2015/09/23

HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI GUDA BIYU

 HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI GUDA BIYU
      Idi guda biyu sune: idin laiyah, da idin azumi, kowanne daga cikinsu yana tare da wata shari'a; saboda idin azumi na kasancewa ne bayan musulmai sun gama azumin watan ramadana, shi kuma na laiyah, yana kasancewa ne a qarshen kwanaki guda goma na farkon watan ''zul-hijjah". An sanya wa idi suna "idi" ne saboda yana dawowa ya yi ta maimaituwa, a lokacinsa.
A nan akwai mas'aloli guda takwas, kamar haka:
Mas'alar farko: Hukuncin sallar idi biyu da kuma dalilai akan haka:
Sallar idi ''farilla ce na kifayah''; idan sashin mutane suka aikata shi, laifin ya sauka ga sauran, idan kuma kowa-da-kowa ya bar shi to dukkan musulmai sun yi laifi; saboda idi na daga alamomin Musulunci na zahiri, kuma saboda Annabi (r) ya dawwama wajen sallatar idi, haka kuma sahabbansa a bayansa. Kuma haqiqa Annabi (r) ya umurci mutane da su fita zuwa ga idi, har da mata, sai dai kuma ya umurci masu haila da su nisanci gurbin sallar. Wannan kuma na daga cikin abubuwan da suke nuna muhimmancinta, da kuma girman falalarta; saboda idan har za a umurci mata da ita tare da cewa basa daga cikin ma'abota taruwar sallar jam'i, to lallai maza su suka fi cancantar yin salla a cikin jam'i. Kuma akwai daga cikin maluma, waxanda suke qarfafa cewa sallar idi: ''fardu aini'' ce.

Mas'ala ta biyu: Sharuxan sallar idi:
Yana daga cikin manya-manyan sharuxanta: shigan lokaci, samun adadi da aka sanya, da riqar-gari da zama a cikinsa na din-din-din. Don haka; Sallar bata halatta gabanin lokacinta, kamar yadda bata halatta ga mutane qasa da uku, haka kuma bata wajaba ga matafiyin da baya zaune a gari.

Mas'ala ta uku: Wuraren da ake sallatar idi a cikinsu:
An sunnata a yi sallar idi a sahara; ba a cikin kewayen gari da gidaje ba; saboda hadisi Abu-sa'id -t- cewa:
"كان النبي r  يَخْرُجُ في الفِطْرِ وَالأَضْحَى إِلَى المُصَلَّى"([1]).
Ma'ana: (Annabi –r- ya kasance a idin azumi da na lahiyah ya kan fita zuwa ''wurin sallah''). Manufar fitan –wallahu a'alam- shine: don bayyanar da wannan alama ta addini (sha'irah). Amma ya halatta a yi sallar idi a masallacin juma'a, in akwai wani uzuri kamar ruwan sama, da iska mai tsanani, da makamancin haka.

Mas'ala ta huxu: Lokacin idi:
Lokacin yin sallar idi shine: bayan xagowar rana gwargwadon "kan mashi", har zuwa lokacin da rana za ta yi zawali, kamar sallar walaha, saboda Annabi (r) da khalifofinsa sun kasance suna sallatarta bayan xagowar rana, kuma saboda gabanin xagowar rana lokaci ne da aka hana sallah([2]). Amma an sunnata gaggauta sallar idin "lahiyah" a farkon lokacinta, da jinkirta sallar idin azumi; saboda haka Annabi (r) ya aikata, kuma saboda mutane suna da buqatar a gaggauta idin lahiyah domin yanka dabbobin layyansu, kamar kuma yadda suke da buqatar a jinkirta sallar idin azumi; saboda su samu su bada ''zakatu alfixr".

Mas'ala ta biyar: Siffar sallar idi, da abinda ake karantawa a cikinta:
Siffarta: Raka'oi biyu ce, a gabanin huxuba; saboda faxin Umar -t-:
"صَلاةُ الْفِطْرِ والأَضْحَى رَكْعَتَانِ رَكْعَتَانِ، تَمَامٌ غَيْرُ قَصْرٍ، عَلَى لِسَانِ نَبِيِّكُمْ، وَقَدْ خَابَ مَنِ افْتَرَى"([3]).
Ma'ana: (Sallar idin azumi dana layyah raka'oi bibbiyu ne, a cike suke, ba qasaru ba, wannan ya zo a harshen annabinku. Haqiqa wanda yayi qirqira ya tave).
Bawa a raka'arsa ta farko -bayan yayi kabbarar farko da ake buxe sallar da ita, gabanin kuma yayi ''a'uzu billahi, bismillahi sannan ya karanta fatiha''- zai yi kabbarori guda shida, a raka'a ta biyu kuma gabanin ya fara karatu zai yi kabbara guda biyar qari akan kabbarar tasowansa; saboda hadisin A'ishah - رضي الله عنها-, daga Annabi (r) yace:
"التكبير فِي الْفِطْرِ وَالأَضْحَى فِي الأُولَى سَبْعَ تَكْبِيرَاتٍ، وَفِي الثَّانِيَةِ خَمْس تَكْبِيرَاتٍ، سِوَى تَكْبِيرَتَيِ الرُّكُوع"([4]).
Ma'ana: (Kabbarori a idin azumi dana lahiyah, a raka'ar fako kabbarori ne guda bakwai, a raka'a ta biyu kuma kabbarori guda biyar; qari akan kabbarori guda biyu na tafiya zuwa ruku'i). Kuma zai xaga hannayensa biyu tare da kowace kabbara; saboda Annabi (r):
"كان يَرْفَعُ يَدَيْهِ مَعَ التَّكْبِيرِ"([5]).
Ma'ana: (Ya kasance yana xaga hannayensa biyu tare da kabbara).
Sa'annan sai ya yi karatu a bayyane –ba tare da wani savani ba a tsakanin maluma-, bayan ya yi ''isti'aza''; yana mai karanta ''fatihah'' a raka'ar farko da kuma ''sabbih isma rabbika al-a'alah'' a raka'a ta biyu kuma ''hal ataka hadisu algashiyah"; saboda faxin Samurah -t-:
"كَانَ r يَقْرَأُ فِي الْعِيدَيْنِ الأعلى: ١ ، وَ الغاشية: ١ "([6]).
Ma'ana: (Annabi –r- ya kasance yana karanta ''sabbih isma rabbika al-a'alah'' da kuma ''Hal ataka hadisu algashiyah'').
Kuma ya inganta cewa Annabi (r) ya kasance a raka'ar farko yana karanta:
ﭑﭒ ق: ١
A raka'a ta biyu kuma ya karanta:
القمر: ١ ([7]).
A nan ana son limami ya kula; sai ya riqa karanta wannan a wannan karon, wancan kuma a wani lokacin na daban, yana mai aiki da sunna, tare kuma da kula da yanayin masu sallah; sai ya karanta abinda zai fiye musu sauqi.

Mas'ala ta shida: Yaushe ake yin huxuba?
Ana yin huxubar sallar idi bayan an idar da sallar; saboda faxin Abdullahi xan Umar -t- cewa:
"كَانَ النبي r، وَأَبُو بَكْرٍ وَعُمَرُ يُصَلُّونَ العِيدَيْنِ قَبْلَ الخُطْبَةِ"([8]).
Ma'ana: (Annabi –r-  da Abubakar da Umar sun kasance suna sallar idin azumi dana lahiya, a gabanin huxuba).

Mas'ala ta bakwai: Shin ana rama sallar idi?
     Ba a sunnata rama idi ga wanda ta kuvuce masa ba; saboda ba wani dalili daga Annabi (r) kan hakan. Kuma saboda kasancewar sallar idi sallah ce da ake yinta a cikin jama'a; akan haka; ba a shar'anta ta ba sai ta wannan fiskar.

Mas'ala ta takwas: Sunnonin idi:
1-     An sunnata yin sallar idi a wuri na zahiri mai faxi, a wajen gari; Musulmai za su haxu a wannan wajen saboda bayyanar da wannan ''sha'irar'', Amma idan da wani uzuri da ya hana hakan; sai aka sallace ta a cikin masallatai to babu laifi.
2-     An sunnata gaggauta idin laiyah, da kuma jinkirta sallar idin azumi, kamar yadda bayani ya gabata akan haka, a inda muka yi bayani kan ''lokacin yinta''.
3-     An sunnata musulmi ya ci dibino gabanin ya fita zuwa idin azumi, kada kuma ya ci komai ranar idin lahiya har sai ya dawo daga sallah; saboda haka Annabi (r) ya aikata; ta yadda dabi'arsa ce a wannan yini; baya fita zuwa idin azumi har sai ya karya da dibinai da ya ke cin su wutri([9]) (uku, biyar, bakwai). Baya kuma cin komai a ranar idin lahiya har sai bayan sallah([10]).
4-     An sunnata sammako wajen fita idi, bayan sallar asubah, sannan kuma ya fita yana mai tafiya da qafa; domin ya samu damar kusantar liman, kana kuma ya samu falalar jiran sallah.
5-     An sunnata wa musulmi ya cava ado, bayan ya yi wanka, sannan kuma ya sanya mafi kyawun tufa, tare da shasshafa tirare.
6-     Kuma an sunnata liman ya yi huxubar idi huxuba gamemmiya da ta qunshi al'amuran addini gabaxaya, yana mai kwaxaitar da su kan zakkar fidda-kai; tare da bayyana musu abinda zasu fitar. Idan kuma idin laiyah ne; liman ya kwaxaitar da mutane kan yin layyar, tare da bayyana musu hukunce-hukuncenta.
Ana so suma mata su zama suna da rabo daga huxubar; saboda suna da buqatuwa zuwa ga hakan, tare da cewa aikata hakan koyi ne da Annabi (r), saboda hadisi ya zo cewa ma'aikin Allah bayan ya idar da sallah da huxuba a wajen maza, ya zo ya yi huxuba ta musamman ga mata; ya musu wa'azi ya tunatar da su([11]).
Huxubar kuma akan yita ne bayan idar da sallah, kamar yadda bayanin haka ya gabata.
7-     An sunnanta yawaita ambaton Allah; (Allahu akbar, la'ila illa Allahu); saboda faxinsa maxaukaki:
البقرة: ١٨٥
Ma'ana: (Kuma domin ku cika qixaya, kuma ku girmama Allah –da yi masa kabbara- saboda shiryar da ku da ya yi) [Baqarah: 185]. Mazaje sunna ne su xaga muryoyinsu da kabbarori, sawa'un a cikin gidaje ne ko a masallatai, ko a kasuwanni, su kuma mata an so su asirta hakan.
8-     Banbanta hanya; an so ya tafi idin ta wata hanya, ya komo ta wata hanyar ta daban; saboda hadisin Jabir -t-, yace:
"كَانَ النَّبِيُّ r إِذَا كَانَ يَوْمُ عِيدٍ خَالَفَ الطَّرِيق"([12]).
Ma'ana: (Annabi –r- ya kasance idan ranar idi ta zo ya kan sava hanya). Maluma sun yi bayani kan hikimar aikata haka, inda suka ce: akan yi hakan ne domin hanyoyin biyu su yi shaida wa mutum. Wassu kuma suka ce: saboda a bayyanar da alamomin Musulunci a dukkan hanyoyin (sha'a'ir). wassu kuma sun faxi wassu hikimomin banda wannan.
Kuma ba laifi cikin gaisuwar sallah ga mutane a ranar idi; kamar mutum ya faxa wa waninsa: Allah shi karva mana kyawawan aiyuka:
(تَقَبَّلَ اللَّهُ مِنَّا وَمِنْكَ صالح الأعمال).
Kuma sahabban Annabi (r) sun kasance suna aikata hakan. Tare da bayyanar da bushasha da farin-ciki ga duk wanda aka haxu da shi.



([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 956), da Muslim (lamba: 889)
([2]) Duba littafin (almugniy, 2/ 232-233)
([3]) Ahmad ya ruwaito shi (1/37), da An-nasa'iy (1/232), da Albaihaqiy (3/200), hadisi ne ingantacce, duba: (Irwa'u algalil, 3/106)
([4]) Abu-dawud ya ruwaito shi (lamba: 1149), hadisi ne ingantacce (duba: Irwa'u algalil, 3/286)
([5]) Ahmad ya ruwaito shi (4/316), Albaniy yace hadisi ne hasan (Irwa'ul galil, lamba:  641)
([6]) Ahmad ya ruwaito shi (5/7), da Ibnu-majah (lamba: 1283), Albaniy ya inganta shi, (Irwa'ul galil, lamba: 644)
([7]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 891)
([8]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 963), da Muslim (lamba:  888)
([9]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 953)
([10]) At-tirmiziy ya ruwaito shi (lamba: 542), da Ibnu-majah (lamba:  1756), Albaniy ya inganta shi (Sahihu Ibni-majah,  lamba: 1422)
([11]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 978)
([12]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 986).  

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...