HUXUBAR LAYYAH DAGA MASALLACIN ANNABI (r)
ALHAMIS, 10/ZULHIJJAH/1436H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo na Allah ne; yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka,
madawwami; da dawwamar izzarSa, da kuma kyan fiskarSa, da girman mulkinSa; Muna gode masa maxaukakin sarki, kuma shine wanda ya cancanci yabo da
godiya. Ba a iya qididdige
ni'imarSa, kuma ba za mu iya qididdige
yabo a gare shi; Saboda shi Allah kamar yadda yayi yabo ne wa
kanSa.
Salati da sallama su qara tabbata ga bawanSa
kuma mafi alheri cikin halittunSa,
salatin da adadinsa baya qarewa,
Wanda kuma bawan dake maimaita shi ba zai tava qoshi daga faxansa
ba.
ALLAHU AKBAR duk lokacin da mai azumi yayi
azumi, sannan ya yi idi, ALLAHU
AKBAR duk lokacin da asuba tayi sannan gari ya waye, ALLAHU AKBAR duk lokacin da mai hajji
yayi aikin hajji, kuma yayi umrah,
ALLAHU AKBAR duk lokacin da shuka ya tsira sannan yayi fure, ALLAHU AKBAR duk lokacin da ya bada wadaci ga
wani bawa sannan ya talautar,
A shekarar hajjin bankwana, a cikin yinin arfah
mai girma, aya mai girma ta sauka;
wacce kuma itace mafi girman ni'ima ga wannan al'ummar; [A yau na cika addininku a gare ku,
kuma na cika ni'imata akanku, kuma na yarje muku musulunci addini]
[Ma'idah: 3]
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya rasu bayan tsayuwan arfah da kwanaki tamanin da xaya (91).
Kuma lallai Allah ya cika addini da Shi (صلى الله عليه وسلم); don haka halittu basa
buqatar wani addinin; wanda ba musulunci ba,
ko kuma wani Annabin wanda ba annabinsu ba (صلى الله عليه وسلم); kuma shine cikamakon
annabawa; Babu abinda yake HALAL sai
abinda ya halatta, Babu kuma HARAM sai
wanda ya haramta, Babu kuma ADDINI sai
abinda ya shar'anta, Allah
ta'alah yana cewa:
"Kuma kalmar Ubangijinka ta cika;
gaskiya da adalci, Babu mai canza kalmominSa" [An'aam: ]. Wato;
gaskiya cikin labarunSa, da kuma adalci cikin umurni da hani.
Allah
ya cika wannan addinin; wannan yasa
mutane basu da buqatar qarin wani abu (ko bidi'a) a cikin addini har
abada; Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya qirqiro abinda babu
shi a cikin addininmu wannan, to an mayar masa",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Saboda haka; Babu wani alheri face Annabi ( صلى الله عليه وسلم) ya nuna shi wa al'ummarSa,
Haka babu wani sharri face ya tsawatar da al'ummarSa akansa.
Allah
ya yarje wa muminai wannan addinin;
don haka ba zai karvi wani addinin ba daga mutane in ba musulunci
ba; Allah ta'alah yana cewa:
"Duk wanda ya nemi wani addinin wanda
ba musulunci ba, to baza a karva masa ba,
Kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara",
[Ali-imraan: 85].
[Musulunci
shine] Addinin da ginshiqansa da qa'idodinsa da halayyansa suka cika, kuma suka kai qololuwa wajen kamala, Allah ta'alah yana cewa:
"Kace: Ya ku mutane lallai ni Manzon
Allah ne zuwa gare ku, gabaxaya, Wanda
yake da mulkin sammai da qassai, Babu
abun bautawa face shi, Yana rayawa yana
kashewa" [A'araaf: 158].
[Musulunci]
Addini na har abada, a mutanen
duniya, tabbatacce, Wanda kuma shine miqaqqen tsarin
rayuwa, Kuma shine kammalalle; duk kuma abinda aka samu na canje-canjen
da zamani ya kawo, ko yawan
banbance-banbancen lokuta, (to addinin yana dacewa da su). Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Kuma duk wanda ya rayu daga
cikinku to lallai zai ga savani dayawa;
Ina horonku kan riqo da sunnata da kuma sunnar halifofi shiryayyu masu
shiryarwa, Sai kuyi riqo da su, kuma ku damqe su da fiqoqi, Kuma ina muku kashedi kan qirqirarrun
al'amura". Ibnu-Hibbana
ya ruwaito shi a cikin sahihinsa, da Alhakim a cikin almustadrak.
Shari'ar
musulunci itace mafi qarkon abinda za a jagoranci al'ummomi da ita, Kuma itace tsarin da yafi maslaha; wanda za a yi hukunci da shi a tsakanin
mutane, Tsari ne da ya dace da kowani
zamani, da kuma kowani wuri, da kuma
kowace al'umma, da kuma kowani
hali, Kai, yadda lamarin yake
shine: Duniya baza ta tava gyaruwa da
wani tsarin wanda ba na musulunci ba.
Kuma duk lokacin da zamani ya qara nisa, al'ummomi suka qara samun bunqasa sai wassu dalilai saabi su sake bayyana
kan ingancin musulunci, da kuma
xaukakar sha'aninsa.
Kuma
yana daga cikin kamalar musulunci kasancewarsa abu ne guda; wanda baya vantaruwa, kuma abu ne dunqulalle baya rarraba, Allah ta'alah yana cewa:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku shiga
musulunci gabaxayansa" [Baqarah: 208].
Baka
samun tufka da warwara cikin hukunce-hukuncen addinin musulunci, kuma baka samun banbance-banbance cikin
shari'arsa, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma da (Alqur'ani) ya kasance daga
wajen wani wanda ba Allah ba, to da sun samu savani dayawa a cikinsa"
[Nisa'i: 82].
Kuma
lallai waxanda basa gudanar da rayuwarsu a qarqashin tsarin Allah, Sai suke hukuntar da wassu tsare-tsare
akansu; waxanda mutane suka samar da su,
Irin waxannan suna cin karo da tsarin rayuwa, kuma lallai rayukansu baza su samu
nitsuwa ba, kuma fixirarsu baza ta
daidaita ba, sannan baza su ji daxin
rayuwarsu ba, Kuma lallai aikata
hakan zai bayyanar da munanan alamomi masu halakarwa masu rushe rayuwa.
Amma
shi kuma musulunci; To tsari ne na
rayuwa cikakke, Wanda yake tsara
alaqar mutum da xan'uwansa mutum,
da kuma alaqar mutum da duniyar; da take kewaye da shi, kuma musulunci yana biyan dukkan buqatun 'yan
adam, a lamuran duniya dana
lahira, a halin zaman lafiya dana
yaqi, a lamarin siyasa dana tattalin
arziqi, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma mun sassaukar da wannan
littafin akanka don ya zama bayani ne ga kowani abu, kuma shiriya da rahama da
albishir ga musulmai" [Nahli: 89].
Kuma
musulunci shari'a ne na Ubangiji,
wanda yake gyara abubuwa na zahiri,
kuma yake bada tarbiyya ga na baxini,
kuma babu wani aibi a cikinsa,
kuma baya bin ganin dacewar halittu, ko son ransu ko maslahar da suke
gani, ko duk abinda yake ingizo
xaixaikunsu, Yayin da su kuma
dokokin da halittu suke tsarawa ko su sanya
koda sun iya magance abubuwa na zahiri,
to lallai baza su iya magance matsalolin zukata ba, Su dokokin da halittu suke sanyawa suna
xauke ne da baji ko taake na qarya, Wanda
kuma baza su
iya kawo wa 'yan adam zaman lafiya ko aminci ba.
Kuma
lallai za a iya samun nasarori na wucin gadi a xan wani lokaci ga wanda ya riqi sabbuban cin nasara, Saidai kuma nasara ce mai tawaya wacce baza
ta xore ba, kuma sharri da matsaloli
zasu dabaibaye nasarar, kuma amincin
da za a iya samu ba zai zama cikakke ba; cikin waxanan tsare-tsaren, tare da
samun qarancin albarka cikin arziqi da 'ya'ya, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma duk wanda ya kawar da kai ga
ambatona to lallai yana da rayuwa ta qunci,
kuma zamu tayar da shi a qiyama makaho" [Xaha: 124].
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL
LAHU, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
Addininmu yana kiyaye hankulan mutane; a don haka,
ya haramta shan giya, da dukkan abubuwa masu bugarwa, ko duk abinda zai lalata hankali.
Kuma addinin ya kiyaye dukiyoyi; shi yasa ya kwaxaitar kan riqe amana, ya kuma
haramta yin sata.
Kuma addininmu yana kiyaye rayuka; wannan yasa ya haramta kashe rayuka ba
tare da haqqi ba.
Kuma addininmu yana kiyaye lafiyar jiki; shi
yasa ya Allah yake cewa:
"Kuma, ku ci, ku sha, kada kuyi
varna; lallai shi baya son mavarnata" [A'araaf: 31].
Kuma musulunci ya haramta alfasha; abinda ya bayyana
daga cikinta, da abinda ya vuya.
Kuma
addininmu yana bada kariya wa alaqoqi, da tsarin dangantaka; ta hanyar tsarin aure da iyalai, kuma yana kiyaye xaukakar xan'adam da
karamarsa; Baya barin sha'awa ta
tafi kara zube; ba tsari; Wannan yasa
musulunci ya bada kariya wa hanyar samun 'ya'ya, ya kuma katange mace, sannan ya sanya tubalin da za a gina
samar da iyalai, wannan kuma domin su
tsira, tsira mai kyau, kuma su bada
'ya'ya masu albarka, Allah ta'alah
yana cewa:
"Yana daga cikin ayoyinSa; Ya halitta
muku mata daga kayukanku domin ku nitsu zuwa gare su, kuma ya sanya qauna da
tausayi a tsakaninku, Lallai cikin
haka akwai abin lura ga mutane masu tunani" [Ruum: 21].
Addinin
adalci tare da baqo, da kuma aboki,
da na nesa harma da
maqiyi, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma idan zaku yi zance kuyi adalci,
koda ya kasance ma'abucin kusanci" [An'aam: 152]. Ya kuma ce:
"Kuma kada qiyayyar wassu mutane ta
hana ku yin adalci; kuyi adalci shi yafi kusa da bin dokokin Allah" [Ma'idah:
2].
Addinin
qarfi da kwazo da aiki da azama,
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Mumini mai qarfi shi yafi
alkhairi kuma shi yafi soyuwa a wurin Allah akan mumini mai rauni, tare da cewa Kowanne yana da alkhairi, Kayi kwaxayin aikata abinda zai amfanar da kai, sai ka nemi taimakon Allah, kada ka gajiya".
Muslim ne ya ruwaito shi.
Musulunci
yana kira zuwa ga xinke zukata, da daidaita
sahun musulmai, kuma shine addinin
soyayya da haxin kai, da tarayya da tausayi ko rahama, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku a
yayin da kuka kasance maqiya sai ya daidaita tsakanin zukatanku; sai kuka wayi gari da ni'imarsa kuna
'yan'uwa" [Ali-imraana: 103].
Kuma lallai idi ya kan zo don ya qara jaddada
waxannan ma'anonin, ya kuma qara
qarfafa dangantaka, da alaqoqi.
Kuma
lallai al'ummar musulmai suna fatan wannan ni'imar (wato: ni'imar haxin kai) ta
lulluve qasar YEMEN mai albarka,
YAMEN garin imani da hikima (kamar yadda Annabi ya shaidar), Har waxanda suka yi fito-na-fito da
shugabanni su koma cikin hankulansu da shiriyarsu, Wato su miqa wuya ga kiran dake cewa: Suyi
amfani da hankulansu, don tsayar da
zubar da jini, da bada kariya ga
rayukan da ake ta kashe su, da
kuma kiyaye lalata dukiyar da aka yi wahala
taquru wajen samar da ita, Allah
ta'alah yana cewa:
"Kuma kada kuyi jayayya sai ku yi
rauni, sai qarfinku ya tafi" [Anfaal: 46].
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana xaukar fito-na-fito da jama'ar musulmai da kuma rabuwa da
su a matsayin ridda irin ta jahiliyyah,
A inda yace:
"Kuma duk wanda ya fice daga
biyayya, ya kuma rabu da jama'a, sai ya mutu; to yayi mutuwa irin ta jahiliyyah",
Muslim ya ruwaito shi.
Addininmu
yana karantar da mu cewa; Lallai IMANI SHINE sababin samun aminci (a cikin
al'ummai), kuma shine sababin kiyaye
tabbatuwansa; "Kuma su bautawa
Ubangijin wannan xakin; Wanda ya ciyar
da su daga yunwa, Ya kuma amintar da
su daga tsoro" [quraish: 3-4].
Irin wannan amincin da muke rayuwa a cikinsa a
qasarmu, muke kuma hutawa a qarqashin inuwarsa, Ni'ima ce da baza a iya misalta girmanta
ba, kuma baiwa ce daga Allah wacce ba
za a iya gama siffantata ba, AMINCI
SUMFUXAXXE CIKAKKE GAMAMME, Wanda ya
bada dama wa kowa-da-kowa (jam'i mai albarka) wajen sauke hajjinsu cikin
sauqi, nitsuwa ta kewaye su, kwanciyar hankali ya lulluve su, Su kuma abubuwan da ka iya aukuwa; su
wuce to lallai basa qaranta qimar
qoqarin da aka yi, da dukiyoyin da aka kashe,
da nasarorin da aka cimma;
waxanda idonuwan mutum adali baza su kuskure musu ba.
Kuma
lallai muna jin baqin ciki da vacin rai da takaici, kan rashin aminci a qasar
SIRIA mai izza; Haqiqa yanayin wannan
qasa ya canza, rayuwa ta gurvace, an qaurace wa gidaje; mutane dayawa sun qaura sun bar qasarsu, An kakkashe rayukan da basu-ji- ko suka-gani-ba, Wassu yaran an mayar da su marayu, wassu matan kuma zawarawa!
Muna
roqon Allah da sunayensa da sifofinsa, ya tabbatar da gaskiya, ya kuma ruguza
varna, kuma ya yaye baqin cikin waxanda
aka mayar da su masu rauni (da gangan),
ya kuma kawar da baqin cikin masu neman mafaka, ya mayar da su gidajensu suna
kuvutattu, ya mayar da makircin
maqiyansu zuwa ga qirazansu.
MASALLACIN
QUDUS shima yanayinsa yana ta kokawa
saboda rashin aminci,
kasancewar an kekketa alfarmarsa,
kuma masu varna sun yi aikinsu na varna a mafi yawancinsa. Kuma wajibi ne akan musulmai; su haxa hannu, suyi taimakakkeniya, tare da
yin kururuwan cewa a taimaka masa, a kiyaye haqqinsa, da bada kariya wa
iyakokinsa, da kuma tsawatar ko yin horo
ga masu yin ta'addanci a gare shi. Kamar yadda muke miqa gaisuwa da jinjina,
tare da qarfafa mazauna garin Qudus da 'yan'uwansu kan gwarzantakarsu, da
matsaya da suka tsaya na nuna izza, da karama, da sadaukarwa; don taimakon masallacin AQSAH, da kuma
sauke wannan nauyi na wajibi.
Musulunci
ya sanya ILIMI da BUNQASA HANKALI don su zama ginshiqin gina al'umma da bunqasa
ta, da kawo cigaba a gare ta, Bai
kuma sanya ilimi ya zama hanyar halakarwa ko rushe-rushe, ko ya dasa kwayoyin
ta'addanci da yaxa zalunci, ko kuma bautar da al'ummomi da xan'adam ba.
Kuma
addininmu yayi fice wajen siffantuwa da tausasawa da kuma sauqi, kuma lallai
tsanantawa da zafafawa baya cikin addini, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Lallai Allah ya wajabta
kyautatawa ga kowani abu", Muslim ya ruwaito shi.
Su
kuma wawayen mutane masu qaiqasasshen zukata da wuce iyakar shari'ar Allah, waxanda suke qone-qone a masallatai, suke rurrushe gine-gine, waxannan ba suna yin hakan ba ne a madadin
musulunci ko kuma da yawunsa, Kai basu ma SAN haqiqanin musuluncin ba, Kuma maqiyan musulunci sune suka shusshuka su
a garurrukan musulmai, domin su munanawa sunan musulunci da sunan musuluncin, kuma sune suke jujjuya su ta qarqashin qasa, bayan sun mori qarancin hankulansu, da
quntataccen tunaninsu; ta hanyar sanya
musu burin samun shugabanci da khalifanci,
da kuma tsayar da daular musulunci,
"Yana musu alkawari kuma yana sanya musu guri, Amma ba komai Shexan yake alkawarta musu ba
face ruxi" [Nisa'i: 120].
Kuma
addininmu yana kiran mutane zuwa aiki da mafi kyan halayya, da aiyuka, Allah ta'alah yana cewa:
"Ka tunkuxe (cutarwar da aka yi a
gare ka) da abinda yafi kyau, Sai wanda a tsakaninka da tsakaninsa akwai adawa
ya zama kamar majivincin makusanci" [Fussilat: 34].
Addininmu
yana umurni da rufa asirin mutane, da
biyan buqatar musulmai, da yaye musu baqin cikinsu, da ziyartar marasa lafiya, da rakiyar gawa, kuma yana umurni da cewa bawa ya so wa
xan'uwansa irin abinda yake so wa kansa.
Kuma
addininmu yana yin umurni kan biyayya wa iyaye, da kyautata mu'amala ga miji da
'ya'ya, da sadar da zumunci, da karrama makwabci, da tausasawa dabbobi, Allah ta'alah yana cewa:
"Lallai Allah yana yin umurni da yin
adalci, da kyautatawa, da yin baiwa ga ma'abota kusanci, kuma yana hana alfasha da munkari, da
zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku
wa'aztu" [Nahli: 89].
Allah
ya yi albarka a gare ni, da ku, cikin alqur'ani mai girma. Ina faxar wannan maganar, kuma ina neman
gafarar Allah wa Ni da Ku; sai ku
nemi gafararSa; lallai shi mai gafara
ne, mai rahama.
…
HUXUBA TA BIYU
Yabo
ya tabbata ga Allah wanda ya halicce mu cikin mafi kyan tsari, Ya kuma sanya asalinmu (babanmu Annabi
Adamu) ya zama daga turvaya, Ina
yin godiya a gare shi kuma ina yaba masa;
shine wanda ya karrama muminai da aikinsu, ya kuma sanya aiyukan kafirai ya zama
watsettse abun sheqewa, Kuma ina
shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; zuwa gare shi makoma take.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne
manzonSa; wanda yayi hani kan gibar
mutum da annamimanci, da zage-zage.
Allah
yayi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa; salatin da zai dawwama har zuwa ranar
hisabi.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL
LAHU, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
Duniya –Ya ku bayin Allah- a cikinta
ake shuka abinda za a girbe a lahira,
Sai ku yi guzuri daga duniyarku ga lahirarku, da kyawawan aiyuka, Saboda a yau duniya aiki ake yi babu
hisabi, Gobe kuma qiyama hisabi ne
babu aiki.
Lallai
yininku wannan yini ne mai girma;
wato: Yinin hajji babba,
Kuma a cikin wannan yinin ne; mahajjata da waxanda ba mahajjatan ba; Suke
yin tarayya wajen zubar da jinin hadaya
da layyah a cikinsa, suna masu
kusantar Allah mabuwayi da xaukaka da aikata hakan, Allah ta'alah yana cewa:
"Naman dabbobinku baya samun Allah,
haka jinanensu, Saidai bin dokokin
Allah wanda yake tare da ku shine yake samunSa" [Hajj:
37].
Kuma
baya halatta ayi layyah da dabba ramammiya, da maras lafiya, da gurguwa, da mai
ido xaya, da makauniya, da wacce ta samu karaya, ko kuma dabbar da qahonta ya
tafi, ko mafi yawan kunnenta. Kuma
raqumin da yake xauke da cutar quraje masu yaxuwa shima baya isarwa a layyah.
Kuma
daga cikin raquma basa isarwa sai wanda ya cika shekaru biyar (05) ko fiye, Daga cikin shanu kuma sai wanda ya cika
shekaru biyu (02), Daga cikin awaki
kuma sai wanda ya cika shekara guda (01),
Daga cikin tumaki kuma sai wanda ya cika watanni shida (6).
Kuma
raqumi xaya ya kan isar wa mutane bakwai (7),
Haka itama saniya ta kan isar wa mutane bakwai (7), Ita kuma akuya ga
mutum xaya da mutanen gidansa.
Kuma
ba zai sayar da wani abu na daga jikin dabbar layyarsa ba, kuma ba zai baiwa mahauci ladan wahalarsa
daga dabbar layyarsa ba.
Kuma
lokacin yankan layya yana farawa ne daga bayan sallar idi, har zuwa faxuwar
ranar yinin goma sha uku (13), daga cikin kwanakin da ake shanya nama don busar
da shi.
Shi
kuma kabbara mai qayyadadden lokacin da ake yinsa bayan sallolin farillai: Yana
farawa ne daga sallar asubar ranar arfah,
har zuwa sallar la'asar na yinin qarshe daga cikin kwanakin da ake shanya
nama don busarwa.
Ya
ku musulmai !
Kuyi
bushasharku da idi, ku sanya tufafi
sabi, kuma ku jaddada ma'anonin
idi, Kuna masu biyayya wa
iyayenku, da ziyartar makusantanku da
'yan'uwanku, kuma ku bibiyi labarin
makwabtanku, kuma ku taimaki miskinai
da faqirai da marayu, Allah ya
karva mana aiyukanmu na kwarai, da aiyukanku.
Kuma kowace shekara Allah ya sa kuna cikin alkhairi.
Kuma
kuyi salati wa fiyayyen halittun Allah; Muhammadu xan Abdullahi; saboda Allah da Mala'ikunSa suna yin
salati a gare shi;
"Ya ku waxanda suka yi imani ku yi salati
a gare shi; da sallama mai yawa".
Ya Allah kayi salati wa Muhammadu da matanSa
da zurriyarSa, kamar yadda kayi salati wa iyalan annabi Ibrahima. …
Huxubar
ta qare,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment