HADISI (NA
3): UMURNI KAN "KOYI'' DA KHALIFOFI GUDA2, BAYAN MANZON ALLAH (S A W);
(a)
LAFAZIN
HADISIN DA RIWAYOYINSA:
الحديث الثالث: ذكر أمر النبي r بالاقتداء بالخليفتين بعده:
عَنْ
حُذَيْفَةَ بْنِ الْيَمَانِ t، قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللهِ r: "إِنِّي لاَ أَدْرِي مَا قَدْرُ بَقَائِي فِيكُمْ؛ فَاقْتَدُوا
بِاللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي, وَأَشَارَ إِلَى أَبِي بَكْرٍ وَعُمَرَ ..."الحديث.
وفي لفظ بدون لفظ الإشارة: "اقْتَدُوا بِاللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي:
أَبِي بَكْرٍ، وَعُمَر".
(b)
FASSARAN
HADISIN:
Ya zo daga
''Huzaifah bn Al-yamaan'' (r a), ya ce: Manzon Allah (s a w) ya ce: ((Lallai ni
ban san kwanakin da suka rage mini na wanzuwata a cikinku ba; Sai ku yi
''koyi'' da mutane guda biyu da za su kasance a bayana, Sai ya yi nuni izuwa;
Abubakar da Umar)).
A wani
lafazin kuma haka hadisin ya zo (ku yi ''koyi'' da mutane guda biyu da za su
kasance a bayana; Abubakar da Umar).
(c)
WASSU DAGA
CIKIN MALUMAN DA SUKA RUWAITO HADISIN TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Wannan
hadisin maluman sunna dayawa sun ruwaito shi a cikin littatafansu, daga cikinsu
Imam Abu-isa At-tirmiziy a cikin
''jami'i'', lamba: 3663, da: 3799, kuma ya ce: hadisi ne hasan. Da kuma
Ibnu-majah a cikin ''as-sunan'', lamba: 97, da "Musnad Ahmad'', lamba:
23245. da kuma wassunsu.
Albaniy ya inganta shi, ya kuma ce an ruwaito
wannan hadisin ta hanyoyin sahabbai guda huxu;
Abdullahi bn Mas'ud, Huzaifah bn Alyamaan, da Anas xan Malik, da kuma Abdullahi xan Umar (r a), kana kuma ya kawo hanyoyin hadisin tare
da nazartar hanyoyin da suka zo hanya-hanya [Duba: littafin ''silsilatu
al-ahadisi as- sahihati'' na Albaniy, {3/ p233-236} lamba: 1233]. [Don
mai-da-martani ga wanda ya raunana shi duba: ''Minhaju as-sunnati, annabawiyyati'', [8/p361-362].
(d)
FA'IDODI BIYU DAGA WANNAN
''HADISI'':
Wannan hadisin ya qunshi vangarori guda biyu
muhimmai; wanda kuma su ne ginshiqai
biyu na wannan ''littafi''; kamar haka:
Na farko: Nuni kan
''khalifancin biyu daga cikin khalifofin Annabi (s a w) shiryayyu; wato:
Abubakar da Umar (r a).
Na biyu: Matsayin
Abubakar da Umar (r a) a cikin addini; da kuma yadda Annabi (s a w) ya yi
umurni kan a riqe su a
matsayin ababen ''koyi''.
Lallai Annabi (s a w) ya kevance khalifofinsa
shiryayyu –kamar yadda ya gabata a cikin hadisi na (2)- akan sauran sahabbai;
ta yadda ya yi umurni kan lazimtar ''sunnonin khalifofinsa shiryayyu'', sai
kuma ya kevance Abubakar
da Umar (r a) daga cikinsu; ta fiskar umurtar mutane kan riqarsu ababen
koyi ''qudwa''; Wannan
ya sanya malamin sunna Abu-muhammad Al'husain bn Muhammad Albagawiy (wanda ya
rasu a: 516h), a cikin littafinsa ''Sharhu as-sunnah, [1/ p208] ya ke cewa:
((Kuma kamar yadda Annabi –s a w-
ya kevance waxannan –Abubakar,
Umar, Usman, da Aliyu r a- daga cikin sauran sahabbai, kan cewa a bi sunnarsu,
to haka kuma ya sake kevance Abubakar
da Umar daga cikin su waxannan, a cikin
hadisin ''Huzaifatu'', daga Annabi -s a w-, ya ce: ku yi ''koyi'' da mutane
guda biyu da za su kasance a bayana; Abubakar da Umar)). Ga maganar tasa cikin
harshen larabci, kamar haka:
«... وَكَمَا خَصَّ
النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَؤُلاءِ مِنْ بَيْنِ الصَّحَابَةِ بِاتِّبَاعِ
سُنَّتِهِمْ، فَقَدْ خَصَّ مِنْ بَيْنِهِمْ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ فِي حَدِيثِ حُذَيْفَةَ
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: اقْتَدُوا بِاللَّذَيْنِ
مِنْ بَعْدِي: أَبِي بَكْرٍ، وَعُمَرَ». شرح السنة للبغوي (ج1/ص208).
Mashahurin
malamin addini; mai suna: Ahmad Ibnu-taimiyyata (r l) shima yana da magana
makamanciyar wacce ta gabata, a inda ya ke cewa –bayan ya ambaci wannan hadisi
da nake magana akansa-:
«وَلَمْ يَجْعَلْ هَذَا لِغَيْرِهِمَا، بَلْ ثَبَتَ عَنْهُ أَنَّهُ
قَالَ: "عَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ الْمَهْدِيِّينَ
مِنْ بَعْدِي. ..." فَأَمَرَ بِاتِّبَاعِ سُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ.
وَهَذَا يَتَنَاوَلُ الأَئِمَّةَ الأَرْبَعَةَ. وَخَصَّ أَبَا بَكْرٍ وَعُمَرَ بِالاقْتِدَاءِ
بِهِمَا. وَمَرْتَبَةُ الْمُقْتَدَى بِهِ فِي أَفْعَالِهِ وَفِيمَا سَنَّهُ لِلْمُسْلِمِينَ:
فَوْقَ سُنَّةِ الْمُتَّبِعِ فِيمَا سَنَّهُ فَقَطْ».
Ma'ana:
((Annabi –s a w- bai bada wannan ''matsayi'' ga wanin Abubakar da Umar; -yana
nufin: matsayin a rike su ''qudwa
–ababen koyi-'', Ya dai tabbata daga gare shi; ya ce: INA UMURTAR KU DA KU RIQI SUNNATA
DA SUNNAR KHALIFOFINA SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA A BAYANA, Sai Annabi –s a w- ya
yi umurni cewa a ''bi'' abinda khalifofi shiryayyu suka ''sunnata''; Wannan
kuma ya game waxannan
khalifofin guda huxu. Sai kuma
ya kevance Abubakar
da Umar kan a riqe su a
matsayin ''ababen koyi'', Shi kuma matsayi da martabar wanda ake koyi da shi
cikin duk ayyukansa, da kuma cikin ''abinda ya sunnata shi'' ga musulmai: tafi
martabar wanda ake ''bi'' a cikin abin da ya ''sunnata'' kawai)).
[Duba:
Majmu'u fatawa Ibni-taimiyyata, {4/p399].
Kuma shi wannan hadisin (na 3) yana nuna cewa ana umurni da a yi xa'a wa Abubakar
da Umar (r a), tare da riqe su ''ababen
koyi –qudwa-'' cikin
''abubuwan da kowannensu ya sunnata wa al'umma, dama xaukacin
aiyukansa''; a yayin khalifancinsa. Haka kuma bayan rasuwarsu; Ta yadda idan
Abubakar da Umar suka yi ''ittifaqi'' a tsakaninsu
cikin mas'alolin addini; to dole ne -da wannan hadisin- mu xauki wannan
''zancen''; don mu saka shi cikin aiki. Idan kuwa aka samu banbancin fahimta
tsakaninsu (Abubakar da Umar) to a nan za a mayar da wannan savanin izuwa ga
Littafin Allah da sunnar Manzon Allah (s a w); sannan kuma a yi aiki da abinda
dalilinsa su ka fi fitowa fili daga cikin ''zantuka guda biyun''. [Duba: ''Minhaju as-sunnati, annabawiyyati'', [8/p364].
Don haka; matsayin Abubakar da Umar (r
a) a cikin addini –da wannan hadisin da kuma makamantansa-, tafi ta 'yan'uwansu
Usman da Aliyu (r a), ballantana kuma sauran sahabbai –Allah shi qara yardarsa
a gare su gabaxaya; Amin-.
WANNAN kuma shi ke nuna cewa: abinda ake
jingina shi izuwa ga Manzon Allah (s a w) wai lallai shi ya ce: (Sahabbaina
kamar taurari su ke; da kowanne daga cikinsu ku ka yi ''koyi'' to kun shiryu) =
magana ce da ta sava da
hadisin ''nan''; da ya keve Abubakar
da Umar (r a) kan rikarsu ''qudwa
-ababen koyi-'', kuma maluma sun tattauna kan wannan hadisin a inda suka
bayyana cewa:
Na farko: Maganar
cewa sahabbansa kamar taurari su ke; duk wanda aka yi aiki da ''maganarsa'', ko
kuma aka yi ''koyi'' da shi, … ko kuma xaya lafazin da ya ce: Iyalaina
kamar taurari su ke; duk wanda ku ka riqe shi ''qudwa –abun
koyi'' = to kun shiriya. Maganganu ne –na farko- da babu su cikin littatafan
hadisi da ake dogara da su. Ga wassu daga cikin laffuzansu cikin larabci:
1-
أصحابي مثل النجوم فأيهم أخذتم بقوله
اهتديتم.
2-
أصحابي بمنزلة النجوم فبأيهم اقتديتم
اهتديتم.
3-
أهل بيتي كالنجوم، بأيهم اقتديتم اهتديتم.
Na
biyu: A littatafan da aka kawo waxannan
laffuzan, da makamantansu: sun zo ne ta hanyoyi masu rauni; wanda haka yasa
maluman yankan-shakka suka musu hukunci da kasancewa: maganganu ne masu rauni,
[Duba: raunatawar Imamu Ahmad a cikin: littafin/ ''almustadrak ala majmu'i
alfatawa'', {2/p121}, da Albazzaar, da kuma Ibnu-taimiyyata, a cikin: Littafin/
''Minhaju as-sunnati, annabawiyyati'', {8/p364].
Hasalima
wassu malaman sun yi hukunci a wannan maganar da cewa: maganar karya ce, [Ka
duba: Silsilatu al'ahadisi adda'ifati walmaudu'ati, na Albaniy, 1/ p144-153,
hadisai guda5, daga lamba: 58, 59, 60, 61, 62].
Na
uku: Dalili na gaba da ke nuna raunin wannan maganar: Shi ne cewa
da ta yi: Wai in an samu savani tsakanin sahabbai a cikin mas'aloli, ko kuma tsakanin
''ahlul-baiti''; wannan ya ce: ''kaza'', wancan kuma ya faxi
''kishiyar maganar na farkon'': to wai, kowanne mutum ya xauka
ya dace da ''shiriya''. Wannan kuma ya sava da
karantarwar musulunci ta kowace fiska; don haka ''hadisin da ya zo da wannan
ma'anar, ba yadda za a yi ya zama ya inganta izuwa Manzon Allah (s a w).
Na
huxu: kuma
na qarshe:
Wannan maganar ta sava wa faxin Manzon Allah (s a w) da ya keve
Abubakar da Umar (r a), da matsayin ''qudwa
-ababen koyi-'' cikin abinda suka ''sunnata wa mutane'', da kuma xaukacin
aiyukansu.
Amma dangane da yadda hadisin ke
nuni kan ''khalifancin Abubakar da Umar (r a) bayan Manzon Allah (s a w) kai-tsaye,
to shi kuma saboda faxinsa:
"اللَّذَيْنِ مِنْ بَعْدِي: أَبِي بَكْرٍ، وَعُمَرَ".
Kuma lallai
''ishara'' kan khalifancinsu (r a) zai qara zuwa a
cikin hadisai da suke tafe; da dama. Allah ya fahimtar da mu addininsa!
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا
محمد وآله وصحبه أجمعين.
Marubuci: Abubakar Hamza Zakaria
4 / Shawwal /1434h daidai 11/08/2013 miladiyya.
No comments:
Post a Comment