HADISI (NA 4): DAKE ALBISHIR KAN SAMUWAR ''KHALIFOFI
GOMA SHA BIYU''; WAXANDA A ZAMANINSU
MUSULUNCI ZAI ZAMO MAI QARFI; MAI IZZA, DA KARIYA:
(a)
LAFAZIN
HADISIN DA RIWAYOYINSA:
الحديث الرابع: ذكر الخلفاء
الاثني عشر من قريش يكون الإسلام في عهدهم قويًّا؛ عزيزًا منيعًا:
في
الصحيحين عَنْ
جَابِرَ بْنِ سَمُرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صلى الله عليه
وسلم يَقُولُ:"يَكُونُ اثْنَا عَشَرَ أَمِيرًا" فَقَالَ كَلِمَةً
لَمْ أَسْمَعْهَا، فَقَالَ أَبِي: إِنَّهُ قَالَ:"كُلُّهُمْ مِنْ
قُرَيْشٍ".
وفي
لفظ عند مسلم: "إِنَّ هَذَا الأَمْرَ
لا يَنْقَضِي حَتَّى يَمْضِيَ فِيهِمِ اثْنَا عَشَرَ خَلِيفَة"، وفي آخر
عنده: "لا يَزَالُ الدِّينُ قَائِمًا
حَتَّى تَقُومَ السَّاعَةُ، أَوْ يَكُونَ عَلَيْكُمُ اثْنَا عَشَرَ خَلِيفَة كُلُّهُمْ مِنْ
قُرَيْشٍ"،
وفي آخر: "لا يَزَالُ هَذَا
الدِّينُ عَزِيزًا مَنِيعًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً"، وفي آخر: "لا يَزَالُ الإِسْلامُ عَزِيزًا
إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَة".
وعند أبي
داود زيادة متكلّمٌ عنها، هذا لفظها: "كُلُّهُمْ تَجْتَمِعُ عَلَيْهِ الأُمَّة".
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya
zo a cikin sahihu Al-bukhariy da Muslim daga Jabir bn Samurah (ra),
ya ce: Na ji Annabi (saw) yana cewa: "Amir, amir'' guda goma sha
biyu za su kasance. Sai Annabi (saw) ya faxi wata kalma da ban ji ta ba, Sai
babana ya ce: Dukkansu daga kabilar quraishawa su ke.
A
wani lafazi –a wajen Imam Muslim-: Lallai ''wannan lamari'' ba zai shige ba;
har sai khalifa guda goma sha biyu sun samu, a cikinsu.
A
wani lafazin kuma –a wajensa-: Addini ba zai gushe ba yana miqe; har a yi
''kiyama'', ko kuma a samu khalifofi goma sha biyu; dukkansu daga quraishawa.
A
wani lafazin kuma: Wannan addini ba zai gushe ba yana da ''izza, da kuma
kariya'' izuwa khalifofi guda goma sha biyu.
A
wani kuma: Musulunci ba zai gushe ba ''yana da izza'' har izuwa khalifofi goma
sha biyu.
Amma
a lafazin Abu-dawud kuma akwai qarin
lafazin da ke tafe: ((Dukkansu al'umma za ta haxu akansu)).
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SU KA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Wannan hadisin maluman sunna da dama sun ruwaito
shi a cikin littatafansu, Daga cikinsu; akwai: Imam Al-bukhariy a cikin
''sahihinsa'', [lamba: 7222], da Muslim a ''sahihinsa'' [lamba: 1821].
Haka shima Abu-dawud a cikin littafinsa
''as-sunan'' ya ruwaito shi da qarin
''lafazi'' –kamar yadda ya gabata- [lamba: 4279].
Saidai kuma ''Wassu maluma'' sun raunata
''isnadin'' wannan qari da ya zo
ta hanyar Abu-dawud.
[Ka duba: littafin ''silsilatu al-ahadisi as- sahihati'' na
Albaniy, -1/ p720- a ''takhrijinsa'' ga hadisi mai 376].
(d)
MA'ANAR
WANNAN HADISI, TARE DA AMBATO RA'AYOYI BIYU NA MALUMAN ''SUNNA'' WAJEN FASSARA
SHI:
Lallai
wannan hadisin ya yi ''albishir'' kan kasancewar khalifofi guda goma sha biyu a
cikin wannan al'umma, Saidai kuma shi hadisin –da dukkan riwayoyinsa- bai
ambaci khalifofin da sunansu ba, kamar yadda kuma bai fito bolo-bolo, ya yi
bayanin shin wadannan khalifofin a jejjere zamaninsu ya ke, ko kuma wassunsu za
su zo a lokuta mabanbanta? Wannan yasa aka samu banbancin ra'ayi wajen fahimtar
hadisin ta ''fiskoki biyun'' a wajen maluman ''Ahlus-sunnah''.
Tare
da cewa hadisin ya ambaci sifofi da yawa; ta fiskar adadin wadannan khalifofi,
da kuma halin da musulunci zai samu kansa na karfi da daukaka, a
zamaninnikansu, da kuma haduwan galibin mutane akan yi musu mubaya'a da da'a;
kamar haka:
1-
Yawan khalifofi da
musulunci zai siffanta da siffofi masu zuwa a zamaninsu su guda goma sha biyu
ne.
2-
Dukkansu daga kabilar
quraishawa su ke, ba daga wassunta ba.
3-
Al'umma gaba-dayanta zata
hadu akansu, ko kuma dai a ce: mafi rinjayen gaske daga cikinsu.
4-
Musulunci –a zamaninsu ba
zai gushe ba yana tsayeyye, mai kuma yaduwa da karfi, izza da buwaya, kana
makiyin musulunci kuma na wadda aka rinjaye shi; na cikin tsoron islam; baya
kwadayin samun wani abu a cikinsa ballentana ya yi tunanin tinkararsa, jihadi
na tsaye, gaskiya kuma na bayyane; kana tana sane, al'amarin musulmai shi ke
gudana.
Waxannan
sune muhimman sifofi dangane da su waxannan
khalifofi guda goma sha biyu, da kuma zamaninsu.
Kuma kamar yadda Manzon Allah (saw) ya
yi albishir kan zuwan khalifofin nan -a cikin wannan hadisin-, to haqiqa Allah
ta'alah shima da kansa ya sauqar
da ''bishara'' akansu -a cikin attaura-; a yayin da ya ke bishara da samuwar
annabi Isma'ila (as), ya tabbatar da cewa, daga tsatsonsa za a samu manyan
mutane guda goma sha biyu, kamar yadda zai zo:
Babban malami ''Imadu ad-dini
Al-hafiz Ibnu Kasir'' yana cewa:
«وَمَعْنَى هَذَا الْحَدِيثِ: الْبِشَارَةُ بِوُجُودِ اثْنَيْ
عَشَرَ خَلِيفَةً صَالِحًا يُقِيمُ الْحَقَّ وَيَعْدِلُ فِيهِمْ»([1]).
Ma'ana:
((Ma'anan wannan hadisin shi ne: albishir ne kan samuwar khalifofi guda goma
sha biyu; salihai, da za su tsayar da gaskiya a cikin mutane, su kuma yi adalci
a cikinsu).
[Duba: ''Tafsiru alqur'ani al'azimi'', v2/
p47]. Haka shima ''Ibnu-taimiyyata''
yana cewa:
«وَهَؤُلاءِ الاثْنَا عَشَرَ خَلِيفَةً هُمُ الْمَذْكُورُونَ
فِي التَّوْرَاةِ; حَيْثُ قَالَ فِي بِشَارَتِهِ بِإِسْمَاعِيلَ: "وَسَيَلِدُ
اثْنَيْ عَشَرَ عَظِيمًا».
Ma'ana: (Waxannan khalifofi guda goma sha biyu su
ne aka ambace su a cikin ''attaura'' a inda ake cewa dangane da bishara da aka
yi da annabi Isma'il –as-: Kuma zai haifi manyan mutane goma sha biyu).
[Duba:
littafin ''Minhaju as-sunnati annabawiyyati'', v8/p241].
Amma
dangane da wai shin waxannan khalifofin a jere su ke ko kuma sun kasance
ko za su kasance a lokuta mabanbanta?
A
nan zan fara kawo ra'ayin farko da ke nuna cewa: ba dole ne zamanin waxannan khalifofi
ya zama a jere ba; maluman da su ke da wannan ra'ayin
su ne:
1-
Abu-dawud a cikin
littafinsa ''as-sunan'', ta yadda ya kulla wani littafi da ya masa taken
''littafi da ke magana akan mahdiy'', a karshensa kuma ya ce: ''karshen
littafin mahdiy [Duba: 1832-1840 a cikin: aunu alma'abudi]''. Ya kuma ambaci
babi guda a cikin wannan littafi, sannan ya qunsa hadisai guda goma sha uku a cikin
wannan littafi, ya fara ambaton hadisin ''Jabir bn Samurah'', wadda ya ke cewa:
Na ji Manzon Allah (saw) yana cewa:
"لا يزال
هذا الدين قائما
حتى يكون عليكم إثنا عشر خليفة..." الحديث.
Malamin musulunci mai suna
Abdurrahman jalalu addini Assuyuxiy
yana cewa a qarshen
littafinsa ''al'arfu alwardiy fiy akhbari almahdiy, [p155-156]'':
(إنّ
في ذلك إشارة إلى ما قاله العلماء أنّ المهدي أحد الإثني عشر).
Ma'ana:
(Lallai ambaton wannan hadisin –da ke albishir kan zuwan khalfifo guda goma sha
biyu waxanda a
zamaninsu musulunci ba zai gushe yana da izza ba- a cikin littafin da ke magana
kan: mahdiy, Ishara ce izuwa abinda Malamai su ka faxa na cewa:
MAHDIY XAYA NE DAGA
CIKIN WAXANNAN KHALIFOFIN
GUDA GOMA SHA BIYU''.
[Duba:
littafin shehinmu; Abdulmuhsin al-abbad, mai taken: Aqidatu
ahlis-sunna wal asar, fiy almahdiy almuntazar, p133-134 ].
2-
Malami na biyu da ya
bayyana wannan ra'ayi shi ne: Alhafiz Ibnu-Kasir a cikin ''tafsirinsa''
[v2/p47]. A inda ya ke cewa:
«وَمَعْنَى هَذَا الْحَدِيثِ: الْبِشَارَةُ بِوُجُودِ اثْنَيْ
عَشَرَ خَلِيفَةً صَالِحًا يُقِيمُ الْحَقَّ وَيَعْدِلُ فِيهِمْ، وَلا يَلْزَمُ مِنْ
هَذَا تَوَالِيهِمْ وَتَتَابُعُ أَيَّامِهِمْ، بَلْ قَدْ وُجِدَ مِنْهُمْ أَرْبَعَةٌ
عَلَى نَسَق، وَهُمُ الْخُلَفَاءُ الأَرْبَعَةُ: أَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ، وَعُثْمَانُ،
وَعَلِيٌّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ، وَمِنْهُمْ: عُمَرُ بْنُ عَبْدِ الْعَزِيزِ بِلا
شَكٍّ عِنْدَ الأَئِمَّةِ، وَبَعْضُ بَنِي الْعَبَّاسِ. وَلا تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى
تكون ولايتهم؛ لا محالة. والظاهر أنَّ مِنْهُمُ: الْمَهْدِيُّ الْمُبَشَّرُ بِهِ فِي
الأَحَادِيثِ الْوَارِدَةِ بِذِكْرِهِ: أَنَّهُ يُواطئُ اسمُه اسْمَ النَّبِيِّ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَاسْمُ أَبِيهِ اسْمَ أَبِيهِ، فَيَمْلأُ الأَرْضَ عدْلا
وقِسْطًا، كَمَا مُلِئَتْ جَوْرا وظُلْمًا».
Ma'ana: ((Ma'anar wannan hadisin shine: Bishara
ne kan zuwan khalifofi goma sha biyu; salihai, da za su tsayar da gaskiya, da
adalci a cikinsu. Kuma ba dole ne wa'yannan khalifofin su kasance a jere ba,
hasali ma an samu mutum hudu daga cikinsu a jeren; wadanda kuma su ne;
khalifofi guda hudu; Abubakar, Umar, Usman, da Aliyu –r a-. Kana kuma a cikinsu
akwai: Umar bn Abdul'aziz, ba tare da shakka ba –a wajen maluma, da sashin
khalifofi a daular abbasiyya. Kiyama ba zata tsaya face khalifancinsu
–khalifofi 12- ya kasance; ba makawa. Kuma a zahiri: Mahdiy da aka yi albishir
da zuwansa a cikin hadisai masu yawa; wadda kuma daga cikin sifofinsa akwai
cewa: sunansa yana daidai da sunan annabi –saw-, sunan babansa yana daidai da
sunan baban annabi, zai cika duniya da adalci, kamar yadda ta cika da zalunci,
Ga zahiri wannan bawan Allah yana daga cikin khalifofin goma sha biyun)).
Wadannan
wassu ne daga cikin jiga-jigan maluman da su ke da ra'ayin cewa; ba dole
zamanin khalifofin goma sha biyu ya zama a jere ba. Wannan dai it ace fahimtarsu; sai dai kuma
bas hi ne fahimta da ked a goyon baya ta fiskar dalilai ba; kamar yadda bayani
akan haka ke tafe.
Fahimta
ta biyu da ke nuna cewa; zamanin khalifofi goma sha biyu -da aka yi albishir da
zuwansu- a jere ya ke, tare da Ambato wassu daga cikin maluman da su ka yi
bayani akan haka:
Kadan daga
cikin maluman da su ka tabbatar da wannan fassara:
1- Shekhul
islam ibnu taimiyyata: Yana cewa a cikin littafinsa: ''minhaju
as-sunnati annabawiyyati'' [v8/p242]:
«الاثْنَا
عَشَرَ: هُمْ الَّذِينَ وُلُّوا عَلَى الأُمَّةِ مِنْ قُرَيْشٍ وِلايَةً عَامَّةً،
فَكَانَ الْإِسْلامُ فِي زَمَنِهِمْ عَزِيزًا، وَهَذَا مَعْرُوفٌ».
Ma'ana: (Mutum goma sha biyu su ne: wa'yanda
su ka yi ''wilaya a-mmah; wato: khalifanci gamemme'', kuma ya musulunci ya
zamto mai izza a zamaninsu. Wannan kuma abu ne sanan ne).
Ya kuma fadada magana akan haka a wani wuri; a
inda ya ke cewa:
«...
وَفِي لَفْظٍ: لا يَزَالُ الإِسْلامُ عَزِيزًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً كُلُّهُمْ
مِنْ قُرَيْشٍ. وَهَكَذَا كَانَ، فَكَانَ الْخُلَفَاءُ: أَبُو بَكْرٍ، وَعُمَرُ، وَعُثْمَانُ،
وَعَلِيٌّ، ثُمَّ تَوَلَّى مَنِ اجْتَمَعَ النَّاسُ عَلَيْهِ وَصَارَ لَهُ عِزٌّ وَمَنَعَةٌ:
مُعَاوِيَةُ، وَابْنُهُ يَزِيدُ، ثُمَّ عَبْدُ الْمَلِكِ وَأَوْلَادُهُ الْأَرْبَعَةُ،
وَبَيْنَهُمْ عُمَرُ بْنُ عَبْدِ الْعَزِيزِ. وَبَعْدَ ذَلِكَ حَصَلَ فِي دَوْلَةِ
الْإِسْلَامِ مِنَ النَّقْصِ مَا هُوَ بَاقٍ إِلَى الْآنَ ; فَإِنَّ بَنِي أُمَيَّةَ
تَوَلَّوْا عَلَى جَمِيعِ أَرْضِ الْإِسْلَامِ، وَكَانَتِ الدَّوْلَةُ فِي زَمَنِهِمْ
عَزِيزَةً، وَالْخَلِيفَةُ يُدْعَى بِاسْمِهِ: عَبْدَ الْمَلِكِ، وَسُلَيْمَانَ، لَا
يَعْرِفُونَ عَضُدَ الدَّوْلَةِ، وَلَا عِزَّ الدِّينِ، وَبَهَاءَ الدِّينِ، وَفُلانَ
الدِّينِ، وَكَانَ أَحَدُهُمْ هُوَ الَّذِي يُصَلِّي بِالنَّاسِ الصَّلَوَاتِ الْخَمْسَ،
وَفِي الْمَسْجِدِ يَعْقِدُ الرَّايَاتِ، وَيُؤَمِّرُ الأُمَرَاءَ، وَإِنَّمَا يَسْكُنُ
دَارَهُ، لا يَسْكُنُونَ الْحُصُونَ، وَلا يَحْتَجِبُونَ عَنْ الرَّعِيَّةِ». (قاله في كتابه: منهاج السنة
النبوية: (ج8/238).
Ma'ana: (… A wani lafazin: ''Musulunci ba zai
gushe ba yana mai izza izuwa khalifofi goma sha biyu; dukkaninsu suna daga
quraishawa'', kuma haka lamarin ya kasance; ta yadda aka samu khalifofi;
Abubakar, Umar, Usman da Aliyu, kana kuma aka samu wadda dukkan mutane su ka
hadu wajen yi masa mubaya'a; ya zamto yana da izza da buwaya; wato Mu'awiyatu,
kana 'dansa Yazidu, sa'annan sai Abdulmalik, da kuma 'ya'yansa guda hudu, A
tsakaninsu kuma aka samu Umar bn Abdul'aziz.
To kuma bayan wadannan ne gaba-daya aka fara samun nakasa a cikin daular
musulunci, wadda hakan ya wanzu har izuwa yau; saboda ''banu-umaiyata'' sun yi
shugabancinsu ne ga duniyar musulunci (ba ga wata kasa kawai ba), kuma daula –a
zamaninsu- ta kasance tana da izza, shi kuma ''khalifa'' ana kiransa da
sunansa; kamar a ce: Abdulmalik, da Sulaiman, Ba su san a kira su da ''Adudi-addini, ko Izzu-addini, ko
Baha'u-addini, ko wanen addini'' ba, -ma'ana sunaye da ke nuna: kwarzantawa;
mai karfafa addini, mai cicciba addini- A wancan lokacin dayansu ya kasance shi
ke limancin salla ga mutane, kuma daga masallaci ya ke tura bataliya, ya nada
gwamnoni, kuma a gidajensu su ke zaune; ba a wani makareren gida da aka
ganuwance shi ba; don haka basu kasance suna buya ga talakawansu ba).
2- Alhafiz
Ibnu-hajar a sharhi da yayi ga wannan hadisin shima ya tabbatar da cewa su
wa'yannan khalifofi a jere su ke, kamar yadda ya ce:
«جميع من ولي الخلافة من الصديق إلى عمر بن عبد العزيز أربعة عشر
نفسًا، منهم اثنان لم تصح ولايتهما ولم تطل مدتهما، وهما: معاوية بن يزيد، ومروان
بن الحكم، والباقون اثنا عشر نفسًا على الوَلاء، كما أخبر r، وكانت
وفاة عمر بن عبد العزيز سنة إحدى ومائة، وتغيرت الأحوال بعده، وانقضى القرن الأول
الذي هو خير القرون، ولا يقدح في ذلك قوله (يجتمع عليهم الناس) لأنه يحمل
على الأكثر الأغلب؛ لأنّ هذه الصفة لم تفقد منهم... وكانت الأمور في غالب أزمنة
هؤلاء الاثني عشر منتظمة، وإنْ وُجد في بعض مدتهم خلاف ذلك فهو بالنسبة إلى
الاستقامة نادرٌ، والله أعلم»([2]).
Ma'ana: ('Daukaci wadanda su ka yi
khalifan tun daga zamanin Abubakar as-siddiq, izuwa Umar bn Abdul'aziz rai goma
sha hudu ne, daga cikinsu akwai mutum mutum biyu; wadda khalifancinsu bai
inganta ba, kana kuma zamaninsu bai yi tsayi ba; wadannan kuma su ne:
Mu'awiyatu bn Yazid, da Marwan bn Alhakam. Su kuma sauran goma sha biyun sun
kasance a jere; kamar yadda annabi –s a w- ya bada labara. Kuma wafatin Umar bn
Abdil'aziz ya kasance a shekara ta dari da daya (101h). Sai lamura su ka
jirkita a bayansa. Kuma ''karnin farko'' wadda wadda kuma shi ne mafi alherin
''karnuka'' sai ya kare. Kuma riwayar da ta nuna cewa: ''dukkaninsu mutane za
su hadu wajen yi musu bai'a ko da'a'' bata yin su ka ga wannan hadisi; saboda
ana daukar wannan ''hadisi'' ga abin da ya fi yawa kuma shine galibi; saboda ba
a rasa wannan ''sifar'' ba a cikinsu. … Kuma lamura sun kasance a lokacin
khalifanci wa'yannan mutum sha-biyu suna tafiya akan turba; ba matsala. Kuma
koda cewa an samu wa'yansu abubuwan sun tafi akan sabanin yadda ake so; to sai
dai: haka din dan kadan ne. wallahu a'alam!). [Fat'hul bariy:
v13/p265].
Bayan kuma
ya ambaci ''hanyoyi da wannan hadisin yazo'' ya kuma ambaci maganar malami mai
suna ibnu-aljauziy, da kuma alkhaxxabiy sai ya ce:
«وينتظم من مجموع ما ذكراه أوجه، أرجحها الثالث من أوجه القاضي؛
لتأييده بقوله في بعض طرق الحديث الصحيحة (كلهم يجتمع عليه الناس)، وإيضاح
ذلك: أنَّ المراد انقيادهم لبيعته، والذي وقع أنّ الناس اجتمعوا على أبي بكر ثم
عمر ثم عثمان ثم عليّ إلى أنْ وقع أمر الحكمين في صفين، فسُمِّي معاوية يومئذ
بالخلافة، ثم اجتمع الناس على معاوية عند صلح الحسن، ثم اجتمعوا على ولده يزيد،
ولم ينتظم للحسين أمرٌ بل قتل قبل ذلك، ثم لما مات يزيد وقع الاختلاف إلى أن
اجتمعوا على عبد الملك بن مروان بعد قتل ابن الزبير، ثم اجتمعوا على أولاده
الأربعة: الوليد، ثم سليمان، ثم يزيد، ثم هشام، وتخلل بين سليمان ويزيد عمر بن عبد
العزيز؛ فهؤلاء سبعة بعد الخلفاء الراشدين، والثاني عشر هو الوليد بن يزيد بن عبد
الملك اجتمع الناس عليه لما مات عليه عمُّه هشام؛ فولِي نحو أربع سنينن ثم قاموا
عليه فقتلوه، وانتشرت الفتن وتغيرت الأحوال من يومئذ، ولم يتفق أنْ يجتمع الناس
على خليفة بعد ذلك؛ لأنّ يزيد بن الوليد الذي قام على ابن عمه الوليد بن يزيد لم
تطل مدته، بل ثار عليه قبل أنْ يموت ابنُ عم أبيه مروان بن محمد بن مروان. ولما
مات يزيد ولي أخوه إبراهيم فغلبه مروان، ثم ثار على مروان بنو العباس إلى أنْ قتل،
ثم كان أول خلفاء بني العباس أبو العباس السفاح، ولم تطل مدته مع كثرة مَن ثار
عليه، ثم ولي أخوه المنصور فطالت مدته، لكن خرج عنهم المغرب الأقصى باستيلاء
المروانيين على الأندلس، واستمرت في أيديهم متغلبين عليها ... وانفرط الأمر في
جميع أقطار الأرض إلى أنْ لم يبقَ من الخلافة إلا الاسم في بعض البلاد بعد أن كانوا في أيام بني عبد الملك
بن مروان يخطب للخليفة في جميع أقطار الأرض شرقا وغربا وشمالا ويمينا مما غلب عليه
المسلمون، ولا يتولى أحد في بلد من البلاد كلها الإمارة على شيء منها إلا بأمر الخليفة.
ومَن نظر في أخبارهم عرف صحة ذلك! فعلى هذا؛ يكون المراد بقوله: (ثم يكون الهرج)
يعني: القتل الناشئ عن الفتن وقوعا فاشيا؛ يفشو ويستمر ويزداد على مدى الأيام، وكذا
كان. والله المستعان!» (فتح الباري، ج13/ص263-264).
Ma'ana:
(Kan an tattara duk abubuwan da su ka fada to za a samu fiskoki da yawa; sai
dai kuma fiskar da tafi rinjaye daga cikinsu: itace fiska ta uku; daga cikin
fiskokin da ''Alkali Iyadh'' ya ambata; saboda ya karfafe shi da wani abin da
ya zo a cikin sashin hanyoyin hadisin ingancecce: ''Dukkansu mutane zasu hadu
akansu''; Bayani akan haka kuma shi ne: Lallai manufar wannan shi ne: zasu mika
wuya kan ''mubaya'a da aka yi musu''; kuma abun da ya auku shi ne: Lallai
mutane sun hadu kwansu-da kwarkwatarsu akan Abubakar, kana kuma Umar,
kana kuma Usman, kana kuma Aliyu, har izuwa lokacin da lamarin
alkalancin mutum biyu ''bayan yakin siffin'', sai a wannan yinin aka kira
Mu'awuyatu da khalifanci, kana kuma daga baya mutane gaba-dayansu su ka yi
ijma'i kan yin mubaya'a wa sahabi Mu'awuyatu; a lokacin da sahabi
Alhasan ya yi sulhu da shi. Sa'annan sai su ka hadu kan dansa Yazid, Shi
kuma sahabi Alhusain khalifanci bai kasance masa ba; hasali ma an kashe shi
gabanin haka. Sa'annan bayan mutuwar Yazidu sai sabani ya kasance; izuwa
haduwan mutane kan mika-wuya ga Abdulmalik bn Marwan bayan
kashe sahabi Abdullahi bn Az-zubairu, sa'annan kuma mutane su ka mika-wuya ga: 'ya'yansa
guda hudu; wato: Alwalid, sa'annan Sulaiman, sa'annan Yazid,
sa'annan kuma Hisham. Kuma a tsakanin Sulaiman da Yazidu ne aka samu
khalifancin Umar bn Abdil'aziz, Wadannan su ne mutum bakwai bayan
khalifofi shiryeyyu guda hudu. Na goma sha biyunsu shi ne: Walid bn Yazid bn
Abdulmalik; mutane sun mika masa wuya yayin da baffansa Hisham ya mutu; sai
ya yi shugabanci na tsawon shekara hudu; sa'annan su ka masa zanga-zanga su ka
kashe shi. To daga nan kuma sai fitina ta yadu, duk halaye su ka canza daga
wannan lokaci, wannan yasa daga nan kuma ba a sake haduwa kan khalifa guda daya
ba bayan haka; saboda ''Yazid bn Alwalid'' wadda ya yi fito-na-fito wa dan
baffansa ''Al-walid bn Yazid'' zamaninsa bai yi tsayi ba; hasali ma kafin ya
mutu dan baffan ubansa ne mai suna: ''Marwan bn Muhammad bn Marwan'' ya yi
fito-na-fito da shi, A yayin da kuma ''Yazidu bn Alwalid'' ya mutu kuma sai shi
dan'uwansa ''Ibrahim'' ya zama shugaba, wadda kuma shi ''Marwan'' bai bar shi
ba; sai ya kwace masa, Sa'annan sai ''daular Abbasiyyah'' su ka yi
–fito-na-fito da shi; har izuwa lokacin da suka kashe shi; su ka kwace
khalifanci; Wannan yasa farkon khalifofin ''daular Abbasiyyah'' ya zama wadda
ake masa alkunya da lakabi da ''Abu-al'abbas As-saffah –wato mai yawan zubar da
jini''; shima kuma lokacinsa bai yi tsayi ba, tare da yawaitar wadanda su ka yi
fito-na-fito da shi, Sa'annan sai dan'uwansa da ake kira: ''Almansuur'' ya zama
khalifa; zamaninsa kuma ya yi tsayi; Sai dai kuma bangaren da ake kiransa
''almagrib al'aqsah'' ya balle masa; a lokacin da ''Iyalen Marwan'' su ka kwace
yankin ''Andalus'' kuma yankin ya ci gaba da zama a hanunsu; suna masu
mulkarsa, wadanda kuma su ka yi rinjaye akansa … Daga nan dai lamarin
''khalifancin musulunci'' ya yi ta tasgarewa yana rugujewa a duniya, har ya
zama dai abin da ya rage wa ''khalifanci'' a masarautu da yawa shi ne sunansa,
a kuma sasani duniya da yawa. BAYAN DA KHALIFA YA KASANCE A LOKACIN ''YAYAN
ABDULMALIK BN MARWAN; -DAULAR UMAWIYYATU- A DUKKAN DUNIYAR DA MUSULMI SUKA
BUDE; GABAS DA YAMMA, KUDU DA AREWA, ANA YIN HUDUBA NE WA KHALIFA GUDA TAK,
KUMA WANI MUTUM BA ZAI ZAMA GWAMNAN YANKI DAGA CIKIN YANKUNA BA SAI DA UMURNIN
KHALIFA. DON HAKA; Duk mutumin day a yi
nazari cikin tarihin ''daula umawiyya'' to zai tabbatar da gaskiyar haka.
Kuma
akan haka ne ma'anan fadin annabi –s a w-:
"ثم يكون الهرج يعني:
القتل".
Zai
kasance: -Sa'annan bayan khalifofi guda goma sha biyun sun shude, Sai
kashe-kashe ya kasance-. Ma'ana kashe-kashen da fitintunu su ka haifar da shi;
ta yadda zai yadu matuka, ya kuma ci gaba yana mai karuwa gwargwadon tafiyan
zamani. Kuma haka lamarin ya yi ta kasancewa kuma yak e kasancewa. Wallahu
almusta'an).
[Duba: littafin fat'hul bariy
na Ibnu-hajar, v13/p263-264].
Wadda ya
fahimci karatun nan da kyau: zai hakiki ce gaskiyar Manzon Allah (s a w) da ya
bayyana cewa za a samu khalifofi guda goma sha biyu (12) wadanda musulunci ba
zai gushe ba a zamaninsu yana mai karfi, izza da buwaya, kana kuma madaukaki…
Yayin da kuma bayan shudewar wadannan khalifofin musulunci zai yi ta yin rauni,
izzarsa tana komawa baya, kwar-jininsa yana zagwanyewa, kafirai basa jin
tsoronsa.
Kuma
wannan shi ke nuna cewa ''maganar da ta gabata'' wadda Alhafiz ''Ibnu-kasir''
ya karfafe ta: ta zama bata da karfi; saboda manzon Allah (s a w) ya fada a
cikin hadisin cewa:
«لا يَزَالُ الإِسْلامُ
عَزِيزًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً كُلُّهُمْ مِنْ قُرَيْشٍ»
Ma'ana:
''Musulunci ba zai gushe ba yana da karfi da izza a zamanin khalifofi guda
goma-sha-biyu''; Ka ga anan duk wadda ya ce wadannan
khalifofin ba dole ne su zamto a jere ba, ko ya ce: wani daga cikinsu zai iya
ksancewa a karshen zamani (duniya); kamar Almahdiy: to maganarsa tana hukunta
ya ce: a wannan zamani namu da wadda ke gabaninsa musulunci yana da karfi, izza
da buwayar addinan da ba shi (yahudanci, nasaranci da sauranci). Wadda kuma
lamarin ba haka ya ke ba; saboda fadin:
«لا يَزَالُ...»
A cikin
hadisin; da take nuna cewa: Sifar
daukakar musulunci ba za ta gushe ba a khalifancin mutane goma sha biyu. Bayan
shudewarsu kuma sai ta gushe a khalifancin wassunsu da sannu-sannu. Wannan kuma
shi yasa ''Ibnu-taimiyyata'' y ace:
«وَهَذَا
يَدُلُّ عَلَى أَنَّهُ يَكُونُ أَمْرُ الإِسْلامِ قَائِمًا فِي زَمَانِ وِلايَتِهِمْ،
وَلا يَكُونُ قَائِمًا إِذَا انْقَطَعَتْ وِلايَتُهُمْ». (قاله في كتابه: منهاج
السنة النبوية: (ج8/ ص253).
Ma'ana: (Wannan hadisin na nuna cewa
''al'amarin musulunci'' zai kasance tsayeyye, da karfi a lokacin,
khalifancinsu. Ba zai kuma kasance tsayeyye bayan yankewar khalifancin nasu)
[Duba: ''Minhaju assunnati'' v8/ p253].
Wallahu ta'ala a'alamu!
HADISAI HAMSIN (50) KAN KHALIFANCIN KHALIFOFIN MANZON ALLAH (S A W) DA
FALALOLINSU (6)
HADISI
(4): DAKE ALBISHIR KAN SAMUWAR ''KHALIFOFI (12) ''; WADANDA A ZAMANINSU
MUSULUNCI ZAI ZAMO MAI KARFI; MAI IZZA,
DA KARIYA:
…
(ci
gaba)
(e)
MUHIMMAN
LAMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN ''KHALIFOFIN ANNABI (SAW) SHIRYEYYU'' WADDA
SUKE NUNA IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YADUWARSA:
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai!
Idan
ba a manta ba Hadisinmu da ya gabata ya nuna cewa a tsawon khalifancin halifofi
guda goma sha biyu (12) musulunci ba zai gushe ba yana madaukaki mai izza,
kamar yadda wannan lafazin ke nunawa:
"لا يَزَالُ
هَذَا الدِّينُ عَزِيزًا مَنِيعًا إِلَى اثْنَيْ عَشَرَ خَلِيفَةً".
Sananne
ne cewa musulunci ya fara yana karami mai rauni, kana kuma bako, wannan kuma a
fili ya ke idan muka duba rayuwar manzon Allah (SAW) ta Makka; wadda tsananin
yanayin da su ka samu kansu a cikinsa yasa manzon Allah (SAW) ya yi izini wa
sahabbansa da cewa su yi hijira izuwa ''Habasha'', hijirar habashan kuma ta
kasance har sau biyu. Sa'annan sai annabi (SAW) da sahabbai su ka yi hijira
izuwa garin Madina. Alhafiz Ibnu-rajab yana cewa a cikin littafinsa ''kashfu
alkurbati fi wasfi ahli algurbati'':
(ثم ظهر الإسلام بعد الهجرة إلى المدينة وعز وصار أهله ظاهرين كل
الظهور، ودخل الناس بعد ذلك في دين الله أفواجا، وأكمل الله لهم الدين وأتم عليهم
النعمة. وتوفي رسول الله صلى الله عليه وسلم والأمر على ذلك، وأهل الإسلام على غاية
من الاستقامة في دينهم، وهم متعاضدون متناصرون، وكانوا على ذلك في زمن أبي بكر وعمر
رضي الله عنهما).
Ma'ana: (Sa'annan sai musulunci ya bayyana bayan
hijira izuwa madina, ya kuma samu izza, kana kuma ma'abutansa su ka zama
madaukaka iya daukaka, lamarinsu kuma a bayyane iya bayyana. Mutane kuma su ka
shiga cikin addinin Allah jama'a jama'a, Allah kuma ya cika mu su addini, kana
kuma ya cika musu ni'imarsa. Manzon Allah -SAW- ya rasu lamarin yana nan akan
haka –madaukaki-; ta yadda ma'abuta musulunci sun kai makura wajen tsayuwa akan
mikakken addininsu, suna masu taimakekkeniya a tsakaninsu –tsintsiya madaurinki
daya-. Kuma akan haka su ka kasance a lokacin khalifancin Abubakar da Umar
–RA-).
Kamar
yadda musulunci ya ke da izza da daukaka a rayuwar manzon Allah (SAW); ta
madina, haka kuma lamarin ya ci gaba da kasancewa a khalifancin khalifofin da
su ka biyo bayansa 12, duk da cewa abin ya fara yin baya-baya; Wannan ma'anar
kuma itace hadisin ''musulunci ba zai gushe ba yana madaukaki mai izza izuwa
khalifofi 12 daga kuraishawa…''. Don fito da wannan ma'anar fili, tare da
Ambato yadda musulunci ya yi ta bunkasa yana yaduwa; musamman a zamanin khalifofi
guda hudu (4) na farko: zan koro bayanai da ke tafe:
NA
FARKO: Muhimman abubuwan da su ka faru a zamanin khalifar manzon Allah
(SAW); Abubakar (RA) masu nuna izzar musulunci da yaduwarsa:
1-
Mai bibiyan ''tarihin
musulunci'' zai ga cewa gabanin rasuwar manzon Allah (SAW) da wani lokaci da
bashi da tsayi an samu wassu sun fito suna da'awar ''annabta'', kuma lallai
annabi (SAW) ya karyata su kana kuma ya fara tattaunawa da sashinsu kamar
''Musailimatu'' ta hanyar tura masa wasika, Daga cikin wadanda su ka yi da'awar
''annabtan'' akwai:
a- Wadda
ya shahara da ''al'aswad al'ansiy'' wadda kuma shine mutane da dama na
kasar "Yemen'' su ka yi ridda kana su ka bi shi.
b- Da
kuma ''Dulaihatu bn Khuwailid al'asadiy'' wadda daga baya ya sake komowa
cikin musulunci, amma gabanin haka; lokacin da ''Uyainatu bn Hisn'' ya yi
ridda; ya tsaya sosai wajen taimaka wa ''Dulaihatu'' akan da'awarsa ta
''annabta'', har ma ya jagorancin mutanensa ''banu-fazaarata'' izuwa goya masa
baya.
c- Da
kuma "Musailimatu alkazzaab'' wadda shi ya jagoranci
''banu-hanifata'' kan riddarsu. Da sauransu.
kamar yadda
kuma an samu ''ridda'' da kuma ficewa daga cikin musulunci da ga wajen mutane
da yawan gaske bayan rasuwar tasa (manzon Allah -SAW), don haka; ''kabilar
asad da gadfana'' sun yi ridda, haka ''kabilar kindah da masu biye mata'',
da ''kabilar mizhaj da masu biye mata'', da ''Banu-hanifata'', da
''kabilar sulaim'', da ''Banu-tamim'', da sauransu. Kai! Kabilun
da su ka yi ridda suna da yawa, harma tarihin ya tabbatar da cewa: a wancan
lokacin garurrukan da ake sallar juma'a a masallatansu guda uku ne kacal;
Makka, Madina, sai kuma wani kauye da ake kiransa ''Juwasa''.
Ta gefe
guda kuma akwai wadanda su ka hana zakka, wassunsu suna ganin cewa ga annabi
(SAW) ne kawai ake bada ita.
Yana daga
cikin manya-manyan abubuwan da khalifan manzo; Abubakar ya yi a wancan lokacin,
wadda kuma hakan ya sake dawo da mutane cikin ''kewayen musulunci'' daura
damarar yaki da dukkan wa'yancan bangarori da su ka yi ridda ta fiskoki
mabanbanta, kai dama aiwatar da yakin a aikace, kuma Allah ta'alah ya bashi
nasarar gaske kan hakan; ta yadda ya dauki tutar yakar:
a-
Mai da'awar annabta
''Dulaihatu al'asadiy'' ya bada ita ga ''khalid bn Alwalid (RA)''.
b-
Tutar yakar ''Musailimatu
alkazzaab'' da jama'arsa (banu-hanifata) kuma ya damka ta ga "Ikrimatu
bn Abiy-jahal'', daga baya ya sake karfafarsa da ''Shurahbiyl bn
Hasanata''.
c-
Ya kuma bada tutar yakan
wa'yanda su ke farko-farkon ''Shaam'' ga ''Khalid bn Sa'id bn Al'aas''.
d-
Ya tura ''Amru bn Al'aas
(RA)'' izuwa ''Kuda'ata da wadi'atu da Alhaarith''.
e-
Ya kuma umurci (Al'ala'i
bn Alhadramiy'' ya tafi garin ''Bahraini''.
f-
''Huzaifatu bn Mihsin
algadfaniy'' shi kuma aka kulla masa tutar yakar mutanen '' Daba, da
Arfajata, da Harsamata''.
g-
Tutar yakar ''Banu-saliim,
da wadanda su ke tare da su na kabilar Hawazin'' ya bada ita ga ''darafata
bn Hajib''. Kana kuma ''Suwaid bn Mukarrin'' aka bashi tutar yakar
''Tihamar Yemen''.
Abubakar (RA) bayan ya tura wadannan rundunoni
izuwa yakar ''masu ridda'', ya kuma rubuta musu wannan rubutun ya aike musu:
(بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ
الرَّحيم، مِنْ أَبِي بَكْرٍ خَلِيفَةَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
إِلَى مَنْ بَلَغَهُ كِتَابِي هَذَا، مِنْ عامَّة وخاصَّة، أَقَامَ عَلَى إِسْلامِهِ
أَوْ رَجَعَ عَنْهُ، سَلامٌ عَلَى مَنِ اتَّبع الْهُدَى وَلَمْ يَرْجِعْ بَعْدَ الْهُدَى
إِلَى الضَّلالة وَالْهَوَى، فإنِّي أَحْمَدُ اللَّهَ إِلَيْكُمُ الَّذِي لا إِلَهَ
إِلا هُوَ، وَأَشْهَدُ أَنْ لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، وأنَّ
مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، نُقرُّ بِمَا جَاءَ بِهِ، ونُكفِّر مَنْ أَبَى ذَلِكَ
وَنُجَاهِدُهُ. أَمَّا بَعْد: ...) إلى قوله: (وَقَدْ بَلَغَنِي رُجُوعُ
مَنْ رَجَعَ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ بَعْدَ أَنْ أقرَّ بِالإِسْلامِ، وَعَمِلَ بِهِ،
اغْتِرَارًا بِاللَّهِ وَجَهْلا بِأَمْرِهِ، وَإِجَابَةً للشَّيطان). ... إلى
أن قال في آخرها: (وَإِنِّي بعثت إليكم فِي جَيْشٍ مِنَ الْمُهَاجِرِينَ وَالأَنْصَارِ،
والتَّابعين بِإِحْسَانٍ، وَأَمَرْتُهُ أَنْ لا يَقْبَلَ مِنْ أَحَدٍ إِلا الإِيمَانَ
بِاللَّهِ، وَلا يَقْتُلُهُ حَتَّى يَدْعُوَهُ إِلَى اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ، فَإِنْ
أَجَابَ وأقرَّ وَعَمِلَ صَالَحَا قبِلَ مِنْهُ، وَأَعَانَهُ عَلَيْهِ وَإِنْ أَبَى
حاربه عليه حتى يفئ إِلَى أَمْرِ اللَّهِ، ثمَّ لا يُبْقِي عَلَى أَحَدٍ مِنْهُمْ قَدَرَ
عَلَيْهِ، وَأَنْ يحرِّقهم بالنَّار وَأَنْ يَقْتُلَهُمْ كُلَّ قِتْلَةٍ، وَأَنْ يَسْبِيَ
النِّساء والذَّراري، وَلا يَقْبَلَ مَنْ أَحَدٍ غَيْرَ الإِسْلامِ، فَمَنِ اتَّبعه
فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ، وَمَنْ تَرَكَهُ فَلَنْ يُعْجِزَ اللَّهَ، وَقَدْ أَمَرْتُ رَسُولِي
أَنْ يَقْرَأَ كِتَابَهُ فِي كُلِّ مَجْمَعٍ لَكُمْ. والدَّاعية الأَذَانُ فَإِذَا
أذَّن الْمُسْلِمُونَ فكفُّوا عَنْهُمْ، وَإِنْ لم يؤذِّنوا فَسَلُوهُمْ مَا عَلَيْهِمْ،
فَإِنْ أَبَوْا عَاجِلُوهُمْ، وَإِنْ أقرُّوا حمل منهم عَلَى مَا يَنْبَغِي لَهُم).
Ma'ana: ((Da sunan Allah
mai rahama mai jin kai, Daga Abu-bakar khalifan manzon Allah –SAW- izuwa ga
wadda wasikata ta iske shi na gama-garin mutane da kuma kebantattunsu, sawa'un
ya ci-gaba da wanzuwa cikin musuluncinsa ko ya fita daga cikinsa, amincin Allah
ya tabbata ga wadda ya bi shiriya, bai kuma koma izuwa bata da son zuciya ba
bayan shiriyar! Lallai ina gode wa Allah da babu abun bauta da gaskiya sai shi,
kuma ina shaidawa cewa babu wadda ya cancanci a yi masa bauta sai Allah shi
kadai bashi da abokin tarayya, ina kuma kara shaidawa cewa annabi Muhammadu
bawansa ne kuma manzonsa ne, muna tabbatar da abin da ya zo da shi, kuma muna
kafirta wadda ya ki hakan, kuma za mu yake shi, Bayan haka: ..). –Ya ci gaba da
cewa: ((Kuma labarin wadanda su ka fita daga addininsu daga cikinku, bayan da
can sun yi imani, kuma sun aiki da shi, labarinsu ya zo mini, sun yi haka ne
kuma saboda ruduwa da su ka yi da Allah, da jahiltar al'amarinsa, gami da amsa
wa Shedan)… Ya ci gaba da cewa: ((Kuma lallai na turo runduna izuwa gare ku
wadda ta kunshi ''almuhajiruna da Al'ansaar, da wadanda su ka bisu da kyautatawa''
kuma na umurci jagoransu cewa kada ya karbi wani abu daga wani mutum in banda
imani da Allah, kuma kada ya ''yaki'' wani face ya kira shi izuwa ga Allah
mabuwayi da daukaka; Idan har ya amsa masa; ya kuma yi imani da aiki na kwarai
to ya karba daga gare shi, ya kuma taimake shi akan haka. Idan kuma ya ki to
sai ya yake shi, har sai ya dawo izuwa ga addinin Allah. In kuma ba haka ba; to
kada ya bar wani da ya samu iko akansa; ya kone su da wuta, ya kuma karkashe su
mafi sharrin kisa, ya kama matansu da yaya a matsayin fursunan yaki, kada kuma
ya karbi wani abu a wajen wani daga cikinsu in banda musulunci; duk wadda ya bi
shi to hakan shi ne abin da ya fiye masa alkhairi, wadda kuma ya bar musulunci
to ya sani ba zai gagari Allah ba. Kuma hakika na umurci dan sakona da ya
karanta wasikata ga kowace matattara da ta hada ku. …).
Imam Ahmad bn Muhammad bn Hambal ya kawo a
cikin littafinsa [Fada'ilu assabati, lamba: 68, da sanadi ingancecce] daga
A'ishatu (RA) tace:
(قُبِضَ النَّبِيُّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَارْتَدَّتِ الْعَرَبُ، وَاشْرَأَبَّ النِّفَاقُ
بِالْمَدِينَةِ، فَلَوْ نَزَلَ بِالْجِبَالِ الرَّوَاسِي مَا نَزَلَ بِأَبِي لَهَاضَهَا،
فَوَاللَّهِ مَا اخْتَلَفُوا فِي نُقْطَةٍ إِلا طَارَ أَبِي بِحَظِّهَا وَعَنَائِهَا
فِي الإِسْلام).
Ma'ana: ((Allah ya dauki ran annabinsa –SAW-
sai larabawa su ka yi ''ridda'', munafirci kuma ya leko da kansa a garin
madina, Da abin da ya sauka wa babana ya sauka ne wa manyan duwatsu masu tsayi
da girma wadanda kuma su suke rike da kasa a matsayin tike: to da ya tausasa su
ko kuma ya kakkarya su, na rantse da Allah sahabban annabi ba su yi sabani a
wata mas'ala ba a cikin musulunci face babana ya rabauta da daidai a cikinta).
Yana daga cikin abin da ke kara fito da batun
''riddan larabawa masu dunbun yawa'' bayan rasuwar manzon Allah (SAW), tare
kuma da bayani kan wadanda su ka hana zakka, da kuma yadda Abubakar (RA) ya yi
tsayuwar alif wajen yakarsu, tare da shawara da wassu daga cikin sahabbai su ka
bashi na cewa ya dakata daga wannan yakin, da kuma yadda Allah ya shiryar da
shi izuwa ga lamarin da yama dalilin kara daukakar musulunci: Abin da ya zo a
cikin [''Sahihu Albukhari'', lamba: {6924, 6425}, da ''Sahihu Muslim'', hadisi
na: {20}]:
(عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ t قَالَ: لَمَّا تُوُفِّيَ النَّبِيُّ r وَاسْتُخْلِفَ أَبُو بَكْرٍ، وَكَفَرَ مَنْ كَفَرَ مِنَ الْعَرَبِ قَالَ
عُمَرُ: يَا أَبَا بَكْرٍ كَيْفَ تُقَاتِلُ النَّاسَ وَقَدْ قَالَ رَسُولُ اللهِ r: "أُمِرْتُ
أَنْ أُقَاتِلَ النَّاسَ حَتَّى يَقُولُوا لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ. فَمَنْ
قَالَ: لاََ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ عَصَمَ مِنِّي مَالَهُ وَنَفْسَهُ إِلاَّ بِحَقِّهِ
وَحِسَابُهُ عَلَى الله" قَالَ أَبُو بَكْرٍ: وَاللَّهِ لأُقَاتِلَنَّ مَنْ
فَرَّقَ بَيْنَ الصَّلاَةِ وَالزَّكَاةِ، فَإِنَّ الزَّكَاةَ حَقُّ الْمَالِ، وَاللَّهِ!
لَوْ مَنَعُونِي عَنَاقًا كَانُوا يُؤَدُّونَهَا إِلَى رَسُولِ اللهِ r لَقَاتَلْتُهُمْ عَلَى مَنْعِهَا. قَالَ عُمَرُ: فَوَ اللَّهِ مَا هُوَ
إِلاَّ أَنْ رَأَيْتُ أَنْ قَدْ شَرَحَ اللَّهُ صَدْرَ أَبِي بَكْرٍ لِلْقِتَالِ فَعَرَفْتُ
أَنَّهُ الْحَقُّ([3])).
Ma'ana: (Daga
Abu-hurairata –RA- yace: Yayin da annabi –SAW- ya rasu, Abubakar kuma ya zama
khalifa, wadanda su ka kafirce daga cikin larabawa su ka kafirce, Umar yace: Ya
Abubakar! Ta yaya zaka yaki mutane, alhali manzon Allah –SAW- yace: An umurce
ni da na yaki mutane har sai sun shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah,
Duk wadda ya shaida ''babu abun bauta da gaskiya sai Allah'' to ya kare ransa
da dukiyarsa daga gare ni –ba zan yake shi ba- sai da hakkin musulunci, kuma
hisabinsa naga Allah. Sai Abubakar yace: Na rantse da Allah! Zan yaki wadda ya
rabe tsakanin salla da zakka, saboda zakka hakki ne na dukiya, kuma wallahi! Da
za su hanani koda 'yar akuyar da bata kai shekara ba ''anaaq'' wadda kuma sun
kasance suna bada ita ga manzon Allah –SAW- a matsayin zakka to da na yake su
akan hanawan.
Umar yace: Na rantse da Allah! Ba komai ba ne face dana ga Allah ya bude
zuciyar Abubakar ya cusa masa kudirin yakar masu hana zakka sai na san hakan
-yakar tasu- gaskiya ne).
Yaqar
wadanda su ka yi ''ridda, suka kuma canza sheka daga musulunci izuwa kafirci''
da kuma wadanda suka hana zakka da Abubakar (RA) ya yi duk sun kasance ne bayan
dan lokaci kadan daga rasuwar manzon Allah (SAW), wadda hakan ya sa lamarin
musulmai ya sake izza da bunkasa, ya kuma koma kamar yadda annabi (SAW) ya tafi
ya barshi.
-Yana kuma daga cikin manya-manyan abubuwan
da Abubakar (RA) ya aikata su A wannan lokacin wadda kuma sun kara wa musulunci
tagomashi, tare da dura ruwa a cikin kafirai, kana kuma musulunci ya kara
kwar-jini a idanunsu, su ka ci gaba da tsoronsa, sa'annan abin da annabi
(SAW) ya bayyana a cikin albishir da ya yi wadda ya gabata; na cewa:
(... عزيزًا منيعًا)
Ya kara tabbata: Abun da Abubakar ya yi na
zartar da rundunar da Annabi (SAW) ya shirya don su yaki ''rumawa da su ke
shaam'' karkashin shugabancin Usamah bn Zaid (RA); Bayan kuma sahabbai da
yawa sun yi taraddadi kan tura su a irin wannan lokacin, Alhafiz Ibnu-kasir
(RL) a cikin littafinsa [Albidayah wannihayah, v6/p335] ya ce:
(وَالْمَقْصُودُ: أنَّه لَمَّا وَقَعَتْ هَذِهِ الأُمُورُ
أَشَارَ كَثِيرٌ مِنَ النَّاس عَلَى الصِّديق: أَنْ لا يُنْفِذَ جَيْشَ أُسَامَةَ؛
لاحْتِيَاجِهِ إليه فيما هو أهمّ، لأنَّ ما جهِّز بِسَبَبِهِ فِي حَالِ السَّلامة،
وَكَانَ مِنْ جُمْلَةِ مَنْ أَشَارَ بِذَلِكَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ، فَامْتَنَعَ
الصِّديق مِنْ ذَلِكَ، وَأَبَى أشدَّ الإِبَاءِ، إِلا أَنْ يُنْفِذَ جَيْشَ أُسَامَةَ،
وَقَالَ: وَاللَّهِ لا أَحُلُّ عُقْدَةً عَقَدَهَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَلَوْ أنَّ الطَّير تخطَّفنا، والسَّباع مِنْ حَوْلِ الْمَدِينَةِ
وَلَوْ أنَّ الْكِلابَ جَرَتْ بِأَرْجُلِ أُمَّهَاتِ الْمُؤْمِنِينَ لأجهزنَّ جَيْشَ
أُسَامَةَ، وَأَمَرَ الْحَرَسَ يَكُونُونَ حَوْلَ الْمَدِينَةِ. فَكَانَ خُرُوجُهُ
فِي ذَلِكَ الْوَقْتِ مِنْ أَكْبَرِ الْمَصَالِحِ وَالْحَالَةُ تِلْكَ، فَسَارُوا لا
يمرُّون بحيٍّ مِنْ أَحْيَاءِ الْعَرَبِ إِلا أُرْعِبُوا مِنْهُمْ، وَقَالُوا: مَا
خَرَجَ هَؤُلاءِ مِنْ قَوْمٍ إِلا وَبِهِمْ مَنَعَةٌ شَدِيدَةٌ، فقاموا أربعين
يوماً ويقال: سبعين يوماً، ثمَّ أتوا سَالِمِينَ غَانِمِين).
Ma'ana: (Makasudi anan shi ne: yayin da
wadannan abubuwa su ka auku –wato: barin musulunci da wassu su ka yi bayan
rasuwar manzon Allah- Mutane da yawa sun bada shawara ga Abubakar as-siddiq
cewa: ya dakatar da tura rundunar da Usamatu ke jagoranta; saboda matsanancin
bukatuwarsa izuwa ga rundunar, ga abin da yafi abin da za su tafi izuwa gare
shi muhimmanci; saboda annabi –SAW- ya tura su ne a lokacin da ake cikin
amintuwa daga musibar da ta auku na gama-garin ridda, daga cikin wa'yanda suka
bada irin wannan shawarar akwai Umar bn Alkhaddab, Amma sai Abubakar assidiq ya
ki karbar wannan shawari, ya kuma turje akan ra'ayinsa na cewa sai ya zartar da
rundunar da manzon Allah –SAW- ya aika karkashin Usamatu iyaka turjewa, ya kuma
ce: ''Wallahi! Ba zan warware kullin da manzon Allah –SAW- ya kulla ba; Koda za
a kaddara cewa tsuntsaye sun zo suna dauke mu, dabbobi masu farauta suna kewaye
da madina, kai koda ace karnuka sun gudu da kafofin ''uwayen muminai'' wallahi
sai na zartar da tura rundunar Usamatu. Sai kuma Abubakar ya umurci masu gadi
da su kasance a kewayen madina. Sai fitar Usamatu da rundunarsa a wannan
lokacin ya zama daga cikin abubuwa masu maslahar gaske manya; ta yadda basa
shige wata unguwa –kauye- daga cikin kauyukan larabawa, face sun tsorita da su;
su kuma kama cewa: Wadannan basu fito daga wata al'umma ba face wannan
al'ummar suna da: kariya ta musamman mai matukar tsanani, Su usamatu su ka
je su ka yi kwana 40, a wani kaulin kuma aka ce: kwana 70, sa'annan su ka dawo
madina da ganima, babu kuma wani abun da ya same su).
-Yana kuma daga cikin abubuwan da Abubakar
(RA) ya yi na yada musulunci, da kokarin shiryar da bayin Allah
izuwa ga addinin Allah, don su ji dadin rayuwar duniya, su kuma tsira a lahira:
Tura bataliyoyi don tallen musulunci: Wannan kuma ya kasance bayan Abubakar ya
gama da ''jaziratu al'arab'', musulunci ya komo mai karfi a cikinta bayan
rauninsa; saboda ridda da bayaninsa ya gabata, Sai ya nada bataliyoyi, ya kuma
basu tutar yaki, ya tura ''khalid bn Alwalid'' izuwa ga Iraq yakin da
ake kira: ''Gazwatu zati assalasil ta zamanin Abubakar''.
Kamar yadda kuma ya tura wadannan gomnoni kuma
jagororin bataliyoyi ta bangaren ''tsohuwar shaam'', kamar haka:
a-
''Yazid bn Abiy-sufyan''
wadda aka tura shi da mutane masu tsananin yawa, izuwa ''Damashk''.
b-
''Abu-ubaidata bn
Aljarrah'' da aka tura shi izuwa ''Hims''.
c-
''Amru bn Al'aas''
wadda ya tura shi izuwa ga ''Falastinu''.
Waxannan aiyukan,
dama wassunsu na daga aiyukan da Abubakar (RA) ya aikata na bunkasa musulunci
da yada shi duk Abubakar din ya aikata su ne a tsukin shekara biyu da watanni
kamar uku, kasancewar ya fara khalifancinsa ne a watan 3 na shekara ta goma sha
daya, izuwa rasuwarsa, wata ta 6 na shekara ta goma sha uku, wato shekara 2 da
wata uku. (watan 3/ 11 na hijirar Annabi, zuwa watan 6/13h).
[domin
Karin bayani kana bin da ya gabata a duba, abubuwa das u ka faru a shekarar
hijira 11, 12, da 13, a cikin babban kundin tarihi mai suna: Albidayatu
wannihayatu, Na Alhafiz Ibnu Khasir, {v6/p332 zuwa karshensa}, da {v7/p5-20}, da kuma
littafin ''Hukbatun min attarikh, na Assheikh Usman bn Muhammadu alkhamis,
{p63-77}].
NA
BIYU: MUHIMMAN LAMMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN ''UMAR (RA)'' WADDA SUKE
NUNA IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YADUWARSA
Lallai
musuluntar Umar bn Al-khaddab (RA) ya kasance sababi daga cikin sabbuban
daukakar musulunci, saboda gabanin musuluntarsa ya kasance mutum ne mai tsanani
ga musulmai, amma bayan ya shiga musulunci sai tsananinsa ya zama ga makiya
Allah; kafirai, kana kuma bunkasa da izza ga musulunci da musulmai, kamar yadda
Abdullahi bn Mas'uud (RA) a [Sahihul
Bukhariy, lamba: 3684, babin falalar Umar, da kuma lamba: 3863 a babin da ke
magana kan musuluntar Umar] ya ke cewa:
«مَا زِلْنَا أَعِزَّةً مُنْذُ أَسْلَمَ عُمَرُ».
Ma'ana: (Bamu gushe ba muna madaukaka masu
izza da buwaya tun da Umar ya musulunta).
A wata riwaya kuma da ta zo a cikin littafin
[Tarihin Madinah na Ibnu-shabbah, 2/661] ya karasa wannan maganar da fadinsa:
«لَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا نَسْتَطِيعُ أَنْ نُصَلِّيَ
فِي الْبَيْتِ حَتَّى أَسْلَمَ عُمَرُ، فَلَمَّا أَسْلَمَ عُمَرُ قَاتَلَهُمْ حَتَّى
تَرَكُونَا نُصَلِّي».
Ma'ana: (Hakika mun kasance bama iya mu yi
salla a dakin ka'abah har sai da Umar ya musulunta, yayin da Umar ya musulunta
sai ya yaki kafiran kuraishawa, har sai da suka kyale mu muke salla).
Kuma hakika lamarin samun izzar musulmai da
kuma shi kansa addinin da sababin musuluntar Umar (RA) ya zamto amsawar Allah
ne ga addu'ar manzonsa; da ta zo cikin fadinsa (SAW):
«اللَّهُمَّ أَعِزَّ الإِسْلامَ بِأَبِي جَهْلِ بْنِ هِشَامٍ
أَوْ بِعُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ» فَأَصْبَحَ عُمَرُ فَغَدَا عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَأَسْلَمَ، ثُمَّ صَلَّى فِي الْمَسْجِدِ ظَاهرا.
Ma'ana: (Ya Allah! Ka bada
izza da buwaya ga musulunci da musuluntar Abu-jahl bn Hishaam, ko kuma Umar bn
Al-khaddaab. Kashe-gari sai kawai Umar ya yi sammako izuwa ga manzon Allah
–SAW- ya karbi musulunci, sa'annan ya tafi masallaci ya yi salla a bayyane).
A wani lafazin kuma:
«اللَّهُمَّ أَعِـزَّ الإِسْـلاَمَ بِأَحَـبِّ هَـذَيْنِ
الرَّجُلَـيْنِ إِلَيْكَ؛ بِأَبِي جَهْلٍ أَوْ بِـعُمَرَ بْنِ الخَـطَّـابِ.
قَالَ: وَكَانَ أَحَبَّهُمَا
إِلَيْهِ عُمَرُ».
Ma'ana: (Ya Allah! Ka daukaka musulunci ka
bashi izza da musuluntar dayan mutumin da ka fi so daga cikin mutane guda biyu;
Abu-jahl ko kuma Umar bn Al-khaddaab. Maruwaicin ya ce: To sai ya zamto wadda
Allah ya ke so daga cikinsu shi ne: Umar).
[Wannan hadisin ya zo ta hanyoyi da riwayoyin
sahabbai da dama, daga cikinsu akwai A'ishah da Ibnu-abbas, da Ibnu-umar da
sauransu –RA-. Daga cikin maluman musulunci da suka fitar da shi kuma akwai:
Imamut tirmiziy, 3681, ya kuma inganta shi, da Ahmad, lamba: 5696, da Al-hakim,
lamba: 4886 da kuma lambobin da su ke gabaninsa. Malam Albaniy a cikin
As-silsilatus sahihah, lamba: 3225 shima ya inganta shi].
Wannan kuma shi ya sa malamin musulunci
Ibnu-hibban gabanin ya ambaci wannan hadisin da ya gabata sai da ya kulla
kanun-magana mai taken:
(ذِكْرُ الْبَيَانِ بِأَنَّ عِزَّ الْمُسْلِمِينَ بِإِسْلامِ
عُمَرَ كَانَ ذَلِكَ بِدُعَاءِ الْمُصْطَفَى صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ)
Ma'ana: (Magana da bayani kan lallai samun
izzar musulmai da musuluntar Umar ya kasance sakamakon addu'ar annabi –SAW-).
[v15/305, gabanin hadisi mai lamba: 6881].
Duk mutumin da ya bibiyi tarihin Umar (RA)
dukkaninsa zai samu cewa rayuwarsa gaba-dayanta izza ce da buwaya ga musulunci
da musulmai, kasancewar Allah ya karbi addu'ar manzonsa da ta gabata akansa,
wannan kuma shi ne dalilin da yasa A wani lafazin na Abdullahi bn Mas'uud (RA)
a cikin littafin [Tarikhul madinah na Ibnu-shabbah, v2/p661] ya ke cewa:
«كَانَ إِسْلامُ عُمَرَ فَتْحًا، وَكَانَتْ هِجْرَتُهُ
نَصْرًا، وَكَانَتْ إِمَارَتُهُ رَحْمَةً، لَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا نَسْتَطِيعُ أَنَّ
نُصَلِّيَ بِالْبَيْتِ حَتَّى أَسْلَمَ عُمَرُ، فَلَمَّا أَسْلَمَ عُمَرُ قَاتَلَهُمْ
حَتَّى تَرَكُونَا فَصَلَّيْنَا».
Ma'ana: (Lallai musuluntar Umar ya kasance
wani budi ne, hijirarsa kuma daga Makka zuwa Madina wani taimako, shugabancinsa
kuma rahama; lallai mun kasance bama iya mu yi salla a dakin ka'abah har sai da
Umar ya musulunta, yayin da Umar ya musulunta sai ya yaki kafiran kuraishawa,
har sai da su ka barmu mu ke salla).
A
nan zan kawo muhimman abubuwan da su ka auku a tsawon zamanin halifancin Umar
(RA) da ya kai shekaru goma (wato daga shekara 13-23 na hijira) su kuma shekarun
khalifancinsa suna cikin mafi kyan shekarun da musulunci ya rayu a cikinsu;
bayan zamani ko rayuwar manzon Allah (SAW), da kuma lokacin khalifanci Abubakar
(RA); hadisin mu na gaba (na 6 da ke tafe) na nuna haka. Su kuma misalan
abubuwan da su ka auku, da ambatonsu ke tafe zasu kara nuna mana izzar musulunci
da yaduwarsa a zamanin halifanci Umar bn Al-khaddab, da kuma yadda musulmai su
ke da kwar-jini a idanun makiyansu = Ga misalan kamar haka:
(1)
A duniyar wancan zamanin
akwai manya-manyan dauloli da masarautun kafirai masu karfin gaske guda biyu;
Na farkonsu ita ce: daula da masarautar Rumawa ta nasara masu riya bin addinin
annabi Isah (AS), wacce take yankin tsohuwar SHAAM, Sarkinsu kuma ana yi masa
lakabi da "Kaisar", Sai kuma ta biyun ita ce: daula ko masarautar
Farisawa masu bautar wuta (majusawa), wacce ita kuma ta ke yankin tsohuwar IRAQI
DA ABIN DA KE BAYANTA, sarkinsu kuma ana yi masa lakabi da "Kisrah".
Wadannan
daulolin guda biyu an ci garfin biranensu aka shigar da musulunci a cikinsu aka
bubbude su, duk a halifanci Umar (RA), ta bangaren masarautar Shaam a farkon
khalifancinsa ne Allah ta'alah ya bada gagarumar nasara ga musulmai a
"Yarmuuk" akan rundunonin rumawa masu dunbun yawa, aka kuma bude
garin Damashk, da Hims, da Kansarin, da Ajnaadin, daga bisani kuma aka bude
Baitul-makdis aka shigar da musulunci. Wannan kuma shi ya bada dama ga musulmai
kan shiga ko-ina a masarautar rumawa, ta kuma yadda suka ga-dama.
A bangare
guda kuma Sai Amru bn Al-aas (RA) ya fiskanci yankin Misra ya bude ta. daga
bisani kuma sai musulunci ya shiga sauran garurrukan Afrika.
Shi kuma
Sa'ad bn Abiy-wakkas (RA) da rundunarsa su ka nufi masarautar gabas; garurrukan
masu bautar wuta; Farisawa su ka yake su kana suka shigar da musulunci cikinsu,
Allah kuma ya basu gagarumar nasara, musamman a yakin Kadisiyyah da sauransu,
sannan aka bude biranen Khurasaan da wassunsu.
Shi kuma
wannan lamari na cewa musulunci zai bunkasa, ya yadu, ta yadda zai mamaye
daulolin nan guda biyu (daular rumawa data farisawa) tun tuni manzon Allah
(SAW) ya riga ya yi albishir da cin nasarar musulmai akan masarautunsu, tare da
bayyana cewa za a ciyar da taskokin dukiyarsu don daukakar musulunci, a cikin
fadinsa (SAW):
«إِذَا هَلَكَ كِسْرَى فَلاَ كِسْرَى بَعْدَهُ، وَإِذَا
هَلَكَ قَيْصَرُ فَلاَ قَيْصَرَ بَعْدَهُ، وَالَّذِي نَفْسُ
مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ،
لَتُنْفِقُنَّ كُنُوزَهُمَا فِي سَبِيلِ اللَّهِ»
Ma'ana:
(Idan sarki kisrah na farisa ya halaka to babu wani kisrah da zai zo a bayansa,
kuma idan Sarki Kaisar na Rumawa ya halaka to babu wani kaisar din a bayansa,
Na rantsen da Allan da ran Muhammadu ke hannunsa! lallai za a ciyar da taskokin
masarautunsu guda biyu fi-sabillah).
[Sahihul
Bukhariy, Lamba: 3618, Sahihu Muslim, lamba: 76].
Haka kuma
lamarin ya kasance a khalifancin Umar (RA), ta yadda aka rabe dukiyoyinsu a
garin madina a matsayin ganima.
(2)
Ga nan muhimman yaquka da budin
shigar da musulunci da su ka kasance a khalifancin Umar (RA) a
jejjere kuma a taqaice:
a-
Yakin
"Kadisiyyah" a watan Al-muharram, shekara ta goma sha hudu (14, bayan
hijira), karkashin jagorancin Sa'ad bn Abiy-wakkas (RA) ta yadda musulmai su ka
fiskanci Rustum daga bangaren farisawa masu bautar wuta cikin babbar rundunarsa
da sojojinta suka kai dubu tamanin ko fiye (80, 000), su kuma musulmai cikin
runduna mai sojoji dubu hudu ko shida (4000, 6000), amma duk da haka sai Allah
ya bada nasara ga musulmai a wannan yaki mai girma, har aka kashe jagoran yaki
ta bangaren farisawa mai suna Rustum bayan ya hau alfadarinsa ya riga ya gudu.
b-
Bayan wannan nasarar mai
girma da musulunci ya samu ta bangaren farisawa sai Umar bn Al-khaddab (RA) ya
tura wata tawagar don ta fiskanci masarautar Rumawa, a shekara ta (15, bayan
hijira), a yakin Ajnadin, karkashin jagorancin Amru bn Al-aas (RA), su kuma
rumawa jagoransu a wannan yakin shi ne: "Al-ardabun", haka aka yi
wannan yakin, Allah kuma ya bada nasara ga musulmai, har shi shugaban sojojin
rumawa Ardabun ya gudu ya buya a Baitul-makdis.
c-
A shekara ta goma sha shida
(l6, na daga hijira) kuma aka bude Baitul-makdis, bayan Abu-ubaidah (RA) ya
killace su a cikin garinsu, ba-shiga ba-fita, har sai da suka nemi a yi sulhu,
da sharadin Amirul-miminin Umar (RA) cewa ya zo, da Umar ya je Shaam sai ya yi
sulhu da Nasara da su ke Baitul-makdis, ya kuma shardanta musu fitar da Rumawa
daga masallaci, daga bisani kuma ya shiga masallacin ta kofar da manzon Allah
(SAW) ya shige shi a lokaci ISRA'I, ya kuma sallaci asubah a cikinsa.
d-
Shigar da musulunci garin
"Tustar" da "As-suus", da kame Al-hurmuzaan (a shekara ta,
17 hijira) na "Ahwaaz": Wadda ya shugabanci wannan lamari shi ne
An-nu'uman bn Mukarrin, da aka fara karawa sai shi Al-hurmuzaan da rundunarsa
su ka gudu zuwa "Tustar", sai musulmai kuma suka bi su, aka yi ta
bata-kashi, aka bada amana ga shi Al-hurmuzan kamar yadda ya nema, har a ka
kawo shi gaban Umar (RA) daga bisani kuma ya musulunta.
e-
Babban yakin NAHAWAND a
shekara ta ashirin da daya (21, bayan hijira): Wannan yakin yana daga cikin
manyan yakuka da aka yi shi tsakanin musulmai da masu bautar wuta; Farisawa, a
wannan yakin su farisawan sun gina ma kansu ganuwa da su ka labe a cikinsa; don
haka basu fita yakar musulmai ba, Sai dai kuma musulman karkashin jagorarsu sun
yi musu hikima da wayo irin na yaki, sai da su ka fitar da su daga ganuwar ta
su gabadaya, a wani yakin da mutane basu ji labarin irinsa ba, kuma daga karshe
Allah ya bada nasara ga musulmai. Wadda da wannan musulunci y agama da daular farisawa
masu bautar wuta a khalifancin Umar (RA).
f-
Wadannan su ne muhimman
abubuwan da suka auku a cikin shekara goman da Umar ya yi khalifanci, wadda
kuma dukkaninsu daukaka ne da bunkasa da izza ga musulunci da musulmai, ta
yadda aka samu adadi mai yawan gaske na mutane sun shiga addinin Allah a wancan
lokacin daga cikin masu bautar wuta, da kuma masu bautar alloli guda uku;
Nasara. [Don Karin bayani, a duba: abubuwan da su ka auku daga shekara 13-23 na
hijira, a cikin littafin: al-bidayah wan-nihayah, na Ibnu-kasiir, da kuma
littafin: Hikbatun minat tarikh, shafi 87-96].
NA
UKU: MUHIMMAN LAMMURA DA SU KA AUKU A KHALIFANCIN ''USMAN (RA)'' WADDA SUKE NUNA
IZZAR MUSULUNCI DA KUMA YAXUWARSA:
(((Zamu ci
gaba akan wannan Bi iznillahi ta'alah!)))
No comments:
Post a Comment