2015/09/27

HATSARIN MINAH A HAJJIN BANA (1436h daidai 2015m) QADDARA TA RIGA FATA


HATSARIN "MINAH" A HAJJIN BANA QADDARA TA RIGA FATA
(KUMA TAKA-TSAN-TSAN BAYA IYA TUNKUXE SHI)
            A ranar alamis 10 ga zulhijjah, na shekarar hijira ta 1436, wanda tayi daidai da 24 ga satumba 2015 na miladiyya, a yinin layya, wanda kuma shine mafi girman yini a warin Allah (ranar hajji da tafi girma),  a kuma gari mai girma (Makkah), Lallai hatsari mai munin gaske ya auku wa mahajjata xakin Allah; bayan fitowansu daga Muzdalifah, a hanyarsu ta zuwa jifan Shexan, a qarshen Minah, wanda lamarin  yayi sanadiyyar mutuwan fiye da mutane xari bakwai, kamar yadda alqaluman da hukumomi suka bayar suka nuna. Kuma hukumomi sun tsayu wajen binciko musabbabinta ta hanyar kama komiti na musamman akan haka, da fatan magance aukuwar irinta a gaba, tare kuma da yin hukunci ga wanda yayi sakaci a cikinta, gwargwadon yadda binciken ya nuna. Amma ya zuwa yanzu kamar yadda bayanan farko suka fara nunawa kan musabbabin wannai musibar shine: Savawa tsare-tsaren gudanar da wannan aikin wanda sashin mahajjata suka tafka, da kuma yadda wassu mahajjatan bayan sun yi jifa suka dawo ta hanyar masu tafiya, wanda hakan ya haifar da cunkoso, da turarreniyar da ya haifar da rasuwan mahajjata da dama; nan take, wassun kuma bayan an kaisu wuraren basu kula na musamman. Saidai kuma wani abun lura a nan, shine wannan musibar lallai bata taqaita da iyalan waxanda abin ya shafa kaxai ba; a, a ! wannan musiba ce ta dukkan musulmai  gabaxayansu, a ko-ina suke, a duniya. Kuma a wannan gaxar akwai abubuwan day a kamata a xauka na darasi, kamar haka:
(1)           Lallai waxannan mahajjatan da suka fito daga muzdalifa, suka nufi wurin jifa, suna xauke da burace-burace dayawa, a wannan yini, sun kuma shirya yin aiyuka dadama, faraway das hi jifan, sai soke rakuman hadaya ko yanka shanu da awaki ko tumaki, sannan sai aski, daga bisani kuma su shiga garin Makkah domin yin xawafi, da sa'ayi, Sai kuma su dawo birnin Minah don su kwana biyu, ko uku, domin yin jifa, sai kuma xawafin bankwana, kana su koma garurrukansu,    waxannan bayin Allan babu wanda ya san cewa mutuwarsa za ta dufafe shi a gurbin da ta haxu da shi, kuma babu wanda ya san cewa za su yi irin wannan mutuwar a wannan wurin, saboda "Rai bata san a wani gari zata mutu ba" [Luqman:]. Wannan shi yake nuna muhimmancin kowani musulmi ya kasance cikin tanadi da jiran mutuwa,  a safiya da maraice, da kuma a kowani hali.
(2)           Lallai mahajjatan nan basu yi hasarar rayuwarsu ba, idan muka duba nassoshin da suke nuna cewa: wanda ya rasu a cikin wani yanayi za a tayar das hi akan halin day a rasu a cikinsa. Wannan yasa wani hadisin ya bayyana cewa kada a lulluve kan sahabin day a rasu a cikin haramarsa, haka kada a lulluve masa fiska; saboda "Za a tayar das hi a ranar qiyama yana TALBIYYAH". Haka wassu hadisan sun nuna cewa: Shahidai guda biyar ne, Sai kuma ya ambace su; Wanda ciyon ciki ya kashe, da wanda aka soke shi, da wanda Katanga ta ruso masa, da wanda ruwa ya shanye, sai kuma wanda ya yi shahada fisabillahi. Kuma lallai wani hadisin ya nuna cewa aikin hajji shima yana shiga cikin "fisabilillah", saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya tambayi matar da mijinta ya rasu, kan taje hajji sai tace: mijinta ya bar abun hawa, saidai kuma ya sanya shi waqafi fiysabilillah, don haka bata da abin hawa zuwa hajji, sai Annabi yace mata ta hau wannan raqumin zuwa hajji domin shima fiysabillahi ne.
(3)           Wannan musibar ta auku ne a ranar farin cikin mai girma  a wajen dukkan musulmai, sai ta cakuxa musu farin cikin da baqin ciki mai girma, wannan kuma shi yake nuna cewar rayuwar duniya bata zama garaua 100/100 ga mutane, akan haka baya dacewa musulmi ya ruxu da farin cikin duniya, saboda baqin ciki da hawaye za su iya gaurayuwa das hi a cikin kowani hali. Gidan daxi na shi ne kaxai aljannah, Allah ya shigar da waxannan mahajjatan, da mu gabaxaya cikinta, amin.
(4)           Farin cikin musulmai guda xaya ne, haka baqin cikinsu, saboda wannan musibar ta jijjiga musulman duniya gabaxayansu, Wannan kuma yana qara tabbatar da maganar Manzon Allah (لى الله عليه وسلم) da yake cewa:
"Musulmi ga musulmi kamar gini ne; sashinsa yana qarfafa sashi". Da hadisin da yake cewa: "Misalin muminai cikin soyayyarsu da tausasawarsu da yin rahama wa junansu kamar misalin jiki ne guda xaya,  Idan sashi ya tavu sai sauran jikin ya taya shi jin zogi, da rashin barci".
(5)           Hadisin da Alhakim da wassunsa suka ruwaito, kuma malamai suka ce hadisi ne mai kyau "hasan", wanda yake bayyana cewa:
"لا يغني حذر من قدر".
Ma'ana: "Taka-tsantsan baya tunkuxe qaddara". Saboda kayi mamakin irin abinda hukumomin qasar Makkah suke kashewa gabanin hajji, da lokacinsa, da kuma bayansa don ganin mahajjata sun huta, ba tare da sun sha wahala  ba, Amma tak-tsantsan xinsu, ba zai tava tunkuxe abinda Allah ya qaddara ba. Musulmi kuma dole ne akansa yayi imani da haka.
Bayan haka;
Zai kyautu na kawo tarjamar huxubar Madina ta wannan satin, wacce tayi magana kan karkasuwan mutane dangane da hukunci akan irin abubuwan da ka iya aukuwa zuwa kashi uku, sai kuma in biyo bayanta da huxubar garin Makkah ta Juma'a, wacce itama tayi Magana akan wannan lamari, kamar haka:

HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r),  JUMA'A, 11/ZULHIJJAH/1436H, wacce LIMAMI MAI HUXUBA SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY ya gabatar,   

Limamin a cikin huxubarsa ta biyu yace:
           
Mutane dangane da hukunci akan abubuwan da suke aukuwa da   annoba  da musibu sun kasu kasha-kashi

Wani kason su kan yi magana akan abinda ya auku ba tare da ilimi ba,      sai suyi ta kukkutsawa a cikin labarin ta hanyar yayata jita-jita, waxanda basu inganta ba,   sai suyi ta ambaton duk abinda suka ji a majalisosi, suna faxa suna nanatawa,    wai da nufin rage ciyon musibar,     Kuma lallai Allah ya hana bin wannan turbar, a inda yake cewa:
(وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا) [إسراء: 36].
"Kada ka bibiyi abinda baka da ilimi  akansa,    Lallai ji da gani da zuciya za a tambaye su akan haka", [Isra'i: 36].

            Akwai wani kason Waxanda suke kukkutsawa cikin labarun abinda ya wakana da niyyoyi munana, da kuma manufofi maqasqanta, suna sanyawa abinda ya auku rigunan qarya, da gyara zance;        da nufin isa zuwa ga wani abinda suke nufi; ko Na tuhumar kuvutattaun mutanen da basu ji ko suka gani ba,   ko kuma qoqarin bunne kyawawan aiyukansu,     Irin waxannan su kan yi iya qoqarinsu wajen mayar da kyawawan aiyuka munana,  ko kuma alheri zuwa sharri,    lafiya kuma su mayar da shi bala'i,   Kuma irin wannan kason a cikin mutane basu san adalci ko kunya ba;      saboda sun riga sun saba yin qarya da qirqiran zance,    ba tare da sun damu ba.
            Wannan kason saboda dai karyarsu ta bayyana,     da yadda suke aukawa cikin walaqanci, da raini daga mutane, sakamakon yadda suke jiran su ji musiba ta aukawa bayin Allah don su yi farin ciki   =  Allah ta'alah (a cikin alqur'ani) ya bayyana mana siffofinsu domin mu nisance su, a inda yake cewa:
(إِن تُصِبْكَ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ وَإِن تُصِبْكَ مُصِيبَةٌ يَقُولُوا قَدْ أَخَذْنَا أَمْرَنَا مِن قَبْلُ وَيَتَوَلَّوا وَّهُمْ فَرِحُونَ * قُل لَّن يُصِيبَنَا إِلَّا مَا كَتَبَ اللَّهُ لَنَا هُوَ مَوْلَانَا وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ) [التوبة: 50-51].
Ma'ana: "Idan kyakkyawa ya same ka sai ya baqanta musu rai,   Idan kuma musiba ta same ka sai su ce: HAQIQA MU TUN GABANIN HAKA MUN XAUKE AL'AMARINMU, Sai su juya alhalin suna farin ciki. Kace: Babu abinda zai same mu sai abinda Allah ya rubuta mana, kuma shine masoyinmu (mai jivintar lamarinmu), Kuma ga Allah ne muminai suke dogara" [Taubah: 50-51].
Kuma Allah ta'alah yace:
(لَقَدِ ابْتَغَوُا الْفِتْنَةَ مِن قَبْلُ وَقَلَّبُوا لَكَ الْأُمُورَ حَتَّىٰ جَاءَ الْحَقُّ وَظَهَرَ أَمْرُ اللَّهِ وَهُمْ كَارِهُونَ) [التوبة: 48].
"Kuma haqiqa sun nemi fitina gabanin haka, kuma suka yi ta jujjuya maka lamura, har gaskiya ta zo, al'amarin Allah ya bayyana alhalin suna qi" [Taubah: 48].

            Sai kaso na uku, Waxanda suka yi aiki da sabbuban da Allah ya shar'anta don kare kansu daga aukawa cikin musiba,    Amma sai abinda Allah ya qaddara yayi rinjaye   (sai musibar ta auku), daga nan; sai suka miqa wuya ga Allah kan abinda ya qaddara sannan ya hukunta,       kaga a nan; sai suka tunkuxe su SABBUBAN da ALLAH, sannan kuma da SABBUBAN DA ALLAH YA SHAR'ANTA.     To waxannan za a basu lada kan miqa wuya da suka yi akan abinda aka qaddara,     kuma waxannan sune ma'abota hankali da shiriya da tunani, Allah ta'alah yana cewa:
(وَلَنَبْلُوَنَّكُم بِشَيْءٍ مِّنَ الْخَوْفِ وَالْجُوعِ وَنَقْصٍ مِّنَ الْأَمْوَالِ وَالْأَنفُسِ وَالثَّمَرَاتِ وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ * الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ) [البقرة: 155-156].
Ma'ana: "Tabbas zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro, da yunwa, da tauyewar dukiya da rayuka da 'ya'yan  itatuwa,    Kayi bushara ga masu haquri Sune waxanda idan musiba ta same su sai suce: LALLAI MU DAGA ALLAH MUKE, KUMA LALLAI MU ZUWA GARE SHI MASU KOMAWA NE" [Baqarah: 155-156].
            Lallai a qarshen hajjin wannan shekarar MUNA YABAWA ALLAH kuma MUNA YIN GODIYA A GARE SHI, akan tsayuwan rukunin aikin hajji da kuma dawwamarsa.
            Kuma lallai duniya sun shaida kan abinda wannan qasar shiryayyiya take yi; na bada kula na musamman ga mahajjatan xakin Allah mai alfarma,    da hidimomi manya-manya, ta kowace fiska,    tare da haxe duk wani qarfi wuri guda don    sauqaqe al'amuran hajji,    tare da bada jagoranci mai hikima cikin kowani hali daga cikin halayyar aikin hajji.

            Kuma duk wanda ya musanta kasancewar haka, to yayi daidai da wanda yake musanta samuwar rana,     Sai ya zama; abin a tuhumi hankalinsa ne   !

            Al'amari kuma duka na Allah ne;  yana aikata abinda ya nufa.   Kuma shi Allah          ma'abocin rahama ne, da hikima.

            Kuma qarfin qasa –a duniya- ba zai iya tsara lamarin wannan taro na hajji ba,    Saidai kuma –da musulunci- Allah ya bada iko a wannan qasar, tana iya tsara shi koyaushe.

            Wannan kuma shine karshen hudubar limamin.
Kuma lallai limamin a cikinta ya tunatar da Mutane ne, akan karkasuwan Mutane, idan WANI ABU YA AUKU, KO MUSIBA TA FARU, ta yadda suke kasuwa kashi uku,    biyu daga cikinsu abun zargi ne, duk da cewa dayansu ya fi muni.      Yayin da kaso na uku shine abinda ake neman DUKKAN MUSULMAI SU KASANCE AKANSA A IRIN WANNAN HALIN KO MAKAMANCINSA.
 Da fatan Allah ya amfanar da mu da abinda ya zo a cikinta.

Daga nan sai mu garzaya garin Makkah don mu saurari me shi kuma limamin a cikin hudubarsa ta biyu yake cewa:

HUXUBAR MASALLACIN KA'ABAH,  JUMA'A, 11/ZULHIJJAH/1436H, wacce LIMAMI MAI HUXUBA SHEHI SALIH BN MUHAMMADU ALU XALIB ya gabatar,   Yace: 
Bayan haka:
Lallai masarautar larabawa ta Saudia da mazajenta da na'urorinta, da dukkan hukumominta = suna aikata aiyuka manya-manya, domin su zamto hidima ga mahajjata da masu umrah da ziyara.
Kuma tun gomannin shekarun da suka wuce ita wannan qasar (ta Saudia) tana jagorantar gudanar da aikin hajji, cikin iyawa da gwanancewa, da bada kulawa na alfahari. Kuma ba zai tava cutar da hakan ba, ko ya tauye shi MAI AUKUWA DA KA IYA BIJIROWA wanda kuma (a wannan karon) ya faru sakamakon cunkoson da ya auku ga wassu mahajjatan da kuma abinda hakan ya haifar na tunkuxar junansu, ko kuma don sava wa wassu tsare-tsaren gudanar da wannan aiki.
Kuma idan a qaddarar Allah, ya zavi ya riqi wassu daga cikin bayinSa a matsayin shahidai; a mafi kyan halin da suka samu kansu a cikinsa, sa'annan a wurin da yafi xaukaka (Makkah), Wassun kuma Ubangiji ya qaddara jarrabarsu da samun raunukan da za a basu lada akansa = to lallai yana daga cikin abinda har abada ba zai samu karvuwa ba, A QARYATA SAMUWAR QOQARI, KO MUSANTA NASARORI DA AKA CIMMA, ko hakan ya zama SABABIN CIN MUTUNCI, DA QIRQIRE-QIRQIRE (KO QARIN GISHIRI). Kuma yana daga cikin mugunta da qaranta: Yin tafi idan musiba ta shafi wani musulmi, da kuma ribatar musibar musulmi don samun wassu buqatu na duniya, ko cimma manufofi na siyasa. Kuma wannan MASARAUTA (ta Saudia) cikin godiyar Allah, tana da cikakken ikon jagorantan lamuran hajji, ba tare da wani qarin qishiri ba.  Kuma lallai hukumar tana da kyakkyawan shugabanci akan abinda Allah ya xaukakata da shi na hidimar harami guda biyu maxaukaka, babu mai jayayya akan haka. Kuma lallai kundin wannan qasar, da tsarin mulkinta na farko; na asali yayi magana akan wannan hidimar.  Kuma kulawar da aka yi ko ake yi ga haramin nan guda biyu, ko ga mutanen da suke nufansu abu ne da idanu suke gani (ba a voye ba). Kuma haqiqa Allah ta'alah ya kewaye xakinSa, da baqinSa, da basu aminci da nitsuwa, a lokutan da duniya suke cikin firgici da rashin tsaro, wanda wutan fitinu da yaquka ke kunnuwa. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya hore wa garinSa mai alfarma masu bashi kariya ma'abota gaskiya, waxanda Allah ya kiyaye addini da su, ya kuma kiyaye garurruka da bayi da shugabancinsu,
(أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا حَرَمًا آمِنًا وَيُتَخَطَّفُ النَّاسُ مِنْ حَوْلِهِمْ) [العنكبوت: 67].
Ma'ana: "SHIN BASU GANI BA NE, LALLAI MUNE MUKA SANYA HARAMI YA ZAMA MAI AMINCI, ALHALIN ANA WAFCE MUTANE A KEWAYENSU…" [Ankabuut: 67].
            Kuma lallai mu, a lokacin da muke godewa Allah akan ni'imominSa; wajen sauqaqe hajji ga xarurrukan dubban mahajjata, da kiyaye su,   to lallai mu muna juyayin baqin ciki akan abinda ya auku, wanda Allah ya qaddara shi ga wassu daga cikin mahajjata, a ranar jiya (10/zulhijjah/1436h), har su ka haxu da ajalinsu, a turerreniyar da ba a ji daxinsa ba a MINAH, Saidai babu wani abinda zamu ce: Sai abinda zai yardar da Ubangijinmu, ba tare da fushi ko yin musu da abubuwan da Allah ya qaddara ba. Kuma ya dace a lokacin da ake bincike kan musabbabin faruwar wannan musibar domin daqile aukuwar irinsa a gaba, ko kuma hukunta wanda yayi sakaci a yanzu = ya dace kada ayi watsi da qoqarin gomannin dubban masu tsara wannan aiki, da masu hidima wa baqin Allah; waxanda suke rakiya ga mahajjata a dukkan matakansu da matsayansu, wajen tsara aikin ko bibiyarsa, suna kuma qoqarin kawo aminci a dukkan hanyoyi, kuma suna tsara tawagogi, da bada kula ga marasa lafiya, da xora vatacce kan hanya, da nusar da mahajjata ko karantar da su, da ciyar da mayunwaci, da shayar da masu qishi, da taimakawa gajiyayye, Ga waxanda suke bada rayuwarsu da dukkan qoqarinsu don hutun mahajjata da walwalarsu muke miqa yabo da godiya, da kuma yin addu'a, da qanqan da kai ga Allah kan ya sakanta musu da alheri. Kuma lallai abinda yake vuya na aikinsu yafi yawa, akan abinda yake bayyana wa mutane. Saidai kawai muce: Allah ya biya su lada, ya kuma ninninka sakayyarsu.
            Saidai kuma yana cikin fajircin husuma: Wassu mutane su yi amfani da abinda ya faru don sanya shakka wa jama'a kan qoqarin da ake yi, ko don yin suka kan kyautuka… . Bayan kuma duniya gabaxayanta ta shaida kan girman kyauta, da manya-manyan abinda ake qaddamar da shi ga waxanda suka nufo xakin Allah, daga wajen mazauna Makkah da Madina, xaixaikunsu ne, ko hukumomi. Kuma saboda idan aka rasa kunsa sai mutumin da ya rasa shi ya iya faxa ko aikata duk abinda yaga dama.
            Kuma lallai yana cikin izgilanci mai xaci: Yayi qoqarin qaqalo kukan rashin SHAHIDAN MINAH Waxanda a tarihance suka karkashe mutane ko mahajjata, tare da aikata ilhadi a HARAMI,  ta hanyar karkashewa, ko qone-qone, da shigar da munanan makamai, tare da tsoratar da mahajjata, da alqawarta azabtar da su, tare da yin qoqarin hana mutane zuwa haramin.
            Kuma yana daga cikin abin mamakin ('yan shi'a) waxanda suke qaqalo kuka ga rayukan musulmai, waxanda a waiwai suke bayyanar da kwaxayinsu kan kiyaye zuban jinin musulmai: Lallai su sune suke tuttura gomannin sojojin gona a qasar Iraqi da Yemen da Siria, don kashe dubban xarurrukan musulmai (sunnah), da qauratar da miliyoyi daga mahallansu, kuma domin su samu damar taskance manya-manyan siton makamai a dayawa daga garurrukan musulmai,  kuma sune suke dasa qiyayya a zukatan waxanda suka yaudaru da su, da kuma laqqana musu faxin kalmomin da ake neman maimaita su, waxanda kuma suke cike da alqawarin yayyaka uku bisa huxun (3/4) musulmai. Da fatan Allah ya kare musulmai daga sharrinsu, ya kuma shiryar da waxanda aka vatar ko kuma waxanda suka ruxar da su. To zuwa ga waxanda suke tiqa rawa akan ciyo ko raunin da aka samu, waxanda kuma sune suka fi tsananin farin ciki kan samuwar haka = muke cewa: Lallai maganar "taqiyyah" ta faxi babu nauyi, kuma wanda yake shakkar cewa ku maqiya ne ya samu tabbaci kan lamarinsa, kuma gari ya riga ya waye ga duk mai idanu guda biyu, kuma Allah ya sanya dayawa daga cikin mutane yanzu suna iya tantance gaskiya daga varna, da kuma wanene maqiyi ko aboki. Kuma duk abinda kuke yi, ihu ne na wanda ya xebe tsammanin nasara, da gurnanin wanda ya kunyata, saboda babu abinda yau-da-gobe ya qara muku sai qara kunyata, abubuwan da suke aukuwa –a nan da can- basa qara muku komai sai ciyo da rauni, Albishirinku da abinda zai faranta wa musulmai, ku kuma ya baqanta muku, wanda kuma zai yaye baqin ciki wa larabawa da musulmai, ku kuma ya qasqantar da ku.  ….
….    Daga nan   sai mai huxubar yayi Magana akan MASALLACIN QUDUS DA IRIN WALAQANCIN DA YAKE GANI A KWANAKIN NAN A HANNUN YAHUDAWA, Sannan yace:
            Ya ku mahajjatan xakin Allah mai alfarma …
            Ku sani lallai wannan qasar (masarautar larabawa ta Saudia) da mazajenta, da na'urorinta da hukumominta, suna yin gagaruman aiyuka don yin hidima a gare ku, da kuma sauqaqe hajjinku, kuma dukkan tsare-tsare an sanya su ne don maslaharku, faxi-tashi kuma gabaxayansa don ku ake yi, SAI KU YI AIKI DA FAXAKARWA, KUMA BI DUKKAN DOKOKI, KU RIKA JINCEWA KU ALHAZAI NE, SAI KU KASANCE AKAN MAFI ALHERIN HALI CIKIN AIYUKA DA HALAYYA, KUMA KU LAZIMCI NITSUWA DA BI SANNU-SANNU, DA TSAKAITAWA, Sannan kuma albishirinku; kasancewar ku masu tafiya ne zuwa ga Ubangiji mai karamci.    Allah ya sanya hajjinku ya zama kuvutacce, aikinku kuma abun godiya, zunubinku kuma abun gafartawa, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.    

            Wannn shine qarshen abinda limamin ya faxa akan wannan lamari.  Sai yayi addu'oi. 

Wannan shine abinda na so na tunatar da 'yan'uwana akansa, kan wannan lamari mai girma, da fatan Allah ta'alah ya karvi waxannan bayin a matsayin shahidai a wurinsa, majinyata kuma ya gaggauta basu lafiya.    Sannan ina roqonsa da sunayensa masu kyau da sifofinsa maxaukaka yak are bayinsa daga aukuwar makamancin haka, a garin Makkah ko a waninta. Amin.

                        Abubakar Hamza Zakariyya,     
                        Madinah,   13/zulhijjah /1436h

                        Daidai da 27/ satumba/ 2015m.               

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...