HADISI (NA
1 ): WANDA KE MAGANA KAN ''KHILAFANCIN ANNABTA'' BAYAN MANZON ALLAH (S A W);
(a)
LAFAZIN
HADISIN DA RIWAYOYINSA:
عَنْ سعيد بن جُمهان، عن سَفِينَةَ مولى
رسول الله r، قَالَ: «قَالَ رَسُولُ اللَّهِ r: "خِلافَةُ
النُّبُوَّةِ ثَلاثُونَ سَنَةً، ثُمَّ يُؤْتِي اللَّهُ الْمُلْكَ، أَوْ مُلْكَهُ
مَنْ يَشَاءُ".
وفي لفظ الترمذي: ثُمَّ قَالَ لِي سَفِينَةُ: أَمْسِكْ خِلاَفَةَ
أَبِي بَكْرٍ، وَخِلاَفَةَ عُمَرَ، وَخِلاَفَةَ عُثْمَانَ، ثُمَّ قَالَ لِي: أَمْسِكْ
خِلاَفَةَ عَلِيٍّ، قَالَ: فَوَجَدْنَاهَا ثَلاَثِينَ سَنَةً.
وفي لفظ أبي داود: قَالَ سَعِيدٌ قَالَ
لِي سَفِينَةُ: «أَمْسِكْ عَلَيْكَ أَبَا بَكْرٍ سَنَتَيْنِ، وَعُمَرُ عَشْرًا، وَعُثْمَانُ
اثْنَتَيْ عَشْرَةَ، وَعَلِيٌّ كَذَا»، وفي رواية: (ستّ سنين).
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya zo daga
Sa'idu bn Jumhaan, daga Safinatu –'yantaccen bawan Manzon Allah s a w-
(Allah ya yarda da shi) Ya ce: Manzon Allah (s a w) ya ce: "Khilafancin
annabta shekaru talatin ne, Sa'annan sai Allah ya bada mulkinsa ga wanda ya
nufa''.
A lafazin
tirmiziy (Sai Safinatu ya ce wa xalibinsa: Riqe! Khalifancin Abubakar, da
khalifancin Umar, da khalifancin Usman, sa'annan ya ce: riqe! Khilafancin
Aliyu. Xalibin ya ce:
Sai mu ka lissafa muka samu khilifancin nasu shekaru talatin ne).
Amma a
lafazin Abu-dawud haka lafazin ya zo: (Sa'id bn Jumhaan, ya ce: Sai Safinatu
ya ce mini: Qirga wannan!
Abubakar da khilafancinsa shekaru biyu, Umar goma, Usmanu goma sha biyu, Aliyu
kuma kaza), a wata riwaya: shekaru shida.
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SU KA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Wannan
hadisin maluman sunna dayawa sun ruwaito shi a cikin littatafansu, daga cikinsu
Imam Abu-dawud a cikin littafinsa ''as-sunan'', lamba: 4646 da 4647, da
Abu-isa At-tirmiziy a cikin ''jami'i'', lamba: 2226, kuma ya ce: hadisi ne
hasan. Alhafiz Ibnu-hajar a cikin littafinsa ''fat-hul bariy, [2/ p2677] '' ya
ce: (Ma'abuta ''sunan'' sun ruwaito wannan hadisin, kuma Ibnu-hibbana da
waninsa sun inganta shi).
Ibnu-taimiyyata
a cikin littafinsa ''minhajus sunnan nabawiyyah, [7/ p50]'' ya ce: (Wassu
maluma sun raunata wannan hadisin, Saidai kuma Imam Ahmad da wassunsa sun ce
hadisi ne tabbatacce. Kuma wannan shine madogararsu daga cikin nassoshi kan
tabbatar da khilafancin Aliyu).
Lallai
shi wannan hadisin ta hanyar ''Sahabi Safinatu (r a)'' da ya gabata hadisi ne
''hasan'', Saidai kuma hadisin ya zo ta hanyoyin wassu sahabbai guda biyu;
wadanda sune: Jabir bn Abdullahi, da Abubakrata as-sakafiy (r a); don haka
hadisin ''sahihi'' ne da waxannan
''shawahid''.
[Ka
duba: littafin ''silsilatu al-ahadisi as- sahihati na Albaniy, -2/ p823- lamba:
459]. Kuma shi ''Albaniy'' ya kawo maluma goma da su ka inganta wannan hadisin.
(d)
ABUN DA HADISIN KE
KARANTARWA:
Lallai
wannan hadisin Na daga cikin hadisan da su ke qara tabbatar da annabcin Annabi
Muhammadu (s a w); saboda haka maluma dadama su ka ambace shi a littatafansu a
babuka da su ke bayanin dalilan annabtaka ''a'alamun nubuwati''; wannan kuma kasancewar
''bada labari kan abinda zai faru a gaba; sa'annan kuma abun ya faru kamar
yadda labarin ya shaidar'' xaya
ne daga cikin alamomin annabta; Manzon Allah (s a w) kuma ya bada labarai
dubbai kan abubuwan da za su faru a wassu lokuta da suke tafe; sai hakan ya
faru kamar yadda ya labarta.
Kamar
yadda ya gabata xaya daga
cikin maruwaitan hadisin daga cikin sahabbai wato; Safinatu (r a) ya ambaci khilafancin
khalifofi huxu; wato
Abubakar, Umar, Usman da Aliyu (r a) a matsayin cewa su suka cike shekaru
talatin na bayan Manzo, wanda ake laqabi wa jagoranci a cikinsu da laqabin ''khalifancin annabta''.
Saidai
kuma wassu masu bin diddigi daga cikin maluma sun lissafa lamarin; ta hanyar
lissafa shekaru da watanni da satuka da kwanaki na khalifancin kowani khalifa
daga cikin khalifofin nan guda huxu,
sai suka samu cewa bayan qarewar khalifancinsu
akwai kamar watanni shida da suka rage a cikin shekarun nan ''talatin''; wanda
kuma su ne mutanen garin ''kufa'' su ka yi mubaya'a wa Alhasan bn Aliyu bn
Abiy-xalib, har zuwa
lokacin da ya je ya zare hannunsa kan khilafanci ya kuma yi mubaya'a ga Mu'awyah
bn Abiy-sufyan wanda shine farkon ''sarakunan Musulmai'' (r a); don haka irin waxannan maluman
suke cewa: Shugabannin musulmai da za a kira jagorancinsu da ''khilafancin
annabta'' su biyar ne, Na qarshensu shi ne: ''Alhasan'', Shi kuma ''Mu'awuyah''
shi ne farkon sarakunan musulmai.
''Ibnu taimiyyata''
yana cewa: (Rasuwar Annabi –s a w- ya kasance a watan uku –rabi'u al'auwal- a
shekara ta goma sha xaya bayan
hijirarsa zuwa garin Madina, bayan nan kuma zuwa shekara talatin shi ne aka
samu sulhu da xan Manzon
Allah –s a w- a tsakanin vangarori guda biyu
na muminai; wato Shugaba Alhasan bn Aliyu; a lokacin da ya yi ''murabus'' ya
barwa Mu'awuyah; shekara ta 41 a watan 5 –jumada al-akhirah, kuma lallai an
kira wannan shekarar da ''shekarar haxewar jama'a''; saboda dukkan mutane a
wannan shekarar sun haxe wajen yin
mubaya'a ga Mu'awiyatu –r a-, kuma shi ne: ''sarkin Musulmai na farko'').
[majmu'u al-fatawa, 35/ p19].
Ya zo
cikin littatafa da su ka yi wa hadisin da ya gabata sharha, kamar littafin
''aunul ma'abuud, [p2020]'', da ''tuhfatul ahwaziy [2/ p1798]'' maganar
''Al-alkamiy'' da ya ke cewa: (A shekara talatin da su ke bayansa –s a w- ba a samu shugabancin wani idan
banda na khalifofi guda huxu, da kuma
watannin Al-hasan … kwanakin khilafancin Abubakar su ne: shekaru biyu, da wata
uku, da kwana goma … ''Nawawiy'' ya faxa a cikin littafin: ''tahzibu
al-asma'i wallugaat'' cewa: khilafancin Umar shekaru goma ne da watanni biyar
da kuma kwana ashirin da xaya. Usman
kuma shekaru goma sha biyu; in banda kwana shida. Aliyu kuma shekaru biyar, A
wani qaulin kuma
shekaru biyar ba wassu 'yan watanni, Sai kuma Al-hasan wata bakwai … ). Wallahu
a'alam!
(e)
BANBANCI TSAKANIN ''KHILAFANCIN
ANNABTA'' DA KUMA ''MULKI'':
A cikin
wannan hadisin lallai Annabi (s a w) ya bayyana cewa bayan tafiyarsa da shekaru
talatin duk jagorancin da ya kasance a wannan tsukin to ''khilafancin annabta''
ne. Bayan haka kuma sai ''mulki''; To
shin akwai banbanci ne tsakanin lamura biyun?
Amsa ita
ce: Kamar yadda Allah ya kasantar da annabawansa kashi biyu, wassu a matsayin
''annabawa kuma masu sarauta –mulki-'' kamar yadda Allah ya bai wa iyalan
annabi Ibrahim mulki mai girma da annabci; sai su ka zama annabawan
Allah kuma cikin daula, wato kamar su annabi Yusuf, haka kuma annabi Dawud da xansa Sulaiman
suma Allah ya shaida cewa ya basu mulki mai fadi; kamar shi annabi Sulaiman Allah
ya hore masa iska, da shexanu don su
masa gine-gine, da shiga cikin ruwa don kwaso albarkatun da ke ciki, da
sauransu.
Kaso na biyun
kuma sune ''Manzannin Allah a matsayin bayi; masu cikakkiyar bauta a gare shi;
ba daula''; Wannan kuma shi ne zavin
annabinmu; annabi Muhammadu lokacin da Allah ya turo masa Mala'ika ya tambaye shi;
shin so ya ke yi ya zama ''Annabi mai mulki, ko kuma Manzo bawa?'' Sai ya ce:
Na zavi na zama
''Manzo kuma bawa; na samu abinci na ci yau, gobe kuma na rasa; idan na qoshi sai in
gode maka, idan kuma naji yunwa sai in roqe ka!''
To haka
lamarin ya ke dangane da ''khilafancin annabta'' ba shugabanci ne na daula, ko
kuma gadar da mulkin ga 'ya'ya suke kasancewa a gaban waxannan
khalifofin ba, Savanin masu
mulki; waxanda cikin
sarakunan musulmai Mu'awuyah bn Abiy-Sufyan (r a)'' shi ne ya kasance na farkonsu.
Ana shan daula, sai dai shi Mu'awuyah an yi daula ne cikin halal.
Kuma lallai
su masu mulki su kan yi qoqarin su gadar
da ''sarautar'' tasu ga 'ya'yansu.
Idan aka
nazarci tarihin khilafancin waxancan
khalifofi guda biyar za a ga ba fantamawa ce, ko daula, ko zurfafawa cikin tufa
ko abinci ko mallakar dawakai na alfarma da sauransu su ke gaban jagororin ba; saidai kawai addini. Yayin
da ''sarakuna'' a bayansu har zuwa yau labarinsu dangane da abinci na alfarma,
abubuwan sha, tufa, abubuwan hawa, ba boyayyen abu ne a wurin mutane ba. Shi yasa lamarinmatakin farkon shi yafi
soyuwa a wajen Allah.
Manufa dai anan: ita ce:
''khalifancin annabta'' na qoqarin
tabbatar da muradun ''annabta'' ne bakixaya, ba gina duniya ko kuma morarta
ba, yayin da shi kuma ''mulki'' gwargwadon mai mulkin ya ke kasancewa; idan ''na
Allah ne'' sai ka ga ya taqaita wajen
morar mulki ga halal kawai, sa'annan ya kula da muradun annabta, in kuma ba
haka ba; to sai yawan zalunci da sharholiya da budun-buduma cikin morar duniya
ta kowace hanya. Wallahu a'alam.
Wanda ke buqatar qarin bayani kan fiskoki masu yawa da
su ka banbance ''mulki'' da ''annabta'', da ''khilafanci annabta'' duk da cewa:
da mai mulki da annabi dama waxanda
suka khalifance shi: mabiya su kan yi musu xa'a. {To sai ya duba Majmu'u fatawa
ibni taimiyya' [35/ p17-32], da kuma p33-35}. Allah ta'alah ya fahimtar da mu
addininsa, amin!
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وآله وصحبه أجمعين.
Marubuci: Abubakar Hamza Zakaria
4 / Shawwal /1434h daidai 11/08/2013 miladiyya.
No comments:
Post a Comment