AMSA WA UBANGIJI KIRANSA
NA AYI HAJJI;
DA KALMOMIN TAUHIDI (KADAITA ALLAH)
(التلبية
بالتوحيد)
Na
Shehin malami
Prof. Abdurrazak bn
Abdulmuhsin Albadr
Fassarar
Abubakar Hamza
Godiya ta tabbata ga Allah wanda
shi ne abun yabo mai girma, Ina shaidawa babu abun bauta da gaskiya sai Allah
shi kadai bashi da abokin tarayya shaidawar mutumin da ke tabbatar ma Allah
tauhidinsa, wanda ke tsarkake shi ga barin abokin tarayya ko kishiya. Kuma ina
shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa; ma'abocin falala da
basa kirguwa da karamomi, tare da dukkan halaye abun yabo; Allah ya yi dadin
salati da sallama a gare shi, da kuma iyalansa da sahabbansa gabadaya. Bayan haka;
Lallai farkon
farin abin da musulmi zai bude aikin hajjinsa da shi na aiyuka shi ne:
TALBIYYAH; fadin: LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA … yana mai shelantawa –ta hanyar
kalmomin talbiyyah masu girma- tauhidinsa ga Allahu (swt) shi kadai, tare da
watsi da aikata shirka, ko sanya ma Allah kishiya. Sa'annan sai ya dauki
hanyarsa ta tafiya dakin Allah 'yantacce, yana mai maimata wadannan kalmomi
"LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIKA, INNAL
HAMDA WAN NI'IMATA LAKA WAL MULKA LA SHARIKA LAKA" zai yi ta maimaita su yana
mai sanin ma'anonin das u ke kunshe da su na tsantsanta aiki (ikhlasi) ga
Allah, tare da kadaita shi (tauhidi), da kuma abin da su ka kunsa na wajabcin
kadaita Allah shi kadai da bauta, tare da kuma nisantar rikon abokan tarayya
tare da Allah. Zai rika fadin wadannan kalmomin yana mai halarto da su a cikin
zuciyarsa, yana kuma tabbatarwa cewa lallai ubangijinsa (swt) shi ne ya kadaita
da bada ni'imomi da kyautayi, babu wanda ke tarayya da shi cikin haka, kamar
yadda shi kadai ya takaita da cancantar kadaitawar bayinsa, babu mai
kishiyantarsa.
No comments:
Post a Comment