2015/11/02

MATASA MANYAN GOBE الشباب عدة الأمل Hudubar Masallacin Annabi saw ta Assubaitiy juma'a 15 Jumadal ula 1436hijira








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A,15/JUMADAL ULA/1436H

MAI TAKEN
MATASA MANYAN GOBE
(الشباب عُدّة الأمل)



LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijina, Babu abin bautawa idan ba shi ba,  akansa na dogara, kuma zuwa gare shi ake tuba, Ina yin yabo a gare shi, tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ina gode masa akan ni'imar lafiya datasamartaka.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, kuma babu mai warware hukuncinSa, Shine mai saurin hisabi.     
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonsa;  yayi hanikan fasiqanci da zage-zage.
Allah ya yi qarin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abota hankali da tunani.

Bayan haka:
Ina yin wasiyya a gare KU, da NI kaina da bin dokokin Allah,     Allah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah, iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai" [Ali-imrana: 102].

            YANAYIN SAMARTAKA YANAYI NE NA KAZAR-KAZAR, KUMA ZAMANI NE NA AIKI, SANNANLOKACINJIN DAXIN IBADA,
            Tarihi ya rubuta matsaya masu yawa kuma madawwama, ga wassu daga cikin MATASA; waxanda suka san Ubangijinsu, sannan suka yi riqo da addininsu;     Sai Qur'ani ya tabbatar da ambatonsu;    Allah mabuwayi da xaukaka yana faxa dangane da annabi Ibrahima (عليه السلام):
"Mun ji wani MATASHI yana aibanta su, anace da shi: Ibrahima" [Anbiya'i: 60].
Ya kuma faxa, dangane da ma'abota kogo:
"Lallai su MATASA ne waxanda suka yi imani da Ubangijinsu, sai muka qara musu shiriya   *  Kuma muka yi xauri akan zukatansu; a lokacin da suka tashi sai suka ce: Ubangijinmu shine Ubangijin sammai da qassai,  baza mu yi bauta wa wani abin bauta idan bashi ba,   Lallai idan muka yi haka, mun faxi zalunci" [Kahfi: 13-14].

            MATASA sune tanadin da ake qulla buri akansu, sannan sune burin al'ummomi domin rayuwar gobe da ake fiskanta, suna da matsayi mai girma a cikin addinin Musulunci, kuma suna daga cikin mutane guda bakwai; waxanda Allah zai sanya su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai tasa "Da SAURAYIN da ya taso cikin bautar Allah".

            Shekarun samartaka qarfi ne da yake da tasiri ga al'ummomi, kuma samartaka azamace da iko da qarfi, da nashaxi,  Lallai kuma waxannan sifofin suna hukuntawa SAURAYI ya yi qoqarin jagorantar rayuwarsa; da kansa, cikin hikima, yana mai kiyaye kansa, tare da sanya linzami wa ransa, ko dabaibayi ko birki; don ya hana ta sauri, sannan ya fiskantar da kansa zuwa ga aiyukan alkhairi da samun rabo, kuma ana son saurayi ya zana wa kansa ko ya tsara wassu manufofin da yake fatan cimma su a rayuwarsa, waxanda zai yi ta hawa matakan xaukaka da su, har kuma ya iya bada gudumawarsa a rayuwar mutane, tare da tabbatar da wata manufa ko isar da wani saqo, a bayan qasa.
            Kuma tabbas idan a rayuwar matasalamarin MANUFA ya zagwanye,to sai rayuwarsu ta wayi gari bata da wata qima, sa'annan abubuwan da matasan suke basu muhimmanci su zama tauyayyu da naqasa, "Rayuwar duniya ba komai ba ce, face abar shagala da wasa, kuma lallai lahira tabbas itace rayuwa, da sun kasance suna sani" [Ankabut: 64].

            LOKACIshine mafi tsadan abinda saurayi a rayuwarsa yake mallaka, kuma a cikin lokacin saurayi yake shuka burace-buracensa, yake kuma qoqarin tabbatar da manufofinsa; ta hanyar neman ilimi mai amfani, da aiki managarci, da yin ibada da xa'a, da samun nau'ukan wayewa mabanbanta masu fa'ida, da yin aiyuka masu muhimmanci masu haske, waxanda za su zama ma'auni ga manufofinsa da aiyukansa, kuma su bunqasa masa rayuwarsa a gare shi. Kuma a cikin lokacin,Saurayi yake kwarewa cikin wata sana'a wacce zata bunqasa gwanancewarsa, da kuma wassu aiyukan da zai iya gina ko xora rayuwarsa akansu.

            Kuma idan lokacin samari ya wofanta daga manufofi maxaukaka, to sai munanan aqidunda suke zamar da MATASAko karkatar da su, su silale; zuwa gare su, Sai MATASAsu shagalta da abubuwan da basu da qima, da kuma tunani cikin yasassun al'amura, Daga nan, sai sabuban vatansu daga miqaqqiyar turba su yi qarfi.

Kuma lallai rashin aikin yi (ga matasa), da zaman banza:Sune gona mai yabanya; wacce ake shuka dukkan sharri, da dangin nau'ukan vata.
Imam Asshafi'i (رحمه الله) yace: "Rai, idan baka shagaltar da ita da gaskiya ba, to sai ta shagaltar da kai da varna".

            Kuma yana da hatsari: Vata lokacin da ake yi wajen yawo tsakanin shafukan sada zumuncinda suke cutar da aqida, suke kuma yin tasiri ga halayya,ko rikita su, suke kuma raunata alaqoqin da suka qulle tsakanin iyalai, ta hanyar sanya mutum cikin rayuwar kaxaici alhalin yana cikin jama'a. Kuma mummunan tasirin waxannan lamuran abu ne, da yake a fili; baya vuya.

            MATASA suna fiskantar makirce-makirce daga maqiya addini; ta hanyar bijiro musu abubuwan sha'awa na haram da kuma ruxinsu, da nufin shafe musu abin alfaharinsu (addini), tare da vata musu ko tuntsurar da abinda suka fiskanta na kyakkyawiyar rayuwa, da qoqarin ruguza musu samartakarsu,  da kuma jefa su cikin ximuwa da vata, da kawar da hankulansu daga himmatuwa da cinma burace-buracensu maxaukaka, da muhimman lamuran garurrukansu da al'ummarsu (musulma).
            Tsira kuma zata kasance ne kawai cikin yin tarbiya wa rai da (littafin Allah) alqur'ani, da baiwa zuciya abincin imani, da yin tafiya cikin tawagar salihan bayi.

Shi kuma qosar da sha'awowi ko buqatu ta hanyoyin da aka shar'anta:Na tabbatar wa mutum moriya, da cin nasara da karama.
            Saboda shi AURE ga MATASA buqata ce ta halitta, kuma ya kan zama nitsuwa ga rai, sannan aure garkuwa ne ga xabi'ar saurayi da halayyarsa.Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Ya ku taron MATASA! Duk wanda ya samu iko a cikinku sai ya yi aure, saboda aure shi ya fi rintsar da ido, kuma ya fi bada garkuwa ga farji. Wanda kuma bai samu iko ba to sai ya lazimci azumi; saboda azumi kamar fixiya ne a gare shi".
            Shi kuma jinkirta aure ga wanda yake da ikon yinsa yana da irin nasa cutarwar; ga halayyan mutum da kuma rai, da kuma wassu cutarwar ga xaukacin al'umma.  Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Idan wanda kuka yarda da addininsa da halayyarsa ya zo muku, to ku aurar masa, Idan ba ku aikata haka ba, to fitina zata kasance a bayan qasa, da kuma varna mai faxi".

            Saurayi yana da buqatar a rayuwarsaya riqa daidaita tsakanin aiki da hankali da kuma axifar soyayya, Wannan kuma saboda kasancewar zamanin samartaka = yanayi ne da axifar soyayya mai yawa take ruruwa a cikinsa, wanda kuma za su iya yin mummunan tasiri a rayuwar saurayi ta gobe da yake fiskanta, idan har ba a tankwara ta ga hasken Qur'ani, ko abinda hankali ke hukuntawa ba.
Kuma lallai axifar so ko ta qi matsananci, wanda babu hasken wahayi a cikinta, tana iya jagorantar saurayi zuwa ga qetare iyaka, ko zuwa ga taqaitawa, ko izuwa ga bauxe wa hanya, ko ga yin qari ga addini.
            Kuma ana magance matsalar axifar so da take da qarfi a wajen saurayi, ta hanyar qosar masa da ita a cikin iyalansa, da jiyar da shi, ko kuma kewaye saurayi da yanayi na bada kulawa, da kuma bada aminci, tare da tarbiyantar da ransa akan kamewa, da kuma rintse idanu, tare da jin kunyar Allah (تعالى).
An ruwaito daga Jarir xan Abdullahi yace: Na tambayi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) dangane da gani na bazata, Sai ya umurce ni da na kawar da ganina.
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ya kai Aliyu! Kada ka biyar da gani akan gani, saboda ganin farko naka ne, amma na qarshen banaka ba ne".

            Kuma yana daga abinda yake taimaka wa MATASA wajen gina mutum qaqqarfa mai amfani: Gina ko qarfafa alaqarmatasan da iyalansu; kasancewar iyalai sune garkuwan samari, kuma sune mafaka a gare su, wanda ke samar da nitsuwar zuci a gare su, da hutu, da kwanciyar hankali.  Kuma saboda kasancewar iyalai sune matabbatar nasiha da faxakarwa ga 'ya'yansu, da yin tarbiyya irin ta imani a gare su, tare da qarfafarsu. Yayin da rashin iyalai ko yin watsi da su, ko kuma samun raunin alaqar da ke tsakanin iyaye da 'ya'yansu, ke kai MATASA xaukar tarbiyyarsu daga wuraren renon da aka jahilta, da kuma qungiyoyin da za su shafe hankulansamari, sannan su jefa su cikin ramukan vata masu nisa.

            Yin wa'azi da faxakarwa a rayuwar saurayi sune abinci ga ruhinsa (zuciya), da samun nitsuwa a ransa,  Kuma lallai alqur'ani ya qarfafa hakan; saboda kasancewarsa abu mai muhimmanci wajen gina mutum lafiyayye, tare da amintar da takunsa a cikin duniyarsa, Ya zo a cikin wasiyyoyin annabi Luqmanu ga xansa,  "Kuma yayin da Luqmanu yace wa xansa, a lokacin da yake masa wa'azi; Ya kai qaramin xana! kada ka yi shirka wa Allah, lallai haxa Allah da wani zalunci ne mai girma" [Luqman: 13].
Sannan ya ce: "Ya kai qaramin xana! Lallai aiki idan ya kasance koda gwargwadon kwayar komayya ne, sai ya kasance a cikin wani dutse, ko a cikin sammai ko a cikin qassai, to Allah zai zo da shi, Lallai Allah Mai tausasawa ne Masani    *    Ya kai qaramin xana! Ka tsayar da sallah, kuma ka yi umurni da kyakkyawa, kuma ka yi hani ga mummuna, sannan ka yi haquri game da abinda zai same ka, Lallai wannan yana daga muhimman al'amura" [Luqman: 16-17].

            Irin aikin da saurayi zai yi; ta hanyar tafiya a sasannin qasa, (don rufa wa kansa asiri) wannan xaukaka ne ga mutuncinsa, kuma karama ce ga iyalansa,   daxin daxawa kuma aikata hakan shine mafi daxin hanyoyin neman arziqi;   An tambayi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) cewa Wani aiki ne ya fi daxi? Sai ya ce:
"Aikin mutum da hannunsa, da kuma kowani kasuwanci na halal kuvutacce".
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya sanya tara itatuwa da sayar da su a matsayin abinda yafi alkhairi ga mutum, akan ya roqi mutane; sun ba shi ko sun hana shi.
Kuma Umar (رضي الله عنه) yana cewa:
"Na kan ga saurayi sai ya burge ni, amma idan aka ce: Bashi da wata sana'a to sai qimarsa ta zube  daga idona". Sa'annan yana cewa:
"Kada wani daga cikinku ya zauna ya qi neman arziqi; sai yayi ta cewa: Ya Allah! Ka azurta ni; Ai kun san cewa sama bata zubo da ruwan zinari ko azurfa".
            Kuma lallai saurayi mai manufa ya kan qaurace wa zaman banza, sai ya fiskanci yin aiki; koda kuwa yaya nau'in aikin yake, ba tare da ya raina wata sana'a aiyananniya, ko wani aiki sananne ba.
            Su kuma al'umma da dukkan vangarorinsu ana nemansu da su sauqaqe hanyoyin samun aiyukan da suka dace, tare da bubbuxe qofofin kasuwanci, domin samari su zama masu amfanar da kansu, da garurrukansu da al'ummarsu.
           
            Kuma ya dace ga saurayi cikin saukansa da tashinsa, da tafiyarsa (wassu qasashen) da zamansa (a garinsu, ko qasarsu):Ya zamto mai alfahari da addininsa da al'adarsa, da riqa jin xaukakar aqidarsa; kada ya riqa jinkunyar bayyanar da musuluncinsa.Kuma da aikata haka ne kawai; zai qetare qullin jin naqasa, da makauniyar bin maqiyan Allah, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma jin izza na Allah ne da ManzonSa da kuma muminai" [Munafiquna: 8].

            Nitsuwa a rayuwar saurayi hali ne abun yabo, kuma xabi'a ce da za a iya kwaikwayarta, kuma wani qarfi ne da ke nuna hankalin wanda ya siffanta da ita.
Shi kuma tsanani cikin mu'amala, da halin tunzura, ko neman xaukar fansa, dukkansu alamomi ne masu hatsari, sannan kuma fizga ne irin naShexan, waxanda muninsu zai iya cutar da samari, ya kuma tunkuxar da qarfinsu, kamar yadda hakan zai zama matsala ga al'umma gabaxayanta.

Kuma wajibi ne akan saurayi, a lokacin jin qarfi da samartaka da nashaxi;Ya kula da sunnar rayuwa, da canzuwar yanayi da hali, da tafiyan dare da yini; sai ya yi aiki a samartakanta saboda tsufansa, da kuma lokacin lafiyarsa saboda cutarsa, kuma kada ya ruxu da halin qarfi da yake ciki; saboda samartaka tsufa ne ke biye da ita, qarfi kuma yakan tafi zuwa ga rauni, kamar yadda ita kuma lafiya cuta ke yi mata barazana, Allah ta'alah yana cewa:
"Allah shine wanda ya halitta ku daga rauni, sa'annan ya sanya wani qarfia bayan raunin, sa'annan ya sanya a bayan qarfin wani rauni da furfura, yana halittar abinda ya yi nufi, Shine Masani Mai qudura" [Rum: 54].

            Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah, ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
>>> 
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai  * Mai rahama mai jin qai  * Mamallakin ranar sakamako.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,  abun bautan na farko da na qarshe.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa, majivincin masu taqawa.

            Bayan haka;
            Ina yin wasici a gare KU, da NI kaina da bin dokokin Allah, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku bi dokokin Allah, sai Allah ya ilmantar da ku" [Baqara: 282].

            Shi saurayi musulmi zuciyarsa ta kan cika da son Allah da son Manzonsa (صلى الله عليه وسلم), Kuma da zai dulmuya cikin wani abu na savo,to da saizuciyarsa ta yimotsi da jin tsoron Allah, da kuma nadama akan wannan zunubin, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Lallai bawa idan ya aikata kuskure sai a xiga wani baqin xigo a cikin zuciyarsa, idan kuma ya bari sannan ya tuba sai a kankare zuciyarsa, idan kuma ya koma wa zunubin; to sai a qara wannan alamar, har sai ta rufe zuciyar, kuma shine tsatsar da Allah ya ambata; ((A'aha! kawai dai; ya sanya tsatsa ne akan zuciyarsu abinda suka kasance suke aikatawa)) [Muxaffifina: 14]".

            Wassu samarin sun riski kuma sun gane kuskurensu, kuma tabbas sun san haramcin abinda suke aukawa cikinsu, saidai kuma suna jinkirta tuba, kuma suna cewa da-sannu, da-sannu; Shi kuma faxin haka; -ma'ana: da, sannu zan dena, da sannu zan tuba- shine mafi girman abinda ke hana mutum tuba, kuma faxin (Da sannu) runduna ne daga cikin rundunonin shexan.

            Shi kuma dogewar wassu MATASA cikin zunubai yana dahatsari mai girma, kuma sharri ne mai bazuwa.
            Kuma lallai mai hankali yana jin tsoron matsalar savo, kasancewar wutan savo yana ci ne ta qarqashin toka;   saboda zai yiwu a jinkirta uqubansa, kamar yadda zai yiwu uqubar ta zo da gaggawa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Lallai Allah yana yin talala wa azzalumi, har idan ya tashi kama shi, ba zai suvuce masa ba. Sannan sai ya karanta: ((Kuma haka, kamun Ubangijinka ya ke; idan zai kama alqarya alhalin tana zalunci, lallai kamunsa mai raxaxi ne mai tsanani)) [Hudu: 102]".
Kuma manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Idan kaga Allah yana baiwa bawa duniya akan savonsa abinda yake so, to lallai wannan talala ne. Sannan sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya karanta: ((Yayin da suka mance abinda aka tunatar da su, sai muka bubbuxe qofofin kowani abu a gare su, har sai da suka yi farin ciki da abinda aka basu sai muka kama su, kwatsam, sai ga su sun xebe tsammanin dukkan alkhairi)) [An'am: 44]".

            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
            Ya Allah!Ka yarda da khalifofi gudahuxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu,    da Iyalan annabi da sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka aljanna, da abinda yake kusantarwazuwa gare ta, na zance ko na aiki, kuma muna neman tsarinka daga wuta, da kuma abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko na aiki.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shine kariya ga al'amarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce a cikinta rayuwarmu take, kuma ka gyara mana lahirarmu wacce zuwa gare ta za mu koma, ka sanya rayuwa ta zama qarin alkhairi ne a gare mu, mutuwa kuwa ka sanya ta hutu ne a gare mu daga kowani sharri. Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka shiriya da taqawa da kamewa da wadaci da arziqi.
            Ya Allah! Ka taimake mu kada ka taimaki wassu akanmu, ka bamu nasara kada ka bada nasara ga wassu akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla ma wassu akanmu, ka shirye mu, kuma ka sauqaqe shiriyarka a gare mu, kuma ka taimake mu akan wanda ya yi zalunci akanmu.
            Ya Allah! Ka sanya mu zama masu ambatonka, masu yin godiya a gare ka, masu qanqan da kai a gare ka, masu yin kuka da mayar da al'amari zuwa gare ka.
            Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, ka tabbatar da hujjojinmu, kuma ka daidaita harshenmu, ka zare dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai mu muna neman tsarinka daga gushewar ni'imarka, da canzuwar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan abinda zai sanya ka fushi.
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana albarkokinka da rahamarka da falalarka da arziqinka.
            Ya Allah! Ka yi mana albarka cikin shekarunmu, kuma ka sanya mana albarka cikin matanmu, da 'ya'yanmu, da zurriyarmu, da aiyukanmu da shekarunmu, ka sanya mu; mu zama masu albarka a duk inda muke, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka tabbatuwa cikin lamarin addini, da kuma azama akan aikin shiriya, da ribatar kowace biyayya, da kuvuta daga kowani savo, da rabauta da aljanna, da kuvuta daga wuta.
            Ya Allah! Ka taimaki wanda ya taimaki addini, kuma ya Allah ka tavar da duk wanda ya tavar da musulunci da musulmai, Ya Allah! Ka taimaki addininka da littafinka da sunnar annabinka da kuma bayinka muminai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulmai… a kowani wuri, Ya Ubangjin talikai, Ya Allah! ka kasance wa musulmai… a qasar Sham Ya mafificin masu jin qai, Ya Allah! Ka kasance musu Mai qarfafawa, Mai taimako, Mai tallafawa, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ubangijin gaskiya, Ya Allah wanda ya saukar da littatafai, mai gudanar da gajimare, wanda ya rusa rundunoni, ka kwace nasara daga maqiyanka; maqiyan addini, kuma ka taimaki musulmai akansu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi! Ka taimaki musulunci da ma'abotansa, a kowani wuri.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada lafiya ga majinyatanmu, ka yaye baqin cikinmu, ka sunce fursunoninmu, ka jivinci lamarinmu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka yi dace wa shugabanmu da abinda kake so, kuma ka yarda, Ya Allah ka datar da shugabanmu mai hidimar harami guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu, Kuma ina roqonka ka datar da na'ibansa guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, lallai kai mai iko ne akan  komai.
            Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai gabaxaya wajen yin aiki da littafinka, da yin aiki da shari'arka, Ya mafificin rahamar masurahama.
            Ya Allah! Kai ne abin bauta; babu abin bautawa da gaskiya sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma faqirai, ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! Shayarwar rahama, ba shayarwar azaba ko bala'i ko rusau, ko dulmuya ba, Ya Allah! Ka rayar da garurruka da shi, ka bada ruwan sama ga bayi, ka sanya shi ya kai birni da qauye, Ya mafificin rahama masu rahama.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da imani, kada ka sanya a cikin zuciyarmu wani qulli ga waxanda suka yi imani; Ya Ubangijinmu lallai kai ne Mai tausasawa ne Mai rahama" [Hash,ri: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...