2015/11/14

KYAUTA ZUWA GA AMARYA (MACE TAGARI) صفات المرأة الصالحة

MACEN DA TAFI ALKHAIRI
DA WACCE TAFI SHARRI

            Bismillahir Rahmanir Rahim!
Wassalatu wassalamu ala nabiyyina Muhammad, wa ala alihi, wasahbihi.
Bayan haka;
Lallai Manzon Allah (صلى الله تعالى عليه وسلم) ya bayyana daxin Duniya, kuma ya nuna cewar Mafi alkhairin daxinta Shine: Mace tagari; a inda yake cewa:
«الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَخَيْرُ مَتَاعِ الدُّنْيَا الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ» [صحيح مسلم، رقم: 1467].
Ma'ana: "Duniya xan jin daxi ne, kuma mafi alkhairin daxinta shine: Mace tagari",[Muslim, lamba: 1467]. A cikin littafin [Sunan na Ibnu-Majah kuma, lamba: 1855] ya  zo cewa:
«إِنَّمَا الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَلَيْسَ مِنْ مَتَاعِ الدُّنْيَا شَيْءٌ أَفْضَلَ مِنَ الْمَرْأَةِ الصَّالِحَةِ».
Ma'ana: "Duniya xan  jin daxi ne, Kuma babu wani abu daga mata'in duniya wanda yafi Mace tagari".
Kuma yazo ta hanyarAbdullahi xan Salam (رضي الله عنه), LallaiAnnabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
«خَيْرُ النِّسَاءِ تَسُرُّكَ إِذَا أَبْصَرْتَ، وَتُعْطِيكَ إِذَا أَمَرْتَ، وَتَحْفَظُ غَيْبَتَكَ فِي نَفْسِهَا وَمَالِكَ».
Ma'ana: "Mafi alherin Mata itace take faranta maka idan ka kalle ta, take kuma baka idan ka umurce ta, sannan ta kiyaye kanta da dukiyarka idan baka nan", [Axxabaraniy, a cikinMu'ujam kabir, lamba: 386, kuma hadisi ne da sashin hanyoyinsa suke inganta sashi].
عَنْ أَبِي أُمَامَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَنَّهُ كَانَ يَقُولُ: «مَا اسْتَفَادَ الْمُؤْمِنُ بَعْدَ تَقْوَى اللَّهِ خَيْرًا لَهُ مِنْ زَوْجَةٍ صَالِحَةٍ، إِنْ أَمَرَهَا أَطَاعَتْهُ، وَإِنْ نَظَرَ إِلَيْهَا سَرَّتْهُ، وَإِنْ أَقْسَمَ عَلَيْهَا أَبَرَّتْهُ، وَإِنْ غَابَ عَنْهَا نَصَحَتْهُ فِي نَفْسِهَا وَمَالِهِ».
Daga Abu-Umamah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya  kasance yana cewa:
"Mumini bai fa'idanta da wani abu –bayan tsoron Allah- ba; wanda yafi alkhairi fiye da Mace tagari; Idan ya umurce ta sai ta yi masa biyayya, in kuma ya kalle ta sai ta faranta masa rai, Idan kuma yayi rantsuwa akanta sai ta kuvutar da shi, in kuma baya tare da ita; to sai ta kiyaye shi a karan-kanta da dukiyarsa" [Sunan Ibnu-Majah, lamba: 1857].
A wani lafazin kuma,
«أَلَا أُخْبِرُكَ بِخَيْرِ مَا يَكْنِزُ الْمَرْءُ؟ الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ، إِذَا نَظَرَ إِلَيْهَا سَرَّتْهُ، وَإِذَا أَمَرَهَا أَطَاعَتْهُ، وَإِذَا غَابَ عَنْهَا حَفِظَتْهُ».
Ma'ana: "Shin ba zan baka labarin mafi alherin abinda Mutum ya taskance ba? Itace mace tagari; Idan ya kalle ta sai ta faranta masa, in kuma ya umurce ta sai ta yi masa xa'a, idan kuma baya wurinta sai ta kiyaye shi" [SunanAbiy-Dawud, lamba: 1664].
وعن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "أَرْبَعٌ مِنَ السَّعَادَةِ: الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ، وَالْمَسْكَنُ الْوَاسِعُ، وَالْجَارُ الصَّالِحُ، وَالْمَرْكَبُالْهَنِيءُ.
وَأَرْبَعٌ مِنَ الشَّقَاوَةِ: الْجَارُ السُّوءُ، وَالْمَرْأَةُ السوء، والمسكن الضيق، والمركب السوء".إسناده صحيح على شرط البخاري.
Kuma an ruwaitodagaSa'adxanAbiyWaqqas (رضي الله عنه) yace: ManzonAllah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Abu guda huxu suna daga Samun  rabo: Mace tagari, da wajen zama mai yalwa, da makwabci nagari, da abin hawa mai lafiya.
Abu guda huxu kuma suna daga tavewa; Mummunan makwabci, da Matar banza, da wajen zama mai qunci, da abin hawa mummuna", [Ibnu-Hibban, lamba: 4032, kumaMaluma sun inganta hadisin].

            Kuma lallai mafarkin kowani Xa namiji dangane da aure ko samun matar da zai yi rayuwa da ita, bai wuce, Ya samu matar da zai samu nitsuwa da ita, wacce take sonsa, ta kuma damu da shi, mai bashi kulawa a ko da yaushe.
Kuma lallai idan Mutane suka nazarci ayoyin Alqur'ani mai karimci da hadisan Annabi (صلى الله عليه وسلم) za su ga cewa lallai NASSOSHIN sun yi bayanin sifofin MACE TAGARI; abar neman MASU HANKALI, da cewa itacemai sifar: RIQO da addini, da qoqarin baiwa Allah haqqoqinsa da kuma miji,  Haka kuma sun nuna cewa itace: Saliha, mai xa'a, bayan kasancewarta Musulma, ko Mumina. Mace tagari ta kan zama mai gaskiya, da haquri, mai sallah, da azumi, da sadaka ko zakka, mai yawan ambaton Allah, tare da yin biyayya wa mijinta, da kiyaye farji daga alfasha, da kuma kiyaye dukiyar mijinta daga tozartawa, da kuma iyalansa.  Har wani hadisin ya nuna cewa, Mace ba za ta lazimci waxannan  aiyukan ba face ta shiga aljannar Ubangijinta, a indaAnnabi (صلى الله عليه وسلم) yake cewa:
"إِذَا صَلَّتِ الْمَرْأَةُ خَمْسَهَا، وَصَامَتْ شَهْرَهَا، وَحَفِظَتْ فَرْجَهَا، وَأَطَاعَتْ زَوْجَهَا، قِيلَ لَهَا: ادْخُلِي الْجَنَّةَ مِنْ أَيِّ أَبْوَابِ الْجَنَّةِ شِئْتِ".
Ma'ana: "Idan Mace ta yi sallolinta guda biyar, ta yi azumin watanta guda xaya, ta kuma kiyaye farjinta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, Sai ace da ita: Ki shiga aljanna daga qofar da kika ga dama daga cikin qofofin aljannah" [Musnad Ahmad, lamba: 1661, Hadisi ne, hasan].
            Kuma don qoqarin taqaicewa Mutane sifofin Macen da tafi alkhairi Wassu masu hikima da ilimi sun dunqule sifofin irin wannan matar cikin maganganunsu taqaitattu masu fasaha.  
Kamar yadda suka yi bayanin wacece asharariyar Mace,
Xaya daga cikinsu yana cewa:
1)  Itace: Take yardar da Ubangijinta  (تُرضي ربَّها).
2)  Take kuma shagwavar da Mijinta (تُدلِّل زوجَها).
3)  Kuma bata barin zaman gidanta (لا تفارق بيتَها).
4)  Kuma tana yin sallolinta guda biyar (تصلِّي خمسَها).
5)  Kuma bata fitar da sirrinta (لا تُخْرِج سِرَّها).
6)  Kuma ba a ganin takalminta (لا يُرى نَعلُها).
7)  Kuma ba a jin sautinta (لا يُسمَع صوتُها).
8)  Kuma ba a sanin siffarta (لا يُعْرَفُ وصفُها).
9)  Mai izza a cikinMutanenta (العزيزة في قومها).
10)                 Mai jin qasqanci a karan-kanta (الذليلة في نفسها).

11)                 Ga xanta qarami; Mai shayar da shi ne, Mai rarrashinsa (لوليدها مرضعةٌ حانيةٌ).
12)                 Gidanta kuma aljanna ce, da abin tsinkanta suke a kusa (بيتها جنَّة دانية).

13)                 Idan ta samu wani alkhairi daga Mijinta sai ta yi godiya (إنْ وجَدَت مِن زوجها خيرًا شكَرَتْ).
14)                 Idan kuma ta ga wani sharri a wurinsa sai ta yi haquri (وإنْ رأَتْ منه شرًّا صبَرَتْ).

15)                 Idan kuma ya shigo wurinta sai ta yi  farin  ciki tana murmushi (إنْ دخَل عليها سُرَّت وتبسَّمَتْ).
16)                 Idan kuma ya fita daga gidanta sai ta yi baqin ciki, tana yin bege (إنْ خرَج مِنْ بيتِها حزِنَتْ وتشوَّقَتْ).
17)                 Idan yayi fushi da ita sai ta jure ta yi haquri (إنْ غضِب منها تحمَّلَتْ وتحلَّمَتْ).

18)                 Idan ta fiskanto shi sai ta burge shi (إنْ أَقْبَلَتْ عليه أعْجَبَتْه).
19)                 Idan kuma baya tare da ita to sai ta kiyaye shi (إنْ غاب عنها حفِظَتْه).
20)                 Idan ta ga aibinsa sai ta voye (إنْ رأَتْ عَيْبَه ستَرَتْه).
21)                 Idan ya nemi ta yi masa uzuri sai ta karvi uzurinsa (إنْ اعتذر منها عَذَرَتْه).

Da aka tambaye shi kuma, Wacece mai sharri a cikin Mata, Sai yace:
1.    Itace: Mai yawaita rashin lafiya (الممراض).
2.    Mai yawaita haila (المحياض).
3.    Wacce take kuka ba tare da sababi ba (التي تبكِي مِن غيرسبب).
4.    Mai kuma yin dariya ba tare da an samu abinda yake sanya al'ajabi ba (وتضحكُ مِن غير عجب).
5.    Idan zata fita sai ta yi ado, ta kuma bubbuxe jiki (إنْ خرَجَتْ تبرَّجَتْ وتكشَّفَتْ).
6.    Idan kuma ta shiga; sai ta yankwane, ta bubbushe (إنْ دخَلَتْ ذبُلَتْ وتقشَّفَتْ).

7.    Maganarta mai ciyo ne (كلامُها وعيد).
8.    Sautinta kuma mai tsanani ne (وصوتُها شديد).

9.    Tana bubbune kyawawa (تدْفَنُ الحسنات).
10.                      Sai kuma ta riqa yaxa munana (وتُفْشِي السيئات).
11.                      Kuma bata yin haquri akan musibu (ولا تَصْبِر على النكبات).

12.                      Tana taimakon zamani akan Mijinta (تعينُ الزمانَ على زوجها).
13.                      Shi kuma, Bata taimakonsa akan zamanin (ولا تُعِينُه على الزمان).

14.                      Idan ya shiga, sai ta fita (إنْ دخَل خرَجَتْ).
15.                      Idan kuma ya fita, sai ta shiga (وإنْ خَرَجَ دخَلَتْ).
16.                      Idan ya kusance ta sai ta gudu (إنْ قَرَبَها نفَرَتْ).
17.                      Kuma, ga abokin zamanta (miji) Mai butulci ne (ولعشيرها كفَرَتْ).
18.                      Kuma idan ta yi fushi sai ta yi fajirci (إذا غضِبَتْ فجَرَتْ).

19.                      Xanta a koyaushe yana cikin yunwa (طفلُها جائع).
20.                      Farillarta kuma, abar tozartawa ce (وفرضُها ضائع).

21.                      Ubangijinta yana Mai fushi (ربُّها غضبانُ).
22.                      Shi kuma Mijinta, yana ta nadama (وزوجُها ندْمانُ).
23.                      Kuma "Shexan" yana sonta (ويحبُّها الشيطانُ).

24.                      Tana kai kuka, alhalin itace Mai zalunci (تشتكِي وهيَ ظالمةٌ).
25.                      Tana yin shaida, alhalin bata wurin (وتشهَد وهي غائبةٌ).
26.                      Tana kuma yin zargi alhalin itace mai aibin (وتذُمُّ وهي عائبةٌ).

27.                      Harshenta yana da tsayi (لسانُها طويلٌ).
28.                      Tufanta kuma, gajere ne (وثوبُها قصيرٌ).

29.                      Shi kumagidanta, tana qaurace masa (وبيتُها هجير).
30.                      Zancenta qarya ne (قولُها زورٌ).
31.                      Shi kuma hawayenta na fajirci ne (ودمعُها فُجُور).
32.                      An jarrabe ta da, azabar rami, da tavewa (ابتُلِيَت بالويل والثبور).
33.                      Da kumamanya-manyan al'amura (وعظائم الأمور).
[Duba littafin  / Almustaxraf fi kulli fannin Mustazraf, shafi 463-464].

Ni da Ku gabaxaya; Allah ta'alah ya azurta mu, da mafi alherin Mata, Ya kuma tsare mu daga sharrinsu.

                        Abubakar Hamza Zakariyya Misau,     
                        Madinah,   01/Safar /1437h

                        Daidai da 13/Nobenba/ 2015m.

2 comments:

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...