2015/12/03

HUXUBAR MASALLACIN ANNABI saw JUMA'A, 22/SAFAR/1437H ta Assheikh Assubaitiy, daidai 04 Disamba 2015m








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 22/SAFAR/1437H






LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya yi baiwa ga bayinsa Muminai, da tabbatuwa cikin addini, da kuma gaskiyar danganta kai zuwa gare shi, Ina yin yabo a gare shi (tsarki ya tabbata a gare shi), kuma ina gode masa, a cikin halin farin ciki da cuta, Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Shine abin bautawa a cikin qasa, da cikin sama. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa; Mafi alherin wanda ya yi salla, ya yi azumi, kuma harshensa ya furta godiya wa Allah, da yabo a gare shi. Allah ya yi qarin salati a gare shi, da kuma iyalansa, da sahabbansa; Ma'abuta falala da rigaye, da soyayya.   
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku da Ni kaina da bin dokokin Allah; saboda taqawa guzuri ne a lahira, kuma qarfi ne a yanayin tsanani, kuma kariya ne a lokacin ibtila'i,  Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi Imani ku bi dokokin Allah, kuma ku faxi Magana ta daidai   *   Zai gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, Kuma wanda ya yi biyayya wa Allah da ManzonSa to haqiqa ya rabauta da rabo mai girma" [Ahzab: 70-71 ].

DANGANTA KAI ;
Lallai DANGANTA KAI qari ne da xaukaka, kuma ji ne na-jiki da yake tunkuxa mai jinsa zuwa ga aikata aiyukan bunqasawa, yake kuma qara qarfafa soyayyar Mutum, da yadda yake jin falala.
Kuma mafi xaukakar dangantuwa itace: Xaukakar Bawa da sadar da aikin da zai yi, ga Ubangijinsa mabuwayi maxaukaki, wanda zai kai, izuwa ga aminci, da nitsuwa, da kuma samun rabo na har abada, "Lallai masoyan Allah babu  tsoro akansu, kuma ba za su yi baqin ciki ba" [Yunus: 62].
YANA DAGA MISALAN DANGANTUWA: Danganta kai, zuwa ga addinin Musulunci wanda kuma shine mafi girman ni'imah.
Kuma idan fitintinu suka sauka, aka kuma samu hanyoyin ruxin Mutane nau'i-nau'i, musibu suka yi tsanani, kuma aka kunno matsanancin yaqi a kan Musulunci = To ana son Danganta Kai, izuwa ga Musulunci a wannan lokacin ya qara wanzuwa cikin qarfi; kar ya raurawa, Mutane su tabbatu kada su yi taraddadi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku yi jihadi a cikin al'amarin Allah iyakar jihadi, Shi ne ya zave ku, Kuma bai sanya wani qunci ba a cikin addini, a kanku, Addinin Ubanku Ibrahim, Shine ya yi muku suna Musulmai, daga gabanin haka, Da kuma a cikin wannan; domin Manzo ya kasance Mai shaida a kanku, ku kuma ku kasance Masu shaida a kan Mutane, Sai ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi riqo da Allah shi ne majivincinku, Madalla da Shi, ya zama masoyi majivinci, Madalla da Shi, ya zama Mai taimako" [Hajj: 78].
            Muna qara ganin girman danganta kai, izuwa ga Musulunci wajen yadda yake xaukaka dukkan alaqoqi don su nisanci sharrace-sharracen qabilanci; saboda (a Musulunci) Balarabe bashi da wani fifiko akan Ba'ajame, ko kuma Fari akan Baqi, sai in ya fi shi da taqawar Allah da bin dokokinSa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya ku Mutane! Lallai ne Mu, mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da qabiloli, domin ku san juna. Lallai mafificin daraja a wurin Allah daga cikinku shine mafificinku a taqawa" [Hujuraat: 13].
            Musulunci yana qin duk wata danganta kai, ta qungiyanci, mai qunci, da kuma qabilanci abin qyama, Ballantana kuma danganta kai zuwa ga Mavarnata, Allah (تعالى) yana cewa:
"Sai (al'ummar) suka yan-yanke al'amarinsu (na addini) a tsakaninsu guntu-guntu, kowace qungiya suna tinqaho da xan abinda ya ke a gare su" [Muminuna: 53].
Wannan kuma saboda danganta kai, ya zama abu guda xaya kwara, maxaukaki, tatacce, "Waxannan sune qungiyar Allah, kuma lallai qungiyar Allah sune masu samun babban rabo" [Mujadala: 22].
Shi DANGANTA KAI ZUWA GA MUSULUNCI Shine: Miqa wuya ga Allah, da sallamawar zuci a gare shi, da lazimtawa gavvai yin biyayya ga Allah, da son Allah, da son ManzonSa, da yin so don su, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai abin sani kawai, majivincinku Allah ne da ManzonSa da waxanda suka yi Imani, waxannan da, suke tsayar da salla, kuma suke bayar da zakka, kuma suna ruku'i" [Ma'ida: 55].
            Kuma danganta kanmu zuwa ga addinin Musulunci yana hukunta danganta kai zuwa ga al'ummar Musulmai, tare da jin ciyon yanayin da ta samu kanta a ciki, da kuma yin aiki don taimakonta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Misalin Muminai cikin soyayyarsu da yin rahamarsu da tausayawarsu, kamar misalin jiki ne guda xaya, Idan wata gava daga cikinsa ta yi ciyo, sai sauran jikin ya taya ta kwanan zaune, da jin zogi".
            Kamar kuma yadda –a cike da alfahari- muke danganta kayukanmu zuwa ga TARIHINMU NA MUSULUNCI wanda ya xauki tutar shiryarwa zuwa ga xaukacin Duniya, da kuma HARSHENMU NA LARABCI dawwamamme; harshen alqur'ani mai karimci; Allah (تعالى) yana cewa:
"Abin karantawa ne na larabci ba mai wata karkata ba, don ko za su samu taqawa" [Zumar: 28].
Kuma ya ce:
"Da harshe na larabci Mabayyani" [Shu'ara'i: 195].

            Kuma itama danganta kai ta SOYAYYA, Addinin Musulunci ya tsaftace ta, kuma ya xora ta akan hanya, ya kuma kiyaye yadda zata yi motsinta, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ba za ka sami Mutane masu imani da Allah, da Ranar lahira suna soyayya da wanda ya sava wa Allah da ManzonSa ba;" [mujadala: 22].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Xayanku ba zai yi Imani ba har sai na kasance Ni na fi soyuwa a gare shi akan mahaifinsa, da xansa, da kuma Mutane gabaxaya". Kuma ya sake cewa:
"Wanda ya yi soyayya don Allah, kuma ya yi qiyayya don Allah, ya bayar don Allah, ya hana don Allah, to lallai ya cika imani".

            Kuma a ta vangaren XABI'U, Nan ma gaskiyar dangantawar da Musulmi ya ke yi wa kansa zuwa ga Musulunci ya kan bayyana, cikin yanayinsa, da maganarsa, da tufafinsa, da halayyansa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Allah ya la'anci masu yin kama da Mata a cikin Maza, Kuma Allah ya la'anci Matan da suke yin kama da Maza".
Kuma ya ce:
"Musulmi ba ya yin alfasha, ko ballagaza cikin zance, kuma ba Musulmi ba ne mai yawan suka, ko tsinuwa".
Kuma lallai rugujewar xabi'u ragujewar alamomi da suke nuna kyawun danganta kai (zuwa ga Musulunci) ne.
            Kuma, Idan DANGANTA KAI ZUWA GA MUSULUNCI ya yi rauni to sai zagwanyewar MUTUNTAKA da sakwarkwacewanta ya haxu da hakan, Kuma, ta kan yiwu Wannan Mutumin ya riqa jin kunyar bayyanar da wassu daga cikin alamomin addininsa.
            Kuma, kamar yadda Musulunci ya himmatu wajen gyaran zuciya da baxini, to haka ya bada himma ga kyan abinda yake bayyana (na zahiri), Wannan kuma domin Mutum Musulmi ya fito, daban, kuma domin kada ya kasance, mai makauniyar bi (taqalidi), Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Kada xayanku ya kasance maras ra'ayi; Mai cewa: Ni dai ina tare da Mutane, Idan Mutane suka kyautata nima zan kyautata, In kuma suka munana nima zan munana, Saidai ku horar da kanku; ta yadda idan Mutane suka kyautata sai ku kyautata tare da su, In kuma suka munana sai ku nisanci munanawansu".

            Shi kuma danganta kai zuwa, GARI KO QASA lamari ne da aka kimsa shi cikin jiki, kuma son qasa abu ne da aka halicci Mutum da shi, Kuma yaya Mutum ba zai so qasar da ya taso ko ya rayu akanta ko a cikinta ba, ya kuma girma akan turvayanta, ya kuma samu qulluwar alaqa da Mutanen cikinta da tarihinta? Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai, da Mu za mu wajabta musu cewa, Ku kashe kayukanku, ko fita daga cikin garurrukanku, da ba su aikata shi ba, face kaxan daga cikinsu" [Nisa'i: 66].
Kuma lallai Allah ya jarrabi annabinSa; Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) da rabuwa da garinsa (Makkah), Sai ya ce:
"Lallai ke ce mafi alherin qasar Allah, kuma mafi soyuwa daga cikin qasar Allah a wurin Allah, Kuma ba don an fitar da ni daga cikinki ba, da ban fita ba".
Kuma yayin da Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya san cewa, zai wanzu a matsayin xan gudun hijira, to sai ya roqi a sanya masa son garin Madina. Kuma ya kasance yana yin addu'ar alkhairi a garinsa: "Ya Allah! Ka sanya wa garin Madina ninki biyun abinda ka sanya wa garin Makka na albarka".
            Kuma lallai Musulunci ya tsara yadda son qasa ya kamata ya kasance, ya kuma kyautata wajen bayanin yadda za a fiskanci hakan.
Kuma danganta kai zuwa ga qasa yana dacewa da danganta ta zuwa ga addini, hasalima son qasa ya samo asali ne daga danganta kai zuwa ga addinin Musulunci, saboda danganta kai ga qasa, son qasar ne da hukuncin shari'a, wannan kuma wani abu ne da Musulunci ya bashi qima, domin a gina al'umma mai qarfi, a cikin aqidarta, da kuma saboda tarin yawan Mutanenta.
Kuma wanda ya fi gaskiya cikin sonsa ga qasa, da kuma yin fatan alkhairi a gare ta, Shi ne: Wanda ya fi su qarfin Imani, irin wannan mutumin kuma kasancewar yana yin aiki ne saboda neman samun rabo a Duniya da Lahira.
Kuma qarfin danganta kai ga qasa, yana azizita samun aminci da dukkan nau'ukansa, kuma zai bada kariya daga yaqar tunanin Mutanenta, ya kuma qarfafa danqon zumuntar 'ya'yanta na cikin gida, wacce za ta bada kariya daga waxanda suke son kawo fitintinu a cikin qasa, da xaga hankulan Mutane.
KUMA YANA DAGA CIKIN ABINDA DANGANTA KAI GA QASA KE HUKUNTAWA: Son qasar, da kuma sadaukar da rai don ita, da girmama Malumanta, da yin biyayya wa shugabanninta, da tsayuwa wajen aikata wajibai, da abubuwan da suka rataya a wuyan Mutane, da kiyaye ko bada kariya ga abinda qasar ta mallaka, da ma'aikatunta (mu'assasoshi), da girmama tsare-tsarenta da bin dokokinta. Sannan uwa-uba, Kada xan-qasa ya zama hanyar da masu son ganin sharri za su bi ta kanta, ko kuma waxanda su ke son cutar da wannan qasar.
KUMA YANA DAGA CIKIN DANGANTA KAI GA QASA: Bada dukiya ga faqiranta, da miqa hannu ga 'ya'yanta, da qarfafa aiyukan da ake qirqirowa a cikinta. Saboda kamar yadda ka ni'imtu da alkhairorin da suke cikin qasa, ka sha daga daddaxan ruwanta, to yana daga cikin haqqin wannan qasar ka sakanta mata, da abu mai kyau, kuma ka taimaka wajen aiyukan bunqasata, saboda "Shin kyautatawa tana da wani sakamako idan ba kyautatawa ba" [Rahman: 60]. 
    KUMA YANA DAGA CIKIN DANGANTA KAI GA QASA: Kyautatawa makwabta, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ba zai shiga aljanna ba, Wanda makwabcinsa bai aminta daga sharrinsa ba".
KUMA YANA DAGA ABINDA TAKE HUKUNTAWA: Son alkhairi ga 'ya'yan wannan qasar, da samar da taimakakkeniya a tsakaninsu, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Xayanku za zai yi Imani ba, har sai ya so wa xan'uwansa abinda ya ke so ma kansa".
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ku taimaki juna akan biyayya da taqawa, Kuma kada ku taimaki juna akan zunubi da zalunci" [Ma'ida: 2].
            KUMA YANA DAGA CIKIN DANGANTA KAI GA QASA: Yin kyauta, da adalci da kyautatawa, har ga Waxanda ba Musulmai ba, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ku saurara! Duk wanda ya zalunci kafirin amana, ko ya tauye haqqinsa, ko ya kallafa masa aikin da ya fi qarfinsa, ko ya xaukar masa da wani abu ba tare da yardarsa ba, to nine mai husumar da zai rinjaye shi da hujja ranar qiyama".

            Allah yayi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,
>>> 
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah; wanda ya shiryar da mu zuwa ga Musulunci, ya sanya mu, muka zamto mafi alherin al'umma a cikin Mutane. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai mulki Mai yawan sani. Kuma ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, Mafi alherin wanda ya yi salla, ya yi azumi, kuma yayi tsayuwar dare. Ya Allah ka yi daxin salati a gare shi, da kuma iyalansa da sahabbansa; jagorori masu ilimi.
Bayan haka:
Ina yin wasici a gare ku, da Ni kaina da bin dokokin Allah.
Lallai danganta kai ga IYALAI, a Musulunci, rukuni ne mai girma, kuma manufa ne maxaukaki mai qarfi.  Kuma lallai Musulunci ya kevance dangi na kusa, da cewa sune suka fi cancantar samu, ko a gabatar musu da abin amfani, da alherori, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Mutum mai kiyo ne a gidansa, kuma shi abun tambaya ne kan abinda aka bashi kiyo, Itama Mace mai kiyo ce a gidan mijinta kuma abar tambaya ce akan abin da aka bata kiyo".
            Kuma lallai qarfin yadda iyalai suka ginu, da kuma kasncewarsu salihai, yana shiga cikin sarqar yadda za a gina qasa, da kuma al'umma. Kamar yadda rashin kyakkyawiyar alaqa tsakanin iyalai yana sabbaba tsattsagewan yadda za a gina qasa, da al'umma.
            Kuma danganta kai na-kwarai yana girma ya bunqasa ne, a cikin Iyalai na-kwarai, waxanda suke tsayawa, kuma su rayu cikin soyayyar junansu da tausasawa, Cikin nitsuwa, da nisantar savani.
            Sannan Musulmi, Dole ya sani cewa, lallai Nasabarsa, ko dangantakarsa ba za ta wadatar da shi da komai ba daga Allah, saboda Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma dukiyoyinku basu zama ba, haka xiyanku ba su zama abinda zasu kusantar da ku wani muqami a wurinmu ba, face wanda ya yi Imani, kuma ya aikata aikin kwarai, To, waxannan suna da sakamakon ninkawa, saboda abinda suka aikata. Kuma su a cikin benaye amintattu ne" [Saba'i: 37].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Wanda aikinsa ya yi saivi da shi Nasabarsa ba za ta yi sauri da shi ba".

            Kuma dukkan Ma'aikatu mabanbanta ababen tambaya ne kan samar da DANGANTA KAI MANAGARCI, GA QASA DA SONTA; kamar Iyalai, Makaranta, Malami, da tsarin karatu, da Masallatai, da Maluman addini, da Masu da'awa, da Kafafen yaxa labaru, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Dukkanku masu kiyo ne, kuma dukkanku abun tambaya ne, kan abin kiyonsa".
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! kayi salati wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi Ibrahima, kuma ka yi albarka wa Annabi Muhammadu da iyalanSa da zurriyarSa, kamar yadda kayi albarka wa iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abun godiya ne, Mai girma.
            Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu,    da Iyalan annabi da sahabbansa masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka ruguza kafirci da kafirai, kuma Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Duk wanda ya nufe mu ko ya nufi Musulunci da mummunan abu to ka shagaltar da shi da kansa. Sau uku.
Kuma ka sanya rugujewarsa a cikin tsarinsa, Ya mai amsa addu'a.
            Ya Allah! Ka kiyaye Musulmai a kowani wuri, Ya Allah! Ka kasance wa musulmai… a kowani wuri, Ya Ubangjin talikai, Ya Allah! ka kasance wa musulmai… a kowani wuri, Ya Allah! Ka kasance musu Mai qarfafawa, Mai taimako, Mai tallafawa, Ya Allah! Lallai su, suna jin yunwa ka ciyar da su, qafofin wassunsu babu takalmi, ka ba su, Wassu kuma babu rig aka tufatar da su, Ya Allah an zalunce su; ka taimaka musu. Ya Allah an zalune su ka taimaka musu, Ya Allah an zalunce su, ka taimaka musu. Ya Allah! Ka daidaita harbinsu, ka haxa kansu, akan gaskiya, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka aljanna, da abinda yake kusantarwa zuwa gare ta, na zance ko na aiki, kuma muna neman tsarinka daga wuta, da kuma abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko na aiki.
            Ya Allah! Ka gyara mana addininmu wanda shine kariya ga al'amarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce a cikinta rayuwarmu take, kuma ka gyara mana lahirarmu wacce zuwa gare ta za mu koma, ka sanya rayuwa ta zama qarin alkhairi ne a gare mu, mutuwa kuwa ka sanya ta hutu ne a gare mu daga kowani sharri. Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka shiriya da taqawa da kamewa da wadaci da arziqi.
            Ya Allah! Ka taimake mu kada ka taimaki wassu akanmu, ka bamu nasara kada ka bada nasara ga wassu akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla ma wassu akanmu, ka shirye mu, kuma ka sauqaqe shiriyarka a gare mu, kuma ka taimake mu akan wanda ya yi zalunci akanmu.
            Ya Allah! Ka sanya mu zama masu ambatonka, masu yin godiya a gare ka, masu qanqan da kai a gare ka, masu yin kuka da mayar da al'amari zuwa gare ka.
            Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, ka tabbatar da hujjojinmu, kuma ka daidaita harshenmu, ka zare dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada lafiya ga majinyatanmu, ka yaye baqin cikinmu, ka sunce fursunoninmu, ka jivinci lamarinmu, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka yi dace wa shugabanmu da abinda kake so, kuma ka yarda, Ya Allah ka datar da shugabanmu mai hidimar harami guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka, Ya Ubangijin halittu, Kuma ina roqonka ka datar da na'ibansa guda biyu zuwa ga abinda kake so, kuma ka yarda, lallai kai mai iko ne akan  komai.
            Ya Allah! Ka datar da jagororin musulmai gabaxaya wajen yin aiki da littafinka, da yin aiki da shari'arka, Ya mafificin rahamar masu rahama.
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...