم الجيم وإسكان الميم-
الأسلمي أبو حفص البصري، صدوق له أفراد، من الرابعة، مات سنة ست وثلاثين (رقم
الترجمة: 2279، ص174).
وقال
الحافظ ابن حجر في تقريب التهذيب وهو يترجم لسفينة: سفينة مولى رسول الله r يكنى أبا عبد الرحمن، يقال: كان
اسمه مهران أو غير ذلك، فلُقب سفينة لكونه حَمل شيئًا كثيرًا في السفر، مشهور، له أحاديث
(رقم الترجمة: 2458، ص185).
في مجموع
الفتاوى (ج35/ ص19) لابن تيمية رحمه الله:
«وَوَفَاةُ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَتْ فِي شَهْرِ رَبِيعٍ الأَوَّلِ سَنَةَ إحْدَى عَشْرَةَ مِنْ
هِجْرَتِهِ وَإِلَى عَامِ ثَلاثِينَ سَنَةَ كَانَ إصْلاحُ ابْنِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ السَّيِّدِ بَيْنَ فِئَتَيْنِ مِنْ
الْمُؤْمِنِينَ بِنُزُولِهِ عَنْ الأَمْرِ عَامَ إحْدَى وَأَرْبَعِينَ فِي شَهْرِ جُمَادَى
الأُولَى وَسُمِّيَ " عَامَ الْجَمَاعَةِ " لاجْتِمَاعِ النَّاسِ عَلَى
" مُعَاوِيَةَ " وَهُوَ أَوَّلُ الْمُلُوك».
وفي
كتاب عون المعبود: «قَالَ الْعَلْقَمِيّ: قَالَ شَيْخنَا:
لَمْ يَكُنْ فِي الثَّلاثِينَ بَعْده صلى الله عليه وسلم إِلا الْخُلَفَاء
الأَرْبَعَة وَأَيَّام الْحَسَن. قُلْت: بَلْ الثَّلاثُونَ سَنَة هِيَ مُدَّة
الْخُلَفَاء الأَرْبَعَة كَمَا حَرَّرْته؛ فَمُدَّة خِلافَة أَبِي بَكْر سَنَتَانِ
وَثَلاثَة أَشْهُر وَعَشْرَة أَيَّام، وَمُدَّة عُمَر عَشْر سِنِينَ وَسِتَّة
أَشْهُر وَثَمَانِيَة أَيَّام، وَمُدَّة عُثْمَان أَحَد عَشَرَ سَنَة وَأَحَد
عَشَرَ شَهْرًا وَتِسْعَة أَيَّام، وَمُدَّة خِلافَة عَلِيّ أَرْبَع سِنِينَ
وَتِسْعَة أَشْهُر وَسَبْعَة أَيَّام. هَذَا هُوَ التَّحْرِير فَلَعَلَّهُمْ
أَلْغَوْا الأَيَّام وَبَعْض الشُّهُور. وَقَالَ النَّوَوِيّ فِي تَهْذِيب
الأَسْمَاء: مُدَّة خِلافَة عُمَر عَشْر سِنِينَ وَخَمْسَة أَشْهُر وَإِحْدَى
وَعِشْرِينَ يَوْمًا، وَعُثْمَان ثنْتَيْ عَشْرَة سَنَة إِلا سِتّ لَيَالٍ،
وَعَلِيّ خَمْس سِنِينَ وَقِيلَ خَمْس سِنِينَ إِلا أَشْهُرًا، وَالْحَسَن نَحْو
سَبْعَة أَشْهُر، انْتَهَى كَلام النَّوَوِيّ، وَالأَمْر فِي ذَلِكَ سَهْل. هَذَا
آخِر كَلام الْعَلْقَمِيّ»
(ص2020)، ومثله في تحفة الأحوذي (ج2/ص1798).
HADISI
(NA 2 ): DAKE MAGANA KAN ''LAZIMTAR ABUBUWAN DA KHALIFOFIN ANNABI (S A W)
SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA SU KA ''SUNNATA";
(a)
LAFAZIN
HADISIN:
الحديث الثاني: ذكر الأمر بلزوم سنة الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ الْمَهْدِيِّينَ:
عن الْعِرْبَاض بْن سَارِيَةَ t، في الحديث
المشهور بحديث المَوْعِظَة البَلِيغَة، وفيه أنه قال رسول الله r: "... فَعَلَيْكُمْ
بِسُنَّتِي، وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الْمَهْدِيِّينَ الرَّاشِدِينَ، تَمَسَّكُوا بِهَا وَعَضُّوا عَلَيْهَا
بِالنَّوَاجِذِ، وَإِيَّاكُمْ وَمُحْدَثَاتِ الأُمُورِ، فَإِنَّ كُلَّ مُحْدَثَةٍ بِدْعَةٌ،
وَكُلَّ بِدْعَةٍ ضَلالَةٌ".
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya
zo daga ''Irbadh bn Sariyata'' (r a) a cikin hadisi shahararre; da annabi s a w
ya yi wa'azi mai ratsa jiki ga sahabbansa, ya zo a cikinsa cewa: (Ina umurtarku
da ku lazimci sunnata, da sunnar khalifofina shiryeyyu masu shiryarwa, ku yi
riko da ita, ku yi damka akanta da fikoki, kuma ahir dinku da riko da
kirkirarrun al'amura; saboda kowani kirkirarren abu bidi'a ne, kuma kowace
bidi'a bata ne).
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SU KA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Shi
dai wannan hadisin maluman sunna da dama sun ruwaito shi a cikin littatafansu,
daga cikinsu akwai Imam Abu-dawud a cikin littafinsa ''as-sunan'',
[lamba: 4607], da Abu-isa At-tirmiziy a cikin ''jami'i'', [lamba: 2676], kuma
ya ce: hadisi ne hasan sahihi. Albaniy ma ya inganta hadisin, kana ya yi ishara
cewa: manya manyan maluman hadisi -a jiya da yau- sun yi ittifaqi wajen inganta
shi [Duba/ Silsilatu al'ahadis as-sahihati, 6/p526-527, lamba: 2735].
(d)
LABARI KAN SABANI DA
RARRABUWA DA ZA SU KASANCE A CIKIN WANNAN AL'UMMA, BAYAN MANZON ALLAH –S A W-,
TARE DA BAYANIN CEWA; RIKO DA SUNNAR MA'AIKI DA KUMA TA KHALIFOFINSA SHI NE
MAFITA DAGA GARE SU:
Hadisi
(2) wannan kamar (1) ne, wato dukkaninsu na daga cikin hadisan da su ke kara
tabbatar da annabcin annabi Muhammadu (s a w); Shi wannan na bada labari kan
abun da zai faru na sabani da yawa da rarrabuwa, bayan manzon Allah (s a w),
tare kuma da bayanin mafita daga haka, kuma duk abin da hadisin ya tabbatar ya
auku kamar yadda labarin ya shaidar, Wannan yasa ''Alhafiz Ibnu-rajab'' –a
sharhinsa na fadin manzon Allah s a w- ga wannan jumla a cikin hadisin:
«فَمِنْ يَعِشْ مِنْكُمْ بَعْدِي،
فَسَيَرَى اخْتِلافًا كَثِيرًا، فَعَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ
الْمَهْدِيِّينَ مِنْ بَعْدِي، عَضُّوا عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ»
{Duk wadda ya rayu a cikinku bayana to lallai zai ga sabani da
yawa; Ina horarku da riko da sunnata, da sunnar khalifofina shiryayyu masu
shiryarwa a bayana; ku yi riko akanta da fikoki} yake cewa:
((هَذَا إِخْبَارٌ مِنْهُ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِمَا وَقَعَ فِي أُمَّتِهِ بَعْدَهُ مِنْ كَثْرَةِ الاخْتِلافِ
فِي أُصُولِ الدِّينِ وَفُرُوعِهِ، وَفِي الأَقْوَالِ وَالأَعْمَالِ وَالاعْتِقَادَاتِ،
وَهَذَا مُوَافِقٌ لِمَا رُوِيَ عَنْهُ مِنَ افْتِرَاقِ أُمَّتِهِ عَلَى بِضْعٍ وَسَبْعِينَ
فِرْقَةً، وَأَنَّهَا كُلُّهَا فِي النَّارِ إِلا فِرْقَةً وَاحِدَةً، وَهِيَ مَنْ
كَانَ عَلَى مَا هُوَ عَلَيْهِ وَأَصْحَابُهُ. وَكَذَلِكَ فِي هَذَا الْحَدِيثِ أَمْرٌ
عِنْدَ الافْتِرَاقِ وَالاخْتِلافِ بِالتَّمَسُّكِ بِسُنَّتِهِ وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ
الرَّاشِدِينَ مِنْ بَعْدِهِ، وَالسُّنَّةُ: هِيَ الطَّرِيقَةُ الْمَسْلُوكَةُ، فَيَشْمَلُ
ذَلِكَ التَّمَسُّكَ بِمَا كَانَ عَلَيْهِ هُوَ وَخُلَفَاؤُهُ الرَّاشِدُونَ مِنَ الاعْتِقَادَاتِ
وَالأَعْمَالِ وَالأَقْوَالِ)).
(Wannan bangare daga
hadisin nan labari ne daga manzon Allah –s a w- kan abin da ya faru da
al'ummarsa na yawan sabani cikin mas'alolin addini manya-manya da
kanana-kanana, wadda ake kiransu: ''mas'alolin da su ne; tushen wannan addini,
da wadda su ke ressa'', da kuma abin da ya kasance wa al'ummarsa na sabani a
cikin ''zantuttuka, da aiyuka, da akidoji''. Kuma lallai shi -wannan yanki na
hadisi- ya yi daidai da abin da aka ruwaito daga gare shi –s a w- na cewa:
al'ummarsa zata rarraba izuwa kungiya-kungiya har kashi saba'in da wani abu, da
kuma cewa dukkansu sun cancanci shiga wuta in banda guda 'daya; wacce ita ce:
ta ke kan ''manhajin'' da annabi –s a w- ya ke kansa shi da sahabbansa.
Dadin-da'dawa
–a cikin wannan hadisi- akwai umurni daga manzon Allah s a w a yayin da aka
samu rarraba da sabani cewa mafita ita ce: ayi riko da ''sunnarsa'' da ''sunnar
khalifofi'' shiryayyu a bayansa; Don haka ita wannan wasiyyar ta kunshi: RIKO
DA ABIN DA MANZON ALLAH –S A W- SHI DA KHALIFOFINSA SHIRYAYYU SU KE AKAI; TA
BANGAREN AKIDOJI, DA AYYUKA, DA KUMA ZANTUKA)) [Jami'u al'ulumi walhikami,
p120].
Ka
ga a nan annabi (s a w) ya bayyana sabani da rarrabuwar kai da zai kasance a
cikin al'ummarsa, a bayansa. Kana kuma ya ambaci abin da -matukar an yi aiki da
shi- zai zamo rigakafi da kuma magani ga hakan.
A
cikin wannan hadisin an siffanta wadannan khalifofin da ''arrashiduna''; saboda
sun hada sifofi guda biyu; wadanda su ne:
1- Sanin
gaskiya.
2- Aiki
da shi. Saboda ''arrashid'' kishiyan ''algawiy'' ne; shi kuwa ''algawiy'' shi
ne wadda ya san gaskiya amma ya yi aiki da sabaninsa.
Alhafiz
Ibnu-rajab ya ce: ((Ya zo a wata riwaya ''almahdiyyina''; ma'ana: Allah zai
shiryar da su izuwa gaskiya, ba zai batar da su ita ba; don haka kason mutane
guda uku ne: ''rashid, gawin, da daalun''; Shi ''rashid'' shi ne: wadda ya san
gaskiya ya kuma bi ta, shi kuma ''algawiy'' shi ne: wadda ya san gaskiyan amma
yaki binta, yayin da shi kuma ''addaalu'' shi kuma: shi ne wadda ya bace ga
gaskiyar; bai santa ba, ballantana ya yi aiki da ita; Don haka; kowani
''rashid'': ''muhtad'' ne)) [Jami'u al'ulumi walhikami, p126].
(e)
BANBANCI TSAKANIN
KHALIFOFIN ANNABI SHIRYEYYU DA SAURAN SHUGABANNI WADANDA BA SU BA:
Lallai
wadanda su ka jagoranci wannan al'umma bayan rasuwar manzon Allah (s a w), ko
su ke jagorantarta, ko za su jagorance ta izuwa kiyama suna da yawan gaske;
Amma umurni da Manzon Allah ya yi na cewa: a bi ''sunnarsa'' da kuma ''sunnar
khalifofinsa shiryayyu'' bayan ya bada gamemmiyar doka dangane da 'daukacin
shugabanni; cewa ''a ji, a kuma yi musu biyayya cikin abin da ba sabon Allah ba
ne'': Na nuna cewa lallai ''sunnar khalifofin annabi shiryeyyu'' abar bi ce,
kamar yadda ''sunnar ma'aiki s a w'' ta ke a bar bi; sabanin wadanda ba
wadannan khalifofin ba; na daga sauran shugabanni. Imam Malik bn Anas ya ce:
Umar bn Abdil'aziz ya ce:
((سَنَّ رَسُولُ
اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَوُلاةُ الأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ سُنَنًا؛
الأَخْذُ بِهَا اعْتِصَامٌ بِكِتَابِ اللَّهِ، وَقُوَّةٌ عَلَى دِينِ اللَّهِ، وَلَيْسَ
لأحَدٍ تَبْدِيلُهَا، وَلا تَغْيِيرُهَا، وَلا النَّظَرُ فِي أَمْرٍ خَالَفَهَا، مَنِ
اهْتَدَى بِهَا فَهُوَ مُهْتَدٍ، وَمَنِ اسْتَنْصَرَ بِهَا فَهُوَ مَنْصُورٌ، وَمَنْ
تَرَكَهَا وَاتَّبَعَ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ، وَلاهُ اللَّهُ مَا تَوَلَّى
وَأَصْلاهُ جَهَنَّمَ، وَسَاءَتْ مَصِيرًا)).
Ma'ana:
((Annabi –s a w- da shugabanni da su ka zo a bayansa sun sunnanta wassu
sunnoni; wadanda riko da su aiki ne da littafin Allah, kuma karfi ne ga addinin
Allah, -su wadannan sunnonin- wani ba shi da daman ya kawo canjinsu ko ya
jirkita su, ko kuma dai ya tsaya yana nazari kan wani abu da ya saba musu. Kuma
lallai wadda ya nemi shiriya da su: to shi shiryeyye ne, wadda kuma ya nemi taimakon
Allah da bin wadannan sunnoni: to shi abun a bashi nasara ne, yayin wadda kuma
ya yi watsi das u; ya kuma bi turbar da ba ta muminai ba: sai Allah ya jibinta
masa abin da ya jibinta, ya kuma shigar das hi jahannama; lallai kuma ta yi
matukar muni ta zamto makoma)) [Jami'u al'ulumi walhikami, p123].
(f)
MISALAI NA ABUBUWAN DA
KHALIFOFIN ANNABI (S A W) SHIRYEYYU SU KA SUNNATA WA AL'UMMA:
Abubuwa
da khalifofin annabi (s a w) shiryeyyu su ka ''sunnanta'' a tsawon khalifancin
da ya kai shekara talatin suna da yawa, [ka duba: Jami'u al'ulumi walhikami,
p129] zan bada misali akan wassu daga cikinsu, kamar haka:
1-
Tattara ''mus'haf'' a cikin
littafi guda: Wadda
Abubakar ya yi a cikin ''khalifancinsa'' da shawarin Umar (r a). Zaidu bn Sabit
(r a) ya kasance a farkon lamari yana ga kada a yi haka; har ma ya ce musu:
Yaya za a yi ku yi abin da annabi (s a w) bai yi ba? Kana daga baya ya fahimci
hakan shi ne maslaha, sai ya gamsu [Duba cikakkiyar kissar a cikin ''sahihul
Bukhari'', lamba: 4679].
2-
Yakar wadanda su ka hana
zakka: Lallai
Abubakar assidiq (r a) ya yi azama kan haka, 'Dan uwansa Umar bn khaddab (r a)
shi kuma a farkon lamari ya kasance yana ga kada a yi haka, har zuwa lokacin da
Allah ya sa ya gamsu [Duba cikakkiyar kissar a cikin ''sahihul Bukhari'',
lamba: 1399, 1400].
3-
Hada masu sallar ''kiyamu ramadana'' ga
limami guda wadda Umar alfaruq (r a) ya yi: Mutane kuma su ka hadu akan
haka tun daga zamaninsa; da lokacin khalifancin Usman da Aliyu (r a), har zuwa
wannan rana. Sai ya zama daya daga cikin sunnonin khalifofi shiryayyu. [Duba
kissar a cikin ''Muwaddah Malik'', lambobi: 378, 379, 380, 381].
4-
Kiran salla na farko ranar
juma'a wadda Usman (r a) ya kara, kuma ake yinsa a kasuwa: Saboda
bukatuwan mutane izuwa gare shi; don su je su shirya wa sallar juma'a, kuma
Aliyu bn Abiy-dalib (r a) shi ma a lokacin khalifancinsa ya tabbatar da hakan
bai canza ba, haka kuma aikin musulmi ya kasance a kan haka; izuwa yau. [Duba
kissar a cikin ''Musnadu Ahmad'', lamba: 15969]. Da sauransu.
A
takaice;
Wannan hadisi da ke umurni kan riko da sunnonin ''khalifofin manzo'' wadanda
kuma su ka tafiyar da khalifancinsu gaba-dayansu tsawon shekara (30) akan
''minhajun nubuwati'' na numa mana matsayin wadannan bayin Allah a cikin
addinin Allah; wadda don fitar da shi wannan matsayin a fili Manzon Allah (s w
t) ya umurce mu da bin ''sunnarsa'' da ''tasu'' a matsayin mafita daga kowani
sabani ko rarrabuwa da za a samu a cikin wannan addini.
Ya
Allah ka dora mu kan turbar ma'aiki (s a w) da kuma ''sunnonin khalifofinsa
shiryeyyu'' kana ka kashe mu akan haka, amin!
HADISI
(3): DAKE UMURNI KAN "KOYI'' DA KHALIFOFI GUDA BIYU, BAYAN MANZON ALLAH (S
A W);
(a)
LAFAZIN
HADISIN DA RIWAYOYINSA:
الحديث الثالث: ذكر أمر النبي r بالاقتداء بالخليفتين بعده:
عَنْ
حُذَيْفَةَ بْنِ الْيَمَانِ t، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللهِ r: "إِنِّي لاَ أَدْرِي مَا قَدْرُ بَقَائِي فِيكُمْ؛ فَاقْتَدُوا
بِاللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي, وَأَشَارَ إِلَى أَبِي بَكْرٍ وَعُمَرَ ..."الحديث.
وفي لفظ بدون لفظ الإشارة: "اقْتَدُوا بِاللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي:
أَبِي بَكْرٍ، وَعُمَر".
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya
zo daga ''Huzaifah bn Al-yamaan'' (r a), ya ce: Manzon Allah (s a w) ya ce:
((Lallai ni ban san kwanakin da su ka rage na wanzuwata a cikinku ba; amma ku
yi ''koyi'' da mutum biyu da za su kasance a bayana, Sai ya yi nuni izuwa
Abubakar da Umar)).
A
wani lafazin kuma haka hadisin ya zo (ku yi ''koyi'' da mutum biyu da za su
kasance a bayana; Abubakar da Umar).
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SU KA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Wannan hadisin maluman sunna da yawa sun
ruwaito shi a cikin littatafansu, daga cikinsu Imam Abu-isa At-tirmiziy a cikin ''jami'i'', lamba: 3663,
da: 3799, kuma ya ce: hadisi ne hasan. Da kuma Ibnu-majah a cikin ''as-sunan'',
lamba: 97, da "Musnad Ahmad'', lamba: 23245. da kuma wassunsu.
Albaniy ya inganta shi, ya kuma ce an ruwaito
wannan hadisin ta hanyoyin sahabbai guda hudu; Abdullahi bn Mas'ud, Huzaifatu
bn Alyamaan, da Anas bn Malik, da kuma Abdullahi bn Umar (r a), kana kuma ya
kawo hanyoyin hadisin yana mai nazari kansu hanya-hanya [Duba: littafin
''silsilatu al-ahadisi as- sahihati'' na Albaniy, {3/ p233-236} hadisi mai
lamba: 1233]. [Don mai-da-martani ga wadda ya raunana shi duba: ''Minhaju as-sunnati, annabawiyyati'', [8/p361-362].
(d)
FA'IDODI BIYU DAGA WANNAN
''HADISI'':
Wannan hadisin ya kunshi bangarori guda
biyu muhimmai; wadda kuma su ne ginshikai biyu na wannan ''littafi''; kamar
haka:
Na farko: Nuni kan
''khalifancin biyu daga cikin khalifofin annabi (s a w) shiryeyyu; wato:
Abubakar da Umar (r a).
Na biyu: Matsayin
Abubakar da Umar (r a) a cikin addini; da kuma yadda annabi (s a w) ya yi
umurni kan a rike su abun ''koyi''. Lallai Annabi (s a w) ya kebance
kalifofinsa shiryeyyu –kamar yadda ya gabata a cikin hadisi na (2)- akan sauran
sahabbai; ta yadda ya yi umurni kan lazimtar ''sunnonin khalifofinsa
shiryeyyu'', sai kuma ya kebance Abubakar da Umar (r a) daga cikinsu; ta fiskar
umurtar mutane kan rikarsu abun koyi ''qudwa''; Wannan yasa malamin sunna
Abu-muhammad Al'husain bn Muhammad Albagawiy (wadda ya rasu a: 516h), ya ke
cewa a cikin littafinsa ''Sharhu as-sunnah, [1/ p208]:
((Kuma
kamar yadda annabi –s a w- ya kebance wadannan –Abubakar, Umar, Usman, da Aliyu
r a- daga cikin sauran sahabbai, kan cewa a bi sunnarsu, to haka kuma ya
kebance Abubakar da Umar daga cikin su wadannan, a cikin hadisin ''Huzaifatu'',
daga annabi -s a w-, ya ce: ku yi ''koyi'' da mutum biyu da za su kasance a
bayana; Abubakar da Umar)). Ga maganar tasa cikin harshen larabci:
«... وَكَمَا خَصَّ النَّبِيُّ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَؤُلاءِ مِنْ بَيْنِ الصَّحَابَةِ بِاتِّبَاعِ سُنَّتِهِمْ،
فَقَدْ خَصَّ مِنْ بَيْنِهِمْ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ فِي حَدِيثِ حُذَيْفَةَ عَنِ النَّبِيِّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: اقْتَدُوا بِاللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي: أَبِي
بَكْرٍ، وَعُمَرَ». شرح
السنة للبغوي (ج1/ص208).
Mashahurin
malamin addini; mai suna: Ahmad Ibnu-taimiyyata (r l) shima yana da magana
makamanciyar wacce ta gabata, a inda ya ke cewa –bayan ya ambaci wannan hadisi
da nake magana akansa-:
«وَلَمْ يَجْعَلْ هَذَا لِغَيْرِهِمَا، بَلْ ثَبَتَ عَنْهُ أَنَّهُ
قَالَ: "عَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ الْمَهْدِيِّينَ
مِنْ بَعْدِي. ..." فَأَمَرَ بِاتِّبَاعِ سُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ.
وَهَذَا يَتَنَاوَلُ الأَئِمَّةَ الأَرْبَعَةَ. وَخَصَّ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ بِالاقْتِدَاءِ
بِهِمَا. وَمَرْتَبَةُ الْمُقْتَدَى بِهِ فِي أَفْعَالِهِ وَفِيمَا سَنَّهُ لِلْمُسْلِمِينَ:
فَوْقَ سُنَّةِ الْمُتَّبِعِ فِيمَا سَنَّهُ فَقَطْ».
Ma'ana:
((Annabi –s a w- bai bada wannan ''matsayi'' ga wanin Abubakar da Umar; -yana
nufin: matsayin a rike su ''qudwa –abun koyi-'', Ya dai tabbata daga gare shi;
ya ce: INA UMURTAR KU DA KU RIKI SUNNATA DA SUNNAR KHALIFOFINA SHIRYEYYU MASU
SHIRYARWA A BAYANA, Sai annabi –s a w- ya yi umurni cewa a ''bi'' abin da
khalifofi shiryeyyu su ka ''sunnata''; Wannan kuma ya game wadannan khalifofin
guda hudu. Sai kuma ya kebance Abubakar da Umar kan a rike su a matsayin ''abun
koyi'', Shi kuma matsayi da martabar wadda ake koyi da shi cikin duk ayyukansa,
da kuma cikin ''abin da ya sunnata shi'' ga musulmai: tafi martabar wadda ake
''bi'' a cikin abin da ya ''sunnata'' kawai)).
[Duba:
Majmu'u fatawa Ibni-taimiyyata, {4/p399].
Kuma shi wannan hadisin (3) na nuna cewa
ana umurni da a yi da'a wa Abubakar da Umar (r a), tare da rikonsu ''abun koyi
–qudwa-'' cikin ''abubuwan da kowannensu ya sunnata wa al'umma, dama daukacin
aiyukansa''; a yayin khalifancinsa. Haka kuma bayan rasuwarsu; Ta yadda idan
Abubakar da Umar su ka yi ''ittifaqi'' a tsakaninsu cikin mas'alolin addini; to
dole ne -da wannan hadisin- mu dauki wannan ''zancen''; don mu saka shi cikin
aiki. In kuwa aka samu banbancin fahimta tsakaninsu (Abubakar da Umar) to a nan
za a mayar da wannan sabanin izuwa ga Littafin Allah da sunnar Manzon Allah (s
a w); kana kuma a yi aiki da abin da dalilinsa su ka fi fitowa fili daga cikin
''zantuka biyun''. [Duba: ''Minhaju
as-sunnati, annabawiyyati'', [8/p364].
Don haka; matsayin Abubakar da Umar (r
a) a cikin addini –da wannan hadisin da kuma makamantansa-, tafi ta 'yan'uwansu
Usman da Aliyu (r a), ballantana kuma sauran sahabbai –Allah shi kara yardarsa
a gare su; Amin-.
WANNAN kuma shi ke nuna cewa: abin da
ake jingina shi izuwa ga manzon Allah (s a w) wai ya ce: (Sahabbaina kamar taurari
su ke; da kowanne daga cikinsu ku ka yi ''koyi'' to kun shiryu) = magana ne da
ta saba da hadisin ''nan''; da ya kebe Abubakar da Umar (r a) kan rikarsu
''qudwa -abun koyi-'', kuma maluma sun tattauna kansa su ka bayyana cewa:
Na farko: Maganar
cewa sahabbansa kamar taurari su ke; duk wadda aka yi aiki da ''maganarsa'', ko
kuma aka yi ''koyi'' da shi, … ko kuma daya lafazin da ya ce: Iyalaina
kamar taurari su ke; duk wadda ku ka rike shi ''qudwa –abun koyi'' = to kun
shiriya. Maganganu ne –na farko- da babu su cikin littatafan hadisi da ake
dogara da su ba. Ga wassu daga cikin laffuzansu cikin larabci:
1-
أصحابي مثل النجوم فأيهم أخذتم بقوله
اهتديتم.
2-
أصحابي بمنزلة النجوم فبأيهم اقتديتم
اهتديتم.
3-
أهل بيتي كالنجوم، بأيهم اقتديتم اهتديتم.
Na
biyu: A littatafan da aka kawo wadannan laffuzan, da
makamantansu: sun zo ne ta hanyoyi masu rauni; wadda haka yasa maluman
yankan-shakka su ka musu hukunci da kasancewa: maganganu ne masu rauni, [Duba:
raunatawar Imamu Ahmad a cikin: littafin/ ''almustadrak ala majmu'i alfatawa'',
{2/p121}, da Albazzaar, da kuma Ibnu-taimiyyata, a cikin: Littafin/ ''Minhaju as-sunnati, annabawiyyati'', {8/p364].
Hasali
ma wassu maluman sun yi hukunci a wannan maganan da cewa: maganar karya ce, [Ka
duba: Silsilatu al'ahadisi adda'ifati walmaudu'ati, na Albaniy, 1/ p144-153,
hadisai guda biyar, lamba: 58, 59, 60, 61, 62].
Na
uku: Dalili na gaba da ke nuna raunin wannan maganar: Shi ne cewa
da ta yi: Wai in an samu sabani tsakanin sahabbai a cikin mas'aloli, ko kuma
tsakanin ''ahlul-baiti''; wannan ya ce: ''kaza'', wancan kuma ya fadi
''kishiyarsa'': to wai kowanne mutum ya dauka ya dace da ''shiriya''. Wannan
kuma ya saba da karantarwar musulunci ta kowace fiska; don haka ''hadisin da ya
zo da wannan ma'anar, ba yadda za a yi ya zama ya inganta izuwa manzon Allah (s
a w).
Na
hudu: kuma na karshe: Wannan maganar ta saba wa fadin manzon Allah
(s a w) da ke kebe Abubakar da Umar (r a), da matsayin ''qudwa -abun koyi-''
cikin abin da suka ''sunnata wa mutane'', da kuma daukacin aiyukansu.
Amma dangane da yadda hadisin ke
nuni kan ''khalifancin Abubakar da Umar (r a) bayan manzon Allah (s a w) to shi
kuma saboda fadinsa:
"اللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي: أَبِي بَكْرٍ، وَعُمَرَ".
Kuma
lallai ''ishara'' kan khalifancinsu (r a) zai kara zuwa a cikin hadisai da su
ke tafe; da dama. Allah ya fahimtar da mu addininsa!
وأيضا فإذا كان الاقتداء بهما يوجب
الائتمام بهما فطاعة كل منهما إذا كان إماما وهذا هو المقصود، وأما بعد زوال إمامته
فالاقتداء بهما أنهما إذا تنازعا رد ما تنازعا فيه إلى الله والرسول.
وأما قوله: " «أصحابي كالنجوم فبأيهم اقتديتم اهتديتم»
"، فهذا الحديث ضعيف ضعفه أهل الحديث؛ قال البزار: هذا حديث لا يصح عن رسول الله
- صلى الله عليه وسلم -، وليس هو في كتب الحديث المعتمدة.
وأيضا فليس فيه لفظ (بعدي) والحجة هناك قوله (بعدي) .
وأيضا فليس فيه الأمر بالاقتداء بهم وهذا فيه الأمر بالاقتداء
بهم.
(منهاج السنة، ج8/ ص364).
قَالَ الشَّيْخُ الحسين البغوي تعليقا على حديث (وسنة
الخلفاء الراشدين): وَالْحَدِيثُ يَدُلُّ عَلَى تَفْضِيلِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ
عَلَى مَنْ سِوَاهُمْ مِنَ الصَّحَابَةِ، وَهُمْ: أَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ، وَعُثْمَانُ،
وَعَلِيٌّ، فَهَؤُلاءِ أَفْضَلُ النَّاسِ بَعْدَ النَّبِيِّينَ وَالْمُرْسَلِينَ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِمْ، وَتَرْتِيبُهُمْ فِي الْفَضْلِ، كَتَرْتِيبِهِمْ فِي الْخِلافَةِ،
فَأَفْضَلُهُمْ أَبُو بَكْرٍ، ثُمَّ عُمَرُ، ثُمَّ عُثْمَانُ، ثُمَّ عَلِيٌّ.
وَكَمَا خَصَّ
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَؤُلاءِ مِنْ بَيْنِ الصَّحَابَةِ بِاتِّبَاعِ
سُنَّتِهِمْ، فَقَدْ خَصَّ مِنْ بَيْنِهِمْ أَبَا بَكْرٍ، وَعُمَرَ فِي حَدِيثِ حُذَيْفَةَ
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: اقْتَدُوا بِاللَّذَيْنِ
مِنْ بَعْدِي: أَبِي بَكْرٍ، وَعُمَرَ ". شرح السنة للبغوي
(ج1/ص208).
قال ابن تيمية رحمه الله في منهاج
السنة (8/ص361):
الحجة في قوله: " «باللذين من بعدي»
" أخبر أنهما من بعده، وأمر بالاقتداء بهما فلو كانا ظالمين أو كافرين في كونهما
بعده لم يأمر بالاقتداء بهما فإنه لا يأمر بالاقتداء بالظالم، فإن الظالم لا يكون قدوة
يؤتم به بدليل قوله: {لا ينال عهدي الظالمين} [سورة البقرة: 124] فدل على أن الظالم
لا يؤتم به. والائتمام هو الاقتداء؛ فلما أمر بالاقتداء بمن بعده والاقتداء هو الائتمام
مع إخباره أنهما يكونان بعده دل على أنهما إمامان قد أمر بالائتمام بهما بعده، وهذا
هو المطلوب.
يقال: النص يوجب الاقتداء بهما فيما
اتفقا عليه وفيما اختلفا فيه فتسويغ كل منهما المصير إلى قول الآخر متفق عليه بينهما
فإنهما اتفقا على ذلك.
وأيضا فإذا كان الاقتداء بهما يوجب الائتمام
بهما فطاعة كل منهما إذا كان إماما وهذا هو المقصود، وأما بعد زوال إمامته فالاقتداء
بهما أنهما إذا تنازعا رد ما تنازعا فيه إلى الله والرسول.
وأما قوله: " «أصحابي كالنجوم فبأيهم
اقتديتم اهتديتم» "، فهذا الحديث ضعيف ضعفه أهل الحديث؛ قال البزار: هذا حديث لا يصح عن رسول الله
- صلى الله عليه وسلم -، وليس هو في كتب الحديث المعتمدة.
وأيضا فليس فيه لفظ (بعدي) والحجة هناك
قوله (بعدي) .
وأيضا فليس فيه الأمر بالاقتداء بهم
وهذا فيه الأمر بالاقتداء بهم.
(منهاج السنة، ج8/ ص364).
HADISAI HAMSIN (50) KAN KHALIFANCIN KHALIFOFIN
MANZON ALLAH (S A W) DA FALALOLINSU (5)
HADISI
(4): DAKE ALBISHIR KAN SAMUWAR ''KHALIFOFI GWOMA SHA BIYU''; WADANDA A
ZAMANINSU MUSULUNCI ZAI ZAMO MAI KARFI; MAI IZZA, DA KARIYA:
(a)
LAFAZIN
HADISIN DA RIWAYOYINSA:
الحديث الرابع: ذكر الخلفاء
الاثني عشر من قريش يكون الإسلام في عهدهم قويًّا؛ عزيزًا منيعًا:
في
الصحيحين عَنْ
جَابِرَ بْنِ سَمُرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صلى الله عليه
وسلم يَقُولُ:"يَكُونُ اثْنَا عَشَرَ أَمِيرًا" فَقَالَ كَلِمَةً
لَمْ أَسْمَعْهَا، فَقَالَ أَبِي: إِنَّهُ قَالَ:"كُلُّهُمْ مِنْ
قُرَيْشٍ".
وفي
لفظ عند مسلم: "إِنَّ هَذَا الأَمْرَ
لا يَنْقَضِي حَتَّى يَمْضِيَ فِيهِمِ اثْنَا عَشَرَ خَلِيفَة"، وفي آخر
عنده: "لا يَزَالُ الدِّينُ قَائِمًا
حَتَّى تَقُومَ السَّاعَةُ، أَوْ يَكُونَ عَلَيْكُمُ اثْنَا عَشَرَ خَلِيفَة كُلُّهُمْ مِنْ
قُرَيْشٍ"،
وفي آخر: "لا يَزَالُ هَذَا
الدِّينُ عَزِيزًا مَنِيعًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً"، وفي آخر: "لا يَزَالُ الإِسْلامُ عَزِيزًا
إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَة".
وعند أبي
داود زيادة هذا لفظها: "كُلُّهُمْ تَجْتَمِعُ عَلَيْهِ الأُمَّة".
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya
zo a cikin sahihu al-bukhariy da muslim daga Jabir bn Samurata (ra),
ya ce: Na ji annabi (saw) yana cewa: "Amir-na-dukan-amir'' guda
goma sha biyu za su kasace. Sai annabi (saw) ya fadi wata kalma da ban ji ta
ba, Sai babana ya ce: Dukkansu daga kabilar quraishawa su ke.
A
wani lafazi –a wajen Imam Muslim-: Lallai ''wannan lamari'' ba zai shige ba;
har sai khalifa guda goma sha biyu sun samu a cikinsu.
A
wani lafazin kuma –a wajensa-: Addini ba zai gushe ba yana mike; har a yi
''kiyama'', ko kuma a samu khalifofi goma sha biyu; dukkansu daga quraishawa.
A
wani kuma: Wannan addini ba zai gushe ba yana da ''izza, da kuma kariya'' izuwa
khalifofi guda goma sha biyu.
A
wani kuma: Musulunci ba zai gushe ba ''yana da izza'' har izuwa khalifofi goma
sha biyu.
Amma
a lafazin Abu-dawud kuma akwai wannan karin lafazi da ke tafe: ((Dukkansu
al'umma za ta hadu akansu)).
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SU KA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Wannan hadisin maluman sunna da dama sun
ruwaito shi a cikin littatafansu, daga cikinsu; akwai: Imam Al-bukhariy a cikin
''sahihinsa'', [lamba: 7222], da Muslim a ''sahihinsa'' [lamaba: 1821].
Kana kuma Abu-dawud a cikin littafinsa
''as-sunan'' ya ruwaito shi da karin ''lafazi'' –kamar yadda ya gabata- [lamba:
4279].
Sai dai kuma ''Wassu maluma'' sun raunata
''isnadin'' wannan kari da ya zo ta hanyar Abu-dawud.
[Ka duba: littafin ''silsilatu al-ahadisi as- sahihati'' na
Albaniy, -1/ p720- a ''takhrijinsa'' ga hadisi mai 376].
(d)
MA'ANAR
WANNAN HADISI, TARE DA AMBATO RA'AYOYI BIYU NA MALUMAN ''SUNNA'' WAJEN FASSARA
SHI:
Lallai
wannan hadisin ya yi ''albishir'' kan kasancewar khalifofi guda goma sha biyu a
cikin wannan al'umma, Sai dai kuma shi hadisin –da dukkan riwayoyinsa- bai
ambaci khalifofin da sunansu ba, kamar yadda kuma bai fito bolo-bolo, ya yi
bayanin shin wadannan khalifofin a jejjere zamaninsu ya ke, ko kuma wassunsu za
su zo a lokuta mabanbanta? Wannan yasa aka samu banbancin ra'ayi wajen fahimtar
hadisin ta ''fiskoki biyun'' a wajen maluman ''Ahlus-sunnah''.
Tare
da cewa hadisin ya ambaci sifofi da yawa; ta fiskar adadin wadannan khalifofi,
da kuma halin da musulunci zai samu kansa na karfi da daukaka, a
zamaninnikansu, da kuma haduwan galibin mutane akan yi musu mubaya'a da da'a;
kamar haka:
1-
Yawan khalifofi da
musulunci zai siffanta da siffofi masu zuwa a zamaninsu su guda goma sha biyu
ne.
2-
Dukkansu daga kabilar
quraishawa su ke, ba daga wassunta ba.
3-
Al'umma gaba-dayanta zata
hadu akansu, ko kuma dai a ce: mafi rinjayen gaske daga cikinsu.
4-
Musulunci –a zamaninsu ba
zai gushe ba yana tsayeyye, mai kuma yaduwa da karfi, izza da buwaya, kana makiyin
musulunci kuma na wadda aka rinjaye shi; na cikin tsoron islam; baya kwadayin
samun wani abu a cikinsa ballentana ya yi tunanin tinkararsa, jihadi na tsaye,
gaskiya kuma na bayyane; kana tana sane, al'amarin musulmai shi ke gudana.
Wadannan sune muhimman sifofi dangane da
su wadannan khalifofi guda goma sha biyu, da kuma zamaninsu.
Kuma kamar yadda manzon Allah (saw) ya
yi albishir kan zuwan khalifofin nan -a cikin wannan hadisin-, to hakika Allah
ta'ala shima da kansa ya saukar da ''bishara'' akansu -a cikin attaura-; a
yayin da ya ke bishara da samuwar annabi Isma'ila (as), ya tabbatar da cewa,
daga tsatsonsa za a samu manyan mutane guda goma sha biyu, kamar yadda zai zo:
Babban malami ''Imadu ad-dini
Al-hafiz Ibnu Kasir'' yana cewa:
«وَمَعْنَى هَذَا الْحَدِيثِ: الْبِشَارَةُ بِوُجُودِ اثْنَيْ
عَشَرَ خَلِيفَةً صَالِحًا يُقِيمُ الْحَقَّ وَيَعْدِلُ فِيهِمْ»([1]).
Ma'ana:
((Ma'anan wannan hadisin shi ne: albishir ne kan samuwar khalifofi guda goma
sha biyu; salihai, da za su tsayar da gaskiya a cikin mutane, su kuma yi adalci
a cikinsu).
[Duba:
''Tafsiru alqur'ani al'azimi'', v2/ p47].
Haka shima ''Ibnu-taimiyyata'' yana cewa:
«وَهَؤُلاءِ الاثْنَا عَشَرَ خَلِيفَةً هُمُ الْمَذْكُورُونَ
فِي التَّوْرَاةِ; حَيْثُ قَالَ فِي بِشَارَتِهِ بِإِسْمَاعِيلَ: "وَسَيَلِدُ
اثْنَيْ عَشَرَ عَظِيمًا».
Ma'ana:
(Wadannan khalifofi guda goma sha biyu su ne aka ambace su a cikin ''attaura''
a inda ake cewa dangane da bishara da aka yi da annabi Isma'il –as-: Kuma zai
haifi manyan mutane goma sha biyu).
[Duba:
littafin ''Minhaju as-sunnati annabawiyyati'', v8/p241].
Amma
dangane da wai shin wadannan khalifofin a jere su ke ko kuma sun kasance ko
za su kasance a lokuta mabanbanta?
A
nan zan fara kawo ra'ayin farko da ke nuna cewa: ba dole ne zamanin wa'yannan
khalifofi ya zama a jere ba; maluman da su ke
da wannan ra'ayin su ne:
1-
Abu-dawud a cikin
littafinsa ''as-sunan'', ta yadda ya kulla wani littafi da ya masa taken
''littafi da ke magana akan mahdiy'', a karshensa kuma ya ce: ''karshen
littafin mahdiy [Duba: 1832-1840 a cikin: aunu alma'abudi]''. Ya kuma ambaci
babi guda a cikin wannan littafi, ya kunsa hadisai guda goma sha uku a cikin
wannan littafi, ya fara ambaton hadisin ''Jabir bn Samurata'', wadda ya ke
cewa: Na ji manzon Allah (saw) yana cewa:
"لا يزال
هذا الدين قائما
حتى يكون عليكم إثنا عشر خليفة..." الحديث.
Malamin musulunci mai suna Abdurrahman jalalu
addini Assuyudiy yana cewa a karshen littafinsa ''al'arfu alwardiy fiy akhbari
almahdiy, [p155-156]'':
(إن
في ذلك إشارة إلى ما قاله العلماء أن المهدي أحد الإثنى عشر).
Ma'ana:
(Lallai ambaton wannan hadisin –da ke albishir kan zuwan khalfifo guda goma sha
biyu wadanda a zamaninsu musulunci ba zai gushe yana da izza ba- a cikin
littafin da ke magana kan: mahdiy, Ishara ce izuwa abin da maluma su ka fada na
cewa: MAHDIY DAYA NE DAGA CIKIN WA'YANNAN KHALIFOFI GOMA SHA BIYU''.
[Duba:
littafin shehinmu; Abdulmuhsin al-abbad, mai taken: akidatu ahlis-sunna wal
asar, fiy almahdiy almuntazar, p133-134 ].
2-
Malami na biyu da ya
bayyana wannan ra'ayi shi ne: Alhafiz Ibnu-Kasir a cikin ''tafsirinsa''
[v2/p47]. A inda ya ke cewa:
«وَمَعْنَى هَذَا الْحَدِيثِ: الْبِشَارَةُ بِوُجُودِ اثْنَيْ
عَشَرَ خَلِيفَةً صَالِحًا يُقِيمُ الْحَقَّ وَيَعْدِلُ فِيهِمْ، وَلا يَلْزَمُ مِنْ
هَذَا تَوَالِيهِمْ وَتَتَابُعُ أَيَّامِهِمْ، بَلْ قَدْ وُجِدَ مِنْهُمْ أَرْبَعَةٌ
عَلَى نَسَق، وَهُمُ الْخُلَفَاءُ الأَرْبَعَةُ: أَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ، وَعُثْمَانُ،
وَعَلِيٌّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ، وَمِنْهُمْ: عُمَرُ بْنُ عَبْدِ الْعَزِيزِ بِلا
شَكٍّ عِنْدَ الأَئِمَّةِ، وَبَعْضُ بَنِي الْعَبَّاسِ. وَلا تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى
تكون ولايتهم لا محالة. والظاهر أن مِنْهُمُ: الْمَهْدِيُّ الْمُبَشَّرُ بِهِ فِي الأَحَادِيثِ
الْوَارِدَةِ بِذِكْرِهِ: أَنَّهُ يُواطئُ اسمُه اسْمَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ، وَاسْمُ أَبِيهِ اسْمَ أَبِيهِ، فَيَمْلأُ الأَرْضَ عدْلا وقِسْطًا، كَمَا
مُلِئَتْ جَوْرا وظُلْمًا».
Ma'ana: ((Ma'anar wannan hadisin shine:
bishara ne kan zuwan khalifofi goma sha biyu; salihai, da za su tsayar da
gaskiya, da adalci a cikinsu. Kuma ba dole ne wa'yannan khalifofin su kasance a
jere ba, hasali ma an samu mutum hudu daga cikinsu a jeren; wadanda kuma su ne;
khalifofi guda hudu; Abubakar, Umar, Usman, da Aliyu –r a-. Kana kuma a cikinsu
akwai: Umar bn Abdul'aziz, ba tare da shakka ba –a wajen maluma, da sashin
khalifofi a daular abbasiyya. Kiyama ba zata tsaya face khalifancinsu
–khalifofi 12- ya kasance; ba makawa. Kuma a zahiri: Mahdiy da aka yi albishir
da zuwansa a cikin hadisai masu yawa; wadda kuma daga cikin sifofinsa akwai
cewa: sunansa yana daidai da sunan annabi –saw-, sunan babansa yana daidai da
sunan baban annabi, zai cika duniya da adalci, kamar yadda ta cika da zalunci,
Ga zahiri wannan bawan Allah yana daga cikin khalifofin goma sha biyun)).
Wadannan
wassu ne daga cikin jiga-jigan maluman da su ke da ra'ayin cewa; ba dole
zamanin khalifofin goma sha biyu ya zama a jere ba. Wannan dai it ace fahimtarsu; sai dai kuma
bas hi ne fahimta da ked a goyon baya ta fiskar dalilai ba; kamar yadda bayani
akan haka ke tafe.
Fahimta
ta biyu da ke nuna cewa; zamanin khalifofi goma sha biyu -da aka yi albishir da
zuwansu- a jere ya ke, tare da Ambato wassu daga cikin maluman da su ka yi
bayani akan haka:
Kadan daga
cikin maluman da su ka tabbatar da wannan fassara:
1- Shekhul
islam ibnu taimiyyata: Yana cewa a cikin littafinsa: ''minhaju
as-sunnati annabawiyyati'' [v8/p242]:
«الاثْنَا
عَشَرَ: هُمْ الَّذِينَ وُلُّوا عَلَى الأُمَّةِ مِنْ قُرَيْشٍ وِلايَةً عَامَّةً،
فَكَانَ الْإِسْلامُ فِي زَمَنِهِمْ عَزِيزًا، وَهَذَا مَعْرُوفٌ».
Ma'ana: (Mutum goma sha biyu su ne: wa'yanda
su ka yi ''wilaya a-mmah; wato: khalifanci gamemme'', kuma ya musulunci ya
zamto mai izza a zamaninsu. Wannan kuma abu ne sanan ne).
Ya kuma fadada magana akan haka a wani wuri; a
inda ya ke cewa:
«...
وَفِي لَفْظٍ: لا يَزَالُ الإِسْلامُ عَزِيزًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً كُلُّهُمْ
مِنْ قُرَيْشٍ. وَهَكَذَا كَانَ، فَكَانَ الْخُلَفَاءُ: أَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ، وَعُثْمَانُ،
وَعَلِيٌّ، ثُمَّ تَوَلَّى مَنِ اجْتَمَعَ النَّاسُ عَلَيْهِ وَصَارَ لَهُ عِزٌّ وَمَنَعَةٌ:
مُعَاوِيَةُ، وَابْنُهُ يَزِيدُ، ثُمَّ عَبْدُ الْمَلِكِ وَأَوْلَادُهُ الْأَرْبَعَةُ،
وَبَيْنَهُمْ عُمَرُ بْنُ عَبْدِ الْعَزِيزِ. وَبَعْدَ ذَلِكَ حَصَلَ فِي دَوْلَةِ
الْإِسْلَامِ مِنَ النَّقْصِ مَا هُوَ بَاقٍ إِلَى الْآنَ ; فَإِنَّ بَنِي أُمَيَّةَ
تَوَلَّوْا عَلَى جَمِيعِ أَرْضِ الْإِسْلَامِ، وَكَانَتِ الدَّوْلَةُ فِي زَمَنِهِمْ
عَزِيزَةً، وَالْخَلِيفَةُ يُدْعَى بِاسْمِهِ: عَبْدَ الْمَلِكِ، وَسُلَيْمَانَ، لَا
يَعْرِفُونَ عَضُدَ الدَّوْلَةِ، وَلَا عِزَّ الدِّينِ، وَبَهَاءَ الدِّينِ، وَفُلانَ
الدِّينِ، وَكَانَ أَحَدُهُمْ هُوَ الَّذِي يُصَلِّي بِالنَّاسِ الصَّلَوَاتِ الْخَمْسَ،
وَفِي الْمَسْجِدِ يَعْقِدُ الرَّايَاتِ، وَيُؤَمِّرُ الأُمَرَاءَ، وَإِنَّمَا يَسْكُنُ
دَارَهُ، لا يَسْكُنُونَ الْحُصُونَ، وَلا يَحْتَجِبُونَ عَنْ الرَّعِيَّةِ». (قاله في كتابه: منهاج السنة
النبوية: (ج8/238).
Ma'ana: (… A wani lafazin: ''Musulunci ba zai
gushe ba yana mai izza izuwa khalifofi goma sha biyu; dukkaninsu suna daga
quraishawa'', kuma haka lamarin ya kasance; ta yadda aka samu khalifofi;
Abubakar, Umar, Usman da Aliyu, kana kuma aka samu wadda dukkan mutane su ka
hadu wajen yi masa mubaya'a; ya zamto yana da izza da buwaya; wato Mu'awiyatu,
kana 'dansa Yazidu, sa'annan sai Abdulmalik, da kuma 'ya'yansa guda hudu, A
tsakaninsu kuma aka samu Umar bn Abdul'aziz.
To kuma bayan wadannan ne gaba-daya aka fara samun nakasa a cikin daular
musulunci, wadda hakan ya wanzu har izuwa yau; saboda ''banu-umaiyata'' sun yi
shugabancinsu ne ga duniyar musulunci (ba ga wata kasa kawai ba), kuma daula –a
zamaninsu- ta kasance tana da izza, shi kuma ''khalifa'' ana kiransa da
sunansa; kamar a ce: Abdulmalik, da Sulaiman, Ba su san a kira su da ''Adudi-addini, ko Izzu-addini, ko
Baha'u-addini, ko wanen addini'' ba, -ma'ana sunaye da ke nuna: kwarzantawa;
mai karfafa addini, mai cicciba addini- A wancan lokacin dayansu ya kasance shi
ke limancin salla ga mutane, kuma daga masallaci ya ke tura bataliya, ya nada
gwamnoni, kuma a gidajensu su ke zaune; ba a wani makareren gida da aka
ganuwance shi ba; don haka basu kasance suna buya ga talakawansu ba).
2- Alhafiz
Ibnu-hajar a sharhi da yayi ga wannan hadisin shima ya tabbatar da cewa su
wa'yannan khalifofi a jere su ke, kamar yadda ya ce:
«جميع من ولي الخلافة من الصديق إلى عمر بن عبد العزيز أربعة عشر
نفسًا، منهم اثنان لم تصح ولايتهما ولم تطل مدتهما، وهما: معاوية بن يزيد، ومروان
بن الحكم، والباقون اثنا عشر نفسًا على الوَلاء، كما أخبر r، وكانت
وفاة عمر بن عبد العزيز سنة إحدى ومائة، وتغيرت الأحوال بعده، وانقضى القرن الأول
الذي هو خير القرون، ولا يقدح في ذلك قوله (يجتمع عليهم الناس) لأنه يحمل
على الأكثر الأغلب؛ لأنّ هذه الصفة لم تفقد منهم... وكانت الأمور في غالب أزمنة
هؤلاء الاثني عشر منتظمة، وإنْ وُجد في بعض مدتهم خلاف ذلك فهو بالنسبة إلى الاستقامة
نادرٌ، والله أعلم»([2]).
Ma'ana: ('Daukaci wadanda su ka yi
khalifan tun daga zamanin Abubakar as-siddiq, izuwa Umar bn Abdul'aziz rai goma
sha hudu ne, daga cikinsu akwai mutum mutum biyu; wadda khalifancinsu bai
inganta ba, kana kuma zamaninsu bai yi tsayi ba; wadannan kuma su ne:
Mu'awiyatu bn Yazid, da Marwan bn Alhakam. Su kuma sauran goma sha biyun sun
kasance a jere; kamar yadda annabi –s a w- ya bada labara. Kuma wafatin Umar bn
Abdil'aziz ya kasance a shekara ta dari da daya (101h). Sai lamura su ka
jirkita a bayansa. Kuma ''karnin farko'' wadda wadda kuma shi ne mafi alherin
''karnuka'' sai ya kare. Kuma riwayar da ta nuna cewa: ''dukkaninsu mutane za
su hadu wajen yi musu bai'a ko da'a'' bata yin su ka ga wannan hadisi; saboda
ana daukar wannan ''hadisi'' ga abin da ya fi yawa kuma shine galibi; saboda ba
a rasa wannan ''sifar'' ba a cikinsu. … Kuma lamura sun kasance a lokacin
khalifanci wa'yannan mutum sha-biyu suna tafiya akan turba; ba matsala. Kuma
koda cewa an samu wa'yansu abubuwan sun tafi akan sabanin yadda ake so; to sai
dai: haka din dan kadan ne. wallahu a'alam!). [Fat'hul bariy:
v13/p265].
Bayan kuma
ya ambaci ''hanyoyi da wannan hadisin yazo'' ya kuma ambaci maganar malami mai
suna ibnu-aljauziy, da kuma alkhaddabiy sai ya ce:
«وينتظم من مجموع ما ذكراه أوجه، أرجحها الثالث من أوجه القاضي؛
لتأييده بقوله في بعض طرق الحديث الصحيحة (كلهم يجتمع عليه الناس)، وإيضاح
ذلك: أنَّ المراد انقيادهم لبيعته، والذي وقع أنّ الناس اجتمعوا على أبي بكر ثم
عمر ثم عثمان ثم عليّ إلى أنْ وقع أمر الحكمين في صفين، فسُمِّي معاوية يومئذ
بالخلافة، ثم اجتمع الناس على معاوية عند صلح الحسن، ثم اجتمعوا على ولده يزيد،
ولم ينتظم للحسين أمرٌ بل قتل قبل ذلك، ثم لما مات يزيد وقع الاختلاف إلى أن
اجتمعوا على عبد الملك بن مروان بعد قتل ابن الزبير، ثم اجتمعوا على أولاده
الأربعة: الوليد، ثم سليمان، ثم يزيد، ثم هشام، وتخلل بين سليمان ويزيد عمر بن عبد
العزيز؛ فهؤلاء سبعة بعد الخلفاء الراشدين، والثاني عشر هو الوليد بن يزيد بن عبد
الملك اجتمع الناس عليه لما مات عليه عمُّه هشام؛ فولِي نحو أربع سنينن ثم قاموا
عليه فقتلوه، وانتشرت الفتن وتغيرت الأحوال من يومئذ، ولم يتفق أنْ يجتمع الناس
على خليفة بعد ذلك؛ لأنّ يزيد بن الوليد الذي قام على ابن عمه الوليد بن يزيد لم
تطل مدته، بل ثار عليه قبل أنْ يموت ابنُ عم أبيه مروان بن محمد بن مروان. ولما
مات يزيد ولي أخوه إبراهيم فغلبه مروان، ثم ثار على مروان بنو العباس إلى أنْ قتل،
ثم كان أول خلفاء بني العباس أبو العباس السفاح، ولم تطل مدته مع كثرة مَن ثار
عليه، ثم ولي أخوه المنصور فطالت مدته، لكن خرج عنهم المغرب الأقصى باستيلاء
المروانيين على الأندلس، واستمرت في أيديهم متغلبين عليها ... وانفرط الأمر في
جميع أقطار الأرض إلى أنْ لم يبقَ من الخلافة إلا الاسم في بعض البلاد بعد أن كانوا في أيام بني عبد الملك
بن مروان يخطب للخليفة في جميع أقطار الأرض شرقا وغربا وشمالا ويمينا مما غلب عليه
المسلمون، ولا يتولى أحد في بلد من البلاد كلها الإمارة على شيء منها إلا بأمر الخليفة.
ومَن نظر في أخبارهم عرف صحة ذلك! فعلى هذا؛ يكون المراد بقوله: (ثم يكون الهرج)
يعني: القتل الناشئ عن الفتن وقوعا فاشيا؛ يفشو ويستمر ويزداد على مدى الأيام، وكذا
كان. والله المستعان!»
(فتح
الباري، ج13/ص263-264).
Ma'ana: (Kan an tattara duk abubuwan da
su ka fada to za a samu fiskoki da yawa; sai dai kuma fiskar da tafi rinjaye
daga cikinsu: itace fiska ta uku; daga cikin fiskokin da ''Alkali Iyadh'' ya
ambata; saboda ya karfafe shi da wani abin da ya zo a cikin sashin hanyoyin
hadisin ingancecce: ''Dukkansu mutane zasu hadu akansu''; Bayani akan haka kuma
shi ne: Lallai manufar wannan shi ne: zasu mika wuya kan ''mubaya'a da aka yi
musu''; kuma abun da ya auku shi ne: Lallai mutane sun hadu kwansu-da
kwarkwatarsu akan Abubakar, kana kuma Umar, kana kuma Usman,
kana kuma Aliyu, har izuwa lokacin da lamarin alkalancin mutum biyu
''bayan yakin siffin'', sai a wannan yinin aka kira Mu'awuyatu da khalifanci,
kana kuma daga baya mutane gaba-dayansu su ka yi ijma'i kan yin mubaya'a wa
sahabi Mu'awuyatu; a lokacin da sahabi Alhasan ya yi sulhu da shi.
Sa'annan sai su ka hadu kan dansa Yazid, Shi kuma sahabi Alhusain
khalifanci bai kasance masa ba; hasali ma an kashe shi gabanin haka. Sa'annan
bayan mutuwar Yazidu sai sabani ya kasance; izuwa haduwan mutane kan mika-wuya
ga Abdulmalik bn Marwan bayan kashe sahabi Abdullahi bn
Az-zubairu, sa'annan kuma mutane su ka mika-wuya ga: 'ya'yansa guda hudu;
wato: Alwalid, sa'annan Sulaiman, sa'annan Yazid, sa'annan
kuma Hisham. Kuma a tsakanin Sulaiman da Yazidu ne aka samu khalifancin Umar
bn Abdil'aziz, Wadannan su ne mutum bakwai bayan khalifofi shiryeyyu guda
hudu. Na goma sha biyunsu shi ne: Walid bn Yazid bn Abdulmalik; mutane
sun mika masa wuya yayin da baffansa Hisham ya mutu; sai ya yi shugabanci na
tsawon shekara hudu; sa'annan su ka masa zanga-zanga su ka kashe shi. To daga
nan kuma sai fitina ta yadu, duk halaye su ka canza daga wannan lokaci, wannan
yasa daga nan kuma ba a sake haduwa kan khalifa guda daya ba bayan haka; saboda
''Yazid bn Alwalid'' wadda ya yi fito-na-fito wa dan baffansa ''Al-walid bn
Yazid'' zamaninsa bai yi tsayi ba; hasali ma kafin ya mutu dan baffan ubansa ne
mai suna: ''Marwan bn Muhammad bn Marwan'' ya yi fito-na-fito da shi, A yayin
da kuma ''Yazidu bn Alwalid'' ya mutu kuma sai shi dan'uwansa ''Ibrahim'' ya
zama shugaba, wadda kuma shi ''Marwan'' bai bar shi ba; sai ya kwace masa,
Sa'annan sai ''daular Abbasiyyah'' su ka yi –fito-na-fito da shi; har izuwa
lokacin da suka kashe shi; su ka kwace khalifanci; Wannan yasa farkon
khalifofin ''daular Abbasiyyah'' ya zama wadda ake masa alkunya da lakabi da
''Abu-al'abbas As-saffah –wato mai yawan zubar da jini''; shima kuma lokacinsa
bai yi tsayi ba, tare da yawaitar wadanda su ka yi fito-na-fito da shi,
Sa'annan sai dan'uwansa da ake kira: ''Almansuur'' ya zama khalifa; zamaninsa
kuma ya yi tsayi; Sai dai kuma bangaren da ake kiransa ''almagrib al'aqsah'' ya
balle masa; a lokacin da ''Iyalen Marwan'' su ka kwace yankin ''Andalus'' kuma
yankin ya ci gaba da zama a hanunsu; suna masu mulkarsa, wadanda kuma su ka yi
rinjaye akansa … Daga nan dai lamarin ''khalifancin musulunci'' ya yi ta
tasgarewa yana rugujewa a duniya, har ya zama dai abin da ya rage wa
''khalifanci'' a masarautu da yawa shi ne sunansa, a kuma sasani duniya da
yawa. BAYAN DA KHALIFA YA KASANCE A LOKACIN ''YAYAN ABDULMALIK BN MARWAN;
-DAULAR UMAWIYYATU- A DUKKAN DUNIYAR DA MUSULMI SUKA BUDE; GABAS DA YAMMA, KUDU
DA AREWA, ANA YIN HUDUBA NE WA KHALIFA GUDA TAK, KUMA WANI MUTUM BA ZAI ZAMA
GWAMNAN YANKI DAGA CIKIN YANKUNA BA SAI DA UMURNIN KHALIFA. DON HAKA; Duk mutumin day a yi nazari cikin
tarihin ''daula umawiyya'' to zai tabbatar da gaskiyar haka.
Kuma
akan haka ne ma'anan fadin annabi –s a w-:
"ثم يكون الهرج يعني:
القتل".
Zai
kasance: -Sa'annan bayan khalifofi guda goma sha biyun sun shude, Sai
kashe-kashe ya kasance-. Ma'ana kashe-kashen da fitintunu su ka haifar da shi;
ta yadda zai yadu matuka, ya kuma ci gaba yana mai karuwa gwargwadon tafiyan
zamani. Kuma haka lamarin ya yi ta kasancewa kuma yak e kasancewa. Wallahu
almusta'an).
[Duba: littafin fat'hul bariy
na Ibnu-hajar, v13/p263-264].
Wadda ya
fahimci karatun nan da kyau: zai hakiki ce gaskiyar Manzon Allah (s a w) da ya
bayyana cewa za a samu khalifofi guda goma sha biyu (12) wadanda musulunci ba
zai gushe ba a zamaninsu yana mai karfi, izza da buwaya, kana kuma madaukaki…
Yayin da kuma bayan shudewar wadannan khalifofin musulunci zai yi ta yin rauni,
izzarsa tana komawa baya, kwar-jininsa yana zagwanyewa, kafirai basa jin
tsoronsa.
Kuma
wannan shi ke nuna cewa ''maganar da ta gabata'' wadda Alhafiz ''Ibnu-kasir''
ya karfafe ta: ta zama bata da karfi; saboda manzon Allah (s a w) ya fada a
cikin hadisin cewa:
«لا يَزَالُ الإِسْلامُ
عَزِيزًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً كُلُّهُمْ مِنْ قُرَيْشٍ»
Ma'ana:
''Musulunci ba zai gushe ba yana da karfi da izza a zamanin khalifofi guda
goma-sha-biyu''; Ka ga anan duk wadda ya ce wadannan
khalifofin ba dole ne su zamto a jere ba, ko ya ce: wani daga cikinsu zai iya
ksancewa a karshen zamani (duniya); kamar Almahdiy: to maganarsa tana hukunta
ya ce: a wannan zamani namu da wadda ke gabaninsa musulunci yana da karfi, izza
da buwayar addinan da ba shi (yahudanci, nasaranci da sauranci). Wadda kuma
lamarin ba haka ya ke ba; saboda fadin:
«لا يَزَالُ...»
A cikin
hadisin; da take nuna cewa: Sifar
daukakar musulunci ba za ta gushe ba a khalifancin mutane goma sha biyu. Bayan
shudewarsu kuma sai ta gushe a khalifancin wassunsu da sannu-sannu. Wannan kuma
shi yasa ''Ibnu-taimiyyata'' y ace:
«وَهَذَا
يَدُلُّ عَلَى أَنَّهُ يَكُونُ أَمْرُ الإِسْلامِ قَائِمًا فِي زَمَانِ وِلايَتِهِمْ،
وَلا يَكُونُ قَائِمًا إِذَا انْقَطَعَتْ وِلايَتُهُمْ». (قاله في كتابه: منهاج
السنة النبوية: (ج8/ ص253).
Ma'ana:
(Wannan hadisin na nuna cewa ''al'amarin musulunci'' zai kasance tsayeyye, da
karfi a lokacin, khalifancinsu. Ba zai kuma kasance tsayeyye bayan yankewar
khalifancin nasu) [Duba: ''Minhaju assunnati'' v8/ p253]. Wallahu ta'ala a'alamu!
HADISAI HAMSIN (50) KAN KHALIFANCIN KHALIFOFIN MANZON ALLAH (S A W) DA FALALOLINSU
(6)
HADISI
(4): DAKE ALBISHIR KAN SAMUWAR ''KHALIFOFI (12) ''; WADANDA A ZAMANINSU
MUSULUNCI ZAI ZAMO MAI KARFI; MAI IZZA,
DA KARIYA:
…
(ci
gaba)
(e)
MUHIMMAN
LAMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN ''KHALIFOFIN ANNABI (SAW) SHIRYEYYU'' WADDA
SUKE NUNA IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YADUWARSA:
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai!
Idan
ba a manta ba Hadisinmu da ya gabata ya nuna cewa a tsawon khalifancin halifofi
guda goma sha biyu (12) musulunci ba zai gushe ba yana madaukaki mai izza,
kamar yadda wannan lafazin ke nunawa:
"لا يَزَالُ
هَذَا الدِّينُ عَزِيزًا مَنِيعًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً".
Sananne
ne cewa musulunci ya fara yana karami mai rauni, kana kuma bako, wannan kuma a
fili ya ke idan muka duba rayuwar manzon Allah (SAW) ta Makka; wadda tsananin
yanayin da su ka samu kansu a cikinsa yasa manzon Allah (SAW) ya yi izini wa
sahabbansa da cewa su yi hijira izuwa ''Habasha'', hijirar habashan kuma ta
kasance har sau biyu. Sa'annan sai annabi (SAW) da sahabbai su ka yi hijira
izuwa garin Madina. Alhafiz Ibnu-rajab yana cewa a cikin littafinsa ''kashfu
alkurbati fi wasfi ahli algurbati'':
(ثم ظهر الإسلام بعد الهجرة إلى المدينة وعز وصار أهله ظاهرين كل
الظهور، ودخل الناس بعد ذلك في دين الله أفواجا، وأكمل الله لهم الدين وأتم عليهم
النعمة. وتوفي رسول الله صلى الله عليه وسلم والأمر على ذلك، وأهل الإسلام على غاية
من الاستقامة في دينهم، وهم متعاضدون متناصرون، وكانوا على ذلك في زمن أبي بكر وعمر
رضي الله عنهما).
Ma'ana: (Sa'annan sai musulunci ya bayyana
bayan hijira izuwa madina, ya kuma samu izza, kana kuma ma'abutansa su ka zama
madaukaka iya daukaka, lamarinsu kuma a bayyane iya bayyana. Mutane kuma su ka
shiga cikin addinin Allah jama'a jama'a, Allah kuma ya cika mu su addini, kana
kuma ya cika musu ni'imarsa. Manzon Allah -SAW- ya rasu lamarin yana nan akan
haka –madaukaki-; ta yadda ma'abuta musulunci sun kai makura wajen tsayuwa akan
mikakken addininsu, suna masu taimakekkeniya a tsakaninsu –tsintsiya madaurinki
daya-. Kuma akan haka su ka kasance a lokacin khalifancin Abubakar da Umar
–RA-).
Kamar
yadda musulunci ya ke da izza da daukaka a rayuwar manzon Allah (SAW); ta
madina, haka kuma lamarin ya ci gaba da kasancewa a khalifancin khalifofin da
su ka biyo bayansa 12, duk da cewa abin ya fara yin baya-baya; Wannan ma'anar
kuma itace hadisin ''musulunci ba zai gushe ba yana madaukaki mai izza izuwa
khalifofi 12 daga kuraishawa…''. Don fito da wannan ma'anar fili, tare da
Ambato yadda musulunci ya yi ta bunkasa yana yaduwa; musamman a zamanin
khalifofi guda hudu (4) na farko: zan koro bayanai da ke tafe:
NA
FARKO: Muhimman abubuwan da su ka faru a zamanin khalifar manzon Allah
(SAW); Abubakar (RA) masu nuna izzar musulunci da yaduwarsa:
1-
Mai bibiyan ''tarihin
musulunci'' zai ga cewa gabanin rasuwar manzon Allah (SAW) da wani lokaci da
bashi da tsayi an samu wassu sun fito suna da'awar ''annabta'', kuma lallai
annabi (SAW) ya karyata su kana kuma ya fara tattaunawa da sashinsu kamar
''Musailimatu'' ta hanyar tura masa wasika, Daga cikin wadanda su ka yi da'awar
''annabtan'' akwai:
a- Wadda
ya shahara da ''al'aswad al'ansiy'' wadda kuma shine mutane da dama na
kasar "Yemen'' su ka yi ridda kana su ka bi shi.
b- Da
kuma ''Dulaihatu bn Khuwailid al'asadiy'' wadda daga baya ya sake komowa
cikin musulunci, amma gabanin haka; lokacin da ''Uyainatu bn Hisn'' ya yi
ridda; ya tsaya sosai wajen taimaka wa ''Dulaihatu'' akan da'awarsa ta
''annabta'', har ma ya jagorancin mutanensa ''banu-fazaarata'' izuwa goya masa
baya.
c- Da
kuma "Musailimatu alkazzaab'' wadda shi ya jagoranci
''banu-hanifata'' kan riddarsu. Da sauransu.
kamar yadda
kuma an samu ''ridda'' da kuma ficewa daga cikin musulunci da ga wajen mutane
da yawan gaske bayan rasuwar tasa (manzon Allah -SAW), don haka; ''kabilar
asad da gadfana'' sun yi ridda, haka ''kabilar kindah da masu biye mata'',
da ''kabilar mizhaj da masu biye mata'', da ''Banu-hanifata'', da
''kabilar sulaim'', da ''Banu-tamim'', da sauransu. Kai! Kabilun
da su ka yi ridda suna da yawa, harma tarihin ya tabbatar da cewa: a wancan
lokacin garurrukan da ake sallar juma'a a masallatansu guda uku ne kacal;
Makka, Madina, sai kuma wani kauye da ake kiransa ''Juwasa''.
Ta gefe
guda kuma akwai wadanda su ka hana zakka, wassunsu suna ganin cewa ga annabi
(SAW) ne kawai ake bada ita.
Yana daga
cikin manya-manyan abubuwan da khalifan manzo; Abubakar ya yi a wancan lokacin,
wadda kuma hakan ya sake dawo da mutane cikin ''kewayen musulunci'' daura damarar
yaki da dukkan wa'yancan bangarori da su ka yi ridda ta fiskoki mabanbanta, kai
dama aiwatar da yakin a aikace, kuma Allah ta'alah ya bashi nasarar gaske kan
hakan; ta yadda ya dauki tutar yakar:
a-
Mai da'awar annabta
''Dulaihatu al'asadiy'' ya bada ita ga ''khalid bn Alwalid (RA)''.
b-
Tutar yakar ''Musailimatu
alkazzaab'' da jama'arsa (banu-hanifata) kuma ya damka ta ga "Ikrimatu
bn Abiy-jahal'', daga baya ya sake karfafarsa da ''Shurahbiyl bn
Hasanata''.
c-
Ya kuma bada tutar yakan
wa'yanda su ke farko-farkon ''Shaam'' ga ''Khalid bn Sa'id bn Al'aas''.
d-
Ya tura ''Amru bn Al'aas
(RA)'' izuwa ''Kuda'ata da wadi'atu da Alhaarith''.
e-
Ya kuma umurci (Al'ala'i
bn Alhadramiy'' ya tafi garin ''Bahraini''.
f-
''Huzaifatu bn Mihsin
algadfaniy'' shi kuma aka kulla masa tutar yakar mutanen '' Daba, da
Arfajata, da Harsamata''.
g-
Tutar yakar ''Banu-saliim,
da wadanda su ke tare da su na kabilar Hawazin'' ya bada ita ga ''darafata
bn Hajib''. Kana kuma ''Suwaid bn Mukarrin'' aka bashi tutar yakar
''Tihamar Yemen''.
Abubakar (RA) bayan ya tura wadannan rundunoni
izuwa yakar ''masu ridda'', ya kuma rubuta musu wannan rubutun ya aike musu:
(بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ
الرَّحيم، مِنْ أَبِي بَكْرٍ خَلِيفَةَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
إِلَى مَنْ بَلَغَهُ كِتَابِي هَذَا، مِنْ عامَّة وخاصَّة، أَقَامَ عَلَى إِسْلامِهِ
أَوْ رَجَعَ عَنْهُ، سَلامٌ عَلَى مَنِ اتَّبع الْهُدَى وَلَمْ يَرْجِعْ بَعْدَ الْهُدَى
إِلَى الضَّلالة وَالْهَوَى، فإنِّي أَحْمَدُ اللَّهَ إِلَيْكُمُ الَّذِي لا إِلَهَ
إِلا هُوَ، وَأَشْهَدُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، وأنَّ
مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، نُقرُّ بِمَا جَاءَ بِهِ، ونُكفِّر مَنْ أَبَى ذَلِكَ
وَنُجَاهِدُهُ. أَمَّا بَعْد: ...) إلى قوله: (وَقَدْ بَلَغَنِي رُجُوعُ
مَنْ رَجَعَ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ بَعْدَ أَنْ أقرَّ بِالإِسْلامِ، وَعَمِلَ بِهِ،
اغْتِرَارًا بِاللَّهِ وَجَهْلا بِأَمْرِهِ، وَإِجَابَةً للشَّيطان). ... إلى
أن قال في آخرها: (وَإِنِّي بعثت إليكم فِي جَيْشٍ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالأَنْصَارِ،
والتَّابعين بِإِحْسَانٍ، وَأَمَرْتُهُ أَنْ لا يَقْبَلَ مِنْ أَحَدٍ إِلا الإِيمَانَ
بِاللَّهِ، وَلا يَقْتُلُهُ حَتَّى يَدْعُوَهُ إِلَى اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ، فَإِنْ
أَجَابَ وأقرَّ وَعَمِلَ صَالَحَا قبِلَ مِنْهُ، وَأَعَانَهُ عَلَيْهِ وَإِنْ أَبَى
حاربه عليه حتى يفئ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ، ثمَّ لا يُبْقِي عَلَى أَحَدٍ مِنْهُمْ قَدَرَ
عَلَيْهِ، وَأَنْ يحرِّقهم بالنَّار وَأَنْ يَقْتُلَهُمْ كُلَّ قِتْلَةٍ، وَأَنْ يَسْبِيَ
النِّساء والذَّراري، وَلا يَقْبَلَ مَنْ أَحَدٍ غَيْرَ الإِسْلامِ، فَمَنِ اتَّبعه
فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ، وَمَنْ تَرَكَهُ فَلَنْ يُعْجِزَ اللَّهَ، وَقَدْ أَمَرْتُ رَسُولِي
أَنْ يَقْرَأَ كِتَابَهُ فِي كُلِّ مَجْمَعٍ لَكُمْ. والدَّاعية الأَذَانُ فَإِذَا
أذَّن الْمُسْلِمُونَ فكفُّوا عَنْهُمْ، وَإِنْ لم يؤذِّنوا فَسَلُوهُمْ مَا عَلَيْهِمْ،
فَإِنْ أَبَوْا عَاجِلُوهُمْ، وَإِنْ أقرُّوا حمل منهم عَلَى مَا يَنْبَغِي لَهُم).
Ma'ana:
((Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Daga Abu-bakar khalifan manzon Allah
–SAW- izuwa ga wadda wasikata ta iske shi na gama-garin mutane da kuma
kebantattunsu, sawa'un ya ci-gaba da wanzuwa cikin musuluncinsa ko ya fita daga
cikinsa, amincin Allah ya tabbata ga wadda ya bi shiriya, bai kuma koma izuwa
bata da son zuciya ba bayan shiriyar! Lallai ina gode wa Allah da babu abun
bauta da gaskiya sai shi, kuma ina shaidawa cewa babu wadda ya cancanci a yi
masa bauta sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, ina kuma kara shaidawa
cewa annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, muna tabbatar da abin da ya
zo da shi, kuma muna kafirta wadda ya ki hakan, kuma za mu yake shi, Bayan
haka: ..). –Ya ci gaba da cewa: ((Kuma labarin wadanda su ka fita daga
addininsu daga cikinku, bayan da can sun yi imani, kuma sun aiki da shi,
labarinsu ya zo mini, sun yi haka ne kuma saboda ruduwa da su ka yi da Allah,
da jahiltar al'amarinsa, gami da amsa wa Shedan)… Ya ci gaba da cewa: ((Kuma
lallai na turo runduna izuwa gare ku wadda ta kunshi ''almuhajiruna da
Al'ansaar, da wadanda su ka bisu da kyautatawa'' kuma na umurci jagoransu cewa
kada ya karbi wani abu daga wani mutum in banda imani da Allah, kuma kada ya
''yaki'' wani face ya kira shi izuwa ga Allah mabuwayi da daukaka; Idan har ya
amsa masa; ya kuma yi imani da aiki na kwarai to ya karba daga gare shi, ya
kuma taimake shi akan haka. Idan kuma ya ki to sai ya yake shi, har sai ya dawo
izuwa ga addinin Allah. In kuma ba haka ba; to kada ya bar wani da ya samu iko
akansa; ya kone su da wuta, ya kuma karkashe su mafi sharrin kisa, ya kama
matansu da yaya a matsayin fursunan yaki, kada kuma ya karbi wani abu a wajen
wani daga cikinsu in banda musulunci; duk wadda ya bi shi to hakan shi ne abin
da ya fiye masa alkhairi, wadda kuma ya bar musulunci to ya sani ba zai gagari
Allah ba. Kuma hakika na umurci dan sakona da ya karanta wasikata ga kowace
matattara da ta hada ku. …).
Imam Ahmad bn Muhammad bn Hambal ya kawo a
cikin littafinsa [Fada'ilu assabati, lamba: 68, da sanadi ingancecce] daga
A'ishatu (RA) tace:
(قُبِضَ النَّبِيُّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَارْتَدَّتِ الْعَرَبُ، وَاشْرَأَبَّ النِّفَاقُ
بِالْمَدِينَةِ، فَلَوْ نَزَلَ بِالْجِبَالِ الرَّوَاسِي مَا نَزَلَ بِأَبِي لَهَاضَهَا،
فَوَاللَّهِ مَا اخْتَلَفُوا فِي نُقْطَةٍ إِلا طَارَ أَبِي بِحَظِّهَا وَعَنَائِهَا
فِي الإِسْلام).
Ma'ana: ((Allah ya dauki ran annabinsa –SAW-
sai larabawa su ka yi ''ridda'', munafirci kuma ya leko da kansa a garin
madina, Da abin da ya sauka wa babana ya sauka ne wa manyan duwatsu masu tsayi
da girma wadanda kuma su suke rike da kasa a matsayin tike: to da ya tausasa su
ko kuma ya kakkarya su, na rantse da Allah sahabban annabi ba su yi sabani a
wata mas'ala ba a cikin musulunci face babana ya rabauta da daidai a cikinta).
Yana daga cikin abin da ke kara fito da batun
''riddan larabawa masu dunbun yawa'' bayan rasuwar manzon Allah (SAW), tare kuma
da bayani kan wadanda su ka hana zakka, da kuma yadda Abubakar (RA) ya yi
tsayuwar alif wajen yakarsu, tare da shawara da wassu daga cikin sahabbai su ka
bashi na cewa ya dakata daga wannan yakin, da kuma yadda Allah ya shiryar da
shi izuwa ga lamarin da yama dalilin kara daukakar musulunci: Abin da ya zo a
cikin [''Sahihu Albukhari'', lamba: {6924, 6425}, da ''Sahihu Muslim'', hadisi
na: {20}]:
(عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ t قَالَ: لَمَّا تُوُفِّيَ النَّبِيُّ r وَاسْتُخْلِفَ أَبُو بَكْرٍ، وَكَفَرَ مَنْ كَفَرَ مِنَ الْعَرَبِ قَالَ
عُمَرُ: يَا أَبَا بَكْرٍ كَيْفَ تُقَاتِلُ النَّاسَ وَقَدْ قَالَ رَسُولُ اللهِ r: "أُمِرْتُ
أَنْ أُقَاتِلَ النَّاسَ حَتَّى يَقُولُوا لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ. فَمَنْ
قَالَ: لاََ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ عَصَمَ مِنِّي مَالَهُ وَنَفْسَهُ إِلاَّ بِحَقِّهِ
وَحِسَابُهُ عَلَى الله" قَالَ أَبُو بَكْرٍ: وَاللَّهِ لأُقَاتِلَنَّ مَنْ
فَرَّقَ بَيْنَ الصَّلاَةِ وَالزَّكَاةِ، فَإِنَّ الزَّكَاةَ حَقُّ الْمَالِ، وَاللَّهِ!
لَوْ مَنَعُونِي عَنَاقًا كَانُوا يُؤَدُّونَهَا إِلَى رَسُولِ اللهِ r لَقَاتَلْتُهُمْ عَلَى مَنْعِهَا. قَالَ عُمَرُ: فَوَ اللَّهِ مَا هُوَ
إِلاَّ أَنْ رَأَيْتُ أَنْ قَدْ شَرَحَ اللَّهُ صَدْرَ أَبِي بَكْرٍ لِلْقِتَالِ فَعَرَفْتُ
أَنَّهُ الْحَقُّ([3])).
Ma'ana: (Daga
Abu-hurairata –RA- yace: Yayin da annabi –SAW- ya rasu, Abubakar kuma ya zama
khalifa, wadanda su ka kafirce daga cikin larabawa su ka kafirce, Umar yace: Ya
Abubakar! Ta yaya zaka yaki mutane, alhali manzon Allah –SAW- yace: An umurce
ni da na yaki mutane har sai sun shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah,
Duk wadda ya shaida ''babu abun bauta da gaskiya sai Allah'' to ya kare ransa
da dukiyarsa daga gare ni –ba zan yake shi ba- sai da hakkin musulunci, kuma
hisabinsa naga Allah. Sai Abubakar yace: Na rantse da Allah! Zan yaki wadda ya
rabe tsakanin salla da zakka, saboda zakka hakki ne na dukiya, kuma wallahi! Da
za su hanani koda 'yar akuyar da bata kai shekara ba ''anaaq'' wadda kuma sun
kasance suna bada ita ga manzon Allah –SAW- a matsayin zakka to da na yake su
akan hanawan.
Umar yace: Na rantse da Allah! Ba komai ba ne face dana ga Allah ya bude
zuciyar Abubakar ya cusa masa kudirin yakar masu hana zakka sai na san hakan
-yakar tasu- gaskiya ne).
Yakar wadanda su ka yi ''ridda, suka kuma canza sheka daga
musulunci izuwa kafirci'' da kuma wadanda suka hana zakka da Abubakar (RA) ya
yi duk sun kasance ne bayan dan lokaci kadan daga rasuwar manzon Allah (SAW),
wadda hakan ya sa lamarin musulmai ya sake izza da bunkasa, ya kuma koma kamar
yadda annabi (SAW) ya tafi ya barshi.
-Yana kuma daga cikin manya-manyan abubuwan
da Abubakar (RA) ya aikata su A wannan lokacin wadda kuma sun kara wa musulunci
tagomashi, tare da dura ruwa a cikin kafirai, kana kuma musulunci ya kara
kwar-jini a idanunsu, su ka ci gaba da tsoronsa, sa'annan abin da annabi
(SAW) ya bayyana a cikin albishir da ya yi wadda ya gabata; na cewa:
(... عزيزًا منيعًا)
Ya kara tabbata: Abun da Abubakar ya yi na
zartar da rundunar da Annabi (SAW) ya shirya don su yaki ''rumawa da su ke
shaam'' karkashin shugabancin Usamah bn Zaid (RA); Bayan kuma sahabbai da
yawa sun yi taraddadi kan tura su a irin wannan lokacin, Alhafiz Ibnu-kasir
(RL) a cikin littafinsa [Albidayah wannihayah, v6/p335] ya ce:
(وَالْمَقْصُودُ: أنَّه لَمَّا وَقَعَتْ هَذِهِ الأُمُورُ
أَشَارَ كَثِيرٌ مِنَ النَّاس عَلَى الصِّديق: أَنْ لا يُنْفِذَ جَيْشَ أُسَامَةَ؛
لاحْتِيَاجِهِ إليه فيما هو أهمّ، لأنَّ ما جهِّز بِسَبَبِهِ فِي حَالِ السَّلامة،
وَكَانَ مِنْ جُمْلَةِ مَنْ أَشَارَ بِذَلِكَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ، فَامْتَنَعَ
الصِّديق مِنْ ذَلِكَ، وَأَبَى أشدَّ الإِبَاءِ، إِلا أَنْ يُنْفِذَ جَيْشَ أُسَامَةَ،
وَقَالَ: وَاللَّهِ لا أَحُلُّ عُقْدَةً عَقَدَهَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَلَوْ أنَّ الطَّير تخطَّفنا، والسَّباع مِنْ حَوْلِ الْمَدِينَةِ
وَلَوْ أنَّ الْكِلابَ جَرَتْ بِأَرْجُلِ أُمَّهَاتِ الْمُؤْمِنِينَ لأجهزنَّ جَيْشَ
أُسَامَةَ، وَأَمَرَ الْحَرَسَ يَكُونُونَ حَوْلَ الْمَدِينَةِ. فَكَانَ خُرُوجُهُ
فِي ذَلِكَ الْوَقْتِ مِنْ أَكْبَرِ الْمَصَالِحِ وَالْحَالَةُ تِلْكَ، فَسَارُوا لا
يمرُّون بحيٍّ مِنْ أَحْيَاءِ الْعَرَبِ إِلا أُرْعِبُوا مِنْهُمْ، وَقَالُوا: مَا
خَرَجَ هَؤُلاءِ مِنْ قَوْمٍ إِلا وَبِهِمْ مَنَعَةٌ شَدِيدَةٌ، فقاموا أربعين
يوماً ويقال: سبعين يوماً، ثمَّ أتوا سَالِمِينَ غَانِمِين).
Ma'ana: (Makasudi anan shi ne: yayin da
wadannan abubuwa su ka auku –wato: barin musulunci da wassu su ka yi bayan
rasuwar manzon Allah- Mutane da yawa sun bada shawara ga Abubakar as-siddiq
cewa: ya dakatar da tura rundunar da Usamatu ke jagoranta; saboda matsanancin
bukatuwarsa izuwa ga rundunar, ga abin da yafi abin da za su tafi izuwa gare
shi muhimmanci; saboda annabi –SAW- ya tura su ne a lokacin da ake cikin
amintuwa daga musibar da ta auku na gama-garin ridda, daga cikin wa'yanda suka
bada irin wannan shawarar akwai Umar bn Alkhaddab, Amma sai Abubakar assidiq ya
ki karbar wannan shawari, ya kuma turje akan ra'ayinsa na cewa sai ya zartar da
rundunar da manzon Allah –SAW- ya aika karkashin Usamatu iyaka turjewa, ya kuma
ce: ''Wallahi! Ba zan warware kullin da manzon Allah –SAW- ya kulla ba; Koda za
a kaddara cewa tsuntsaye sun zo suna dauke mu, dabbobi masu farauta suna kewaye
da madina, kai koda ace karnuka sun gudu da kafofin ''uwayen muminai'' wallahi
sai na zartar da tura rundunar Usamatu. Sai kuma Abubakar ya umurci masu gadi
da su kasance a kewayen madina. Sai fitar Usamatu da rundunarsa a wannan
lokacin ya zama daga cikin abubuwa masu maslahar gaske manya; ta yadda basa
shige wata unguwa –kauye- daga cikin kauyukan larabawa, face sun tsorita da su;
su kuma kama cewa: Wadannan basu fito daga wata al'umma ba face wannan
al'ummar suna da: kariya ta musamman mai matukar tsanani, Su usamatu su ka
je su ka yi kwana 40, a wani kaulin kuma aka ce: kwana 70, sa'annan su ka dawo
madina da ganima, babu kuma wani abun da ya same su).
-Yana kuma daga cikin abubuwan da Abubakar
(RA) ya yi na yada musulunci, da kokarin shiryar da bayin Allah
izuwa ga addinin Allah, don su ji dadin rayuwar duniya, su kuma tsira a lahira:
Tura bataliyoyi don tallen musulunci: Wannan kuma ya kasance bayan Abubakar ya
gama da ''jaziratu al'arab'', musulunci ya komo mai karfi a cikinta bayan
rauninsa; saboda ridda da bayaninsa ya gabata, Sai ya nada bataliyoyi, ya kuma
basu tutar yaki, ya tura ''khalid bn Alwalid'' izuwa ga Iraq yakin da
ake kira: ''Gazwatu zati assalasil ta zamanin Abubakar''.
Kamar yadda kuma ya tura wadannan gomnoni kuma
jagororin bataliyoyi ta bangaren ''tsohuwar shaam'', kamar haka:
a-
''Yazid bn Abiy-sufyan''
wadda aka tura shi da mutane masu tsananin yawa, izuwa ''Damashk''.
b-
''Abu-ubaidata bn
Aljarrah'' da aka tura shi izuwa ''Hims''.
c-
''Amru bn Al'aas''
wadda ya tura shi izuwa ga ''Falastinu''.
Wadannan
aiyukan, dama wassunsu na daga aiyukan da Abubakar (RA) ya aikata na bunkasa
musulunci da yada shi duk Abubakar din ya aikata su ne a tsukin shekara biyu da
watanni kamar uku, kasancewar ya fara khalifancinsa ne a watan 3 na shekara ta
goma sha daya, izuwa rasuwarsa, wata ta 6 na shekara ta goma sha uku, wato
shekara 2 da wata uku. (watan 3/ 11 na hijirar Annabi, zuwa watan 6/13h).
[domin
Karin bayani kana bin da ya gabata a duba, abubuwa das u ka faru a shekarar
hijira 11, 12, da 13, a cikin babban kundin tarihi mai suna: Albidayatu
wannihayatu, Na Alhafiz Ibnu Khasir, {v6/p332 zuwa karshensa}, da {v7/p5-20}, da kuma
littafin ''Hukbatun min attarikh, na Assheikh Usman bn Muhammadu alkhamis,
{p63-77}].
NA
BIYU: MUHIMMAN LAMMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN ''UMAR (RA)'' WADDA SUKE
NUNA IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YADUWARSA
Lallai
musuluntar Umar bn Al-khaddab (RA) ya kasance sababi daga cikin sabbuban
daukakar musulunci, saboda gabanin musuluntarsa ya kasance mutum ne mai tsanani
ga musulmai, amma bayan ya shiga musulunci sai tsananinsa ya zama ga makiya
Allah; kafirai, kana kuma bunkasa da izza ga musulunci da musulmai, kamar yadda
Abdullahi bn Mas'uud (RA) a [Sahihul
Bukhariy, lamba: 3684, babin falalar Umar, da kuma lamba: 3863 a babin da ke
magana kan musuluntar Umar] ya ke cewa:
«مَا زِلْنَا أَعِزَّةً مُنْذُ أَسْلَمَ عُمَرُ».
Ma'ana: (Bamu gushe ba muna madaukaka masu
izza da buwaya tun da Umar ya musulunta).
A wata riwaya kuma da ta zo a cikin littafin
[Tarihin Madinah na Ibnu-shabbah, 2/661] ya karasa wannan maganar da fadinsa:
«لَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا نَسْتَطِيعُ أَنْ نُصَلِّيَ
فِي الْبَيْتِ حَتَّى أَسْلَمَ عُمَرُ، فَلَمَّا أَسْلَمَ عُمَرُ قَاتَلَهُمْ حَتَّى
تَرَكُونَا نُصَلِّي».
Ma'ana: (Hakika mun kasance bama iya mu yi
salla a dakin ka'abah har sai da Umar ya musulunta, yayin da Umar ya musulunta
sai ya yaki kafiran kuraishawa, har sai da suka kyale mu muke salla).
Kuma hakika lamarin samun izzar musulmai da
kuma shi kansa addinin da sababin musuluntar Umar (RA) ya zamto amsawar Allah
ne ga addu'ar manzonsa; da ta zo cikin fadinsa (SAW):
«اللَّهُمَّ أَعِزَّ الإِسْلامَ بِأَبِي جَهْلِ بْنِ هِشَامٍ
أَوْ بِعُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ» فَأَصْبَحَ عُمَرُ فَغَدَا عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَأَسْلَمَ، ثُمَّ صَلَّى فِي الْمَسْجِدِ ظَاهرا.
Ma'ana: (Ya Allah! Ka bada
izza da buwaya ga musulunci da musuluntar Abu-jahl bn Hishaam, ko kuma Umar bn
Al-khaddaab. Kashe-gari sai kawai Umar ya yi sammako izuwa ga manzon Allah
–SAW- ya karbi musulunci, sa'annan ya tafi masallaci ya yi salla a bayyane).
A wani lafazin kuma:
«اللَّهُمَّ أَعِـزَّ الإِسْـلاَمَ بِأَحَـبِّ هَـذَيْنِ
الرَّجُلَـيْنِ إِلَيْكَ؛ بِأَبِي جَهْلٍ أَوْ بِـعُمَرَ بْنِ الخَـطَّـابِ.
قَالَ: وَكَانَ أَحَبَّهُمَا
إِلَيْهِ عُمَرُ».
Ma'ana: (Ya Allah! Ka daukaka musulunci ka
bashi izza da musuluntar dayan mutumin da ka fi so daga cikin mutane guda biyu;
Abu-jahl ko kuma Umar bn Al-khaddaab. Maruwaicin ya ce: To sai ya zamto wadda
Allah ya ke so daga cikinsu shi ne: Umar).
[Wannan hadisin ya zo ta hanyoyi da riwayoyin
sahabbai da dama, daga cikinsu akwai A'ishah da Ibnu-abbas, da Ibnu-umar da
sauransu –RA-. Daga cikin maluman musulunci da suka fitar da shi kuma akwai:
Imamut tirmiziy, 3681, ya kuma inganta shi, da Ahmad, lamba: 5696, da Al-hakim,
lamba: 4886 da kuma lambobin da su ke gabaninsa. Malam Albaniy a cikin
As-silsilatus sahihah, lamba: 3225 shima ya inganta shi].
Wannan kuma shi ya sa malamin musulunci
Ibnu-hibban gabanin ya ambaci wannan hadisin da ya gabata sai da ya kulla
kanun-magana mai taken:
(ذِكْرُ الْبَيَانِ بِأَنَّ عِزَّ الْمُسْلِمِينَ بِإِسْلامِ
عُمَرَ كَانَ ذَلِكَ بِدُعَاءِ الْمُصْطَفَى صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ)
Ma'ana: (Magana da bayani kan lallai samun
izzar musulmai da musuluntar Umar ya kasance sakamakon addu'ar annabi –SAW-).
[v15/305, gabanin hadisi mai lamba: 6881].
Duk mutumin da ya bibiyi tarihin Umar (RA)
dukkaninsa zai samu cewa rayuwarsa gaba-dayanta izza ce da buwaya ga musulunci
da musulmai, kasancewar Allah ya karbi addu'ar manzonsa da ta gabata akansa,
wannan kuma shi ne dalilin da yasa A wani lafazin na Abdullahi bn Mas'uud (RA)
a cikin littafin [Tarikhul madinah na Ibnu-shabbah, v2/p661] ya ke cewa:
«كَانَ إِسْلامُ عُمَرَ فَتْحًا، وَكَانَتْ هِجْرَتُهُ
نَصْرًا، وَكَانَتْ إِمَارَتُهُ رَحْمَةً، لَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا نَسْتَطِيعُ أَنَّ
نُصَلِّيَ بِالْبَيْتِ حَتَّى أَسْلَمَ عُمَرُ، فَلَمَّا أَسْلَمَ عُمَرُ قَاتَلَهُمْ
حَتَّى تَرَكُونَا فَصَلَّيْنَا».
Ma'ana: (Lallai musuluntar Umar ya kasance
wani budi ne, hijirarsa kuma daga Makka zuwa Madina wani taimako, shugabancinsa
kuma rahama; lallai mun kasance bama iya mu yi salla a dakin ka'abah har sai da
Umar ya musulunta, yayin da Umar ya musulunta sai ya yaki kafiran kuraishawa,
har sai da su ka barmu mu ke salla).
A
nan zan kawo muhimman abubuwan da su ka auku a tsawon zamanin halifancin Umar
(RA) da ya kai shekaru goma (wato daga shekara 13-23 na hijira) su kuma shekarun
khalifancinsa suna cikin mafi kyan shekarun da musulunci ya rayu a cikinsu;
bayan zamani ko rayuwar manzon Allah (SAW), da kuma lokacin khalifanci Abubakar
(RA); hadisin mu na gaba (na 6 da ke tafe) na nuna haka. Su kuma misalan
abubuwan da su ka auku, da ambatonsu ke tafe zasu kara nuna mana izzar musulunci
da yaduwarsa a zamanin halifanci Umar bn Al-khaddab, da kuma yadda musulmai su
ke da kwar-jini a idanun makiyansu = Ga misalan kamar haka:
(1)
A duniyar wancan zamanin
akwai manya-manyan dauloli da masarautun kafirai masu karfin gaske guda biyu;
Na farkonsu ita ce: daula da masarautar Rumawa ta nasara masu riya bin addinin
annabi Isah (AS), wacce take yankin tsohuwar SHAAM, Sarkinsu kuma ana yi masa
lakabi da "Kaisar", Sai kuma ta biyun ita ce: daula ko masarautar
Farisawa masu bautar wuta (majusawa), wacce ita kuma ta ke yankin tsohuwar IRAQI
DA ABIN DA KE BAYANTA, sarkinsu kuma ana yi masa lakabi da "Kisrah".
Wadannan
daulolin guda biyu an ci garfin biranensu aka shigar da musulunci a cikinsu aka
bubbude su, duk a halifanci Umar (RA), ta bangaren masarautar Shaam a farkon
khalifancinsa ne Allah ta'alah ya bada gagarumar nasara ga musulmai a
"Yarmuuk" akan rundunonin rumawa masu dunbun yawa, aka kuma bude
garin Damashk, da Hims, da Kansarin, da Ajnaadin, daga bisani kuma aka bude
Baitul-makdis aka shigar da musulunci. Wannan kuma shi ya bada dama ga musulmai
kan shiga ko-ina a masarautar rumawa, ta kuma yadda suka ga-dama.
A bangare
guda kuma Sai Amru bn Al-aas (RA) ya fiskanci yankin Misra ya bude ta. daga
bisani kuma sai musulunci ya shiga sauran garurrukan Afrika.
Shi kuma
Sa'ad bn Abiy-wakkas (RA) da rundunarsa su ka nufi masarautar gabas; garurrukan
masu bautar wuta; Farisawa su ka yake su kana suka shigar da musulunci cikinsu,
Allah kuma ya basu gagarumar nasara, musamman a yakin Kadisiyyah da sauransu,
sannan aka bude biranen Khurasaan da wassunsu.
Shi kuma
wannan lamari na cewa musulunci zai bunkasa, ya yadu, ta yadda zai mamaye daulolin
nan guda biyu (daular rumawa data farisawa) tun tuni manzon Allah (SAW) ya riga
ya yi albishir da cin nasarar musulmai akan masarautunsu, tare da bayyana cewa
za a ciyar da taskokin dukiyarsu don daukakar musulunci, a cikin fadinsa (SAW):
«إِذَا هَلَكَ كِسْرَى فَلاَ كِسْرَى بَعْدَهُ، وَإِذَا
هَلَكَ قَيْصَرُ فَلاَ قَيْصَرَ بَعْدَهُ، وَالَّذِي نَفْسُ
مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ،
لَتُنْفِقُنَّ كُنُوزَهُمَا فِي سَبِيلِ اللَّهِ»
Ma'ana:
(Idan sarki kisrah na farisa ya halaka to babu wani kisrah da zai zo a bayansa,
kuma idan Sarki Kaisar na Rumawa ya halaka to babu wani kaisar din a bayansa,
Na rantsen da Allan da ran Muhammadu ke hannunsa! lallai za a ciyar da taskokin
masarautunsu guda biyu fi-sabillah).
[Sahihul
Bukhariy, Lamba: 3618, Sahihu Muslim, lamba: 76].
Haka kuma
lamarin ya kasance a khalifancin Umar (RA), ta yadda aka rabe dukiyoyinsu a
garin madina a matsayin ganima.
(2)
Ga nan muhimman yakuka da
budin shigar da musulunci da su ka kasance a khalifancin Umar (RA) a
jejjere kuma a takaice:
a-
Yakin "Kadisiyyah"
a watan Al-muharram, shekara ta goma sha hudu (14, bayan hijira), karkashin
jagorancin Sa'ad bn Abiy-wakkas (RA) ta yadda musulmai su ka fiskanci Rustum
daga bangaren farisawa masu bautar wuta cikin babbar rundunarsa da sojojinta
suka kai dubu tamanin ko fiye (80, 000), su kuma musulmai cikin runduna mai
sojoji dubu hudu ko shida (4000, 6000), amma duk da haka sai Allah ya bada
nasara ga musulmai a wannan yaki mai girma, har aka kashe jagoran yaki ta
bangaren farisawa mai suna Rustum bayan ya hau alfadarinsa ya riga ya gudu.
b-
Bayan wannan nasarar mai
girma da musulunci ya samu ta bangaren farisawa sai Umar bn Al-khaddab (RA) ya
tura wata tawagar don ta fiskanci masarautar Rumawa, a shekara ta (15, bayan
hijira), a yakin Ajnadin, karkashin jagorancin Amru bn Al-aas (RA), su kuma
rumawa jagoransu a wannan yakin shi ne: "Al-ardabun", haka aka yi
wannan yakin, Allah kuma ya bada nasara ga musulmai, har shi shugaban sojojin
rumawa Ardabun ya gudu ya buya a Baitul-makdis.
c-
A shekara ta goma sha shida
(l6, na daga hijira) kuma aka bude Baitul-makdis, bayan Abu-ubaidah (RA) ya
killace su a cikin garinsu, ba-shiga ba-fita, har sai da suka nemi a yi sulhu,
da sharadin Amirul-miminin Umar (RA) cewa ya zo, da Umar ya je Shaam sai ya yi
sulhu da Nasara da su ke Baitul-makdis, ya kuma shardanta musu fitar da Rumawa
daga masallaci, daga bisani kuma ya shiga masallacin ta kofar da manzon Allah
(SAW) ya shige shi a lokaci ISRA'I, ya kuma sallaci asubah a cikinsa.
d-
Shigar da musulunci garin
"Tustar" da "As-suus", da kame Al-hurmuzaan (a shekara ta,
17 hijira) na "Ahwaaz": Wadda ya shugabanci wannan lamari shi ne
An-nu'uman bn Mukarrin, da aka fara karawa sai shi Al-hurmuzaan da rundunarsa
su ka gudu zuwa "Tustar", sai musulmai kuma suka bi su, aka yi ta bata-kashi,
aka bada amana ga shi Al-hurmuzan kamar yadda ya nema, har a ka kawo shi gaban
Umar (RA) daga bisani kuma ya musulunta.
e-
Babban yakin NAHAWAND a
shekara ta ashirin da daya (21, bayan hijira): Wannan yakin yana daga cikin
manyan yakuka da aka yi shi tsakanin musulmai da masu bautar wuta; Farisawa, a
wannan yakin su farisawan sun gina ma kansu ganuwa da su ka labe a cikinsa; don
haka basu fita yakar musulmai ba, Sai dai kuma musulman karkashin jagorarsu sun
yi musu hikima da wayo irin na yaki, sai da su ka fitar da su daga ganuwar ta
su gabadaya, a wani yakin da mutane basu ji labarin irinsa ba, kuma daga karshe
Allah ya bada nasara ga musulmai. Wadda da wannan musulunci y agama da daular
farisawa masu bautar wuta a khalifancin Umar (RA).
f-
Wadannan su ne muhimman
abubuwan da suka auku a cikin shekara goman da Umar ya yi khalifanci, wadda
kuma dukkaninsu daukaka ne da bunkasa da izza ga musulunci da musulmai, ta
yadda aka samu adadi mai yawan gaske na mutane sun shiga addinin Allah a wancan
lokacin daga cikin masu bautar wuta, da kuma masu bautar alloli guda uku;
Nasara. [Don Karin bayani, a duba: abubuwan da su ka auku daga shekara 13-23 na
hijira, a cikin littafin: al-bidayah wan-nihayah, na Ibnu-kasiir, da kuma
littafin: Hikbatun minat tarikh, shafi 87-96].
(((Zamu ci
gaba bi iznillahi ta'alah!)))
NA
UKU: MUHIMMAN LAMMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN ''USMAN (RA)'' WADDA SUKE
NUNA IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YADUWARSA:
Fadinsa
تـضْحيته بمـاله: لقـد ضرب الخليفة عثمانt أروع الأمثلة في نصرة الإِسلام وإعلاء كلمته فكان أجود المسلمين حيث
يَجدُّ الجَدُّ ويدعو داعي الجهـاد. روى الترمذي
عن عبد الرحمن بن سمُرة قال: جاء عثمان إلى النبي r بألف دينـار
حين جهز جيش العسرة فنثرها فِى حجره، قال عبد الرحمن: فرأيت النبي r يقلبها في حجره ويقول: "ما ضر عثمان ما عمل
بعد اليوم " مرتين". ومن
مآثره t أنه حفر بئر رُومَة فعن النبي r قال: "من يحفر بئر رومة فله الجنة فحفرها عثمانt وجعلها للمسلمين.رضي الله عنه وأرضاه وعن
الصحابة أجمعين
fadinsa
«وَلَيْسَ هَذَا بِالْمُنْتَظَرِ الَّذِي
يَتَوَهَّمُ الرَّافِضَةُ وُجُودَهُ ثُمَّ ظُهُورَهُ مِنْ سِرْدَابِ "سَامرّاء"؛
فَإِنَّ ذَلِكَ لَيْسَ لَهُ حَقِيقَةٌ وَلا وُجُودٌ بِالْكُلِّيَّةِ، بَلْ هُوَ مِنْ
هَوَسِ الْعُقُولِ السَّخِيفَةِ، وَتَوَهُّم الْخَيَالاتِ الضَّعِيفَةِ، وَلَيْسَ الْمُرَادُ
بِهَؤُلاءِ الْخُلَفَاءِ الاثْنَيْ عَشَرَ: الأَئِمَّةَ الاثْنَيْ عَشَرَ الَّذِينَ
يَعْتَقِدُ فِيهِمُ الاثْنَا عَشْرِيَّةَ مِنَ الرَّوَافِضِ، لِجَهْلِهِمْ وَقِلَّةِ
عَقْلِهِمْ. وَفِي التَّوْرَاةِ الْبِشَارَةُ بِإِسْمَاعِيلَ عَلَيْهِ السَّلامُ، وَأَنَّ
اللَّهَ يُقِيمُ مِنْ صُلْبِه اثْنَيْ عَشَرَ عَظِيمًا، وَهُمْ هَؤُلاءِ الْخُلَفَاءُ
الاثْنَا عَشَرَ الْمَذْكُورُونَ فِي حَدِيثِ ابْنِ مَسْعُودٍ، وَجَابِرِ بْنِ سَمُرة.
وَبَعْضِ الْجَهَلَةِ مِمَّنْ أَسْلَمَ مِنَ الْيَهُودِ إِذَا اقْتَرَنَ بِهِمْ بَعْضُ
الشِّيعَةِ يُوهِمُونَهُمْ أَنَّهُمُ الأَئِمَّةُ الاثْنَا عَشَرَ، فَيَتَشَيَّعُ كَثِيرٌ
مِنْهُمْ جَهْلا وسَفَها، لِقِلَّةِ عِلْمِهِمْ وَعِلْمِ مَنْ لَقَّنَهُمْ ذَلِكَ بِالسُّنَنِ
الثَّابِتَةِ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ»([4]).
A cikin littafi ''alkafiy na alkulainiy'' p206 ance
ولد الإمام الحسن العسكري في رمضان عام
232هـ، وتوفي بعد أن عاش ثمانية وعشرين عاما، بدون أن ينجب ولَدًا)
Ma'ana: ((An haifi Imamhasan
al'askariy a ramadana -watan azumi- shekara ta 232h, ya kuma rasu bayan ya rayu
tsawon shekara ashirin da takwas -28- ba tare da an haifa masa daba)). Wannan riwayar
'dan uwan alhasan al'askari mai suna Ja'afar shi ya bada shaida kan dan uwansa
Imamhasan. Kana kuma a cikin babban littafin shi'a Alkafiy.
Dadin-dadawa wannan maganar
ita tasa malumanku su ka sake kawowa a cikin littafanku; shi'a cewa, Gadon
alhasan al'askariy an raba ta ne wa: Mahaifiyarsa da dan uwansa; Ja'afar,
saboda bashi da 'da.
Ka ji wata shaidar ma daga wani jigo daga cikin malumanku na shi'a da
ake masa lakabi da ''almufid'' ya fada a cikin littafinsa: ''al'irshad'' cewa:
«
فلم يظهر له ولد في حياته ولا عرفه
الجمهور بعد وفاته » (الإرشاد 345
Imamhasan al'askariy lokacin
yana raye, yaro bai bayyana masa ba, bayan ya rasu ma mutane ba su sanshi da
yaro ba. Duba shafi 345.
Maganar da na fada kuma na cewa littafin ''alkafiy
na Alkulainiy'' alamomi suna nuna
maluman shi'a sun yi kare-kare cikinsa bayan mawallafinsa gata cikin larabci,
kuma daga littafanku. Tare da cewa akwai tuntuben harshe a cikin abinda ya gabata na cewa ''babi 30, babi 50'' daidai din
''littafi30, littafi50''; ''Ibnu almudahhir alhilliy'' wadda Ibnu-taimiyata
(rl) ya masa raddi da منهاج
السنة النبوية ya
ce: "وكتاب الكليني
تصنيف محمد بن يعقوب الكليني المسى بالكافي، وهو خمسون كتابا بالأسانيد المذكورة"
duba ''Biharu al'anwar, v107/
p146 Ma'ana: Littafin Alkulainiy mai suna Alkafiy littafi hamsin ne da isnadi
da aka ambata. Shi kuma wannan
malamin ya rasu ne a shekara ta 726h, akwai wani ma wadda ya fadi irin wannar
maganar shi kuma sunansa HUSAIN BN hAIDAR ALKARKIY AL'AMILIY, Shi kuma ya rasu
ne a shekara ta 1076. To abun mamakin
shi ne su wadannan sun samu littafin ne bayan anyi karin arba'in bisa dari a
littafin, saboda in muka duba maganar wani bajamin malamin shi'a wadda shi kuma
ya rasu a shekara ta 460, wato ''addusiy'' zamu ga cewa ya ke yi:
وكتاب الكافي وهو يشتمل على ثلاثين كتابا
أوله كتاب العقل، ... وكتاب الروضة آخر كتاب الكافي... أخبرنا بجميع كتبه ورواياته
الشيخ المفيد
Kaga a nan ya nuna cewa
littafi 30 ne, kuma ga littafin farko, ga na karshe, kana kuma ya karanta shi a
wajen shehinsa almufid. Waya kara kimanin littafi 20 su ka zama hamsin tsakanin
shekara ta 460 da tsakanin 726h Kai aji
tsoron Allah!
No comments:
Post a Comment