BAYANI
KAN
MATSAYAR
'YAN SHI'A ISNAA ASHARIYYA (RAFIDA) DANGANE DA UWAR MUMINAI A'ISHAH
(RADIYALLAHU
ANHA)
FASSARAR:
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
TAMBAYA:
Wassu masu wa'azi
da da'awa suna ganin cewa: Tuhumar Uwar muminai A'isha; mai gaskiya yar mai
gaskiya da cewa ta kafirta, wai kuma tayi alfasha (na zina), tuhuma ce da wassu
tsiraru suka yi mata daga cikin maluman shi'a, kuma wai abinda maluman shi'a; irin
su Yasir Habib da Mujtabah As-shiyraziy da wassunsu suka yi na kafirta ta da
cin mutuncinta = zance ne na tsiraru da bashi da gindin zama a cikin addinin
shi'a, Wai kuma "aqidun shi'a imamiyya" masu imamai guda goma sha biyu (12) basu
qunshi
irin waxannan tuhumce-tuhumcen ba, kuma wai sun barranta daga dukkan
abubuwan da ake danganta mata, kamar yadda malumansu masu takiyyah suke riyawa,
DA FATAN ZAMU SAMU BAYANI AKAN HUKUNCIN SHARI'AR MUSULUNCI KAN WANNAN MAS'ALAR,
Allah ya bada lada?
AMSA:
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah shi
kaxai.
Salati da sallama su qara tabbata ga wanda
babu annabi bayansa. Bayan haka:
Lallai yana daga
cikin abubuwan da suke baqanta rai; yadda wannan yaudara ko rufa-ido ta kama kwakwalen
wassu masu wa'azi da da'awa, har suke gaskata masu aqidar
"taqiyyah", a lokacin da masu
wa'azin ke quduri cewa lallai tuhumar uwar muminai sayyidah A'ishah (radiyallahu
anha) wai baya cikin aqidun shi'a imamiyyah.
Sai dai kuma
bincike ya bayyanar da cewa hakan (tuhumar uwar muminai A'ishah) aqida
ce tabbatacciya wacce 'yan "shi'a imamiyya isnaa ashariyya" suka
gaskata ta.
Daga cikin
manya-manyan maluman shi'a da suke sukar matar manzon Allah (sallal lahu alaihi wa sallama) kuma uwa
ga muminai; a jiya da yau akwai: Malaminsu/ Majlisiy, da Kummiy, da Ayyashiy,
da An-nabaxiy al-bayadiy, da Hashim al-bahraniy, da Yusuf al-bahraniy, da
Ja'afar Murtadah al-amiliy, da Muhammadu al-qummiy
an-najafiy, da Khumainiy, da Muhammadu Jamilu al-amiliy, da wassunsu dayawa.
A ta xaya
hannun kuma, bamu ga wani malami babba ko marja'i da shi'a ke dogara da shi:
yana neman a qona littatafan da suke cin mutuncin matar manzon Allah
(sallallahu alaihi wa sallama), ko dai, alal aqalli yace ya barranta
dasu ko da maluman da suka wallafa su, ko ya barranta daga aqidun da suka zo a
cikinsu, ko yayi hukuncin fita daga musulunci (riddah) ga mutumin da ya qudurci
munanan aqidun da suke cikin littatafan (to, me yasa haka?).
INA CEWA: Lallai yana daga
cikin aqidun shi'a imamiyyah KAFIRTA UWAR MUMINAI A'ISHAH (radiyallahu
anha), kuma wai ita 'yar wuta ce, wai harma tana da kofar shiga wuta da aka
tanada mata na musamman (da ya kevanta da ita), kuma
wai itace uwar sharri, da wassun waxannan
tuhumomin waxanda mutum mai hankali adali ba zai tava
gaskata su ba, koda kuwa ba musulmi ba ne.
Malamin shi'a mai
suna Ja'afar Murtadah al-amiliy a cikin littafinsa mai taken "hadisin
tuhumar A'ishah da aikata zina (hadisul ifki)" [a shafi na: 17] yace:
"إننا نعتقد كما يعتقد به علماؤنا
الأفذاذ –وهم جهابذة الفكر والتحقيق- أنّ زوجة النبيّ يمكن أنْ تكون كافرة كامرأة
نوحٍ وامرأة لوط، ولكن لا يمكن أنْ تكون فاجرة !!"، فبرَّأها من الزنا،
ثم حكم عليها بالكفر.
Ma'ana:
"Lallai aqidarmu itace aqidar
malumanmu zarata -waxanda kuma sune jigajigen ilimi da tahqiqi-
cewa: Lallai matar wannan annabin zata iya kasancewa kafira, kamar matar annabi
Nuhu, da matar annabi Ludu, Sai dai kuma ba zai yiwu ta kasance fajira
(mazinaciya ba)". Sai wannan malami ya barrantar da A'ishah (radiyallahu
anha) daga aikata zina, sannan ya mata hukunci da kafirci (wai ta bar musulunci).
Haka kuma malaminsu Al-ayyashi a cikin
[tafsirinsa, juzu'i2 / shafi: 22], da Almajlisiy a cikin [Biharul anwaar], da
Albahraaniy a cikin littafinsa [Alburhaan, juzu'i2 / shafi 383] Sun Ambato
maganar da suka yi qaryar jingina ta zuwa ga Ja'afar As-sadiq,
a tafsirin faxin Allah ta'alah:
((ولا تكونوا كالتي نقضت غزلها من بعد
قوة أنكاثًا)) [سورة النحل: 92]
Ma'ana:
"Kuma kada ku kasance kamar wacce ta warware saqar
da tayi bayan ya riga yayi qarfi warwarewa"
[Nahli: 92]. Wai yace:
(التي نقضت غزلها من بعد قوة أنكاثًا:
عائشة، هي نكثت إيمانها).
Ma'ana:
"Matar da ta warware abinda ta saqa bayan ya
riga yayi qarfi warwarewa: Itace A'isha; ta warware imaninta".
(sallallahu
alaihi wa sallama)
Haka kuma
malaminsu Hashim Albahraniy a cikin tafsirinsa [juzu'i 4/ shafi: 358] ya Ambato
daga Abu-abdillahi, lallai shi wai yace dangane da tafsirin faxin
Allah ta'alah:
((ضرب الله مثلا للذين كفروا امرأة نوح
وامرأة لوط كانتا تحت عبدين من عبادنا صالحين فخانتاهما فلم يغنيا عنهما من الله
شيئًا وقيل ادخلا النار مع الداخلين)) [التحريم: 10].
Ma'ana:
"Allah ya buga misali kan waxanda suka kafirta;
matar annabi Nuhu, da matar annabi Luxu, sun
kasance qarqashin bayina guda biyu daga cikin
bayina salihai, sai suka ha'ince su, Basu wadatar dasu komai ba daga Allah, Sai
aka ce: Ku shiga cikin wuta tare da masu shiga" [Tahrim: 10]. Wai yace:
(مثلٌ ضربه الله سبحانه في عائشة وحفصة
أنْ تظاهرتا على رسول الله وأفشتا سِرّه).
Ma'ana:
"Wannan misali ne da Allah (SWT) ya buga shi akan A'ishah da Hafsah saboda
wai sun taimaki junansu akan manzon Allah, sun kuma yaxa
sirrinsa".
Shima malaminsu mai suna Muhammadu Xahiru
Alqummiy
an-najafiy ya ambata a cikin littafinsa [Al-arba'ina fiy imamati al-a'immatix
xahirina,
shafi: 610] cewa:
(مما يدل على إمامة أئمتنا الاثني عشر
أنّ عائشة كافرة مستحقة للنار، وهو مستلزم لحقيقة مذهبنا وحقيقة أئمتنا الاثني
عشر... –ثم قال: وكل من قال بإمامة الاثني عشر قال باستحقاقها للعن والعذاب).
Ma'ana:
"Daga cikin dalilan da suke nuna imamancin limamanmu guda goma sha biyu
kasancewar A'ishah ta kafirta, kuma wait a cancanci shiga wuta, wannan kuma
shine abinda qudurta mazhabarmu, da cewa limamanmu goma sha biyu ne ke hukuntawa.
… Sannan yace: Duk mutumin da qudurta cewa limaman
shi'a guda goma sha biyu ne (12), to lallai dole ya qudurta
cancantar A'ishah ga tsinuwa, da kuma azaba".
Shi kuma malaminsu Yusuf albahraniy
cewa yayi A'ishah ta kasance munafiqa ce, sannan kuma sai ta yi ridda bayan
wafatin annabi (SAW), a cikin littafinsa [Ash-shihaabus saqib fiy bayani ma'ana
an-naasib, shafi: 236]:
(إنها كانت في حياته صلى الله عليه
وسلم من المنافقين، لجواز كونها مؤمنة في ذلك الوقت، وأنها ارتدت بعد موته كما
ارتد ذلك الجم الغفير المجزوم بإيمانهم سابقًا).
Ma'ana:
"Lallai A'ishah ta kasance a lokacin rayuwan manzon Allah (sallallahu
alaihi wasallama) daga cikin munafiqai, saboda a wannan
lokacin akwai yiwuwan kasancewarta mumina. Sai kuma tayi riddah bayan rasuwarSa,
kamar yadda mutane masu yawa waxanda ake da tabbacin
kasancewarsu masu imani a da, suka yi riddah".
Lamarin a wajen malaminsu mai suna an-nabaxiy
albayadiy ya kai ga yana riya cewa son da annabi (sallallahu alaihi wasallama)
yake yi ma A'ishah wai ba zai amfane ta ba, a inda yake cewa:
(قالوا: هي محبوبة النبي صلى الله عليه
وآله، وتوفي بين سحرها ونحرها، قلنا: لا تنفعها المحبة) [الصراط المستقيم
لمستحقي التقديم، ج3/ص165].
Ma'ana:
"Sun ce: A'ishah abun so ce a wurin annabi (sallallahu alaihi wa alihi),
kuma ya rasu ne a tsakanin qirjinta da wuyanta. Sai
muka ce: Son da yake mata ba zai amfanar da ita ba" [Littafin/ As-siraxul
mustaqim limustahiqqit taqdim, juzu'i 3, shafi: 165].
Shi kuma malaminsu mai suna Majlisiy a
cikin littafinsa: [Al, I'itiqaadaat,
shafi: 58]:
(ومما عُدّ مِن ضروريات دين الإمامية:
استحلال المتعة، وحج التمتع، والبراءة من أبي بكر وعمر وعثمان ومعاوية وكل مَن
حارب أمير المؤمنين صلوات الله عليه، والرافضة يعتبرون أنّ عائشة قد حاربت في
موقعة الجمَل).
Ma'ana:
"Yana daga abubuwan tilas ga addinin shi'a imamiyyah: halatta auren
mutu'a, da hajjin tamattu'i, da barranta daga Abubakar da umar da Usman da
Mu'awuya, da duk wanda ya yaqi Amirul muminina
(Aliyu) –salawatullahi alaihi-, Shi'ah rafidah na xaukar
A'ishah a matsayin wacce ta yi yaqi, a yaqin
da ake ce masa: yaqin kan raqumi (jamal)". Wannan ya yansa malaminsu Xuwsiy
a cikin littafinsa [Al, iqtisad fiyma yata'allaqu bi li'itiqaad,
shafi: 358]:
(ظاهر مذهب الإمامية أنّ الخارج على
أمير المؤمنين، والمقاتل له: كافرٌ، بدليل الفرقة المحقة على ذلك).
Ma'ana:
"Zahirin mazhabar shi'a imamiyyah ya nuna cewa waxanda
suka fita daga xa'ar amirul muminina; Aliyu, da wanda ya yaqe
shi sun kafirta, dalili kuma shine, qungiyar gaskiya (ma'ana: shi'a a wajensa)
sun kasance akan wannan ra'ayi".
A
kan wannan ne 'yan shi'a suke kafirta A'isha (radiyallahu anha) cikin lafazi
bayyananne. Tare da cewa A'ishah ta fita ne don kawo sulhu, ba don yaqi
ba, kamar yadda 'yan shi'a rafidha ke
riyawa!
Lamarin rafidha 'yan shi'a ya kai ga
sanya ma A'ishah laqabin: Ummush shurur (ma'ana: uwar sharrai) a cikin
littatafansu, kamar yadda malaminsu mai suna An-nabaxiy
albayadhiy ya ambaci haka a cikin littafinsa: As-siraxul mustaqim
limustahiqqit taqdim, juzu'i 3, shafi: 161] a inda yace:
(فصل في أم الشرور).
Ma'ana:
"Fasalin dake bayani kan uwar sharrai"; Wai yana nufin uwar muminai
A'ishah (radiyallahu anha).
NA BIYU: Aqidar
shi'a imamiyyah isnai ashariyyah dangane da kamammemiya tsarkakakkiya matar
manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama), kuma uwa ga muminai; A'ishah
(radiyallahu anha) mai cewa: Wai A'ishah (radiyallahu anha) tana da qofa ta
musamman daga cikin qofofin wuta da zata shiga ta cikinsa,
A inda shehinsu Al-ayyashiy a cikin [tafsirinsa, juzu'i 2/ shafi: 430] daga
Abu-basir daga abu-Abdullahi,
yace:
(يؤتى بجهنم لها سبعة أبواب؛ بابُها
الأول للظالم وهو زريق، وبابها الثاني لحبتر، والباب الثالث للثالث، والرابع
لمعاوية، والباب الخامس لعبد الملك، والباب السادس لعسكر بن هو سر).
Ma'ana:
"Za a zo da wutan jahannama; tana da qofofi
guda bakwai, qofarta ta farko na wanda yayi zalunci ne; wanda kuma shine: zariq
(suna nufin Abubakar as-siddiq), qofarta ta biyun kuma na habtar ne (suna nufin Umar alfaruq),
qofa
ta uku kuma ga na ukun (suna nufin: zun-nuraini Usman), ta huxun
kuma ga Mu'awuya, qofa ta biyar kuma ga Abdulmalik, qofa
ta shida kuma ga askar bn huw sir". Malaminsu Majlisiy ya ambata a cikin
littafinsa [Biharul anwaar, juzu'i 8/ shafi: 302] cewa:
(وعسكر بن هو سر كناية عن بعض خلفاء
بني أمية أو بني العباس).
Ma'ana:
"Sunan "askar bn huw sir" kinaya ne kan wani daga cikin
halifofin zamanin daular umawiyyawa, ko abbasiyyawa". Sannan sai yace:
(ويحتمل أن يكون "عسكر"
كناية عن: عائشة وسائر أهل الجمل؛ إذ كان اسم جمل عائشة "عسكرًا". وروي
أنه كان شيطانًا).
Ma'ana:
"Mai yiwuwa ne kuma "askar" ya kasance kinaya ne kan: A'ishah,
da kuma sauran waxanda suka yi yaqin
"jamal"; saboda kasancewar raqumin
da A'ishah ta hau wai sunansa: askar. Sai dai kuma an rawaito cewa raqumin
nata wani "shexani ne".
Nan kuma xaya
ne daga cikin maluman shi'a rafidha ke tuhumar A'ishah (radiyallahu anha) qarara
da aikata zina; malaminsu an-nabaxiy
albayadiy a cikin [Littafinsa/ As-siraxul mustaqim limustahiqqit
taqdim, juzu'i 3, shafi: 165] cewa yayi:
(قالوا: برّأها الله في قوله: (أولئك
مبرؤون) [النور: 26]، قلنا: ذلك تنزيهٌ لنبيِّه عن الزنا لا لها، كما أجمع
فيه المفسِّرون).
Ma'ana:
"Sun ce: Allah ya kuvutar da ita a cikin faxinSa:
Waxannan
abun kuvutarwa ne" [Nuur: 26]. Sai
muka ce: wannan kuvutarwa ne da Allah yayi ma annabinsa, bag a A'ishah ba,
kamar yadda maluman tafsiri suka yi ijma'I kan hakan".
Malaminsu mai suna Hashim albahraniy a
cikin [tafsirinsa, juzu'i 4/ shafi: 358] ya faxa yace: Aliyu
xan Ibrahim yace: Sannan sai Allah ya buga misali akansu su biyu, yace:
((ضرب الله مثلا للذين كفروا امرأة نوح
وامرأة لوط كانتا تحت عبدين من عبادنا صالحين فخانتاهما فلم يغنيا عنهما من الله
شيئًا وقيل ادخلا النار مع الداخلين)) [التحريم: 10].
Ma'ana:
"Allah ya buga misali kan waxanda suka kafirta;
matar annabi Nuhu, da matar annabi Luxu, sun
kasance qarqashin bayina guda biyu daga cikin
bayina salihai, sai suka ha'ince su" [Tahrim: 10]. Sannan yace:
(والله ما عني بقوله
"فخانتاهما" إلا الفاحشة، وليقيمن الحدّ على فلانة؛ فيما أتت في طريق
البصرة، وكان فلان يحبها. وفي نسخة: طلحة. ولما أرادت أنْ تخرج إلى
البصرة قال لها فلانٌ: لا يحل لك أنْ تخرجي من غير محرم؛ فزوّجت نفسها من فلان،
وفي نسخة: طلحة).
Ma'ana:
"Wallahi! Allah bai nufi komai ba da faxinsa
(Sai suka ha'ince su) in banda alfasha. Kuma tabbasa (mahdin shi'a) zai
tsayar da haddi ga wacce; akan abin da ta aikata a hanyarta ta tafiya garin
Basarah, dama kuma wane yana sonta, -A wani kofin littafin aka ce: Sahabi Xalhat.
A lokacin da ta so ta fita zuwa ga Basarah sai wane yace mata: Baya halatta a
gare ki, kiyi tafiya ba tare da muharrami ba; Sai kawai ta aurar da kanta ga wane
-A wani kofin littafin aka ce ga: Sahabi Xalhat".
Wannan
yasa malaminsu mai suna Ahmad al,ahsa'iy a cikin littafinsa dake magana kan aqidarsu
ta dawowa duniya gabanin qiyamah [Ar-raj'ah, shafi: 116] ya ambata cewa:
(أنّ مهدي الشيعة إذا خرج سيحيي أم
المؤمنين عائشة ويقيم عليها الحدّ، فقد ذكروا أنّ أبا جعفر عليه السلام قال: أما
لو قام القائم لقد رُدّت إليه الحميراء حتى يجلدها الحدّ، وينتقم لأمه فاطمة عليها
السلام منها، قلتُ: -جُعلتُ فداك- ولِمَ يحدّها الحدّ؟ قال: لقذفها على
أمّ إبراهيم).
Ma'ana:
"Lallai Mahdin shi'a idan ya fito zai rayar da uwar muminai A'ishah, kuma
wai zai tsayar mata da haddi; saboda sun ambata cewa lallai Abu-ja'afar alaihis
salam yace: Idan mahdiy mai tasowa ya taso to lallai za a dawo masa da A'ishah
da annabi ya mata laqabi da Alhumaira'u don ya tsayar mata da haddi, ya kuma xauki
fansa daga gare ta, ga mamarsa Fatimah alaihas salamu Sai nace: -Allah
ya sanya ni fansa a gare ka- Don me yasa zai mata irin wannan haddin? Sai
yace: Saboda tayi qazafi ga baiwar annabi da ta Haifa masa xa
Ibrahim". Dama suna cewa:
(قولهم إنّ المبرَّأة في قصة الإفك هي
مارية القبطية لا عائشة رضي الله عنها).
Ma'ana:
"Lallai wacce Allah ya tsarkake a qissar qiren qaryar
zina da aka yi ga matar manzon Allah itace: Mariya baqibxiya,
ba A'ishah (Allah ya qara yardarsa a gare
ta) ba". Malaminsu mai suna Alqummiy a cikin [tafsirinsa,
juzu'i 2, shafi: 75] da wassunsa daga cikin maluma shi'a imamiyyah duk sun
ambaci haka.
Shi kuma babban malaminsu na wannan
zamani dake neman haxewar ahlus-sunnah da 'yan shi'a kamar yadda yake riyawa, mai
suna: Khumainiy ya bada hukuncinsa ne kan matar annabi (sallallahu alaihi
wasallama) da sahabinsa Xalhat da Zubair (Allah ya yarda dasu gabaxaya)
da cewa:
(بأنهم أخبث مِن الكلاب والخنازير).
Ma'ana:
"Wai sun fi karnuka da aladai dauxa"
[kitabux
xaharah, juzu'i 3/ shafi: 457].
Shi kuma xan
shi'a da ake kiransa: Muhammadu Jamilu Hamud al,amiliy a cikin littafinsa mai
taken: Ha'incin da A'isha tayi; tsakanin kore yiwuwarsa da aukuwarsa [Khiyanatu
A'ishah bainal istihalati wal waqi'i, a shafi na:
30-31] cewa yayi:
(الدليل الخامس: لقد دلت الأخبار
الكثيرة من طرق المخالفين على أنّ عائشة كانت تفتي برضاع الكبير، والإرضاع مقدمة
للزنا قطعًا بل هو من أبرز مقدماته ... وإذا جاز لها الكشف عن نهديها لإرضاع رجل
أجنبيّ عنها، جاز لها أنْ تمارس بقية العملية الجنسية معه بكل ارتياح، لا سيما إذا
كان المرتضع بارعًا في الامتصاص واللمس؛ بحيث تنسى المرضعة نفسها، فضلا عن حولها،
ولا سيما إذا كان المرتضع كطلحة مِن المتيَّمين بعائشة، حتى وصل به الغرام إلى
التغزّل بها ولمسها في وليمة لعرس زينب بنت جحش حتى ظهر الغضب على وجه النبي
الأكرم).
Ma'ana:
"Dalili na biyar: Hadisai ta hanyoyin ahlus-sunnah masu yawa sun
nuna cewa A'ishah ta kasance tana bada fatawa kan halaccin shayar da mutum
babba, shi kuma shayarwa mataki ne dake gabatar zina, hasali ma shine mafi
bayyanar matakai da suke gabatarsa… kuma idan har ta iya bubbuxe
nonuwanta don shayar da mutum ajnabiyyinta babba, to ai ta samu dammar ta
aikata sauran aiyukan sha'awa tare da shi, a sake, musamman idan shi wanda ake
shayarwan ya gwanance wajen iya tsotso da shafe-shafe; ta yadda zai mantar da
mai shayar da shi karan-kanta balle abinda yake kewaye da ita, musamman kuma
idan wanda ake shayar da shi irin sahabin annabi Xalhat
ne; wanda yake haukar son A'ishah; har lamarin sonta ya kai shi izuwa ga faxa
mata maganganun batsa, da shafa jikinta, a walimar auren uwar muminai Zainab
bint Jahsh, har fushi ya bayyana a fiskar annabi mai karamci".
Xan shi'an ya
ci gaba da tuhumarta a cikin [shafi: 40] a inda yake cewa:
(فالغاية من تحليلها للإرضاع إنما هو
الشبق الجنسي الذي كانت تتصف به عائشة؛ فلم يكن بإمكانها الصبر عنه أبدًا).
Ma'ana:
"Manufarta na halatta irin wannan shayarwar wai shine jarabar neman saduwar
namiji da mace da A'ishah ta siffanta da shi, wanda kuma har abada ba zata tava
iya haqura
akansa ba".
A wannan [shafin na: 40] ya ci gaba da
cewa:
(ولكنها ابتدعت فتوى إرضاع الكبير
ليتسنى لها ممارسة الجنس مع مَن تريد مِن رجال المسلمين).
Ma'ana:
"Wai, A'ishah ta qirqiro fatawar shayar da babban mutum ne domin ta samu damar yin
zina da wanda take so daga cikin mazajen musulmai". (Mai qarya xan
wuta!). Ya kuma sake cewa [a shafi na: 41]:
(وثمَّة قرائن كثيرة تشير إلى أنَّ
عائشة كانت أكثر نساء النبيّ الأكرم صلى الله عليه وسلم عُرضة للشائعات الجنسية
الطابع، كقصتها مع صفوان بن المعطل السلمي، كما في قصة الإفك).
Ma'ana:
"Akwai dalilai da yawa da suke nuna cewa; A'ishah an fi jifanta da
maganganun yin lalata fiye da sauran matan annabi mai karamci (sallallahu
alaihi wasallama), kamar qissarta tare da Safwan xan
Almu'axxal, as-sulamiy, a cikin qissar qiren qarya
ta zina".
A
[shafi na 47] kuma bayan ya ambato qissishin qarya
cewa yayi:
(فيه من الدلالة على تعاطيها قيادة
الدعارة في مكة بحسب الظاهر، عندما هجرت المدينة أيام عثمان بن عفان فمكثت في مكة
حدود السنتين، وهو غير بعيد في حقها).
Ma'ana:
"A cikinsa akwai dalili da ke nuna cewa itace take shugabancin karuwanci a
garin Makkah, gwargwadon abin da ya bayyana, a lokacin da ta qaura
daga garin Madinah a halifancin Usman xan Affan, ta
je ta zauna a garin Makkah kusan shekaru biyu. Wannan kuma ba abu ne da za a ce
ba zai yiwu ba a wurinta". A [shafi na: 49] ya qara
da cewa:
(مَن كانت بهذه المستوى مِن الجُرأة
الجنسية فلماذا يُستبْعد في حقّها صدور الفاحشة بعد موت رسول الله، وقد اتّهمت به
في حياته).
Ma'ana:
"Matar da lamarin sha'awarta ya kai wannan matsayi to ta yaya za a nisanta
yiwuwan faruwar alfasha a wurinta bayan rasuwar manzon Allah, alhalin kuma an
tuhume ta da aikata shi tun yana da rai!". Sai kuma a qarshen littafinsa
[shafi: 99] ya ke cewa:
(فتحصل مما تقدم: أنّ عائشة خائنة
للرسول الأعظم في عقيدته، وخائنة له في فراشه، هذا ما وصلنا إليه بمقتضى سعينا
الخالص وجهدنا في البحث والتحقيق لفهم الخيانة الواردة في سورة التحريم، والأخبار،
بحق عائشة وحفصة).
Ma'ana:
"Sai muka fahimta daga abinda ya gabata cewa:
Lallai A'ishah ta ha'inci manzo mai girma ta fiskar aqidarsa
(kafirta), ta kuma ha'ince shi a shumfuxinsa
(zina). Wannan kuma shine qoqarinmu da bincikenmu
saboda mu fahimci lafazin "ha'inci" da ya zo cikin "suratut
tahrim", da kuma hadisai, kan A'isha da Hafsah suka kaimu zuwa gare shi".
'Yan shi'a sun ce: A'ishah (radiyallahu
anha) ta kasance baqar mace ce, mummuniya. Don haka:
(فلم تسلَم عائشة رضي الله عنها لا في
عِرضها، ولا في إيمانها، ولا في خِلقتها.
فهذا هو معتقد
الشيعة الإمامية كافة في أم المؤمنين؛ أنها كافرةٌ، بغيٌ، ابنةُ زنديق).
Ma'ana:
"A'ishah –radiyallahu anha- bata kuvuta
a wajen 'yan shi'a ba, la
ta fiskar mutuncinta, da kuma ta vangaren
imaninta, haka kuma ta fiskar sukansu kan halittarta. Wannan kuma shine aqidar
'yan shi'a imamiyyah gabaxayansu akan uwar muminai; ma'ana:
ITA KAFIRA CE, a wurinsu MAZINACIYA (KARUWA), 'YAR ZINDIQI
(wato: Abubakar as-siddiq)".
Abin da muka ambata ya wadatar (wajen
amsa tambayar da ta gabata), Allah ya qara yarda ga
uwar muminai, A'ishah, ya kuma tayar da mu a qiyamah
tare da ita, da kuma annabi Muhammadu, da sahabbansa masu karamci da xa'a
ma Allah.
Salatin
Allah da sallamarsa su qara tabbata ga annabinmu Muhammadu da iyalansa, da sahabbansa.
WASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA
BARAKATUHU…
Marubucin
wannan bayani
ABDULLAHI XAN
MUHAMMADU AS-SALAFIY
Allah ya
gafarta masa shi da iyayensa biyu, da xaukacin
musulmai
Talata:
26/Shawwal/1431h
Fassarar
Abubakar hamza
Juma'a:
03/04/1436h = 23/01/2015m.
A garin
Madinah.