2015/11/12

HADISI KAN LAZIMTAR SUNNONIN ANNABI saw DA WANDA KHALIFOFINSA SHIRYAYYU SUKA SUNNATA

HADISI (NA 2 ): DAKE MAGANA KAN ''LAZIMTAR ABUBUWAN DA KHALIFOFIN ANNABI (S A W) SHIRYAYYU MASU SHIRYARWA SUKA ''SUNNATA";

(a)            LAFAZIN HADISIN:
الحديث الثاني: ذكر الأمر بلزوم سنة الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ الْمَهْدِيِّينَ:
عن الْعِرْبَاض بْن سَارِيَةَ t، في الحديث المشهور بحديث المَوْعِظَة البَلِيغَة، وفيه أنه قال رسول الله r: "... فَعَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي، وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الْمَهْدِيِّينَ الرَّاشِدِينَ، تَمَسَّكُوا بِهَا وَعَضُّوا عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ، وَإِيَّاكُمْ وَمُحْدَثَاتِ الأُمُورِ، فَإِنَّ كُلَّ مُحْدَثَةٍ بِدْعَةٌ، وَكُلَّ بِدْعَةٍ ضَلالَةٌ".
(b)            FASSARAN HADISIN:
Ya zo daga ''Irbadh bn Sariyah'' (r a) a cikin hadisi shahararre; wanda Annabi s a w ya yi wa'azi mai ratsa jiki ga sahabbansa, ya zo a cikinsa cewa: (Ina umurtarku da ku lazimci sunnata, da sunnar khalifofina shiryayyu masu shiryarwa, ku yi riqo da ita, ku yi damqa akanta da fiqoqi, kuma ahir xinku da riqo da qirqirarrun al'amura; saboda kowani qirqirarren abu bidi'a ne, kuma kowace bidi'a vata ce).

(c)            WASSU DAGA CIKIN MALUMAN DA SUKA RUWAITO SHI TARE DA BAYANI AKAN INGANCINSA:
Shi dai wannan hadisin maluman sunna dadama sun ruwaito shi a cikin littatafansu, Daga cikinsu akwai Imam Abu-dawud a cikin littafinsa ''as-sunan'', [lamba: 4607], da Abu-isa At-tirmiziy a cikin ''jami'i'', [lamba: 2676], kuma ya ce: hadisi ne hasan sahihi. Albaniy shima ya inganta hadisin, kana ya yi ishara cewa: manya-manyan Maluman hadisi -a jiya da yau- sun yi ittifaqi wajen inganta shi [Duba/ Silsilatu al'ahadis as-sahihati, 6/p526-527, lamba: 2735].

(d)            LABARI KAN SABANI DA RARRABUWA DA ZA SU KASANCE A CIKIN WANNAN AL'UMMA, BAYAN MANZON ALLAH –S A W-, TARE DA BAYANIN CEWA; RIQO DA SUNNAR MA'AIKI DA KUMA TA KHALIFOFINSA SHI NE MAFITA DAGA GARE SU:
Hadisi (na 2) wannan, kamar (na 1) ne, wato dukkaninsu na daga cikin hadisan da su ke qara tabbatar da annabcin annabi Muhammadu (s a w); Shi wannan na bada labari kan abinda zai faru na savani dayawa da rarrabuwa, bayan Manzon Allah (s a w), tare da yin bayanin mafita daga haka, kuma duk abinda hadisin ya tabbatar ya auku kamar yadda labarin ya shaidar, Wannan ya sanya ''Alhafiz Ibnu-rajab'' –a sharhinsa na faxin Manzon Allah s a w- ga wannan jumla a cikin hadisin:
«فَمِنْ يَعِشْ مِنْكُمْ بَعْدِي، فَسَيَرَى اخْتِلافًا كَثِيرًا، فَعَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ الْمَهْدِيِّينَ مِنْ بَعْدِي، عَضُّوا عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ»
{Duk wanda ya rayu a cikinku bayana to lallai zai ga savani dayawa; Ina horarku da riqo da sunnata, da sunnar khalifofina shiryayyu masu shiryarwa a bayana; ku yi riqo akanta da fiqoqi} yake cewa:
((هَذَا إِخْبَارٌ مِنْهُ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِمَا وَقَعَ فِي أُمَّتِهِ بَعْدَهُ مِنْ كَثْرَةِ الاخْتِلافِ فِي أُصُولِ الدِّينِ وَفُرُوعِهِ، وَفِي الأَقْوَالِ وَالأَعْمَالِ وَالاعْتِقَادَاتِ، وَهَذَا مُوَافِقٌ لِمَا رُوِيَ عَنْهُ مِنَ افْتِرَاقِ أُمَّتِهِ عَلَى بِضْعٍ وَسَبْعِينَ فِرْقَةً، وَأَنَّهَا كُلُّهَا فِي النَّارِ إِلا فِرْقَةً وَاحِدَةً، وَهِيَ مَنْ كَانَ عَلَى مَا هُوَ عَلَيْهِ وَأَصْحَابُهُ. وَكَذَلِكَ فِي هَذَا الْحَدِيثِ أَمْرٌ عِنْدَ الافْتِرَاقِ وَالاخْتِلافِ بِالتَّمَسُّكِ بِسُنَّتِهِ وَسُنَّةِ الْخُلَفَاءِ الرَّاشِدِينَ مِنْ بَعْدِهِ، وَالسُّنَّةُ: هِيَ الطَّرِيقَةُ الْمَسْلُوكَةُ، فَيَشْمَلُ ذَلِكَ التَّمَسُّكَ بِمَا كَانَ عَلَيْهِ هُوَ وَخُلَفَاؤُهُ الرَّاشِدُونَ مِنَ الاعْتِقَادَاتِ وَالأَعْمَالِ وَالأَقْوَالِ)).
(Wannan vangare daga hadisin nan, labari ne daga Manzon Allah –s a w- kan abinda ya faru da al'ummarsa na yawan savani cikin mas'alolin addini manya-manya da qanana-qanana, wanda ake kiransu: ''mas'alolin da su ne; tushen wannan addini, da wanda su ke ressa'', da kuma abinda ya kasance wa al'ummarsa na savani a cikin ''zantuttuka, da aiyuka, da aqidodi''. Kuma lallai shi -wannan yanki na hadisi- ya yi daidai da abinda aka ruwaito daga gare shi –s a w- na cewa: al'ummarsa zata rarraba izuwa kungiya-kungiya har kashi saba'in da wani abu, da kuma cewa dukkansu sun cancanci shiga wuta in banda guda xaya; wacce ita ce: ta ke kan ''manhajin'' da Annabi –s a w- ya ke kansa shi da sahabbansa.
Daxin-daxawa –a cikin wannan hadisi- akwai umurni daga Manzon Allah (s a w) a yayin da aka samu rarraba da savani cewa mafita ita ce: ayi riqo da ''sunnarsa'' da ''sunnar khalifofi'' shiryayyu a bayansa; Don haka ita wannan wasiyyar ta qunshi: RIQO DA ABINDA MANZON ALLAH –S A W- SHI DA KHALIFOFINSA SHIRYAYYU SU KE AKAI; TA VANGAREN AKIDODI, DA AYYUKA, DA KUMA ZANTUKA)) [Jami'u al'ulumi walhikami, p120].
Ka ga a nan, Annabi (s a w) ya bayyana savani da rarrabuwar kai da zai kasance a cikin al'ummarsa, a bayansa. Kana kuma ya ambaci abinda -matuqar an yi aiki da shi- zai zamo rigakafi da kuma magani ga hakan.
A cikin wannan hadisin an siffanta waxannan khalifofin da ''arrashiduna''; saboda sun haxa sifofi guda biyu; waxanda su ne:
1-   Sanin gaskiya.
2-   Aiki da ita. Saboda ''arrashid'' kishiyan ''algawiy'' ne; shi kuwa ''algawiy'' shi ne wanda ya san gaskiya amma ya yi aiki da savaninsa.
Alhafiz Ibnu-rajab ya ce: ((Ya zo a wata riwaya ''almahdiyyina''; ma'ana: Allah zai shiryar da su izuwa gaskiya, ba zai vatar da su ita ba; don haka kason mutane guda uku ne: ''rashid, gawin, da daalun''; Shi ''rashid'' shi ne: wanda ya san gaskiya ya kuma bi ta, shi kuma ''algawiy'' shi ne: wanda ya san gaskiyar amma ya qi binta, yayin da shi kuma ''addaalu'' shi kuma: shi ne wanda ya vace ga gaskiyar; bai santa ba, ballantana ya yi aiki da ita; Don haka; kowani ''rashid'': ''muhtad'' ne)) [Jami'u al'ulumi walhikami, p126].

(e)             BANBANCI TSAKANIN KHALIFOFIN ANNABI SHIRYEYYU DA SAURAN SHUGABANNI WADANDA BA SU BA:
Lallai waxanda suka jagoranci wannan al'ummar bayan rasuwar Manzon Allah (s a w), ko su ke jagorantarta, ko za su jagorance ta har zuwa tashin qiyama suna da yawan gaske; Amma umurni da Manzon Allah ya yi na cewa: a bi ''sunnarsa'' da kuma ''sunnar khalifofinsa shiryayyu'' bayan ya bada gamammiyar doka dangane da xaukacin shugabanni; cewa ''a ji, a kuma yi musu biyayya cikin abinda bai zam savon Allah ba'': Na nuna cewa lallai ''sunnar khalifofin Annabi shiryeyyu'' abar bi ce, kamar yadda ''sunnar ma'aiki s a w'' ta ke a bar bi; savanin waxanda ba waxannan khalifofin ba; na daga sauran shugabanni. Imam Malik bn Anas ya ce: Umar bn Abdil'aziz ya ce:
((سَنَّ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَوُلاةُ الأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ سُنَنًا؛ الأَخْذُ بِهَا اعْتِصَامٌ بِكِتَابِ اللَّهِ، وَقُوَّةٌ عَلَى دِينِ اللَّهِ، وَلَيْسَ لأحَدٍ تَبْدِيلُهَا، وَلا تَغْيِيرُهَا، وَلا النَّظَرُ فِي أَمْرٍ خَالَفَهَا، مَنِ اهْتَدَى بِهَا فَهُوَ مُهْتَدٍ، وَمَنِ اسْتَنْصَرَ بِهَا فَهُوَ مَنْصُورٌ، وَمَنْ تَرَكَهَا وَاتَّبَعَ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ، وَلاهُ اللَّهُ مَا تَوَلَّى وَأَصْلاهُ جَهَنَّمَ، وَسَاءَتْ مَصِيرًا)).
Ma'ana: ((Annabi –s a w- da shugabanni da su ka zo a bayansa sun sunnanta wassu sunnoni; waxanda riqo da su aiki ne da littafin Allah, kuma qarfi ne ga addinin Allah, -Su waxannan sunnonin- wani ba shi da daman ya kawo canjinsu ko ya jirkita su, ko dai ya tsaya yana nazari kan wani abu da ya sava musu. Kuma lallai wanda ya nemi shiriya da su: to shi shiryayye ne, wanda kuma ya nemi taimakon Allah da bin waxannan sunnoni: to shi abun a bashi nasara ne, Wanda kuma ya yi watsi da su; ya kuma bi turbar da ba ta muminai ba: sai Allah ya jivinta masa abinda ya jivinta, ya kuma shigar da shi jahannama; lallai kuma ta yi matuqar muni ta zamo makoma)) [Jami'u al'ulumi walhikami, p123].

(f)              MISALAI NA ABUBUWAN DA KHALIFOFIN ANNABI (S A W) SHIRYEYYU SUKA SUNNATA WA AL'UMMA:
Abubuwa da khalifofin Annabi (s a w) shiryayyu su ka ''sunnanta'' a tsawon khalifancin da ya kai shekaru talatin suna da yawa, [ka duba: Jami'u al'ulumi walhikami, p129] zan bada misali akan wassu daga cikinsu, kamar haka:
1-   Tattara ''mus'haf'' a cikin littafi guda: Wanda Abubakar ya yi a cikin ''khalifancinsa'' da shawarin amininsa Umar (r a). Zaidu bn Sabit (r a) ya kasance a farkon lamari yana ga kada a yi haka; har ya ke ce musu: Yaya za a yi, ku yi abinda Annabi (s a w) bai yi ba? Kana daga baya ya fahimci hakan shi ne maslaha, sai ya gamsu [Duba cikakkiyar qissar a cikin ''sahihul Bukhariy'', lamba: 4679].
2-   Yaqar waxanda su ka hana zakka: Lallai Abubakar assidiq (r a) ya yi azama kan haka, Xan'uwansa Umar bn khaxxab (r a) shi kuma a farkon lamari ya kasance yana ga kada a yi hakan, har zuwa lokacin da Allah ya sa yaji ya gamsu [Duba cikakkiyar qissar a cikin ''sahihul Bukhari'', lamba: 1399, 1400].
3-    Haxa masu sallar "qiyamu ramadana'' ga limami guda wanda Umar alfaruq (r a) ya yi: Mutane kuma su ka haxu akan haka tun daga zamaninsa; da lokacin khalifancin Usman da Aliyu (r a), har zuwa wannan zamani namu. Sai ya hakan ya zama xaya daga cikin sunnonin khalifofi shiryayyu. [Duba qissar a cikin ''Muwaxxah Malik'', lambobi: 378, 379, 380, 381].
4-   Kiran salla na farko, ranar juma'a wanda Usman (r a) ya qara, kuma ake yinsa a kasuwa: Saboda buqatuwan Mutane izuwa gare shi; don su je su shirya wa sallar juma'a, kuma Aliyu bn Abiy-xalib (r a) shi ma a lokacin khalifancinsa ya tabbatar da hakan bai canza ba, haka kuma aikin musulmi ya kasance a kan haka; izuwa yau. [Duba qissar a cikin ''Musnadu Ahmad'', lamba: 15969]. Da sauransu.
A takaice; Wannan hadisi da ke umurni kan riqo da sunnonin ''khalifofin Manzo'' waxanda kuma su ka tafiyar da khalifancinsu gaba-xayansu tsawon shekara (30) akan ''minhajun nubuwah'' na numa mana matsayin waxannan bayin Allah a cikin addinin Allah; wanda don fitar da shi wannan matsayin a fili Manzon Allah (s w t) ya umurce mu da bin ''sunnarsa'' da ''tasu'' a matsayin mafita daga kowani savani ko rarrabuwa da za a samu a cikin wannan addini.

Ya Allah ka xora mu kan turbar ma'aiki (s a w) da kuma ''sunnonin khalifofinsa shiryayyu'', kana ka kashe mu akan haka, Amin!
وصلى الله وسلم وبارك على نبينا محمد وآله وصحبه أجمعين.
Marubuci:  Abubakar Hamza Zakaria
4 / Shawwal /1434h daidai 11/08/2013 miladiyya.

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...