HUXUBAR
MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 20 /ZUL QI'IDAH/1436H
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo da godiya sun tabbata
ga Allah wanda ya haskaka basirar muminai da shari'arSa, Ya kuma bayyana halal daga haram ga
mukallafai (masu hankali, baligai),
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya
ke, bashi da abokin tarayya, kuma bashi da mai taimako.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonSa; da ya bayyanar
da hukunce-hukunce, da qa'idodin musulunci ga masu bi; sannan yace:
"Wanda Allah yake
nufinsa da alkhairi ya kan fahimtar da shi addini".
Salatin Allah da sallamarSa
su qara tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa; khalifofin addini,
waxanda suka cika da yakini.
Bayan haka;
Ya ku musulmai …
Ku kiyaye dokokin
Allah, saboda taqawar Allah itace
mafificin aiki, Yi masa xa'a kuma
shine mafi xaukakar nasaba, ko danganta;
"Ya ku waxanda suka
yi imani ku kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna
musulmai", [Ali-imraan: 102].
Ya ku musulmai …
Aikin hajji xaya ne daga
cikin rukunnai guda biyar waxanda aka gina musulunci akansu, Kuma yana wajaba akan balagagge mai
hankali (mukallafi) da yake da iko, sau xaya a rayuwa.
Kuma duk wanda hajji ya
wajaba akansa, kuma yake da ikon aikata shi
= To dole ne a kansa ya gaggauta
aiwatar da shi; Ya zo daga Abdullahu
xan Abbas (رضي الله عنهما)
yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Duk wanda ya nufi
aikin hajji to ya gaggauta shi;
saboda rashin lafiya ka iya bijirowa, ko hanya ta gurvace, ko wata buqatar ta bijiro". Ahmad da Ibnu-Majah suka ruwaito shi.
Wanda kuma ya mutu gabanin ya sauke farillar hajji, sawa'un yayi sakaci cikin hakan, ko bai yi
sakaci ba, kuma daidai ne yayi
wasicin cewa a yi hajjin a gare shi ko bai yi wasici ba = To
sai a fitar da kimanin abinda zai yi masa hajji da umrah daga cikin abinda ya
bari na dukiya; Saboda hadisin
Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) Lallai
wata mata daga qabilar juhaina ta zo wajen Manzon Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai tace: Lallai uwata tayi bakancen zata yi aikin hajji, sai
bata samu ta yi hajjin ba, hart a mutu; Shin zan mata hajjin? Sai yace: Na'am kiyi mata hajji; Shin idan akwai bashi akan mamarki; zaki
biya mata? Ku biya Allah
bashinSa; saboda Allah shi yafi
cancantar a biya shi". Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Wanda kuma ya samu ikon yin hajji da kansa to bai halatta
ya wakilta wani mutum ya yi hajjin a gare shi ba.
Wanda kuma sharuxan wajabcin hajji suka tabbata
akansa, Sai kuma ya gaza yinsa
da jikinsa; saboda wani uzurin da
aka xebe tsammanin gushewarsa; kamar gurguntaka
da cutar da ta jima, ko dai wani rashin lafiyar da ba a tsammanin warkewarsa,
ko kuma ya kasance ba zai iya tabbata akan abun hawa ba; sai da matsananciyar wahalar
da ba za a iya jure mata ba, ko kuma
ya kasance tsofo ne da qarfinsa ya qare
= To wajibi ne akansa ya samar
da wanda zai yi hajji da umrah a gare shi; Ya zo daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما)
lallai wata mata tace: Ya
ma'aikin Allah! Lallai farillar
Allah akan bayinsa na hajji ta riski babana yana dattijo mai yawan
shekaru; Ba zai iya tabbata akan
abin hawa ba; Shin zan iya yin hajji
a gare shi? Sai yace: E; na'am". Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma duk lokacin da mutum ya wakilta wani yayi masa aikin
hajji, sa'annan sai ya samu
lafiya = To ba wajibi ba ne akansa ya yi wani hajjin
na daban; saboda ya aikata abinda aka
umurce shi da shi; sai ya fita daga
zargi.
Shi kuma wanda yake fatan zai samu ikon yin hajji da kansa, ko kuma ana tsammanin gushewar cutarsa, to lallai baya halatta a gare shi ya
wakilta wanda zai yi hajji a gare shi;
Idan kuma ya aikata haka to bai
isar masa ba.
Shi kuma faqirin da bashi da kuxin aikin hajji to hajjin
baya wajaba akansa, kuma ba zai nemi
wani ya wakilce shi ba, haka ba za a
yi masa hajjin ba. Saidai babu laifi;
Wani ya bashi kuxin hajjin.
Wanda kuma aka biya masa kuxin hajji, sai kuma ya zama baya tsoron idan ya karva
za a yi masa gori, ko a cutar da shi, to
babu laifi ya karva; yayi hajjinsa da shi.
Kuma wanda bai yi hajjin musulunci na wajibi ba to bashi
da damar yayi hajji ga waninsa; Idan
kuma ya aikata hakan to hajjin ya zama nasa; wannan kuma saboda hadisin Abdullahi xan
Abbas (رضي الله عنهما) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yaji
wani mutum yana cewa: Ya Allah na
amsa maka zan yi hajji wa Shubruma, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Wanene Shubruma?
Sai yace: Dangina ne makusanci. Sai yace: Shin ka tava yin hajji? Sai yace: A'a! Sai yace:
Ka mayar da wannan ta zama taka,
Sa'annan daga baya kayi hajji wa Shubrumah". Ahmad da Abu-dawud da Ibnu-Majah suka ruwaito
shi.
Halal ne mutum ya karvi wani lada, idan ya wakilci wani
cikin hajji.
Saidai abinda yafi ga mai
wakiltar waninsa shine ya karbi kuxin da zai biya buqatunsa na hajji, amma kada ya karvi lada.
Yin haramar hajji ga mutane guda biyu baya qulluwa; Don haka duk wanda yayi haramar hajji xaya ga
mutane guda biyu, ko kuma ga kansa da waninsa
= to haramarsa ta auku ne wa
kansa kaxai. Idan kuma ya yi
haramar yin umrah ga wani, sannan yayi aiyukanta har ya kammala. Sa'annan yayi haramar aikin hajji ga
wani mutum na daban to hakan ya
inganta; saboda a wannan yanayin
ibadodi guda biyu ya aikata.
Kuma mustahabbi ne
mutum yayi hajji ga iyayensa guda biyu;
in dukkansu sun mutu, ko kuma
sun gajiya; Amma sai ya fara yin
hajjin wa mahaifiyarsa; kasancewar itace
abar gabatarwa cikin biyayyarsa.
Saidai kuma zai gabatar da hajjin da zai yi wa mahaifinsa na wajibi,
akan wanda zai yi wa mahaifiyarsa na nafila.
Kuma namiji bashi da haqqin ya hana matarsa yin hajjin
musulunci (na wajibi); matuqar ta samu
muharrami; Kuma muharrami ga mace
yana daga ikonta na hajji.
Saidai kuma Imamu Maliki (رحمه الله)
yace: Mace zata iya fita hajji cikin
taron mata ko tawagarsu.
Duk kuma matar da mijinta ya mutu to baza ta fita zuwa ga
hajji ba a cikin kwanakin iddar mutuwa;
saboda idda lokacinta yana qarewa, shi kuma hajji lokacinsa baya
qarewa. Kuma idan labarin rasuwarsa
ya iske ta; alhalin bata yi nisa daga
gida ba to sai ta dawo; don tayi
iddarta a gidanta. Idan kuma tayi
nisa to sai ta cigaba da tafiyarta.
Kuma duk wanda akansa akwai bashin da wajibi ne ya biya
shi; saboda shigar lokacin biyan to
sai ya gabatar da shi akan hajji;
Saidai idan mai bashin yayi masa izinin tafiya hajji. Wanda kuma bashinsa ya zama biyansa
kucul-kucul ne, kuma ya zama ya mallaki kason
kowani lokaci; wanda zai biya idan lokacinsa yayi to sai ya tafi hajjinsa, ba
tare da an sharxanta neman izinin wanda yake bin bashin ba.
Ya ku musulmai …
Barin yin hajjin nafila, ko umrah ta nafila a lokacin tsananin
cunkoson jama'a da nufin yalwatwa
masu rauni da mata da marasa lafiya da tsofaffi masu yawan shekaru; waxanda
suka zo don sauke hajjin farilla
= barin haka shine yafi kusa da
xa'a da alheri da samun lada da sakayya a wurin Allah; Saboda yin hajjin nafila, da umrah ta
nafila sunnah ne, yayin da qoqarin
kiyaye cutar da musulmi kuma wajibi ne; Ya zo daga Abdurrahman xan Auf (رضي الله عنه) yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace
da ni:
"Yaya ka aikata
lokacin tava hajarul aswad? Sai
nace: Na kan tava, Na kan bari. Sai yace: Ka aikata daidai". Ibnu-hibbana ne ya ruwaito shi.
Ma'anan wannan shine: Ya
tava a lokacin da babu cunkoso, ya
kuma bar tava dutsen a yanayi na cunkoso,
Sai Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya bayyana cewa ya dace da
shari'a.
Bada sadaka shima yafi falala akan yin hajjin nafila, da
umrah ta nafila; idan har akwai
danginsa da suke da buqata, ko kuma ana cikin wani zamani na yunwa, ko kuma aka samu wassu daga cikin musulmai
suna da matsananciyar buqatar sadakarsa, ko kuma buqatar ciyarwarsa; Wata rana Abdullahi bn Almubarak
ya fita zuwa ga hajji sai yaga wata budurwa tana xaukar maceccen tsuntsun da
aka jefar da shi a bola, Sai ya tambaye
ta, Sai tace: Ni da 'yar'uwata a
wannan wurin bamu da abinci, sai abinda aka jefar a wannan bolar, Sai Abdullahi ibnul Mubarak ya yi umurnin a
mayar da raquman da suka yi lodin kayansa, ya kuma bata duka abinda ya ware don
buqatar hajjinsa, sa'annan yace: Yin
haka shi yafi falala fiye da muyi hajji a wannan shekarar. Sa'annan ya koma
garinsa.
Ya ku musulmai…
Duk wanda ba a bashi takardar izinin yin hajji ba, daga hukumomi to wajibi ne ya jinkirta hajjinsa, a magana
ingantacciya, har zuwa lokacin da zai samu izinin fita; saboda maslahar shari'a ta hukunta iyakance
adadin waxanda za su yi hajji da umrah;
domin tunkuxe matsalolin cunkoso da turarreniya, da kuma hana yin aikin kara-zube.
Ya ku waxanda kuke bin hanyar qarya, da algus, da wayo wa
hukumomi ko mutane, da rashawa,
domin su guje wa dokokin da suka kawo tsari a aikin hajji !!!
Ya
waxanda kuke bin hanyoyi masu sarqaqiya, da hatsari; domin ku gudu daga wuraren 'yan sandan kan
hanya masu kula da aminci; waxanda ba a sanya su a wuraren aikinsu ba sai don
maslahar hajji da samun aminci a cikinsa, da kuma don samun lafiyar mahajjata !!!
Ya ku waxanda kuke sava wa shari'a, kuke kuma qetare
dokokin Allah (تعالى), kuke aikata haram, sannan ku wuce miqaatai, da wuraren 'yan
sanda ba tare da sanya ihrami ba !!!
Wani irin hajji kuke nufi ?!
Kuma wani lada kuke fatan
samu?!
Alhalin kuma kuna yin
qarya, da wayo, da sava wa dokoki !!!
Ya ku waxanda kuke tsallakar
da waxanda suke sava wa dokoki, da kuma xauka ko tsallakar da waxanda suke
nufin su yi hajji ba tare da sun haxa takardun izini ba
Ku sani! Ladan kwadagonku dukiya ce mai dauxa, kuma
kuxi ne na haram, wanda aka samu ta hanyar savo!
Gabaxayanku!
Ku hanu daga waxannan
aiyukan abun zargi, Sannan ku yi dubi
zuwa ga al'amuran da idanu na hankalta, da hikima, da kuma qoqarin sauke nauyi.
Kuma ku nisanci kafa hujja
da hujjoji rusassu; waxanda suka fi gidan sauro sakwarkwacewa idan za a tattauna
akansu, irin hujjojin da suke sanya
wanda ya yi riqo da su a wajen tattaunawa dalilansa su qare yayi shiru ya kasa
wata magana !!!
Ya Allah ka nuna mana
shiriyarmu,
Ka kuma kare mu daga
sharrin kayukanmu
Ya Mai karamci, Ya Mai girma, Ya Mai rahama!
HUXUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata
ga Allah; wanda ya ilmantar da bayinSa,
ya kuma sanar da su, sannan ya basu fiqihu a cikin addininsu ya fahimtar.
Kuma ina shaidawa babu abun
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Allah yayi daxin salati da
sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da waxanda suka tafi akan turbar
gaskiya, har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Ya ku musulmai…
Ku kiyaye dokokin Allah,
kuma ku kula da su, kuyi masa biyayya,
kada ku sava masa, "Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin
Allah, ku kasance tare da masu gaskiya", [Taubah: 119].
Ya ku musulmai…
Ku lazimci sunnonin da suke
da madogara, waxanda malamai
tabbatattu amintattu suka ruwaito su,
Sannan ku kiyaye bidi'oi da qirqirarrun al'amura,
Ka yi mamakin yawan waxanda
suka tattaru akan bidi'oi,
Ko kuma suka karkace suka
bar sunnoni, suka ware
Kuma ina suke da sunnah
MUTANEN DA suka karkata zuwa ga kaburbura suna fatan samun alheri daga waxanda
suke kwance a cikinsu ?!
Suka kuma fiskantar da
zukatansu zuwa gare su, harma da fiskoki,
Suka riqi kabari abin
dogaro, da wurin yaye bala'i,
Da mafaka, da qofar samu, da
Katanga daga sharri, da wurin fata !
Har suke sujjada akan
qofofinsu,
Suke yanka abun yankansu a
bakin qofofin,
Suke kuma yin xawafi da
kewaya kaburburan,
Wai !!! suna fatan samun
yaye matsaloli daga gare su, da albarka, da kwararan alheri.
Bidi'oi masu girma da ake
kiransu bautar kaburbura.
Wanda kuma tushensu shine
bautar gumaka,
Jiga-jigan maluma masana,
da shehunan musulunci duk sun yi ijma'i da ittifaqi, kan cewa hakan yana cikin bidi'oi masu muni,
waxanda suke cin karo ko warware musulunci da shari'ah. Kamar su Abu-hanifata da Malik da Shafi'i da
Ahmad.
Shi kuma Ubangijinmu Mai
karamci yana kwararo kyauta, yana
kuma jin addu'ar bawa, ba tare da
masu ceto, ko wassu da za a riqa a matsayin tsani ba; daga cikin annabawa ne ko daga cikin
waliyyai.
Ku ziyarci masallacin
Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم)…
Kuna masu nisantar shafa
katangun masallacin ko qofofinsa, da minbarinSa, da mihrabin sallarSa; Domin ita albarka ba a nemanta cikin
shashshafa daskararrun abubuwa.
Sannan ku nisanci neman
albarka da qasar da take kan kaburbura, ko neman waraka da ita, ko kuma jejjefa abinci, da kwayoyi hatsi
da kuxaxe akan kaburbura, ko kuma
roqon waxanda suke kwance a cikinsu;
saboda aikata hakan yana cikin aiyukan jahilai na jahiliyyah.
Aikinku Allah ya gama shi
da karvuwa, da kuma bada lada,
Addu'arku kuma ya gama ta
da yarda da kuma amsawa.
Ya kuma jawo muku arziqi,
ya kuma bubbuxe muku qofofinsa.
انتهت
Kuma kuyi salati ga Ahmad
mai shiryarwa,
Mai kuma ceton mutane
gabaxaya,
Saboda
Duk wanda yayi masa salati
guda xaya
To lallai Allah zai yi masa
guda goma,
Zuwa ga halittu aka turo
shi, don ya zama rahama, mai tausasawa
Kuyi masa salati, da
sallama masu tarin yawa;
Ya Allah kayi salati da
sallama ga bawanka kuma annabinka Muhammad,
Kuma ya Allah ka yarda da
dukkan iyalansa da sahabbai,
Ka haxa da mu, Ya Mai
karamci, Ya Mai yawan baiwa,
Ya Allah ka xaukaka
musulunci da musulmai,
Kuma ka qasqantar da shirka
da mushirkai,
Kuma ka halaka azzalumai, da
masu kasha bayinka, mavarnata, masu qetare iyaka, Ya Ubangijin
halittu!
Ya Allah ka tunkuxe yaquka da
fitintinu da savani da rashin kwanciyar hankali, da jayayya
daga qasashen musulmai gabaxaya,
Ya
Mai karamci!
Ya Allah ka dawwamar wa qasarmu;
ta Saudiyya
Amincinta, da wadacinta, da
xaukakarta, da kwanciyar hankalinta,
Kuma ka datar da shugabanninta
zuwa ga abinda akwai alkhairi a cikinsa da gyaruwan musulmai,
Ya Allah ka datar da shugabanmu;
Mai hidimar masallatai biyu; harami, maxaukaka, da na'ibansa
guda biyu
Zuwa ga abinda xaukakar muslunci
yake cikinsa da gyaruwar musulmai, Ya Ubangijin halittu!
Ya Allah ka warkar da marasa
lafiya daga cikinmu,
Ka yaye ma waxanda aka jarrabe
su daga cikinmu,
Kayi rahama ga mamata daga cikinmu,
Kuma ka fitar da waxanda suke
cikin kurkuku,
Ka taimake akan wanda yayi adawa
da mu,
Ya
Ubangijin halittu!
Ya Allah ka kiyaye mahajjata,
Da masu ziyara, da masu umrah,
Ya Allah ka karvi aiyukansu
Kuma ka tsarkake musu, su
Ka kuma xaga darajarsu,
Ka xaukaka su,
Qarshen addu'armu ita ce:
ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA
!
No comments:
Post a Comment