LITTAFIN HAJJI
Ya qunshi babuka huxu, kamar
haka:
Babin farko: Matashiya kan hajji.
Babi na biyu: Rukunnan hajji, da wajibansa.
Babi na
uku: Abubuwan da yin
harama ke haramtawa, da "fidiya", da "hadayah".
Babi na
huxu: Siffar hajji da umrah.
BABI NA FARKO: MATASHIYA KAN HAJJI:
A nan akwai mas'aloli masu yawa kamar
haka:
Mas'alar
farko: Bayani akan menene hajji?
Hajji a harshen
larabci na nufin: Ziyartar wuri tare da nufansa.
A
shari'ar Musulunci kuma yana nufin: Bautawa Allah ta hanyar yin wassu aiyuka a
wani wuri kevantacce (Makkah, Minah, Arafah da
Muzdalifah), a wani lokaci kevantacce (watannin aikin
hajji), kamar yadda ya zo a cikin sunnar Manzon Allah (r).
Mas'ala
ta biyu: Hukuncin hajji, da falalarsa:
1. Hukuncin aikin
hajji: Wannan aiki xaya ne daga cikin
rukunnan Musulunci da farillolinsa masu girma, wannan kuma saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ
ﮱ ﯓ ﯔ ﯕﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﭼ آل عمران: ٩٧
Ma'ana:
(Kuma Allah ya wajabta wa mutane ziyartar wannan xaki;
ga wanda ya samu hanya i zuwa gare shi, Duk kuma wanda ya butulce –ya kafirce-
to lallai Allah mawadaci ne ga barin talikai) [Aali-imraan::
97]. Da kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﭼ البقرة:
١٩٦
Ma'ana:
(Kuma ku cika hajji da umrah don Allah) [Baqarah:
196].
Da kuma
saboda hadisin Abdullahi xan Umar -t-,
daga Annabi (r):
Ma'ana:
(An gina Musulunci akan ginshiqai guda biyar;) Sai ya ambaci
aikin hajji daga cikinsu.
Kuma haqiqa
al'ummar musulmai sun yi "ijma'i" kan wajabcin hajji akan wanda ya ke
da iko; sau xaya a rayuwa.
2. Falalan aikin
hajji: Hadisai da dama sun zo kan falalar aikin hajji, daga cikinsu
akwai:
Hadisin
Abu-hurairah -t-
daga Annabi (r):
"الْعُمْرَةُ إِلَى الْعُمْرَةِ كَفَّارَةٌ لِمَا
بَيْنَهُمَا. وَالْحَجُّ الْمَبْرُورُ لَيْسَ لَهُ جَزَاءٌ إِلاَّ الْجَنَّة"([2]).
Ma'ana:
(Umrah zuwa wata umarah na kankare zunuban da ke tsakaninsu, hajji kuma kuvutacce
ba shi da sakayya sai aljanna). Annabi (r)
ya sake cewa:
Ma'ana:
(Duk wanda ya yi aikin hajji don Allah, bai yi batsa ko jima'i ba, da
fasikanci: zai komo kamar ranar da uwarsa ta haife shi). Da wassun waxannan
hadisai.
Mas'ala
ta uku: Shin sau nawa aikin hajji ke wajaba a rayuwa?
A
cikin xaukacin rayuwa aikin hajji baya
wajaba sai sau xaya kacal, duk kuma abinda ya qaru
akan haka to "tadawwu'in nafila" ne, wannan kuma saboda hadisin
Abu-hurairah -t-, lallai Annabi (r) ya ce:
"أَيُّهَا النَّاسُ! قَدْ فَرَضَ اللهُ عَلَيْكُمُ
الْحَجَّ، فَحُجُّوا، فَقَالَ رَجُلٌ: أَكُلَّ عَامٍ يَا رَسُولَ اللهِ؟ فَقَالَ:
لَوْ قُلْتُ: نَعَمْ لَوَجَبَتْ، وَلَمَا اسْتَطَعْتُم"([4]).
Ma'ana: (Ya ku mutane! Lallai
Allah ya farlanta muku yin aikin hajji; sai ku yi hajji. Sai wani mutum ya ce:
Shin a kowace shekara ne ya ma'aikin Allah? Sai yace: Da nace: E! da hakan ya
wajaba, da kuma kun gagara iyawa). Da kuma saboda kasancewar Annabi (r) bayan
hijirarsa i zuwa garin Madina bai yi hajji ba sai sau xaya
rak. Kuma hakika malamai sun yi "ijma'i" cewa: aikin hajji baya wajaba
ga wanda ke da iko sai sau xaya tak.
Kuma
wajibi ne akan bawa ya yi gaggawan aiwatar da aikinsa na hajji; matuqar
sharuxansa
sun cika, kuma mutum ya kan yi laifi saboda jinkirta shi; idan babu wani uzuri;
wannan kuma saboda faxinsa (r):
Ma'ana: (Ku yi gaggawan zuwa
hajji; saboda xayanku bai san abinda ka iya bijiro masa ba). Kuma an ruwaito hakan
daga Annabi, da kuma sahabbai (hadisi marfu'i da mauqufi),
ta hanyoyi da sashinsu ke qarfafa sashi cewa:
"مَنْ اسْتَطَاعَ الْحَجّ فَلَمْ يَحُجَّ؛ فَلْيَمُتْ
إنْ شَاءَ يَهُودِيًّا وَإِنْ شَاءَ نَصْرَانِيًّا"([6]).
Ma'ana: (Wanda ya samu damar
ya yi hajji, sai kuma bai yi hajjin ba, to ya mutu in ya ga dama a bayahude, ko
in ya so ya mutu akan addinin nasara).
Mas'ala
ta huxu: Sharuxan hajji:
An
sharxanta
sharuxa guda biyar kafin aikin hajji ya wajaba ga bawa:
1- Musulunci: Aikin
hajji baya wajaba akan kafiri, kuma idan ya yi baya inganta a gare shi; wannan
kuma saboda "Musulunci" sharaxi
ne da dole a same shi gabanin ingantuwar ibada.
2- Hankali:
Aikin hajji baya zama wajibi akan mahaukaci, kuma baya inganta a gare shi idan
ya aikata shi a halin haukarsa; wannan kuma saboda samuwar "hankali" sharaxi
ne na mutum ya zama sharia ta hau kansa, "mukallafi"; shi kuma
mahaukaci baya daga cikin waxanda shari'a ke neman
su aikata wata ibada, kuma an xage masa alqalami
i zuwa ya farfaxo; kamar yadda ya zo a cikin hadisin Aliyu -t- cewa lallai
Manzon Allah (r)
yace:
"رُفِعَ الْقَلَمُ
عَنْ ثَلاثَةٍ؛ عَنِ النَّائِمِ حَتَّى يَسْتَيْقِظَ،
وعَنِ الصَّبيّ حَتَّى يَبْلُغَ، وَعَنِ الْمَجْنُونِ حَتَّى
يفيق"([7]).
Ma'ana:
(An xage
alqalami akan mutane guda uku; maibarci har sai ya tashi, da yaro qarami
har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya wartsake).
3- Balaga: Hajji
baya wajaba akan yaro; saboda (yaro) baya cikin waxanda
shari'a ta wajabta musu ibadodi, kuma an xauke
masa alqalami har sai ya balaga, saboda
hadisin da ya gabata:
"رُفِعَ الْقَلَمُ
عَنْ ثَلاثَةٍ ...".
Saidai da qaramin
yaron da bai balaga ba zai aikata hajji to hajjinsa ya inganta. Idan kuma qarami
ne sosai da bai kai matsayi na "mumayyiz" ba to majibincin lamarinsa
ne zai yi masa niyya. Kuma wannan hajjin baya isar ko ya sauke masa
"hajjin Musulunci", Wannan kuma haka ya ke ba tare da wani "savani"
ba a tsakanin ma'abota ilimi; dalili kuwa saboda abinda Abdullahi xan
Abbas ya ruwaito cewa:
"أنّ امْرَأَةً رَفَعَتْ صَبِيًّا، فَقَالَتْ:
يَا رَسُولَ اللهِ! أَلِهَذَا حَجٌّ؟ قَالَ: نَعَمْ، وَلَكِ أَجْر"([8]).
Ma'ana:
(Lallai wata mata ta xaga wani yaro, sai tace: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai hajji
akan wannan? Sai yace: E, ke kuma kina da lada). Da kuma saboda faxinsa
(r):
"أَيُّمَا صَبِيٍّ حَجَّ ثُمَّ أَدْرَكَ فَعَلَيْهِ
حَجَّة أُخْرَى، وَأَيُّمَا عَبْدٌ حَجَّ ثُمَّ عتِقَ فَعَلَيْهِ حَجَّة أُخْرَى"([9]).
Ma'ana:
(Duk wani yaron da ya yi hajji, sannan ya balaga, to wajibi ne akansa ya yi
wani hajjin na daban, Duk kuma bawan da ya yi hajji sa'annan aka 'yanta shi, to
wajibi ne akansa ya yi wani hajjin na daban).
4- 'Yanci: Hajji
baya zama wajibi akan bawa; saboda bawan da aka mallake shi baya mallakan
komai, Sai dai da zai aikata hajji da aikin hajjinsa ya inganta; matuqar
ya yi shi da izinin shugabansa. Kuma ma'abota ilimi sun yi "ijma'i"
kan cewa: Idan bawa ya yi aikin hajji a halin kasancewarsa bawa, sa'annan sai
aka 'yanta shi: to wajibi ne akansa ya yi hajjin Musulunci; idan ya samu damar
hakan, saboda hajjin da ya yi a halin kasancewarsa bawa bai isar masa ba;
wannan kuma saboda faxinsa (r)
a cikin hadisin da ambatonsa ya gabata:
"وَأَيُّمَا عَبْدٌ حَجَّ ثُمَّ عتِقَ فَعَلَيْهِ
حَجَّة أُخْرَى".
Ma'ana:
(Kuma duk bawan da ya yi hajji sa'annan aka 'yanta shi, to wajibi ne akansa ya
yi wani hajjin na daban).
5- Samun iko: Wannan
kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ
ﮱ ﯓ ﯔ ﯕﯖ ﭼ آل عمران: ٩٧
Ma'ana:
(Kuma Allah ya wajabta wa mutane ziyartar wannan xaki;
ga wanda ya samu hanya da damar zuwa gare shi) [Aali-imraan: 97].
Bawan da
bashi da iko ta fiskar dukiya; kamar wanda bai mallaki guzurin da zai ishe shi
sannan kuma ya ishi iyalansa ba, ko kuma bashi da abin hawan da zai hau; don ya
kai shi garin Makka, kana ya dawo da shi garinsa ba. Ko kuma bashi da iko ta
fiskar karfin jiki; kamar ya zama tsofo mai yawan shekaru, ko maras lafiyan, da
ba zai iya hawa abun hawa ba, ko ba zai iya jure wa wahalar tafiya ba. Ko kuma
hanyar zuwa hajji bata da aminci; kamar ya zamto akwai 'yan fashi, ko annoba,
ko wani abu makamancin wannan waxanda mahajjaci ke
tsorace ma kansa ko dukiyarsa: to a irin waxannan
halayen aikin hajji ba wajibi ba ne akansa, har sai ya samu iko; saboda Allah
ta'alah yana cewa:
ﭽ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﭼ البقرة:
٢٨٦
Ma'ana:
(Allah baya kallafa ma rai sai abinda ta ke da iko) [Baqarah:
286]. Shi "istixa'ah; samun ikon hajji" na
daga cikin "alwus'u" da Allah ya ambata. Yana kuma daga cikin
"samun ikon hajji".
Dangane da
hajjin mace kuma: Samun "muharramin" da zai tafi tare da ita a
tafiyarta ta hajji; saboda baya halatta ga musulma ta yi tafiya; (zuwa ga hajji
ko waninsa) ba tare da muharrami ba; wannan kuma saboda faxinsa
(r):
"لا يَحِلُّ لامْرَأَةٍ تُؤْمِنُ بِاللهِ وَالْيَوْمِ
الآخِرِ، أَنْ تُسَافِرَ سَفَرًا يَكُونُ ثَلاثَةَ أَيَّامٍ فَصَاعِدًا، إِلا وَمَعَهَا
أَبُوهَا، أَوِ
Ma'ana:
(Baya halatta ga wata mace; da ta yi imani da Allah da kuma ranar qarshe;
ta yi tafiya ta kwanaki uku, ko fiye, face a tare da ita akwai ubanta, ko xanta,
ko mijinta, ko dan'uwanta, ko kuma wani muharraminta). Da kuma saboda faxinsa
(r)
ga mutumin "nan" da yace:
"إِنَّ امْرَأَتِي خَرَجَت حَاجَةً، وإِنِّي اكْتُتِبْتُ فِي غَزْوَةِ كَذَا:
(انْطَلِقْ فَحُجَّ مَعَها)"([11]).
Ma'ana:
(Lallai matata ta fita i zuwa ga hajji, lallai ni kuma an rubuta ni don zuwa
yaki wuri kaza: Ka tafi kayi hajji tare da ita).
Idan mace
ta yi hajji ba tare da muharrami ba, to hajjinta ya inganta, amma ta yi laifi.
Mas'ala
ta biyar: Hukuncin umrah, da kuma dalili akan haka:
Umrah tana wajaba a cikin
rayuwa sau xaya tak ga wanda ya ke da iko, wannan kuma saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﭼ البقرة:
١٩٦
Ma'ana: (Kuma ku cika hajji
da umrah don Allah) [Baqarah: 196]. Da kuma saboda faxin
Annabi (r)
ga A'ishah -
رضي الله عنها- a lokacin da ta
tambaye shi, shin akwai "jihadi" akan mata? Sai yace:
Ma'ana: (E, akwai jihadi
akansu wanda babu zubar da jini a cikinsa; aikin hajji da umrah), da kuma
saboda faxinsa (r)
ga Abu-razin -t- yayin da ya tambaye shi cewa
babansa ba zai iya yin hajji da umrah ba, da kuma tafiya, Sai yace:
Ma'ana: (Ka yi hajji ga
babanka, ka yi masa umrah).
Kuma rukunnan umrah su guda uku ne: Harama (Niyya), xawafi
da sa'ayi tsakanin "safah da marwah".
Mas'ala
ta shida: Miqaatin hajji da Umrah:
Miqaati –a harshen larabci- Shine: Iyaka.
A -shari'a-
kuma shine: Wurin yin ibada ko lokacinta. Kuma "miqaati"
ya kasu kashi biyu, miqaati na zamani, da miqaati
na wuri.
Amma dangane da miqaatin
zamani na hajji da umrah; Lallai dai ita umrah ya halatta a aiwatar da ita a
duk lokutan shekara.
Amma shi kuma
"hajji" ya na da watanni sanannu; wanda wani aiki daga cikin aiyukan
hajji ba ya inganta, sai an yi su a cikinsu; wannan kuma saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭼ البقرة:
١٩٧
Ma'ana: (Hajji watanni ne
sanannu) [Baqarah: 197].
Waxannan watannin sune:
watan "Shawwal, da Zul-qi'idah, da kuma
Zulhijjah".
Amma dangane da miqaatin
wuri da ake xaukar hajji da umrah daga gare su: To sune wassu iyakokin da baya
halatta ga mai aikin haji da umrah ya wuce su face yana da harama. Kuma haqiqa
Annabi (r)
ya bayyana "su" a cikin hadisin Abdullahi xan
Abbas -t-, yace:
"وَقَّتَ رَسُولُ اللَّه r
لأَهْلِ المَدِينَةِ ذَا الحُلَيْفَةِ، وَلأَهْلِ الشَّأْمِ الجُحْفَةَ،
وَلأَهْلِ نَجْدٍ قَرْنَ المَنَازِلِ، وَلأَهْلِ اليَمَنِ يَلَمْلَمَ، هُنَّ لَهُنَّ،
وَلِمَنْ أَتَى عَلَيْهِنَّ مِنْ غَيْرِ أهلهِنَّ؛ مِمَّنْ أَرَادَ الحَجَّ وَالعُمْرَةَ،
وَمَنْ كَانَ دُونَ ذَلِكَ، فَمِنْ حَيْثُ أَنْشَأَ، حَتَّى أَهْلُ مَكَّةَ مِنْ مَكَّةَ"([14]).
Ma'ana: (Manzon Allah –r- ya sanya
"ZULHULAIFAH" ga mutanen Madina a matsayin wurin xaura
niyya, mutanen Shaam kuma ya sanya musu "AL-JUHFAH", ga mutanen Najdu
kuma "KARNUL MANAZIL", mutanen Yamen kuma ya sanya musu
"YALAMLAM". Waxannan miqaatan
na waxannan
mutanen ne, da kuma duk wanda ya zo musu ba daga cikin ahlin wajen ba; na waxanda
suka nufi yin hajji da umrah. Wanda kuma yake gaba (ta ciki) da waxannan
miqatai to zai yi niyya ne daga wurin da ya fari hakan, Su kuma
mutanen Makka daga garin Makka).
Duk kuma wanda ya qetare waxannan "miqaatin"
ba tare da ya yi harama ba, to wajibi ne ya dawo zuwa gare su matuqar
ya samu dama, idan kuma bai samu damar komowa i zuwa gare su ba to wajibi ne a
kansa ya yi "fidyah", wacce itace: akuya da zai yanka a garin Makka,
sannan ya raba namanta ga miskinan "harami".
Su kuma mutanen da gidaddajinsu suke gaba (ta ciki-cikin)
waxannan
"miqaatan" to su zasu yi haramarsu ne daga wurarensu; wannan kuma
saboda faxinsa (r)
a cikin hadisin da ya gabata:
"وَمَنْ كَانَ دُونَ ذَلِكَ، فَمِنْ حَيْثُ أَنْشَأَ".
Ma'ana: (Mutumin da kuma ke
gaba -ta cikin- waxannan miqaatan to zai yi
niyyarsa ne daga wurin da ya fari hakan).
BABI NA BIYU: RUKUNNAN HAJJI, DA WAJIBANSA:
A
nan akwai mas'aloli guda biyu:
Mas'alar
farko: Rukunnan aikin hajji:
Rukunnan
hajji guda huxu ne, kamar haka:
1-
Niyyar hajji
wanda ake kiranta (Al'ihraam); Wannan kuma shine nufan hajji; Saboda aikin
hajji ibada ne tsantsa; don haka baya inganta idan ba a yi niyya ba, da
"ijma'in" maluma, dalili kuma akan haka shine faxin
Annabi (r):
Ma'ana:
(Lallai dukkan aiyuka su kan inganta ne tare da niyya).
Ita kuma
niyyah mahallinta shine: zuciya, Sai dai mafificin lamari dangane da hajji
shine a furta ta, tare da ayyana nau'in aikin hajjin da bawa ya niyyata (kamar
ifradi, qirani, da tamattu'i); saboda aiwatar da hakan ya tabbata daga
aikinsa (r).
2-
Tsayuwar arafah: Wannan
shima rukuni ne da "ijma'in" maluma, dalilinsa kuma shine faxinsa
(r):
Ma'ana:
(Aikin hajji shine tsayuwar arafah). Lokacin tsayuwan kuma na farawa ne daga:
bayan zawalin yinin arafah, har zuwa: fudowar alfijir na ranar layyah.
3-
Xawafin ziyara: Da
ake kiransa: xawafin ifadha; Wannan sunan kuma saboda kasancewar xawafin
ya kan kasance bayan an gangaro daga arafah, Kuma lallai shi wannan xawafin
rukuni ne da "ijma'in" maluma; saboda faxinsa maxaukakin
sasrki:
ﭽ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﭼ الحج:
٢٩
Ma'ana:
(Sa'annan sai su kammala aikinsu ta hanyar gusar da dauxar
da ta same su a lokacin haramarsu, su kuma cika bakancensu, su yi xawafi
ga xaki
'yantacce -mai tarihi-) [Hajj: 29].
4-
Sa'ayi tsakanin "safah da
marwah": Wannan shima rukuni ne; saboda hadisin A'ishah - رضي الله عنها-
ta ce:
"مَا أَتَمَّ اللَّهُ حَجَّ امْرِئٍ، وَلاَ عُمْرَتَهُ
لَمْ يَطُفْ بَيْنَ الصَّفَا وَالمَرْوَة" ([17]).
Ma'ana:
(Allah baya cika hajjin mutum ko umrarsa matuqar
bai yi xawafi tsakanin safah da marwah ba), da kuma saboda faxinsa
(r):
Ma'ana:
(Ku yi sa'ayi saboda Allah ta'alah ya wajabta muku yin sa'ayi).
Waxannan
"rukunnan" lallai aikin hajjin mutum baya cika sai ya aikata su, don
haka: Duk wanda ya bar rukuni guda xaya daga
cikinsu to lallai hajjinsa baya cika, har sai ya zo da shi.
Mas'ala
ta biyu: Wajiban hajji:
1-
Yin harama daga miqaatin da shari'a ta sanya.
2-
Tsayuwa a arafah har i zuwa dare:
Ga mutumin da ya zo tun cikin yini; wannan kuma saboda Annabi
(r)
ya tsaya ne har zuwa faxuwar rana –kamar yadda bayanin hakan zai zo a cikin siffar
hajjinsa- sannan kuma yace:
"خُذُوا عَنِّي مَنَاسِكَكُم".
Ma'ana:
(Ku kwaikwayi aikin hajjinku daga gare ni).
3-
Kwana a
"Muzdalifah" a daren layyah har zuwa dare ya raba biyu:
In har ya iso wannan bagiren gabanin haka; saboda haka Annabi
(r)
ya aikata.
4-
Kwana a "Minah" a dararen kwanakin da ake kiransu:
ayyamut tash-riq (11, 12 da 13).
5-
Jifan "jamaraat" a jere
(qaramin shaixan
"as-sugrah", shaixan na tsakiya, "al-wusxah",
sa'annan babban shaixan "al-aqabah").
6- Aske gashi baki-xaya (tal kobo) ko kuma saisaye:
Wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﯟ ﯠ ﯡ ﭼ الفتح: ٢٧
Ma'ana:
(Kuna masu xebe gashin kanku gabaxaya,
da kuma masu saisaye) [Fat'hi: 27].
7-
Xawafin bankwana; Amma banda mai
haila ko mai jinin nifasi; Wannan kuma saboda hadisin Abdullahi xan
Abbas -t-:
"أُمِرَ النَّاسُ أَنْ يَكُونَ آخِرُ عَهْدِهِمْ
بِالْبَيْتِ، إِلا أَنَّهُ خُفِّفَ عَنِ الْمَرْأَةِ الْحَائِضِ"([19]).
Ma'ana:
(An umurci mutane da cewa aikinsu na qarshe
ya zama xawafin xakin Allah ne, Sai dai kuma an yi
rangwame ga macen da take haila).
Duk mutumin da ya bar wajibi guda xaya
daga cikin waxannan wajiban, da gangan ne ko da mantuwa, sai ya
cike wannan givin ta hanyar "yanka dabbah", kuma aikin hajjinsa ya
inganta; wannan kuma saboda abinda ya tabbata daga Abdullahi xan
Abbas -t- cewa:
Ma'ana:
(Duk mutumin da ya manta wani abu daga cikin aikinsa, ko kuma ya barshi to sai
ya zubar da jini).
Duk kuma abinda ba wannan ba na daga aiyuka to sunna ne
ba wajibi ba, Muhimmai daga cikin waxannan
sunnonin kuma sune:
1-
Yin wankan harama, da fesa turare, tare
da xaura
zani da yafa mayafi guda biyu farare.
2-
Yanke farce, da aske gashin gaba da
hamata, da rage gashin-baki, da duk gashin da ya dace a cire shi.
3-
Xawaful-quduum (xawafin gabatowa) ga mai hajjin "ifraadi
ko qiraani".
4-
Sassarfa a kewaye guda uku na farko a xawaful
quduum.
5-
"Al-ixxiba'u" a xawaful
quduum, Wanda
kuma shine maniyyaci ya sanya tsakiyan mayafin da ya yafa, a qarqashin
hamatar hagu, geffan ihramin guda biyu kuma a kafaxarsa
ta hagu.
6-
Kwana a minah a daren arafah.
7-
Yin talbiyyah tun daga lokacin da mai
aiki ya yi harama har zuwa lokacin jifan "jamratul aqabah" (ranar
layyah).
8-
Haxe sallar magrib da ishah a muzdalifah.
9-
Tsayuwa a muzdalifah a
"al-mash'arul haraam" daga ketowan
alfijir, har zuwa duniya ta yi haske gabanin fitowar rana, idan hakan ya samu,
in ba haka ba kuma; Muzdalifah dukkaninta wurin tsayuwa ne.
BABI NA UKU: ABUBUWAN DA HARAMA DA HAJJI
YAKE HANAWA "MAHZUURAATUL IHRAAM"
DA KUMA BAYANI AKAN "FIDIYAH" DA "HADAYAH":
A
nan akwai mas'aloli kamar haka:
Mas'alar
farko: "Mahzuuraatul ihraam":
Wannan sune abubuwan da mai
harami ke nisantar aikata su a cikin haramarsa, saboda umurnin shari'a, Su guda
tara ne:
1-
Sanya xinkakken kaya: Wannan
kuma shine abinda aka auna shi gwargwadon jiki, ko aka auna shi gwargwadon
girman wata gava, na wanduna, da riguna, da wassunsu, Sai dai ga wanda bai
samu gyauto (izaari) ba, to ya halatta a gare shi ya sanya wando. Shi kuma hani
kan sanya xinkakken kaya da haramcinsa ya kevanta
ne ga mahajjata mazaje, Amma ita kuma mace (hajiya) za ta sanya duk abinda ta
ga-dama na daga tufa, sai dai niqaab, da safar hannu,
kamar yadda bayaninsa zai zo.
2-
Amfani da turare a jikin mai harama da
tufarsa, haka kuma yin ganganci shaqar
turare. Amma ya halatta ga mahajjaci ya shaqi
abinda ke da qamshi na tsirrai da suka fito daga qasa,
kamar yadda ya halatta masa ya yi tozali da abinda ba turare a cikinsa.
3-
Gusar da gashi ko faratu, a
wajen xa namiji ne ko mace, Amma ya halatta masa ya wanke kansa cikin
tausasawa, idan kuma farcensa ya karye to a nan ma ya halatta ya jefar da shi.
4-
Haramun ne namiji ya rufe kansa da wani
abu da ke mannuwa da shi: Amma ya halatta mai harama ya
shiga inuwar "hema; tanti", da makamancinta kamar bishiya, yana
halatta ga mai harama ya shiga qarqashin inuwar lema;
idan akwai buqata. Ita kuma mace an hana ta lulluve
fiskarta da wani abinda aka auna shi gwargwadon faxinsa
kamar "Niqaab, da Alburqu'i". sai dai kuma yana
wajaba akanta ta rufe fiskarta da "khimaar", a lokacin shigewar
mazajen da ba muharramanta ba (wato: ajnabai a gare ta; waxanda
aure ke halatta a tsakaninsu). Kuma an hana mace mai harama ta sanya safar
hannu (al-quffazaini). Kuma mace za ta sanya
abinda ta so na tufa, wanda taga sun dace da ita.
Duk kuma
mutumin da ya shafa turare, ko kuma ya rufe kansa, ko ya sanya xinkakken
kaya, da jahilci, ko mantuwa, ko kuma aka tilasta masa kan haka: to babu komai
akansa; wannan kuma saboda faxinsa (r):
Ma'ana:
(Lallai Allah ta'alah ya yi rangwame wa al'ummata kan kuskure da mantuwa, da
kuma abinda aka tilasta su akansa).
Don haka:
duk lokacin da ilimi ya zo ma jahili (kan haramcin waxancan
abubuwan guda huxu), ko aka tunatar da mai mantuwa, ko kuma tilasci ya gushe:
to wajibi ne akan mai harama ya tsayar da amfanuwarsa da waxannan
abubuwan da aka haramta masa.
5-
Haramun ne xaura auren mai harama ga kansa, ko ga waninsa.
6-
Haramun ne takar mace ta cikin farjinta:
Wannan kuma yana lalata aikin hajji, in ya kasance gabanin
abinda ake kiransa "at-tahallul al'auwal" (ma'ana: fita daga harama
na farko). Saboda idan hakan ya faru aikin hajjin ya lalace; koda kuwa jima'in
ya auku ne bayan tsayuwa a arafah.
7-
Haramun ne kwanciya da mace da
rungumarta; qasa
da yi mata jima'i ta cikin farji: Wannan baya
lalata aikin hajji, haka kuma sumbantar mace, da shafarta, da kuma kallonta da
sha'awa.
8-
Haramun ne kashe abun farautar sarari
(ba kogi ba) Amma ya halatta ga mai hajji ya kashe dabbobi da tsuntsaye da
ake kiransu (al-fawaasiq) waxanda
Annabi (r)
ya yi umurni kan a kashe su; (a cikin harami ne ko a waninsa, ga wanda ya yi
harama ko waninsa), waxannan dabbobin kuma sune: hankaka,
da vera,
da kunama, da shirwa, da maciji, da kuma mahaukacin kare.
Kuma baya
halatta ga wanda ya yi harama wajen farautar abun farauta koda kuwa da nuni ne,
balle waninsa. Kamar yadda baya halatta a gare shi da ya ci naman abinda aka
farauto don shi.
9-
Baya halatta ga mai harama ya sare
bishiyar harami, ko danyen tsiro da ya fito a cikinsa matuqar ba ya cutarwa,
Amma ya halatta a gare shi ya cire kamar qayoyi
masu cutarwa a kan hanya. Amma an togace bishiyar "al-izkhir" daga
cikin bishiyoyin harami, wajen halaccin sararta, da kuma duk bishiya ko tsiron
da dan-adam ya shuka su da kansa, wannan kuma maluman Musulunci sun yi
"ijma'i" akansa.
Mas'ala
ta biyu: "Fidiyah" ga wanda ya aikata abubuwan da aka hana:
-
Dangane da aske gashi, da yanke
faratu, da sanya xinkakken kaya, da turare, da lullave
kai, da kuma fitar da minayyi ta hanyar qura-ido wa
mace, ko mace ga namiji, da kuma rungumar mace ba tare da fitar da maniyyi ba,
dangane da waxannan akwai fidiya da ake bada zavi
kan aikata xayan abubuwa guda uku:
1- Azumtar yini guda
uku.
2- Ko kuma ciyar da
miskinai guda shida.
3- Ko kuma yanka
akuya.
Wannan
kuma saboda faxinsa (r)
ga Ka'ab xan Ujrah -t-
a lokacin da kwarkwatan kansa suka cutar da shi:
"احْلِقْ رَأْسَكَ، وَصُمْ ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ،
أَوْ أَطْعِمْ سِتَّةَ مَسَاكِينَ، أَوْ انْسُكْ بِشَاةٍ"([22]).
Ma'ana:
(Ka aske kanka; sai ka yi azumin yini uku, ko ka ciyar da miskinai guda shida,
ko kuma ka kusanci Ubangijinka da yanka akuya).
Su kuma
sauran aiyukan da ambatonsu ya gabata an yi "kiyasinsu ne" akan
wannan mas'alar; saboda dukkansu sun yi tarayya wajen haramci wa mahajjaci daga
shigansa cikin harama, da kuma kasancewar aikata su ga mahajjaci ba ya lalata
masa hajji.
-
Amma dangane
da farautar abun farauta: to a nan ana bada zavi ne ga
wanda ya kashe abun farautar tsakanin ya bada kwatankwacin abinda ya kashe daga
cikin dabbobin ni'imah.
Ko kuma
ayi "kimar kuxi" ga kwatankwacin dabbar da ya farauta, sai ya sayi
abinci da wannan qimar; kana ya ciyar da kowane miskini "mudun alkama
(al-burru)", ko kuma rabin "sa'i" na abinda ba shi ba; kamar
dabino, ko sha'ir.
Ko kuma ya
yi azumin yini xaya a madadin ciyar da kowanne miskini; wannan kuma saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ
ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ
ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﭼ المائدة:
٩٥
Ma'ana:
(Duk wanda ya kashe abun farauta daga cikinku da-gangan, to sakamakonsa shine
ya bada kwatankwacin abinda ya kashe daga dabbobin ni'imah, mutum biyu ma'abota
adalci daga cikinku musulmai su zasu yi hukunci da shi, hadaya da za a yi ta a
Makka. Ko kaffarar ciyar da miskinai, ko kuma azumi kwatankwacin haka)
[Ma'idah: 95].
-
Amma dangane da saduwa da mace a
cikin hajji gabanin "tahallul na farko" to lallai hakan na lalata
aikin hajji, kuma wajibi ne a bada fidiyar raqumi,
haka hukuncin ya ke, sawa'un yayi jima'in ne alhalin ya jahilci (bai san)
hukuncin aikata hakan ba, ko kuma da mantuwa, ko tilasci. Amma idan jima'in ya
kasance bayan "tahallul na farko" to hakan bai vata
hajjinsa ba, amma dole a yanka akuya.
Shi kuma
fitar maniyyi saboda rungumar mace, ko kuma saboda yin wasa da al'aura har
maniyyi ya fito "istimna'i", ko yin sumba, ko shafar mace da sha'awa,
ko maimaita kallo da ya jawo fitar maniyyi, duk waxannan
haramun ne, zai yanka (fidiyar) akuya, sai dai kuma baya lalata aikin hajji,
koda kuwa ya auku ne gabanin "tahallul na farko".
-
Amma dangane "xaurin
aure", Lallai fidiya ba ta wajaba akan haka, sai dai kuma auren lalatacce
ne.
-
Amma dangane da yanke bishiyar da
ta tsira a harami ko abinda ya tsiro a cikinsa wanda ba dan-adam ne ya shuka
shi ba: to za a bada fansar bishiyar da qarama
ce a "urfi" fansar "akuya", babbar bishiya kuma fansarta
"saniya". Su kuma tsirrai ko ganyeyyeki za a bada fansar qimarsu;
kasancewar ana iya yi masu kima.
Wannan hukuncin
haka yake idan wanda ya yi wannan aika-aikan ya aikata shine da ganganci, yayin
da wanda ya jahilci hukuncin ko kuma ya manta babu komai akansa.
Mas'ala
ta uku: "Hadayah" da hukunce-hukuncenta:
"Hadaya":
Itace abinda ake kawo
kyautarsa ga xakin Allah ta'alah na dabbobin ni'imah –raquma,
shanu, da awaki da tumaki-, don neman kusantar Allah maxaukakin
sarki.
Nau'ukan
hadaya:
1-
Hadaya da ake yi saboda aikin hajjin "tamattu'i da qiraani": Wannan
kuma wajibi ne, ga wanda ba mazaunin garin Makkah ba, kuma wannan jini ne na
ibada, ba na cike wani tasgaro da aikin hajji ya samu ba (ana kuma kiransa,
jinin "shukraan"), akan yi haka saboda faxinsa
maxaukakin
sarki:
ﭽ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﭼ البقرة: ١٩٦
Ma'ana:
(Kuma duk wanda ya yi tamattu'i da umrah zuwa hajji, to sai ya yanka abinda ya sauwaqa
na hadaya) [Baqara: 196].
Idan kuma
mahajjaci ya rasa dabbar hadaya, ko kuma ya rasa kuxinta
to zai yi azumin yini uku a cikin kwanakin aikin hajji.
Kuma ya
halatta a azumce su a kwanakin da ake kiransu "kwanakin at-tashriq"
(11, 12 da 13), da kuma kwanaki bakwai idan ya dawo i zuwa ga iyalansa; wannan
kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﰋ ﰌ ﰍ ﭼ البقرة:
١٩٦
Ma'ana:
(Duk kuma wanda bai samu hadaya ba to zai yi azumin yini uku a cikin kwanakin
hajji, da kuma azumi bakwai idan kuka komo) [Baqara:
196].
Kuma
mustahabbi ne ga mahajjaci ya ci daga naman hadayar tamattu'insa ko qiraani;
wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﭼ الحج:
٣٦
Ma'ana:
(Sai ku ci sashi daga cikin hadayanku, kuma ku ciyar da mai-roqo,
da wanda ya kame) [Hajj: 36].
2-
Hadayan cike tasgaro (jubran):
Wannan kuma shine fidiya na wajibi da ake yankawa saboda
barin wani wajibi, ko kuma aikata abinda aka hana aikata shi, daga cikin
abubuwan da "ihrami" ke hana aikata su, ko kuma saboda hana mai
harama qarisa aikinsa idan sababi hakan ya samu; wannan kuma saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ
ﯛ ﯜ ﭼ البقرة:
١٩٦
Ma'ana:
(Idan kuma aka tsare ku, to sai ku yanka abinda ya sauwaka na daga hadaya) [Baqara:
196]. Da kuma saboda faxin Abdullahi xan Abbas -t- cewa:
Ma'ana:
(Duk mutumin da ya manta wani abu daga cikin aikinsa, ko kuma ya barshi to sai
ya zubar da jini).
Wannan
nau'i na hadaya baya halatta a ci sashi daga cikinsa, hasali ma wajibi ne a
sadakar da shi xungurugum xinsa
ga faqiran
haramin Makka.
3-
Hadaya na taxawwu'i: Wannan
nau'in mustahabbi ne ga kowani mai hajji, da dukkanin mai umrah; wannan kuma a
matsayin koyi ne da Annabi (r);
saboda ya yi hadaya da raquma xari a hajjinsa na bankwana.
Kuma
mustahabbi ne mahajjaci ya ci daga wannan nau'i na hadaya; saboda Annabi (r) ya
umurci a xauka daga kowani raqumi; a xauki
wani dan tsoka, sai aka dafa, ya kuma ci sashi daga cikinsa, sannan kuma ya sha
romonsu ([24]).
4-
Hadaya na bakance: Wannan
nau'in kuma shine hadayar da mahajjaci ke yin bakancensa, don qara
kusantar Allah Ubangijinsa a wajen xaki mai
alfarma, kuma wajibi ne a cika irin wannan bakance; saboda faxinsa
maxaukakin sarki:
ﭽ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﭼ الحج:
٢٩
Ma'ana:
(Sa'annan sai su kammala aikinsu ta hanyar gusar da dauxar
da ta same su a lokacin haramarsu, kuma su cika bakancensu, su yi xawafi
ga xaki
'yantacce
–daxaxxe-) [Hajj: 29].
Kuma baya
halatta a ci daga irin wannan nau'i na hadaya.
Lokacin
yanka hadayah:
Hadaya na
"tamattu'i" da kuma na hajjin "qiraani"
lokacin yanka su na farawa ne daga bayan sallar idi, a yinin layyah, har zuwa qarshen
kwanakin tashriq (qarshen yinin 13).
Amma yanka
"fidiyar" aske kai ko sanya tufa shi kuma na farawa ne daga lokacin
da aka aikata wannan aikin, haka ita ma fidiya da take wajaba saboda barin wani
wajibi.
Shi kuma jini na tsare
mahajjaci da hana shi qarisa aikinsa: na kasancewa ne a lokacin da sababinsa ya samu,
wanda akuya ne, ko "xaya-bisa- bakwai xin raqumi,
ko 1/7 saniya; saboda faxinsa maxaukakin
sarki:
ﭽ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ
ﯛ ﯜ ﭼ البقرة:
١٩٦
Ma'ana: (Idan kuma aka tsare
ku, to sai ku yanka abinda ya sauwaka na daga hadaya) [Baqarah:
196].
Wurin
yanka:
Hadaya na aikin hajjin
"tamattu'i" da kuma na "qiraani":
Sunna akansu shine a yanka su a "Minah", amma da mahajjaci zai yanka
shi a kowanne wuri a cikin haramin Makkah ya halatta.
Haka kuma "fidiya"
na barin wani wajibi, ko kuma aikata wani abun da aka hana, shima ba a yanka
shi sai a harami. In banda hadayar tsare mahajjaci da hana shi qarisa
aikinsa shi kam; zai yanka shi ne a gurbin da aka tare shi.
Shi kuma azumi ya halatta a
yi shi a kowani wuri, sai dai kuma mustahabbi ne a yi azumin yini uku a cikin
kwanakin hajji, da kuma bakwai idan ya koma i zuwa ga iyalansa; wannan kuma
saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﰋ ﰌ ﰍ ﰏ ﰐ ﰑ ﭼ البقرة:
١٩٦
Ma'ana: (To idan kuka aminta;
duk mutumin da ya yi tamattu'i da umrah zuwa hajji, to sai ya yanka abinda ya sauwaqa
na hadaya. Duk kuma wanda bai samu hadaya ba to zai yi azumin yini uku a cikin
kwanakin hajji, da kuma azumi bakwai idan kuka komo, wannan kuma azumi goma
kenan cikakku) [Baqarah: 196].
Kuma mustahabbi ne mahajjaci
ya yanka abun yankansa da kansa, idan kuma ya na'ibtar da waninsa ko ya wakilta
shi akan haka to babu laifi.
Kuma mustahabbi ne a wajen
yanka ya ce: "BISMILLAH, ALLAHUMMA HAZA MINKA WA LAKA".
Amma dangane da sharuxan hadayah
kuma to sune sharuxan laiya babu banbanci:
1-
Dole abun
yankan ya zama daga cikin dabbobin ni'imah (raquma,
shanu, awaki da tumaki).
2-
Kuma dole
su wofanta ga barin aibuka da za su hana hadayar inganta, kamar rashin lafiya,
ko rashin ido guda xaya, da gurguntaka, da mummunan rama.
3-
Kamar
yadda dole su cika shekaru da watanni da aka shar'anta: Raquma
shekaru biyar (5), shanu shekaru biyu (2), akuya shekara guda (1), tinkiya
watanni shida.
BABI
NA HUXU:
SIFFAR HAJJI DA UMRAH:
Asali da dalili a wajen
ma'abota ilimi kan siffar hajji Shine: hadisin Jabir xan
Abdullahi -t-
shahararre([25]).
Kuma haqiqa
mun bibiyi riwayoyi ingantattu kuma tabbatattu daga Annabi (r); kuma a
yayin da muka haxa su, sai muka isa i zuwa ga siffar da take tafe:
Idan mutumin da yayi nufin
aikin hajji ko umrah ya isa wurin da ake kiransa "miqaati"
mustahabbi ne a gare shi yayi wanka, ya kuma aske abinda ke buqatar
cire shi na gashi; wato kamar gashin hamata, gaba, da gashin-baki, ya kuma
yanke faratunsa. Daga nan sai mutum namiji ya tobe xinkakkun
kayansa, kana ya sanya turare a jikinsa gabanin yin niyyar shiga cikin aikinsa
(na hajji ko umrah), kuma an so namiji ya xaura
zani da mayafi guda biyu masu tsafta farare.
Ita kuma mace tana da damar
tayi haramarta daga abinda ta so na tufa.
Shi namiji zai lulluve
kafaxarsa
da mayafinsa.
Sai kuma mahajjaci yayi
harama da nau'in aikin da ya nufa (kamar umrah, hajji ifradi, qiraani,
tamattu'i).
Abinda kuma yafi shine
mahajjaci yayi haramarsa bayan ya daidaita akan dabbarsa (ko motarsa).
Idan mai harama yana tsoron
wani abu da zai iya hana shi kammala aikinsa; kamar rashin lafiya, ko 'yan
fashi, ko makamancin haka to a nan zai yi sharaxin
cewa: wurin warwarewan aikinsa shine wurin da wannan uzurin ya riqe
shi.
Mustahabbi ne mahajjaci ya
kasance a wajen da zai yi niyya yana fiskantar alqiblah,
ya kuma ce: Ya Allah! Na yi nufin hajjin da ba riya a ciki, babu kuma yi don a
ji (sum'ah).
Sai kuma ya fara
"LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIKA, INNAL
HAMDAH, WAN NI'IMATAH, LAKA WAL MULKA, LA SHARIKA LAKA". Sahabbai kuma sun
kasance suna qarawa akan haka; Suce: "LABBAIKA ZAL MA'AARIJ, LABBAIKA ZAL
FAWAADIL".
Kuma sunnah ne namiji ya xaga
sautinsa lokacin yin "talbiyyah".
Idan ya isa garin Makkah
mustahabbi ne mahajjaci ko mai umrah yayi wanka, idan kuma ya zo zai fara xawafi
sai yayi abinda ake kiransa "id-xiba'i"
ma'anarsa kuma shine: Namiji ya buxe kafaxarsa
ta dama, sai kuma ya lulluve kafaxarsa ta hagu da "haraminsa".
Kuma sharaxi
ne mahajjaci ya kasance yana da alwala a lokacin da yake yin xawafi.
Mustahabbi ne kuma ya tava
"hajarul aswad" da hannunsa, tare da kuma sumbantarsa da bakinsa,
idan kuma hakan ya gagara sai ya tava shi da
hannunsa, tare da sunbantar hannun, idan hakan kuma bai yiwu ba; to zai yi nuni
ne i zuwa ga dutsin (hajarul aswad) da hannunsa, ba tare da ya sumbanci hannun
nasa ba. Zai kuma aikata haka a kowani zagaye, kuma zai fara kowani zagaye da
kabbara.
In kuma ya fara xawafin
nasa da faxin "BISMILLAHI WALLAHU AKBAR" to hakan ya yi kyau.
Idan kuma ya iso setin dungun
da ake kira da "AR-RUKUNUL YAMANIY" to sai mai xawafi
ya tava
shi; ba tare da ya sumbance shi ba, idan cunkoso kuma ya hana tava
shi; to a wannan halin ba zai yi nuni i zuwa gare shi ba, haka kuma ba zai yi
kabbara ba.
Kuma mustahabbi ne mai xawafi
ya riqa
cewa –a tsakanin "RUKUNUL YAMANIY DA HAJARUL ASWAD"-:
ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البقرة:
٢٠١
Kuma zai yi duk abinda ya sawwaqa
na addu'a a sauran xawafinsa.
Mustahabbi ne mai xawafi
yayi sassarfa (ARRAMALU) a zagaye ukunsa na farkon xawafi.
Sai kuma ya yi tafiyarsa irin ta al'ada a sauran kewaye guda huxun.
Idan kuma ya kammala zagaye
bakwai xinsa to sai ya rufe duka kafaxunsa
guda biyu da mayafinsa. Sa'annan sai ya tafi i zuwa "MAQAAMU-IBRAHIMA"
yana mai karanta:
ﭽ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﭼ البقرة:
١٢٥
Sai kuma mutum ya sallaci
raka'oi guda biyu a bayan wannan wuri "maqaamu-Ibrahima";
yana mai karanta (QUL YA AYYUHAL KAAFIRUUNA) bayan suratul fatihah, a raka'ar
farko, A raka'a ta biyu kuma sai ya karanta (QUL
HUWAL LAHU AHADUN). Idan kuma bai samu damar yin sallah a bayan (maqaamu-Ibrahima)
ba saboda cunkoso, ko makamancin haka; to sai ya yi sallah a kowanne wuri a
cikin wannan masallacin. Wannan xawafin
shi ake kira "xawaful quduum" ga mai hajjin "ifraadi", da "qiraani".
"xawafin umrah" kuma ga mai "tamattu'i".
Daga nan kuma; an shar'anta
masa ya sha ruwan zamzam, ya kwara shi ma kansa.
Sa'annan sai ya dawo i zuwa
"hajarul aswad" ya tava shi -idan hakan
ya sauwaqa.
Sa'annan sai ya fita zuwa ga
dutsen "safah", yana mai karanta:
ﭽ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ البقرة:
١٥٨
Daga nan kuma sai ya hau
dutsen "safah", har sai ya hango xakin
ka'abah, ya fiskanci alqiblah, ya xaga
hannayensa yana cewa:
"ALLAHU AKBAR"; sau
uku,
(لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ،
لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لا إِلَهَ إِلا
اللهُ وَحْدَهُ، أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدَهُ، وَهَزَمَ الأَحْزَابَ وَحْدَهُ).
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHUW, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAH, ANJAZA WA'ADAH, WA NASARA ABDAH, WA HAZAMAL AHZABA
WAHDAH.
Zai aikata wannan ne har sau
uku, tare da yin addu'a mai tsayi a tsakanin zikiri da zikiri.
Sa'annan sai ya sauka yana
mai tafiya i zuwa dutsen "marwah". Idan ya iso tsakanin
"mil" guda biyu kwarra to sai ya yi gudu mai tsanani a tsakaninsu.
Wannan kuma ga mazaje ne kawai; banda mata. Daga nan kuma sai ya ci gaba da
tafiyarsa har sai ya hau dutsen "marwah". Zai kuma aikata akan wannan
dutsen kwatankwacin abinda ya aikata alhalin yana kan safah. Wannan kuma shine
kewaye ko zagaye xaya, sa'annan daga marwah idan har ya dawo safah to wani zagayen
na daban kenan, da haka har ya cika kewaye guda bakwai.
Wannan sa'ayin ga mai aikin
hajjin "ifraadi ko qiraani" shine sa'ayinsa na aikin hajji, kuma waxannan
mutane biyu ba za su yi abinda ake kiransa "tahalluli" ba; a bayan
wannan sa'ayin, hasali ma za su wanzu ne a cikin haramarsu. Ga mai hajjin
"tamattu'i" kuma shine sa'ayin umrarsa.
Shi mai tamattu'i zai yi
tahalluli ya warware daga umrarsa daga zarar ya aske gashin kansa, sai kuma ya
sanya tufafinsa.
Idan ranar takwas ga watan 12
ta zo (ma'ana: yinin da ake kiransa yinin tarwiyyah), To sai mai tamattu'i ya
yi haramar aikin hajjinsa, daga wurin da ya ke zaune.
Haka suma mazauna garin
Makkah, da waxanda suke kusa da ita daga cikin waxanda
ba su yi harama ba.
Kuma mustahabbi ne mahajjaci
–a wannan yinin- ya aikata irin abinda ya aikata a "miqaatinsa";
na yin wanka, da shafa turare, da tsafta. Daga nan kuma sai xaukacin
mahajjata su xunguma su nufi qauyen
"minah" suna masu "talbiyyah", suna masu sallatar azahar,
la'asar, magriba, ishah, da asuba, kowacce daga cikinsu ita xayanta
ba tare da an yi jam'inta da 'yar'uwatta ba, gami da yin kasarun sallah mai
raka'oi huxu daga cikin sallolin guda biyar.
A safiyar yinin tara (9)
mahajjata zasu tafi zuwa filin "arafah", In har kuma da zasu samu
damar sauka a wajen masallacin "Namirah" zuwa lokacin da rana zata yi
zawali to hakan yana da kyau. Idan ranar ta yi zawali sai shugaba ko mai
na'ibtarsa ya yi huxuba gajeruwa, sa'annan ya sallaci azahar da la'asar "qasaru
kuma tare", a lokacin sallar azahar. Kana sai ya shigo yankin filin
arafah. Kuma wajibi ne akan mahajjaci ya tabbatar cewa yana cikin kewayen
arafah. Sai ya fiskanci alqiblah, ya xaga
hannayensa yana mai addu'a da kuma "labbaikal lahumma labbaika", ya
yi ta hamdalah, ya yi ijtihadi sosai wajen qanqan-da-kai
da zikirori da addu'a a wannan yini mai girma. Kuma mafificin abinda ake faxa
a wancan yinin shine:
"لا إِلَهَ إِلا اللَّهُ
وَحْدَهُ لا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ".
LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU
LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
Kuma mustahabbi ne mahajjaci
ya zamto ba ya cikin azumi a tsawon wannan yinin; saboda hakan zai fi bashi qarfi
wajen tsaida bauta. Mahajjaci ba zai gushe ba yana tsaye yana mai qanqan-da-kai,
tare da bayyanar da kaskancinsa i zuwa ga Allah, har rana ta faxi.
Idan rana ta faxi
sai mahajjaci ya gangara daga "arafah" cikin nitsuwa, yana tafiya
yana "talbiyyah" har ya isa filin "muzdalifah"; sai ya
sallaci sallar magriba da ishah a tare, gami da yin qasarun
ishar. Kuma an yi rangwame ga masu rauni su fice daga muzdalifah cikin dare.
Shi kuma mai qarfi dole ne akansa ya wanzu a muzdalifan har sai bayan yayi
sallarsa ta asubah.
Sa'annan kuma sai ya fiskanci
alqiblah,
ya gode ma Allah ta'alah (alhamdu lillahi), ya girmama shi (Allahu akbar), yana
mai yin "la ilaha illal lahu", da sauran zikirori, har sai gari ya yi
haske sosai. Sa'annan sai mahajjaci ya bar muzdalifah gabanin fudowar rana.
Kuma wajibi ne akansa ya tafi a nitse, yana mai yin "talbiyyah". Daga
nan kuma sai ya tsunci duwatsu (tsakuwa) guda bakwai akan hanyarsa. Har idan ya
iso "jamratul aqabah" sai ya jefe ta da tsakuwansa guda bakwai, yana mai yin
kabbara tare da kowanne tsakuwa. daga nan kuma sai ya yanke
"talbiyyah"; yana mai tsayar da yinta kwata-kwata. Sa'annan sai ya
yanka ko soke abun hadayarsa, kuma mustahabbi ne ya ci wani abu daga cikin
wannan naman. Sa'annan sai ya aske gashin kansa. Sai ya yi xawafinsa
na ifadha, tare da yin sa'ayi na aikin hajjinsa in aikin hajjin
"tamattu'i" ya ke yi. Ko kuma "ifraadi ko qiraani"
amma sai ya zama bai yi "sa'ayin" ba a lokacin da ya yi "xawaful
quduum"
dinsa.
Kuma sunnah ita ce a jera waxannan
aiyukan: jifa, sai yanka ko sukar raqumi,
sai kuma aski ko saisaye. Idan kuma mahajjaci ya kauce
ma hakan; ya kuma gabatar da wani aikin daga aiyukan ranar goma akan wani, to
babu laifi. Kuma idan mahajjaci ya aikata abu biyu daga cikin aiyuka uku –jifan
jamratul aqabah, aski ko saisaye, da kuma xawafi
tare da sa'ayi; in har akwai sa'ayin akansa- to ya samu "tahallulin
farko", daga nan kuma kowani abu ya halatta a gare shi wanda
"ihrami" ya haramta masa, in banda kwanciya da matarsa. Idan kuma ya
aikata ukun gabaxaya to ya yi "babban
tahalluli"; sai kowani abu ya zama ya halatta masa; harma kusantar matar
tasa.
Kuma mahajjaci zai kwana a
"minah" daren goma sha xaya da goma
sha biyu (11, 12) a matsayin wajibi, sai
kuma ya yi jifan "jamaraat guda uku" ranar goma sha xaya;
yana mai farawa da "qaramin", sannan sai "alwusxah",
sa'annan sai na karshen (babba). Haka nan zai aikata a rana ta goma sha biyu
(12). Lokacin jifan kuma na farawa ne daga "zawalin rana" har zuwa
asubah. Idan mahajjaci ya jefi "jamrah qarama"
an sunnanta masa ya matsa kaxan ta dama gare
shi, ya tsaya yana mai fiskantar alqiblah,
ya xaga
hannayensa yana addu'a. haka nan idan ya jefi "jamrah ta tsakiya" nan
ma an sunnanta masa ya matsa gaba kaxan
ta vangaren
hagu, ya fiskanci alqiblah, ya tsaya ya jima yana
addu'a, hannayensa sama. Sai dai kuma ba zai tsaya ba bayan ya yi jifan
"jamratul aqabah". Idan kuma ya yi nufin gaggawa to wajibi ne akansa ya
fita daga minah ranar goma sha biyu (12), kafin rana ta faxi.
Yayin da idan ranar ta faxi masa alhalin yana "minah", a cikin zavinsa
to wajibi ne akansa ya kwana zuwa ranar goma sha uku (13).
Idan kuma mahajjaci ya so ya
fice daga garin Makkah to wajibi ne akansa yayi xawafin
bankwana, don ya sanya aikinsa na qarshe
ya zamo xawafin xakin Allah. Shi kuma wannan xawafin
na faxuwa
ga mace mai haila ko kuma mai jinin nifasi.
A
wani lafazin kuma:
"وَمُهَلُّ أَهْلِ الْعِرَاقِ مِنْ ذَاتِ عِرْقٍ".
Ma'ana: (Wurin da mutane Iraaq
zasu xaga sautinsu da niyya shine: ZAATU-IRQIN).
([20]) Ad-daraquxniy ya ruwaito shi
(2/191, lamba: 2512), da Albaihaqiy (5/152),
da wassunsu. Wannan maganar ta tabbata i zuwa ga Abdullahi xan Abbas
cewa shine ya faxe ta, ba
Annabi (r) ba,
kamar yadda Ibnu-abdilbarri ya faxa
(Duba: Al'istizkaar, 12/184), da kuma Albaniy a cikin littafin (Irwa'u algalil,
4/299).
No comments:
Post a Comment