2015/11/05

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI saw Ta Sheikh Assubaitiy 24 Almuharram 1437hijira daidai 06 11 2015m








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A,24/ALMUHARRAM/1437H






LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya halitta Mutum, ya kuma ilmantar da shi bayani, Ina yin yabo a gare shi, tsarki ya tabbata a gare shi- kuma ina gode masa; akan ni'imar shiriya da Imani,
Kuma ina shaidawababu abinbautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Mai karimci Mai girma  Mai yawan baiwa.
Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa, Ma'abocin falala da kyautatawa.
Allah yayi daxin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, duk lokacin da rana da wata suka yi canjin aiki.

Bayan haka:
            Ina yi muku wasici da ni kaina da kiyaye dokokin Allah; Allah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna Musulmai" [Ali-imrana: 102].

Lallai haqiqa Allah ya halitta MUTUM sai ya karrama shi, ya kuma bashi fifikon da ya banbanta shi da sauran halittu, a cikin qirarsa da halittarsa, da kuma cikin umurnin da ya ba shi, da hani; (Kuma Mutum shine) RAI (wato: RUHI) da HANKALI da JIKI.  (Shi kuma Uban Mutane; wato annabi Adamu shine) Damqa xaya daga LAKAR QASA (ta,tavo), da kuma busar rai daga RUHIN ALLAH,
"A yayin da Ubangijinka yace wa Mala'iku: Lallai ne, zan halitta wani mutum daga laka   *   Idan na daidaita shi, kuma na yi busa a gare shi daga ruhina, Sai ku faxi a gare shi, kuna masu sujjada" [Sad:  71-72].
Allah ya halicci Mutum a mafi kyan tsayuwa,      ya kuma sanya masa a cikin jikinsa HALAYYA da JI IRIN NA JIKI, tare da JIN ZAQI ko XACIN ABUBUWA.
Kuma lallai mutanen da a jikinsu suke jin Imani (abincin rai ko ruhi),
da soyayya (kayan zuci),
da tausayi (daga AXIFA);
Sune waxanda suka fi tabbatar da ma'anonin MUTUNTAKA dayawa; fiye da wassunsu, irin mutuntakar da take xaukar SALON RAYUWARTA da QIMARTA daga Musulunci.

            Musulunci ya kiyaye mutum da mutuntaka ta hanyar tsayar da haddodi na shari'a; waxanda daga cikin muhimman manufofinsu akwai: kiyaye haqqoqin xaixaikun mutane.
            Kuma musulunci ya tsarkake mutum, ya kuma xaukaka shi, a cikin da'ira ko karantarwar  alqur'ani,    Kuma duk lokacin da mutum ya kusanci Ubangijinsa da yin sallah da bauta da addu'a to sai mutuntakarsa ta xaukaka,   Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku nemi taimako da yin haquri da sallah" [Baqarah: 45]. Ya kuma ce:
"Lallai sallah tana yin hani daga alfasha da abin qi" [Ankabut: 45]. Kuma yace:
"Ka karvi sadaka daga dukiyoyinsu, kana mai tsarkake su, da kore musu dauxa da ita" [Taubah: 103].
Waxannan ibadodi ne, da suke da tasiri; Suke da tasiri ga ran mutum;  saboda suna bada tarbiyya ga mutum akan haquri da ikhlasi, suna kuma ba shiko samar masa da halayya ababen godiya, sa'annan (a ko-da yaushe) suna tsamar da shi daga sifofi ababen zargi.

            Kuma shi Musulunci a ko- da yaushe yana cikiyar abinda zai xaukaka mutum, ya kuma kawo masa kamala; ta hanyar rayar da KIYAYE ALLAH (تعالى) (a cikin mutane); Allah yana cewa:
"Kuma lallai mutum, hujja ne ga abinda ya shafi kansa, Masani    *   Kuma ko da ya jefa uzurorinsa (to ba za a karva masa ba)" [Qiyamah: 14-15].
Kuma idan Mutum ya jagoranci ransa, ya kuma yi qoqarin gyara ta to sai ta miqa wuya a gare shi, kuma sai mutumtakarsa ta yi haske, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma waxannan, da suka yi qoqari ga neman yardarmu, lallai za mu shiryar da su hanyoyinmu" [Ankabut: 69].
            Kuma lallai MUTUNTAKAR da musulunci ya tsarkake; ta haxa dukkan JINSI da LAUNI, domin mutane su samu sanayyar junansu, kuma su samu sabo, su kuma rayu suna 'yan'uwa, tare da tsayar da wajibin shugabanci da mayewar wassu a bayan wassu a doron qasa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku Mutane! Lallai ne Mu,mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da qabiloli, domin ku san juna. Lallai mafificin daraja a wurin Allah daga cikinku shine mafificinku a taqawa" [Hujuraat: 13]. Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kuMutane! Ku bi dokokin Ubangijinku, wanda ya halitta ku daga rai guda xaya, kuma ya halitta masa matarsa daga kansa, Kuma ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata, Kuma ku bi Allah da taqawa, wanda ku ke roqon juna da shi, da kuma zumunci, Lallai Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne" [Nisa'i: 1].

            Kuma yana daga cikin ABINDA MUTUNTAKA take hukuntawa a cikin Musulunci: Taimakawa juna, da tallafawa, da gina ma'anonin so da rahama da tausayi da sassautawa, da kuma qauracewa qulle mutum ko riqe shi a zuci, da nisantar girman kai, da xaukar fansa, da yaudara da cin amana, da hana zalunci da taimakon mabuqaci, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Kuma ku kasance bayin Allah 'yan'uwan juna".

            Alqur'ani mai karamci yana rayar da ma'anonin Mutuntaka masu girma, kuma yana tabbatar da girman da ya baiwa mutum, kamar yadda alqur'anin yake kare axifar so a wurin mutum daga bauxewa daga manufofinta, kuma yake kare shi daga yin jayayya abun qi, wacce ke cin karo da tausasawa tatacce dake tsakanin  mutune, sa'annan ya sanya mutum yana ganin gaskiya, kuma yana sanin shiriya, yana yin hukunci da hankali, kuma yana cikiyar a ina adalci yake,    Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Kuma ina roqonka yin adalci a cikin halin yarda da na fushi".

            A ko yaushe, Alqur'ani yana tsarkake mutum;domin kada buqatu irin na jiki da sabuban sha'awa su saukar da shi daga matakin girma, zuwa ga matakin da mutane za su wayi-gari suna masu bautawa sha'awowinsu ko neman jin daxinsu. Kuma alqur'ani yana xaukaka matsayin rayuwa; don kar ta canza zuwa ga wata jayayya abar qi, da yaquka masu halakarwa, wanda ran mutum da jikinsa zasu walaqanta a cikinSu.

            Mutuntaka a cikin musulunci ta kai wata daraja mai girma, da martaba maxaukakiya wajen manufofinta da hanyoyin tabbatar da ita,
YANA DAGA CIKIN HAKA:
Kyautata wa IYAYE guda biyu, ta hanyar karrama su, da ciyar da su, da qanqan da kai a gare su,
Da wajen kulawa da MACE, da bata haqqoqinta; UWA ce ko MATA ko 'YA ko 'YAR'UWA,   Allah (تعالى) yana cewa:
"Idan xayansu (iyaye guda biyu) a wurinka ya kai ga tsufa ko kuma dukkansu biyu, to, kada ka ce musu 'Uf', kuma kada ka tsawace su, kuma ka faxa musu Magana mai karimci" [Isra'i: 23].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda aka jarrabe shi da wani abu na 'ya'ya mata, sai ya kyautata musu, to za su zame masa kariya daga faxawa wuta". Kuma yace:
"Wanda ya xauki nauyin 'yan mata biyu har suka balaga, zai zo a ranar qiyama Ni da Shi, Sai Annabi yahaxe tsakanin yatsunsa".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Mafificinku alkhairi shine wanda ya fi ku alkhairi ga iyalansa, kuma Ni, ne mafificinku alkhairi ga iyalaina".

            Kuma an rasa mutuntaka, an kuma shafe alamominta idan aka yi ta'addanci ga (Allah) mahalicci (جل وعلا) a cikin halittarsa, da cikin halattawa da haramtawa,    Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya halitta mutum daga xigon maniyya sai gashi yana mai husuma bayyananniya" [Nahl: 4]. Kuma yace:
"Ya ku waxanda suka yi imani kada ku haramta abubuwa masu daxi da Allah ya halatta muku, kuma kada ku qetare iyaka, Lallai ne, Allah ba ya son masu qetare haddi" [Ma'idah: 87].

            Kuma mutum ya kan yi alfahari, da xagawa, da girman kai, da aikata abinda ya ga dama, a lokacin da ya kai zuwa ga mulki, ko aka yalwata masa ni'imomi da alkhairori,   Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai ne Mutum haqiqa, yana girman kai   *   Domin ya ga kansa, ya wadata" [Alaq:  6-7].
            Kuma wannan nau'i na vata –wato: girman kai, da aikata abinda mutum ya ga dama- yana kaiwa zuwa ga uquba, da bala'o'i, dasamun koma-baya, da xebe albarkar alkhairi da arziqi, wanda Allah ke shumfuxa shi ga bayinsa,  Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma da mutanen alqaryu sun yi imani sun bi dokoki, da, Mun buxe albarkoki akansu, daga sama, da qasa, Saidai kuma sun qaryata, sai muka kama su da abinda suka kasance suna aikatawa" [A'araf: 96].

            Kuma mutuntakar mutum bata inganta, ta kuma kasance tana da wata qima, har sai HANKALI ya 'yantu daga vata, AQIDA kuma ta 'yantu daga gaskata tatsuniyoyi da qarereyin da ake lulluvewa (wato: dajal);
YANA KUMA DAGA CIKIN HAKA;
Abinda ya ke aukuwa na sihiri, da ilimin taurari, da riya yin zance da rayukan boye, da karanta tafin hannu, da sihirin sanya barci, Duk waxannan aiyukan suna lalata mutuntakan mutum, kuma suna vata wa musulmi aqidarsa, da halayensa, kuma yarda da su yana jefar wa mutum hankalinsa da tunaninsa.

            Waxanda suke qona mutane da ransu, suke kuma yin qone-qone, da kashe masu yin sallah a masallatai, lallai haqiqa an shafe mutuntakansu, kuma basirarsu ta yi dufu.

            Kuma waxannan, da suke kutsawa,sannan su yi dauxa wa masallacin da aka yi isra'i da Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم); su yi masa dauxa da jikinsu da kuma takalmansu, sannan su karkashe mata da yara, da manyan mazajen da basa xauke da makamai a cikin filin harabar masallacin, suma zukatunsu sun mutu, kuma sun tove rigar mutuntaka da dukkan ma'anoninta da surorinta,   Allah (تعالى) yana cewa:
"Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa, daga Masallaci mai alfarma zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa wassu daga cikin ayoyinmu, lallai ne Shi, Shine Mai ji, Mai gani" [Isra'i: 1].   Kuma Allah yace:
"Ya ku waxanda suka yi imani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku " [muhammadu: 7].     
            Wannan shine IMANI; wanda idan mutane suka rasa shi,sa'annan suka rasa neman haskaka rayuwarsu da hasken alqur'ani to sai su gangara zuwa can quryar qasa, kuma sai hakan ya tuntsurar da qimar mutum, tare da mayar da mutum zuwa ga matsayin da yake qasa da matsayin da Allah ya ajiye mutum akansa.
            Akan haka; Kuma, lallai Musulmai suna xauke da saqo mai girma zuwa ga DUNIYA, Domin su xaukaka qimar Mutum, kuma domin su fiskanci matsalolin da suka fiskanci duniya, a lokacin da yunwa ke yaxuwa, da yawaitan sharrin cututtuka, da kuma korar miliyoyin mutane daga qasashensu da gidaddajinsu, da kuma kunnuwar wutan fitintinu;    Wannan kuma saboda kasancewar Shi musulmi, yana xauke da zuciyar da take xauke da rayayyen tausayi ga Mutum; wanda ta ke tunkuxa shi zuwa ga yaxa shiriya, da taimakon waxanda aka zalunce su, da qoqarin yaxa dawo da fata cikin jijiyar rayuwar mabuqata, da isar da taimako ga waxanda suka cutu, a sanadin wani bala'i, Hakazalika musulmi yana xauke a tare da shi, da SAQO irin na AMINCI, da TAUSAYI (rahama).
            Kuma, a lokacin da muke tunani cikin tarihin Sahabban Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) zamu ga cewa lallai su, sun bada mafi burgewan misali, a vangaren ciyarwa, da kyautatawa mutane, tare da yaxuwansu a sasanin qasar Allah mai faxi (duniya), suna shiga ko-ina, cikin tafiya mai nisa, domin su SANAR DA MUTANE MUSULUNCI, Wannan kuma ya kasance ne saboda tausayinsu ga halittu, da kuma shiryar da su zuwa ga hanyar gaskiya, tare da xaukaka lamarin mutum;   suna yin haka sunamasu neman yardar Allah.
            Suma masu yin da'awa zuwa ga Allah, a kowani zamani, da kowani wuri, da waxannan da suke bada rayukansu fiysabillahi, da dukiyarsu don yin biyayya wa Allah, da waxannan da suke tsaye akan aiyukan alkhairi, da haddatar da Mutane alqur'ani da karantar da shi, da waxannan da suka kakkafa kayukansu don amfanar da wassunsu,   Dukkan waxancan lallai Allah ya azurta su da mutumtaka da tausayi na gaskiya, da cikakken ji da irin abinda Mutane suke ji da shi (na damuwa ko daxi); Kuma Alqur'ani shi ya tarbiyyantar da su akan haka,   saboda haka; Muna yi muku murnar jin daxin rayuwar duniya, da kuma rabauta da ni'ima mai tabbata (a lahira).

            Kuma lallai ma'anonin mutuntaka da tausayi suna bayyana a wajen jagororin wannan qasa, da mutanenta, saboda gudumawa mai girma da suke bayarwa ga Mutum, wanda kuma yake qarfafa aikin agazawa, a wurare dayawa a faxin duniya.      Kuma suma sauran Musulmai a wurare dayawa a faxin duniya basu taqaita qoqarinsu ba, a wajen fara gabatar da kayan agaji, ga waxanda aka zalunta, da waxanda musiba ta shafa, tare da miqa hannun taimako ga kowani mabuqaci, suna masu nuna mutuntaka ta gaskiya, da ji da irin abinda mutane suke ji da shi (na daxi, ko wahala).   Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma don me bai kutsa cikin al'aqabah?   *   Kuma menene ya sanar da kai abinda ake ce wa al'aqabah?'   *    Itace fansar wuyan bawa    *   Ko kuma ciyarwa a cikin wani yini ma'abocin yunwa  *    Ga maraya, ma'abocin zumunta    *   Ko kuwa ga miskini ma'abocin turvaya (wanda babu komai a wurinsa)" [Balad: 11-16].

            Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
>>> 
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
     Godiya ta tabbata ga Allah; yabo Mai yawa, Mai daxi, Wanda yake cike da albarka, Ina yin godiya a gare shi –tsarki ya tabbata a gare shi- kuma ina yaba masa, Kuma ina shaidawababu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah yayi daxin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa,
Bayan haka:
Ina yi muku wasici da ni kaina da bin dokokin Allah; saboda ita taqawa garkuwa ce mai bada kariya, kuma a cikin aikatata, akwai samun rabo mai girma.

            Kuma YANA DAGA CIKIN abubuwan da suke munana mutuntaka, su kuma gurvata haqiqaninta: Amfani da tsananin da mutane suka samu kayukansu a ciki, da halin qunci, da buqatar mabuqata wajen mu'amala da riba,     Kuma lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya bayyana sakamakon Mutane masu yin mu'amala da riba; a inda yace:
"A wannan daren na yi mafarkin wassu mutane guda biyu waxanda suka zo mini, sai suka fitar da ni zuwa ga qasa mai tsarki, Sai muka tafi har sai da muka iso wani kogi na jini, wanda a cikinsa akwai wani mutum yana tsaye, A gavar kogin kuma ga wani mutum yana tsaye, a gaba gare shi akwai duwatsu , Sai mutumin da yake cikin kogin ya fiskanto, har idan ya so ya fita, Sai wannan mutumin da ke gavar kogin ya jefe shi da dutse a bakinsa, sai ya mayar da shi can inda ya ke, Sai ya zama duk lokacin da ya nufi ya fita sai ya jefe shi a bakinsa da dutse, sai ya koma wurinsa na farko da ya kasance, Sai nace: Wanene wannan wanda yake cikin kogin? Sai yace: Maciyin riba ne"    [Bukhariy ya ruwaito shi].

HUXUBAR TA QARE
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
            Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu,    da Iyalan annabi da sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka aljanna, da abinda yake kusantarwa zuwa gare ta, na zance ko na aiki, kuma muna neman tsarinka daga wuta, da kuma abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko na aiki.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shine kariya ga al'amarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce a cikinta rayuwarmu take, kuma ka gyara mana lahirarmu wacce zuwa gare ta za mu koma, ka sanya rayuwa ta zama qarin alkhairi ne a gare mu, mutuwa kuwa ka sanya ta hutu ne a gare mu daga kowani sharri. Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka shiriya da taqawa da kamewa da wadaci da arziqi.
            Ya Allah! Ka taimake mu kada ka taimaki wassu akanmu, ka bamu nasara kada ka bada nasara ga wassu akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla ma wassu akanmu, ka shirye mu, kuma ka sauqaqe shiriyarka a gare mu, kuma ka taimake mu akan wanda ya yi zalunci akanmu.
            Ya Allah! Ka sanya mu zama masu ambatonka, masu yin godiya a gare ka, masu qanqan da kai a gare ka, masu yin kuka da mayar da al'amari zuwa gare ka.
            Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, ka tabbatar da hujjojinmu, kuma ka daidaita harshenmu, ka zare dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai mu muna neman tsarinka daga gushewar ni'imarka, da canzuwar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan abinda zai sanya ka fushi.
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana albarkokinka da rahamarka da falalarka da arziqinka.
            Ya Allah! Ka yi mana albarka cikin shekarunmu, kuma ka sanya mana albarka cikin matanmu, da 'ya'yanmu, da zurriyarmu, da aiyukanmu da shekarunmu, ka sanya mu; mu zama masu albarka a duk inda muke, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka tabbatuwa cikin lamarin addini, da kuma azama akan aikin shiriya, da ribatar kowace biyayya, da kuvuta daga kowani savo, da rabauta da aljanna, da kuvuta daga wuta.
            Ya Allah! Ka taimaki wanda ya taimaki addini, kuma ya Allah ka tavar da duk wanda ya tavar da musulunci da musulmai, Ya Allah! Ka taimaki addininka da littafinka da sunnar annabinka da kuma bayinka muminai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulmai… a kowani wuri, Ya Ubangjin talikai, Ya Allah! ka kasance wa musulmai… a qasar Sham Ya mafificin masu jin qai, Ya Allah! Ka kasance musu Mai qarfafawa, Mai taimako, Mai tallafawa, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ubangijin gaskiya, Ya Allah wanda ya saukar da littatafai, mai gudanar da gajimare, wanda ya rusa rundunoni, ka kwace nasara daga maqiyanka; maqiyan addini, kuma ka taimaki musulmai akansu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi! Ka taimaki musulunci da ma'abotansa, a kowani wuri.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada lafiya ga majinyatanmu, ka yaye baqin cikinmu, ka sunce fursunoninmu, ka jivinci lamarinmu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka yi dace wa shugabanmu da abinda kake so, kuma ka yarda, Ya Allah ka datar da shugabanmu mai hidimar harami guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu, Kuma ina roqonka ka datar da na'ibansa guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, lallai kai mai iko ne akan  komai.
            Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai gabaxaya wajen yin aiki da littafinka, da yin aiki da shari'arka, Ya mafificin rahamar masu rahama.
            Ya Allah! Kai ne abin bauta; babu abin bautawa da gaskiya sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma faqirai, ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! ka bamu ruwa, Ya Allah! Shayarwar rahama, ba shayarwar azaba ko bala'i ko rusau, ko dulmuya ba, Ya Allah! Ka rayar da garurruka da shi, ka bada ruwan sama ga bayi, ka sanya shi ya kai birni da qauye, Ya mafificin rahama masu rahama.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da imani, kada ka sanya a cikin zuciyarmu wani qulli ga waxanda suka yi imani; Ya Ubangijinmu lallai kai ne Mai tausasawa ne Mai rahama" [Hash,ri: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...