2015/09/18

KUMA KA TSARKAKE DAKINA fadin Allah ne








KUMA KA TSARKAKE …. XAKINA
(برنامج: وطهّر بيتي)












FASSARAR
ABUBAKAR HAMZA


Tun lokacin da Allah ta'alah ya shiryar da badaxinSa annabi Ibrahima (عليه السلام) izuwa wurin da zai gina xakin Allah, ya kuma shirya shi don aikata hakan, sannan ya yi masa izinin ya gina shi, to sai Allah ya umurce shi da tsarkake shi daga alamomin da suke bayyanar da shirka, da gumaka, da dauxa da qazantar da  ake iya gani da kuma ta ma'ana.    Kuma a duk tsawon zamani al'ummar Musulmai basu gushe ba suna matuqar nuna damuwansu tare da bada kulawa ta musamman ga sha'anonin masallatan harami guda biyu masu daraja,    Tsarki ya tabbata ga wanda ya sanya masallacin haramin Makkah ya zama tsayuwa ga lamarin mutane da aminci,     Kuma musulmai suna kai-komo zuwa ga wannan masallacin, sai su koma garurrukansu ba tare da sun ji cewa sun gama biyan buqatarsu daga gare shi ba.      Lallai zukatan masoya sun rataya da xakin masoyinsu, yayin da ya jingina shi zuwa ga kanSa, saboda haka ne duk lokacin da aka ambaci masallaci mai alfarma (na Makkah) sai suyi bege,    Idan kuma suka tuno nisansa da su to sai su yi kukan zuci (su ji zafi),            
            Kuma lallai Allah ya karrama qasar da masallatan nan na harami guda biyu masu daraja suke cikinta;    ta yadda ya  sanya wannan qasa ta zama abin so ga zukata, kuma ta zama wajen kulawan dukkan musulmai, da girmamawarsu, wannan kuma ya samo asali tun lokacin da annabi Ibrahima ya bada shelar a je yin hajji, har zuwa lokacin da Allah zai gaje qasa, da abinda suke cikinta.
            Kuma don ganin anyi aiki da umurnin da shugabanni –Allah ya qara kiyaye su- suka bayar na cewa a gabatar da mafificin hidimar da ta dace; ga masu ziyartar  masallatan nan guda biyu na harami, lallai GAMAMMEN OFISHIN DAKE KULA DA SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA DA KUMA MASALLACIN ANNABI (صلى الله عليه وسلم) qarqashin kulawar qaramin OFISHIN DAKE KULA DA TSAFTA DA KUMA SHUMFUXAN MASALLACIN HARAMIN MAKKAH, sun xauki taken aikinsu daga faxin Allah
( وطهِّر     بيتي ).
Ma'ana: "Kuma ku tsarkake … xakina".
 Domin taken ya zama abin alfahari da xaukaka,   sannan ya zama sababi mai ingizawa, kuma qarin kwarin guiwa wajen yin aiki da cikawa,   a ko-yaushe,  tare kuma da yin amfani da kayayyakin aikin zamani, dangane da shirye-shirye da kuma hanyoyin zartar da su,  waxanda suka dace da yadda aikin yake; a jikin xakin Allah 'yantacce = A ke fahimtar aikin sanya ido, da kuma bin yadda aikin yake gudana daki-daki,   a ofishin tsafta da shumfuxai na masallaci mai alfarma.
            Lallai hidima wa masu hajji, da xinbin jama'ar da suke zuwa umrah; waxanda suke haxe a wuri xaya , kuma a lokaci guda tana buqatar kwazo da aiki tuquri, akan wani tsarin da aka yi nazarinsa,  tare kuma da kyakkyawan kula,  Wannan kuma shine ya sanya ofishin kula da tsafta da shumfuxai yake yin aiki da mutanen  da aka basu horo da tirenin, wanda a                                    yanzu yawansu ya kai mutane  fiye da ma'aikata  xari biyu (200), daga cikin tabbatattun ma'aikata, da waxanda suke aiki a lokacin buqata (kamar lokacin azumi, da hajji), waxanda duk suke aiki qarqashin babbar hukumar kula da masallatan nan guda biyu. Qari akan masu 'aiki da hannayensu maza da mata; waxanda yawansu ya wuce mutane dubu biyu da xari bakwai (2700), Da shugabanninsu da suke kula da su  maza da mata; (مراقب) waxanda yawansu ya kai mutane xari biyu da sittin (260),  Da kuma (مشرف) guda xari xaya (100) mazansu da mata,   wanda duk  aikinsu yake  qarqashin kamfanonin  gudanar da masallacin; waxanda kuma ake kasa lokacin aikinsu zuwa kashi huxu,  a cikin awoyi ashirin da huxu (24).
            Kuma lallai ita wannan hukumar ta samar da kayan aiki na zamani  da hanyoyin gudanar da su don tsayuwa da aiyuka masu yawa, a cikin masallacin ne, ko a harabarsa,  ta yadda hukumar ta samar da motocin lantarki guda arba'in, da kuma amalanken zamani guda xari da ashirin (120) don xauke ababen zubarwa (dauxa ne ko waninsa), Qari akan mashin guda sittin don wanke masallaci mai alfarma da kuma harabobinsa.
            Kuma zamu iya dunqula bayanin aikin HUKUMARTSAFTACE  MASALLACIN KA'ABA DA YI MASA SHUMFUXAI, cikin :
Wankewa, sai kula da shumfuxai,        da gusar da dauxa,     da kankare-kankare da shafa ko fesa turare,
Ta yadda a ake wanke wannan masallaci mai alfarma sau huxu a kowani  tsakanin yini da dare, farawa da filin xawafi,  dana Safah da Marwah, da kuma dutsen Safan kansa,  da harabar waje,  da  matattarar shan ruwa, da wuraren alwala,  wanda su kuma ake wanke su da  omon kawo tsafta, sau biyar a kullum-kullum.
Amma su kuma banxakai  -waxanda yawansu ya kai bayan gida guda dubu goma sha huxu (14, 000)-, to suma ana wanke su har sau huxu a kullum-kullum.
            Kuma duk da tsananin cunkoson mutane, a cikin kowani lokaci, na kwanakin ramadhana dana aikin hajji, to lallai aiyukan kawo tsafta a wannnan bagire basa tsayawa,  kuma ana yin tsaftan a wani tsarin da baya hana ci-gaban aiyukan masu umrah ko mahajjata. Kuma ana wanke filin xawafi gabaxayansa  cikin gwanancewa, a qasa da minti talatin.
            Kuma ana wanke dukkan hanyoyin da suke shigar da mutane cikin masallaci mai alfarma, da kuma qasan masallacin,  da tayil xinsa, da  gadodi,  da manarori,  da qofofi, da matakalan zuwa sama,  da fiskar masallacin, da filoli,     Qari akan tsaftace wuraren tafiyar da ruwan da aka yi amfani da shi, da kuma fesa ruwan kawo tsafta da maganin kashe kwari.
            Kuma tudun da ake wankewa a kullum kuma a ko-yaushe yana kusa ya kai : mitan murabba'iy ; dubu xari bakwai (700, 000) a lissafin murabba'iy.    Kuma lallai bayan an kammala aikin sabon qari da ake yi wa masallacin to wannan tudun zai ninninku har zuwa: mitan murabba'iy miliyon xaya da dubu xari takwas na  lissafin murabba'iy (1, 800000).

WANKE XAKIN KA'ABAH (غسيل الكعبة)
            Kuma qarqashin kulawar Sarki mai hidima wa masallantan harami ne guda biyu, ake wanke xakin Ka'abah har sau biyu a cikin kowace shekara,   Kuma ana wanke Ka'aban ne da ruwan da aka cakuxa shi, da turaren ALWARDU, da kuma turaren AL'UUD na alfahari, wanda yake cakuxe da ruwan ZAMZAM,     Kuma akan zuba ruwan  wanke xakin a cikin masakai na NUHAS wanda an sana'anta su ne don wannan manufar.   
            Masallacin harami da harabarSa ana shumfuxa masa SALLAYA ko KAFET kusan dubu talatin (30, 000),  daga koren sallaya, na alfahari mai tsada,   wanda ake kashe kwayoyin cutuka da kuma tsaftace shi, har sau uku, a kullum.    Kuma an ware injin wanki na zamani na musamman don wanke sallaya ko kafet xin harami, mai maxaukakin kyau,    Kuma kowani kafet a wajen wanke shi da qoqarin kashe kwayoyin cuta daga gare shi, yana bin matakai guda biyar;  Wanda suke farawa daga karkaxe qura da gusar da turvaya,   Sannan sai wankewa,   Bayan haka sai matakin busarwa,   sai kuma a bijirar da shi zuwa ga zafin rana,  Na qarshen kuma sake tamke shi, da kuma qara saqa shi.
            Kuma lallai matsakaicin ababen xauke su don zubarwa daga wannan masallaci a cikin yini guda xaya,  ya kai TON ashirin da biyar (25), a sauran kwanaki.  Saidai kuma yawan su ya kan kai TON casa'in (90) a yini xaya na kwanakin ramadhana dana aikin hajji .
            Kuma lallai wannan MA'AIKATAR ta samar da abinda ya yi kusa da dubu biyu  (2000) na ma'adanin kwashe ababen zubarwa na filastik manya-manya don a riqa tattara ababayen zubarwa, a cikinsu gabanin kwashe su, an kuma ajiye wassunsu a cikin masallacin, wassu kuma  a wajensa.

Kamar yadda aka tanadar da ledodin sanya takalma na filastic, wanda ake yagarsu a bakin qofofin shiga  masallacin harami,  Wanda a kwanakin cunkoso (ramadhana ko hajji) ake amfani da leda kamar miliyan biyu (2, 000000) a kullum-kullum.
Kuma lallai wannan MA'AIKATAR ta kan tsayu wajen shasshafe qofar xakin Ka'abah, da MaqamuIbrahima har sai sun yi sheqi,  haka kuma fitilolin da suke kan Hijru-Isma'ila, da qofofi, da kuma kantotin jejjera alqur'anai,  da kuma kayan kyale-kyalen NUHAS,  qari akan shasshafe ababen shamakance shigewa har sai sun yi sheqi; waxanda ake samunsu a cikin masallaci mai alfarma da kuma a haraba.
Kuma ana shafa turare a jikin Ka'abah maxaukakiya, da Hajarul-Aswad, da Multazam da RuknulYamaniy da mafi tsadan nau'ukan TURAREN WARD da UUD na alfahari, a kullum-kullum.
Kamar yadda masu ziyara suma akan shafa musu turare, kuma akan kunna na wuta,  da kuma fesa turare a kafet, da hanyoyin shigewa da turaren ALWARDU,   Kuma yawan abubuwan da ake amfani da su na turare ya kan kai kusan lita dubu biyu (2000), a kowani wata.

Kuma lallai wannan qoqari da aka yi a baya, kuma ake yi har yanzu; bai gushe ba,  lallai fa ba abu ne mai yiwuwa ba, ba don falalar Allah da   kuma datarwarSa ba, a farkon lamari da qarshensa.  Sai kuma qarfafawan da bashi da iyaka daga Jagororinmu shiryayyu; waxanda suke samun xaukaka da yin hidima wa masallatan harami guda biyu masu girma.    Sai kuma sanya ido, da bibiyan yadda aikin ke gudana a ko-yaushe daga GAMAMMEN SHUGABAN MA'AIKATAR KULA DA SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA NA MAKKAH, DA KUMA MASALLACIN ANNABI, da kuma  Mai na'ibtarsa wajen kula da SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA.   Sa'annan sai kuma qoqarin wassu mutanen da suka riqi hidima wa  masallacin ka'abah 'yantacce, da kuma yin aiki tuquru don waxanda suka tafo fatauci zuwa ga Allah su samu hutu,  suka riqi yin hakan a matsayin biyayya, da neman kusanci zuwa ga Allah,  kuma xaukaka ne, da samun kusancin,  a wannan gari na Makkah mai alfarma.   MANZON ALLAH (صلى الله عليه وسلم) yace:
"لا تَزَالُ هَذِهِ الأُمَّةُ بِخَيْرٍ مَا عَظَّمُوا الْحُرْمَةَ حَقَّ تَعْظِيمِهَا، فَإِذَا تركوها وضَيَّعُوهاَ هَلَكُوا".
"Wannan al'ummar ba zata gushe ba tana cikin alheri, matuqar sun girmama wannan wuri mai alfarma iyaka girmama shi,    Idan kuma suka barshi suka tozarta shi to sai su halaka", Ahmad da Ibnu-Majah suka ruwaito shi,   Kuma Ibnu-Hajar yace hadisi ne mai kyau (hasan).

                         KUMA KA TSARKAKE………… XAKINA   !!!

Al-madinah, 04/ZULHIJJAH/ 1436h
Daidai da 18/09/2015m

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...