HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 27 /ZUL QI'IDAH/1436H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ABDULMUHSIN ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da kuma munanan aiyukanmu.
Duk wanda Allah ya shiryar
to babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa; da sallama mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, saboda Ubangijinmu (Allah) baya karvar
aiki sai wanda aka yi shi da taqawah, Kuma
baya yin rahama sai ga ma'abotanta
Ya ku musulmai …
Allah yana zavan wanda ya
so daga cikin halittunSa
"Kuma Ubangijinka yana
halittar abinda ya nufa, Sai kuma yayi zavi"
[Qasas: 68].
Sai Allah ya zavi manzanni
daga cikin Mala'iku, haka kuma daga cikin mutane. Daga cikin maganganu kuma sai ya zavi
ambatonSa, Daga dukkan qasa kuma =
masallatanSa, Sai kuma daga cikin
watanni, ya zavi watan ramadhana, da kuma watanni huxu
masu alfarma.
Kuma lallai mutanen jahiliyyah sun kasance su kan yi
qarin kwanaki a cikin watanni, ko su jinkirta wassu, suna masu bin son
zuciyarsu; Sai azuminsu ya
kasance ba a lokacinsa ba, Hajjinsu
shima ba a zamaninsa ba.
Har Allah yayi rahama ga
wannan al'ummar; da tayar da Manzon da ya tsayar da wannan addinin; Sai ya aikata hajjinsa (صلى الله عليه وسلم)
hajjin bankwana, bayan zamani ya juya ya daidaita kamar yadda ya kasance; Sai hajjinsa ya auku a cikin watan
zulhijjah, ya kuma bayyana haka a
cikin huxubarSa:
"Lallai zamani ya juya ya
koma kamar yadda yake, a ranar da Allah ya halicci sammai da qassai", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Da wannan, Sai qidaya ta cika, lissafi kuma ya inganta, Lamari shi kuma ya koma kan abinda ya
kasance akansa a farko, kamar
yadda littafin Allah ya bayyanar.
Kuma fifikon da aka sanya a tsakanin darare da yini yana
hukunta a tsayu wajen ribatar alherin da yake cikinsu. Kuma lallai Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) ya
kwaxaitar kan ribatar ni'imomi guda biyar, gabanin gushewarsu; a inda yake
cewa:
"Ka ribaci biyar gabanin
abubuwa biyar; Samartakarka gabanin tsufanka,
Da lafiyarka gabanin cutarka, Da
wadacinka gabanin talaucinka, Da damar
lokaci; gabanin shagaltuwarka, Da
rayuwarka gabanin mutuwarka", Alhakim ya
ruwaito shi.
Kuma
lallai kwanaki goman zulhijjah sun nufo wannan al'ummar, kuma suna daga cikin
kwanakin Allah masu alfarma, kuma
sune cikamakon watannin nan sanannu; waxanda Allah yake faxi akansu:
"Aikin hajji watanni ne
sanannu"
[Baqarah: 197]. Waxanda kuma sune: Watan shawwal, da
zulqi'idah da kwanaki goman zulhijjah (na farko). Kuma saboda girman matsayinsu ne mafi
yawan aiyukan hajji suke aukuwa a cikinsu.
Kuma Allah yayi rantsuwa da dararensu; a inda yake cewa:
"Ina rantsuwa da alfijir * Da
kuma darere guda goma"
[Alfajr: 1-2].
Kuma yininsu yafi girman
falala akan yinin kwanaki goman qarshe na watan ramadhana. Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام):
"Mafificin kwanakin duniya
sune: Yinin kwanaki goma", Ibnu-hibbana ya ruwaito shi.
Kuma darajar kwanaki goman
zulhijjah tayi fifiko saboda haxuwar manya-manyan ibadodi a cikinsu, kamar sallah, da azumi, da zakkah, da kuma
aikin hajji. Wanda hakan kuma baya kasantuwa a wassu kwanakin waxanda ba su ba.
Kuma kowani aiki managarci a cikin waxannan kwanakin
(guda goma) yafi soyuwa a wurin Allah, fiye da irin wannan aikin; idan ya auku
a cikin wassu kwanakin waxanda ba su ba.
Annabi (عليه الصلاة والسلام)
yace:
"Babu waxansu kwanaki da
aiki managarci yafi soyuwa a cikinsu a wurin Allah fiye da waxannan kwanakin
guda goma. Sai
suka ce: Koda jihadi ne fiysabilillah?
Sai yace:
Koda jihadi ne fiysabillahi,
Saidai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa, sai kuma bai koma da
komai ba", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Malam Ibnu-rajab (رحمه الله)
yace:
"Lallai
wannan hadisin yayi nuni cewa: Yin aiki a cikin kwanakin nan guda goma shi yafi
soyuwa a wurin Allah, akan yin aikin a sauran kwanakin duniya, ba tare da an
togance wassu kwanaki ko an ware su daga ciki ba".
Kuma lallai magabatan kwarai (رحمهم الله) sun
kasance suna yin bakin qoqarinsu wajen aikata kyawawan aiyuka a cikin kwanakin
nan guda goma; Sa'idu xan Jubair (رحمه الله) idan kwanaki goman
zulhijjah suka shiga ya kan qara zagewa wajen aiki tuquru, har kamar ba zai iya
ba.
Kuma yana daga falalar Allah da kyautarsa Sai dangogin aiyukan biyayya wa Allah a
cikin kwanakin nan suka yawaita;
Kuma yana daga cikin
abubuwan da aka shar'anta a cikin kwanakin nan:
YAWAITA AMBATON ALLAH, kamar yadda Allah yake cewa:
"Kuma su ambaci sunan Allah a
cikin wassu yini sanannu" [Hajji: 28].
Abdullahi xan Abbas yace:
"Sune: Yini guda
goma".
Kuma ambaton Allah (سبحانه) a cikin waxannan yinin guda
goma yana daga cikin mafificin dangogin nau'ukan biyayya wa Allah; Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya
ce:
"Babu wassu yini da yafi
girma a wajen Allah, ya kuma fi soyuwa a wurinsa ayi aiki a cikinsu fiye da
waxannan guda goman; Sai ku yawaita
faxin: La ilaha illallahu a cikinsu, da yin kabbara, da hamdala", Ahmad ya ruwaito shi.
Imam Annawawiy (رحمه الله) yace:
"Mustahabbi ne
yawaita zikirori a cikin waxannan kwanakin guda goma, qari akan waxanda ake yi a wassu
kwanakin. A ranar arafah kuma
mustahabbi ne a yawaita yin zikirori fiye da sauran kwanakin guda goma".
Mafifici kuma daga dangogin zikiri shine KARATU KO
TILAWAR LITTAFIN ALLAH; Wanda
kuma shine shiriya da haske mabayyani.
Yin kabbarori kuma ko-yaushe a kowani lokaci yana daga
cikin ibadun da suke banbance waxannan yini guda goma; Abdullahi xan Umar da Abu-hurairah (رضي الله عنهما) suna
fita zuwa ga kasuwa, a kwanaki guda goma; suna yin kabbara; mutane kuma suna
yin kabbara da kabbararsu. Bukhariy ne ya rawaito shi.
Kuma an shar'anta yin kabbarori qayyadaddu a bayan sallolin
farilla, daga sallar asubar ranar arafah, ga mahajjata, da waxanda ba su ba. Sheikhul Islam (Ibnu-taimiyyah رحمه الله):
"Maganar da tafi
inganci dangane da kabbarar da magabatan kwarai da faqihai da sahabbai da
manyan maluma ita ce: Mutum ya fara yin kabbara daga sallar asubar ranar
arafah, har zuwa qarshen kwanakin busar
da nama (ATTASHRIQ; 13 ga wata),
Bayan kowace sallah".
Yana kuma daga cikin abubuwa mustahabbai YIN AZUMIN KWANAKI
GUDA TARAN FARKO, DAGA CIKIN GOMAN ZULHIJJAH Imam Annawawiy (رحمه الله) yace:
"Azumtar hakan
mustahabbi ne; abun so mai tsanani".
BADA SADAKA shima aiki ne mai kyau managarci; Kuma da bada sadakar ake yaye baqin
ciki, sannan wahala ta gushe. Kuma mafi alherin sadakar da aka bayar
itace wacce ta kasance a lokacin buqatarta,
da kuma wacce aka bada ita a cikin wani zamani maxaukaki.
Ita kuma TUBA matsayinta a cikin addini maxaukaki ne, Kuma ita sababin tsira ne da
rabauta. Allah ya wajabtata akan al'umma gabaxaya daga
dukkan zunubai; Sai yace; akan mutanen da suka riya cewa Allah yana da
mata, wai kuma yana da xa:
"Shin baza su tuba zuwa ga
Allah ba ne, suna masu neman gafararsa" [Ma'idah: 74].
Kuma ya faxa dangane da
muminai:
"Kuma ku tuba zuwa ga Allah
gabaxaya ya ku muminai, da fatan zaku samu rabo" [Nuur: 31].
Kuma
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana roqon Allah a cikin yini xaya sau xari cewa ya
karvi tubansa; Yana cewa:
"Ya ku mutane ku tuba zuwa
ga Allah; saboda ni nakan tuba a
cikin yini xaya sau xari", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma lallai mune muka fi
buqatar tuba, Kuma lallai mafi
alherin yini ga bawa shine yinin da ya tuba a cikinsa, Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace
wa Sahabinsa Ka'ab xan Malik (رضي
الله عنه):
"Ina yin albishir a gare
ka da mafi alherin yinin da ya tava shigewa a gare ka tun ranar da mahaifiyarka
ta haife ka",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma me yafi kyau fiye da
mai tuba ya yi tubansa a mafi soyuwan kwanaki a wajen Allah!
Duk kuma wanda ya yi
gaskiya cikin tubansa to zai samu xaukakan darajoji, Allah kuma zai canza masa munanan
aiyukansa da masu kyau.
Kuma a cikin kwanaki goma na farkon zulhijjah ake yin HAJJIN
XAKIN ALLAH MAI ALFARMA, Wanda kuma xaya ne daga cikin rukunnan musulunci, masu
girma waxanda musuluncin ya ginu akansu,
Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma lallai Allah ya wajabta
wa mutane yin hajjin wannan xaki; ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi" [Ali-imraana: 97].
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Ya ku mutane an
farlanta hajji akanku; Ku yi aikin hajji", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma aikin hajji yana daga
cikin aiyuka masu fifikon falala a wurin Allah; An tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم)
cewa:
"Wani aiki yafi
falala? Sai yace: Yin imani da Allah da manzonSa, Sai aka ce: Sa'annan sai me? Sai
yace: Sai jihadi fiysabilillahi, Sai aka ce: Sa'annan sai me? Yace: Sai
hajjin da aka yi biyayya a cikinsa. Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma lallai lafiyayyen
hajji (mabruur) bashi da wani sakamako sai aljannah, kuma ana kankare zunubai da shi, da
kura-kurai, Annabi (عليه الصلاة والسلام):
"Wanda yayi hajjin wannan
xakin; bai yi kwarkwaso ba, bai yi
fasiqanci ba, zai fita daga zunubansa
kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi. Kuma lallai Allah yana yin alfahari da waxanda
suka halarci tsayuwan arafah, ga halittunsa na sammai (mala'iku).
Kuma lallai hajji yana da hikimomi masu girma, da
manufofi masu kyau manya-manya, a addinance, da a duniyance, a wannan rayuwar
da kuma a lahira; Kuma na farko daga
cikin waxannan hikimomin shine: TABBATAR DA TAUHIDI, saboda Kalmar da take bakin mahajjata
ko-yaushe itace:
"لَبَّيْكَ
اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ ، لَبَّيْكَ لا شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ ، إِنَّ الْحَمْدَ
وَالنَّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ لا شَرِيكَ لَكَ".
Ma'ana: "Mun amsa maka ya Allah,
muna amsa maka, mun amsa baka da abokin tarayya, mun amsa, Lallai yabo, da
ni'ima naka ne, da mulki; baka da
abokin tarayya".
Yana kuma daga cikin hikimomin aikin hajji: TSANTSANTA NIYYAR AIKI (wato: IKHLASI)
GA ALLAH SHI KAXAI, da kuma YIN
KOYI DA MANZON ALLAH, Allah
ta'alah yana cewa:
"Kuma ku cika hajji da umrah
ga Allah",
[Baqarah: 196].
Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام)
yace:
"Ku koyi aikin hajjinku
daga gare ni",
Muslim ya ruwaito shi.
Yana kuma daga cikin hikimomin aikin hajji: "Domin su halarci amfaninsu" [Hajji:
28], a nan duniya, da
abinda suke samu na alkhairori, da
kuma a lahira ta hanyar shiga aljannoni.
"Sai su ambaci sunan Allah a
cikin kwanaki sanannu", [Hajj: 28] … .
Kuma lallai hajji yana
tunatar da mutane cewa za a bar wannan duniyar; kuma lokacin aiwatar da hajji shine
qarshen kwanakin shekara, Kuma
Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya aiwatar da aikin hajjinsa ne a qarshe-qarshen
rayuwarsa; wanda kuma a cikinsa yayi
bankwana da sahabbansa, Allah ta'alah
kuma a cikin wannan hajjin ya cika wa al'umma addininta; ya kuma saukar masa da
faxinSa a ranar arafah: "A yau na cika addininku a gare ku, na kuma cika ni'imata akanku", [Ma'idah: 3].
Wanda kuma ya gaza yin hajj
saboda wani uzuri to zai yi tarayya da mahajjata a cikin lada; idan har yayi gaskiya cikin niyyarsa, kasancewar ta kan yiwu masu tafiya da
zuciyarsu, su rigayi waxanda suka je kawai
da jikikkunansu.
Kuma a cikin waxannan
kwanaki goman ake samun YININ ARAFAH;
Wanda azumtarsa yake kankare zunuban shekarar da ta wuce, da wacce zata
zo, Kuma "Babu wani yini wanda
Allah yafi 'yanta bayi a cikinsa daga wuta fiye da yinin arafah", Muslim ya ruwaito
shi. Kuma mafi alherin addu'a shine
addu'ar da aka yi ta a ranar arafah.
Kuma a cikin waxannan
kwanaki goman ake samun YININ LAYYA; Wanda shine yini mafi girma daga
cikin kwanakin da ake aiyukan hajji a cikinsu, kuma shi yafi xaukaka a
cikinsu, kuma shi yafi tattara
aiyukan hajji dayawa a cikinsa, don
haka shine: RANAR AIKIN HAJJI DA YAFI GIRMA, Allah yana cewa:
"Kuma, Yin shela daga Allah da
ManzonSa zuwa ga mutane, a ranar hajji wanda yafi girma…" [Taubah: 3].
Kuma wannan yinin (na
layya) shine mafi girman kwanaki a wurin Allah; Annabi (عليه الصلاة والسلام)
yace:
"Lallai mafi girman yini a
wurin Allah shine ranar layya, sa'annan sai ranar goma sha xaya; wanda
mahajjata suke tabbata a Minah",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma yinin layya xaya ne
daga cikin idi guda biyu na musulmai;
ranar farin cikinsu; saboda sun sauke wani rukuni daga cikin rukunnan
musulunci (wato hajji).
Saidai mutane a yanayi na farin-cikin idi zasu iya gafala,
su bar tsayar da ambaton Allah (zikiri),
A irin wannan yanayin yin zikirin yafi falala; Allah yana cewa:
"Ku ambaci Allah a cikin
kwanaki qididdigaggu"
[Baqarah: 203]. Waxanda kuma sune
kwanakin idi (waxanda ake busar da nama a cikinsu; AT-TASHRIQ).
Annabi (عليه الصلاة والسلام)
yace:
"Kwanakin ATTASHRIQ –ma'ana: kwanakin idi-
kwanaki ne na ci, da sha, da kuma ambaton Allah", Muslim ya ruwaito shi.
Ibnu-hajar (رحمه الله) yace:
"Lallai falala ta
tabbata ga kwanakin nan guda goma,
don haka sai ta tabbata ga kwanakin idi (Attashriq)".
A kwanakin layya da na shanya nama (attashriq) ake yin
ibada ta dukiya da jiki (wato: layya), wacce kuma take cikin ibadodin da Allah
yake sonsu dayawa; (kuma saboda girmanta) Allah ya haxa ambatonta tare da
sallah a cikin faxinsa:
"Ka yi sallah wa Ubangijinka,
kuma kayi sukan (raqumi) a gare shi", [Alkausar: 2].
Kuma lallai Allah ya
kwaxaitar kan tsantsanta niyya cikin yanke-yanke ko suka, da cewa: Bawa ya nufi
Allah shi kaxai cikin layya, ba alfahari ko riya, ko don aji labarin mutum yayi,
ko ayi layyar don tsagwaron al'ada ba,
Allah yana cewa:
"Naman dabbobin layya ko
hadayanku baya samun Allah, haka
jinanensu, Saidai taqawarku ce take
samunsa"
[Hajj: 37].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم ) yayi layya da raguna guda biyu, masu baqi-baqi, masu qaho, ya
yanka su da hannunsa"
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma ragon da ake masa
laqabi da AMLAH: Shine baqin da a saman gashinsa akwai fari.
"Aqranaini" kuma
a cikin hadisin: ma'abota qaho.
Babu laifi Mutum ya ci bashi don ya sayi abin layya, sai
kuma ya jira samun mayewar abinda ya kashe daga Allah.
Kuma
bai dace mutum yayi ta qorafin tsadar kuxin dabbar layya ba; saboda ladanta a
wurin Allah yana da yawa.
Kuma duk wanda yayi nufin yayi layyah haramun ne akansa
ya aske gashinsa ko ya yanke wani abu na farcensa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace
"Duk wanda yake da abin
yankan da zai yanka; to idan jinjirin watan zulhijjah ya kama to kada ya aske
gashinsa ko wani abu na farcensa, har zuwa lokacin da zai yi layyan", Muslim ya ruwaito shi.
Bayan haka,
Ya ku musulmai….
Lallai wanda ya rabauta shine wanda ya ribaci muhimman watannin
lokutan ibada da kwanakinsu, ya kuma
kusanci masoyinsa Allah da aiyukan xa'a da biyayya, da fatan wata rahama daga cikin rahamomin
Allah ta lulluve shi; sai ya samu
rabo ya kuma tsira tare da aminta daga
babbakuwa ko faxawa cikin wuta, sa'annan ya samu rabauta da shiga
aljannar da faxinta shine faxin sammai bakwai da qassai. Wanda kuma a can ne zai yi daddaxar
rayuwa ta har abada; Kuma don
neman samun haka mutanen kirki (masu rigaye zuwa ga aikata alkhairi) suka zage
damtse.
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Ku yi gaggawa zuwa ga wata
gafara daga Ubangijinku, da samun aljannar da faxinta shine faxin sammai da
qassai; wacce aka tanade ta ga
waxanda suka yi imani da Allah da Manzanninsa, Wancan kuma falalar Allah ce da yake bayar
da ita ga wanda ya nufa, kuma lallai
Allah shine ma'abocin falala mai girma" [Alhadid:
].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA.
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; godiya kuma tasa ce
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Aikata dangogin savo da
laifuka sababi ne na samun nisa daga Allah,
kamar yadda kuma yin biyayya a gare shi yake sabbaba samun
kusantarSa; saboda yin zunubai yana
da shu'umci da matsala ga xaixaikun jama'a da kuma al'ummai, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku nisanci zunubin
bayyane da kuma wanda ya vuya; lallai
waxanda suke aikata savo to da sannu za a sakanta musu da abinda suka kasance
suke aikatawa"
[An'aam: 120].
Kuma lallai hatsarin savo yana qara girma idan aka aikata su a
lokutan rahama da alkhairori, Allah
ta'alah yana cewa:
"Lallai qidayar watanni a
wurin Allah watanni sha biyu ne, a cikin littafin Allah, tun ranar da ya
halicci sammai da qassai, Daga cikinsu
akwai guda huxu masu alfarma, Wannan
shine addini miqaqqe kada ku zalunci kayukanku a cikinsu" [Taubah; 36].
Qatadah (رحمه الله) yace:
"Yin
zalunci a cikin watanni masu alfarma yafi girman zunubi da kuskure fiye da yin
zalunci a cikin wassu watannin; waxanda ba su ba, tare da cewa yin zalunci a kowani hali yana
da qirma, Saidai kuma Allah yana
girmama abinda ya so daga al'amarinSa".
Kuma kamar yadda yin zunubai a cikin watannin nan laifi
ne mai girma, to haka aikata
kyawawan aiyuka na biyayya a cikinsu shi kuma akwai alheri babba.
Sai ku ribata da lokutan samun rahamomi, da xaukaka
darajojin bayi, kuma ku nisanci
duk abinda zai shamakance samun gafarar Allah, a irin waxannan lokutan, ko a wassunsu.
Sannan ku sani; Lallai
Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa … … …
No comments:
Post a Comment