HUKUNCIN YIN HARAMA DA HAJJI A RANAR TAKWAS GA
WATAN ZUL-HIJJAH (08/12), DA KUMA FITA ZUWA MINAH
Idan ranar "tarwiyah" ta zo, wadda itace ranar
takwas ga zul-hijjah (08/12) mustahabbi ne ga waxanda
suka kammala umrarsu kana suka warware; suke kuma zaune a garin Makkah, da kuma
mazauna garin Makkah na asali waxanda
suka nufi yin aikin hajji, mustahabbi ne akan waxannan
gabaxaya su yi harama da aikin hajji daga wuraren zamansu
(gidajensu, ko masauqansu), saboda sahabban Annabi (r) sun riqi
wurin da ake kiransa AL-ABXAH a matsayin masauqi,
kuma yayin da yinin tarwiyah ya zo sai suka qulla
niyyarsu daga wannan wurin, sakamakon umurnin da Annabi (r) ya yi a
gare su, kuma lallai bai umurce su da cewa su je jikin xakin
ka'abah don su yi niyyarsu daga can, ko kuma daga gindin indaroro ba, haka kuma
bai umurce su da yin xawafin bankwana a yayin fitansu zuwa minah ba, kuma da aikata
hakan shari'a ne to da Annabi ya koya musu shi, kuma dukkan alheri yana cikin
koyi da Annabi (r)
da sahabbansa (y).
Kuma mustahabbi ne mahajjaci ya yi wanka ya kuma tsaftata,
kana ya shafa turare a lokacin haramarsa na aikin hajji, kamar yadda ya aikata
hakan lokacin haramarsa a can miqaati.
Bayan mahajjata sun riga sun qulla
haramarsu ta hajji sunnah ne a gare su, su fiskanci minah gabanin rana ta yi
zawali ko bayan haka, a wannan yinin na takwas (tarwiyah), suna masu yawaita
yin talbiyyah, har zuwa ranar da za su yi jifan "aqabah"
(ranar goma ga watan 12), Sai kuma su yi sallar azahar da la'asar da magriba da
isha'i da asuba (a ranar 08, a
minah). Kuma sunnah shine su sallaci kowacce a lokacinta, qasaru
(ga sallah mai raka'oi guda huxu), ba tare da sun
haxe salloli guda biyu a lokaci xaya
ba (kamar azahar da la'asar, ko magriba da isha'i), Saidai sallar magriba da
asuba su kam ba a yi musu qasaru.
Kuma babu banbanci tsakanin mutanen garin Makkah na asali da
wassunsu, saboda Annabi (r)
ya yi qasarun sallah da mutanen Makkah na asali da wassunsu, a minah
da arafah da muzdalifah, kuma bai umurci mutanen Makkah na asali da cewa su
cika sallah ba, kuma da cika sallar wajibi ne akansu da ya bayyana musu.
Sannan bayan fudowar rana a yinin arafah mahajjaci zai nufi
filin arafah daga minah, kuma sunnah ne mahajjata su fara sauka a filin namirah
(da yake iyaka da filin arafah) har zuwa rana ta yi zawali, gabanin su shiga
cikin filin arafah, idan hakan ya sauqaqa
a gare su, saboda Annabi (r)
ya aikata hakan.
Idan rana ta yi zawali sunnah ne ga limami ko na'ibinsa ya yi
huxuba ga mutane; huxubar
da ta dace da halin da ake ciki, yana mai bayyana wa mahajjata aiyukan da aka
shar'anta musu aikata su a wannan yinin, da kuma kwanakin da suke bayansa, ya
kuma umurce su a cikinta da taqawar
Allah da tauhidinsa, da yi masa ikhlasi (tsantsanta ibada a gare shi, shi kaxai)
a cikin dukkan aiyuka, ya kuma hane su aikata abubuwan da Allah ya haramta
musu, an so ya yi musu wasiyya a cikinta da cewa su yi riqo
da littafin Allah (alqur'ani) da kuma sunnar Annabi (r) da yin
hukunci da su, tare da neman hukuncinsu cikin dukkan lammura, suna masu koyi da
Annabi (r)
cikin wannan dukkansa. Bayan kamala yin huxuba
kuma sai su sallaci azahar da la'asar, qasaru
(raka'a bibbiyu), tare da haxe su
(aikata su) a lokacin sallar farko (azahar), da kiran sallah guda xaya,
tare da yin iqamah guda biyu, saboda haka Annabi (r) ya
aikata, kamar yadda Imam Muslim ya ruwaito hakan a cikin hadisin Jabir (ra) mai
tsayi([1]).
Daga nan, sai mutane su tsaya a arafah, kuma filin arafah
dukkansa wurin tsayuwa ne in banda wurin da ake kiransa BAXANU
URANAH. Kuma mustahabbi ne mahajjaci ya fiskanci alqiblah
tare da dutsen da ake kiransa JABALUR RAHMAH idan hakan ya sauqaqa
masa, idan kuma hakan bai sauwaqa
ba to sai ya fiskanci alqiblar
kawai, koda kuwa bai fiskanci dutsen ba.
Kuma mustahabbi ne ga mahajjaci a wannan matsaya (arafah) ya
yi iya qoqarinsa wajen ambaton Allah (سبحانه وتعالى) da roqonsa, tare kuma da kankan-da-kai a gare shi, kuma zai xaga
hannayensa biyu a yayin addu'a, kuma idan da zai yi talbiyyah ko ya karanta
wani abu na alqur'ani a wannan yinin to hakan ya yi kyau, an kuma sunnanta masa yawaita faxin:
LA ILAHA ILLAL
LAHU WAHDAHU LA SHARIKA
LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU YUHYIY WA YUMIYTU WA HUWA ALA
KULLI SHAI'IN QADIIR, saboda abun da aka ruwaito daga Annabi (r) cewa:
«خَيْرُ الدُّعَاءِ دُعَاءُ يَوْمِ
عَرَفَةَ، وَخَيْرُ مَا قُلْتُ أَنَا وَالنَّبِيُّونَ مِنْ قَبْلِي: لاَ إِلَهَ
إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ وَهُوَ
عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ».
Ma'ana: "Mafi alherin
addu'a shine addu'an yinin arafah, kuma mafi alherin abinda na faxa ni da
annabawa a gabanina shine: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL
MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR"([2]), Kuma ya inganta daga gare shi (r) lallai
ya ce:
«أَحَبُّ الْكَلَامِ إِلَى اللهِ
أَرْبَعٌ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ،
وَاللهُ أَكْبَر».
Ma'ana: "Mafi
soyuwan magana a wajen Allah guda huxu ne;
SUBHANAL LAHI, WAL HAMDU LIL LAHI, WA LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR"([3]).
Don haka; Yana da kyau
a yawaita faxin wannan zikirin tare da maimaita shi cikin nitsuwar zuci,
da halarto da tunani. Kuma ya dace (ga mahajjaci) ya yawaita yin sauran
zikirori da addu'oin da suka zo a shari'a cewa ana yinsu a kowani lokaci,
musamman kuma a wannan bagire da wannan yini mai girma; wato yinin arafah, kuma
yana da kyau mutum ya zavi
gamemmu daga cikin addu'oi da zikirori, Daga cikinsu:
سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ،
سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيم، ﭽ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ
سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ ﭼ الأنبياء: 87
SUBHANAL LAHI WABI HAMDIH, SUBHANAL LAHIL AZIIM. LA ILAHA ILLA ANTA
SUBHANAKA INNIY KUNTU MINAZ ZALIMINA.
Ma'ana:
"Tsarki
ya tabbata ga Allah, kuma godiya tasa ce, tsarki ya tabbata ga Allah mai girma.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, tsarki ya tabbata maka, lallai ni na
kasance daga cikin azzalumai".
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَلَا
نَعْبُدُ إِلَّا إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ، وَلَهُ الْفَضْلُ، وَلَهُ الثَّنَاءُ
الْحَسَنُ، لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ
الْكَافِرُونَ».
Ma'ana: "Babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah, kuma bama bauta ga wani sai kai, ni'ima tasa ce, kuma falala tasa ce,
kuma yabo mai kyau nasa ne, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna masu
tsarkake masa addini, koda kafirai sun qi".
«لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا
بِاللَّهِ».
Bawa bashi da dabarar barin savo,
bashi da qarfin iya biyayya ga Allah, sai ya samu taimakon Allah.
ﭽ ﯜ
ﯝ ﯞ ﯟ
ﯠ ﯡ ﯢ
ﯣ ﯤ ﯥ
ﯦ ﭼ البقرة: ٢٠١
RABBANA ATINA FID-DUNYAH HASANATAN ,
WA FIL AKHIRATI HASANATAN , WA
QINA
AZABAN NAARI.
Ma'ana:
"Ya
Ubangijinmu ka bamu abu mai kyau a duniya, a lahirama
mai kyau, ka kare mu daga azabar wuta".
«اللهُمَّ أَصْلِحْ لِي دِينِي الَّذِي
هُوَ عِصْمَةُ أَمْرِي، وَأَصْلِحْ لِي دُنْيَايَ الَّتِي فِيهَا مَعَاشِي،
وَأَصْلِحْ لِي آخِرَتِي الَّتِي فِيهَا مَعَادِي، وَاجْعَلِ الْحَيَاةَ زِيَادَةً
لِي فِي كُلِّ خَيْرٍ، وَاجْعَلِ الْمَوْتَ رَاحَةً لِي مِنْ كُلِّ شَرٍّ».
ALLAHUMMA AS-LIH LIY
DIYNIY AL-LAZIY HUWA ISMATU AMRIY, WA ASLIH LIY DUNYAY AL-LATIY FIYHA MA'ASHIY,
WA ASLIH LIY AKHIRATIY AL-LATIY FIYHA MA'ADIY, WAJ'ALIL HAYATA ZIYADATAN LIY
FIY KULLI KHAIR, WAJ'ALIL MAUTA RAHATAN LIY MIN KULLI SHARR.
Ma'ana: "Ya Allah ka gyara min addinina
wanda shine gyaran lamarina, ka kuma gyara mini duniyata wacce a cikinta
rayuwata ta ke, ka kuma gyara min lahirata wacce zuwa gare ta makomata ta ke,
ka sanya rayuwa ta zama qaruwa ce a gare ni cikin dukkan
alheri, mutuwa kuma ta zamto hutu daga aikata dukkan sharri".
أَعُوذُ بِاللَّه «مِنْ
جَهْدِ الْبَلَاءِ، وَدَرَكِ الشَّقَاءِ، وَسُوءِ الْقَضَاءِ، وَشَمَاتَةِ
الْأَعْدَاءِ».
A'UZU BILLAHI MIN JAHDIL
BALA'I, WA DARAKISH SHAQA'I, WA
SUW'IL QADA'I, WA SHAMATATIL A'ADA'I.
Ma'ana: "Ina neman tsarin Allah kan
wahalhalun bala'i, da kuma kan riskar wahala, da mummunar qaddara,
da dariyar qeta daga maqiya".
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ
الْهَمِّ وَالْحَزَنِ، وَالْعَجْزِ وَالْكَسَلِ، وَالْجُبْنِ وَالْبُخْلِ، ومِنَ
الْمَأْثَمِ وَالْمَغْرَم، وَمِن ضَلَعِ الدَّيْنِ وَقَهْرِ الرِّجَالِ. اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْبَرَصِ
وَالْجُنُونِ وَالْجُذَامِ وَسَيِّءِ الأَسْقَام».
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZAN,
WAL AJZI WAL KASLI, WAL JUBNI WAL BUKHLI, WA DALA'ID DAINI, WA GALABATIR
RIJAALI.
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MINAL BARASI, WAL
JUNUNI, WAL JUZAAMI , WA SAYYI'IL ASQAAMI.
Ma'ana:
"Ya
Allah lallai ni ina neman tsarinka daga baqin ciki, da gajiyawa da
kasala, da tsoro da rowa, da kuma savo, da bashi, da kuma
nauyinsa (bashi), da rinjayen mazaje. Ya
Allah ka tsare ni daga ciyon kuturta, da hauka, da kuturta mai yanke yatsu, da
kuma munanan cutuka".
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ، فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL AFWA WAL AFIYAH, FID
DUNYA WAL AKHIRAH.
Ma'ana: "Ya Allah ina roqonka
afuwa da lafiya, a duniya da lahira".
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الْعَفْوَ وَالْعَافِيَةَ فِي دِينِي وَدُنْيَايَ وَأَهْلِي وَمَالِي».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL
AFWA WAL AFIYAH, FIY DIYNIY, WA DUNYAY, WA AHLIY, WA MALIY.
Ma'ana: "Ya Allah lallai ni ina roqonka
afuwa da lafiya, a addinina da duniyata da iyalaina da dukiyata".
«اللَّهُمَّ اسْتُرْ عَوْرَاتِي،
وَآمِنْ رَوْعَاتِي، اللَّهُمَّ احْفَظْنِي مِنْ بَيْنِ يَدَيَّ، وَمِنْ خَلْفِي،
وَعَنْ يَمِينِي، وَعَنْ شِمَالِي، وَمِنْ فَوْقِي، وَأَعُوذُ _ بِعَظَمَتِكَ _
أَنْ أُغْتَالَ مِنْ تَحْتِي».
ALLAHUMMA US-TUR AURAATIY, WA
AAMIN RAU'AATIY, ALLAHUMMA IHFAZNIY MIN BAINI YADAYYA WA MIN KHALFIY, WA AN
YAMIYNIY, WA AN SHIMALIY, WA MIN FAUQIY,
WA A'UZU –BI AZAMATIKA- AN UGTALA MIN TAHTIY.
Ma'ana: "Ya Allah ka suturce min
al'aurata, ka amintar da tsorona, Ya Allah ka bani kariya ta gaba gare ni da
kuma ta bayana, da ta damana da ta hagun xina, da
ta samana, kuma ina neman tsari –da girman Allah- kar a halaka ni ta qasana
(kamun qasa ko makamancin haka)".
«اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي خَطِيئَتِي
وَجَهْلِي، وَإِسْرَافِي فِي أَمْرِي، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي».
ALLAHUMMA IGFIR LIY KHAXIY'ATIY
WA JAHLIY , WA ISRAFIY FIY AMRIY, WAMA ANTA A'ALAMU BIHI
MINNIY.
Ma'ana: "Ya Allah ka gafarta mini
kurakuraina da jahilcina, da wuce iyakata a cikin lamura, da abinda kaine mafi
saninsa fiye da ni".
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي جِدّي وَهَزْلِي،
وخَطَئِي وَعَمْدِي، وَكُلُّ ذَلِكَ عِنْدِي.
ALLAHUMMA IGFIR LIY JIDDIY ,
WA HAZLIY , WA KHAXA'IY WA AMDIY , WA
KULLU ZALIKA INDIY.
Ma'ana:
"Ya
Allah ka gafarta min gaskena da wargina, da kuskurena da gangancina, saboda
akwai dukkan hakan daga wajena".
"اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ
وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ وَمَا أَعْلَنْتُ، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ
مِنِّي، أَنْتَ الْمُقَدِّمُ وَأَنْتَ الْمُؤَخِّرُ، وَأَنْتَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ".
ALLAHUMMA IGFIR LIY MA QADDAMTU
WAMA AKKHARTU, WAMA ASRARTU WAMA A'ALANTU, WAMA ANTA A'ALAMU BIHI MINNIY, ANTAL
MUQADDIMU WA ANTAL MU'AKKHIRU, WA ANTA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
Ma'ana: "Ya Allah ka gafarta mini abinda
na gabatar, da abinda na jinkirtar, da abinda na asirta (voye) da
abinda na bayyanar, da kuma abinda kaine mafi saninsa fiye da ni, kai ne mai
gabatarwa, kai ne kuma mai jinkirtarwa, kuma kai mai iko ne akan komai".
"اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ
الثَّبَاتَ فِي الْأَمْرِ، وَالْعَزِيمَةَ عَلَى الرُّشْدِ، وَأَسْأَلُكَ شُكْرَ
نِعْمَتِكَ، وَحُسْنَ عِبَادَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ قَلْبًا سَلِيمًا، وَلِسَانًا
صَادِقًا. وَأَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا تَعْلَمُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا
تَعْلَمُ، وَأَسْتَغْفِرُكَ لِمَا تَعْلَم، وَأَنْتَ عَلَّامُ الْغُيُوبِ".
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAS
SABATA FIL AMRI, WAL AZIYMATA ALAR RUSHDI, WA AS'ALUKA SHUKRA NI'IMATIKA, WA
HUSNA IBADATIKA, WA AS'ALUKA QALBAN SALIYMAN, WA
LISANAN SADIQAN, WA AS'ALUKA MIN KHAIRI MA TA'ALAMU, WA A'UZU BIKA MIN
SHARRI MA TA'ALAMU, WA ASTAGFIRUKA LIMA TA'ALAMU, WA ANTA ALLAMUL GUYUUB".
Ma'ana: "Ya Allah lallai ina roqonka
tabbatuwa cikin addini, da azama akan shiriya, Ina kuma roqonka
godiya ga ni'imominka, da kyautata
bauta a gare ka, kuma ina roqon ka
bani zuciya kuvutacciya, da harshe mai gaskiya, Ina kuma roqonka
alherin abinda ka sani, ina neman tsarinka daga sharrin da ka riga ka sani, ina
kuma neman gafararka daga abinda ka sani, kuma kai ne masanin abubuwan da suke
fake (voye, na gaibu)".
اللَّهُمَّ رَبَّ النَّبِيِّ
مُحَمَّدٍ عليه الصلاة والسلام اغْفِرْ لِي ذَنْبِي، وَأَذْهِبْ غَيْظَ قَلْبِي،
وَأَجِرْنِي مِنْ مُضِلاَّتِ الْفِتَنِ مَا أَبْقَيْتَنِي.
ALLAHUMMA RABBAN NABIYYI
MUHAMMADIN (ALAIHIS SALATU WAS SALAM), IGFIRLIY ZANBIY ,
WA AZHIB GAIZA QALBIY , WA AJIRNIY MIN
MUDILLATIL FITANI MA ABQAITANIY.
Ma'ana: "Ya Allah Ubangijin annabi
(Muhammadu) tsira da amincin Allah su qara
tabbata a gare shi, ka gafarta mini zunubina, ka tafiyar da baqin cikin
zuciyata, ka kare ni daga fitintinu masu batarwa tsawon lokacin da ka wanzar da
ni (a raye)".
اللَّهُمَّ رَبَّ السَّماوَاتِ
السَّبْعِ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، رَبَّنَا وَرَبَّ كُلِّ شَيْءٍ،
مُنْزِلَ التَّوْرَاةِ وَالإِنْجِيلِ وَالْقُرْآنِ، فَالِقَ الْحَبِّ وَالنَّوَى،
لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ شَيْءٍ أَنْتَ آخِذٌ
بِنَاصِيَتِهِ، أَنْتَ الأَوَّلُ لَيْسَ قَبْلَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الآخِرُ لَيْسَ
بَعْدَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ الظَّاهِرُ لَيْسَ فَوْقَكَ شَيْءٌ، وَأَنْتَ
الْبَاطِنُ لَيْسَ دُونَكَ شَيْءٌ، اقْضِ عَنَّا الدَّيْنَ، وَأَغْنِنَا مِنَ
الْفَقْر.
ALLAHUMMA RABBAS SAMAWATIS
SABA'I, WA RABBAL ARSHIL AZIIM, RABBANA WA RABBA KULLI SHAI'IN, MUNZILAT
TAURATI WAL INJILI WAL QUR'ANI,
FALIQAL HABBI WAN NAWAH, LA ILAHA ILLA ANTA, A'UZU BIKA MIN SHARRI KULLI
SHAI'IN ANTA AAKHIZUN BI NASIYATIHI, ANTAL AUWALU FA LAISA QABLAKA
SHAI'UN, WA ANTAL AAKHIRU FA LAISA BA'ADAKA SHAI'UN, WA ANTAZ ZAHIRU FA LAISA
FAUQAKA SHAI'UN, WA ANTAL BAXINU
FA LAISA DUNAKA SHAI'UN, IQDI ANNA
AD-DAINA WA AGNINA MINAL FAQRI.
Ma'ana: "Ya Allah Ubangijin sammai guda
bakwai, ubangijin al'arshi mai girma, Ubangijinmu kuma Ubangijin komai da kowa,
wanda ya sauqar da littafin attaurah da injilah da alqur'ani,
kai ka qagi halittar kwayan tsirrai da kwallonsu, Ina neman tsarinka
daga dukkan sharri wanda kai ne ka ke riqe da maqyamqyamarsa,
Ya Allah kai ne farko; babu wani abu gabaninka, kuma kai ne qarshe;
babu wani abu a bayanka, kai ne maxaukaki;
babu wani abu a samanka, kai ne kuma iliminka ya game; babu wani abu da ya fice
daga iliminka, (ya Allah) ka biya mana bashin da yake kanmu, kuma ka wadatar da
mu daga talauci".
«اللَّهُمَّ ائْتِ نَفْسِي تَقْوَاهَا،
زَكِّهَا أَنْتَ خَيْرُ مَنْ زَكَّاهَا، أَنْتَ وَلِيُّهَا وَمَوْلَاهَا».
ALLAHUMMA ATI NAFSIY TAQ-WAHA,
ZAKKIHA ANTA KHAIRU MAN ZAKKAHA, ANTA WALIYYUHA WA MAULAHA.
Ma'ana: "Ya Allah ka bawa raina taqawarta,
ka tsarkake ta; saboda kaine mafi alherin wanda ya jivinceta
kuma masoyinta".
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ
الْعَجْزِ وَالْكَسَلِ ، وَالْجُبْنِ وَالْهَرَمِ ، وَالْبُخْلِ وَعَذَابِ
الْقَبْرِ».
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA
MINAL AJZI WAL KASALI, WAL JUBNI WAL HARAMI, WAL BUKHLI WA AZABIL QABRI".
Ma'ana" Ya Allah ina neman tsarinka daga
gajiyawa da kasala, da tsoro, da mummunan tsufa, da rowa da kuma azabar qabari".
«اللهُمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ، وَبِكَ
آمَنْتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خَاصَمْتُ،
اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِعِزَّتِكَ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْ تُضِلَّنِي،
أَنْتَ الْحَيُّ الَّذِي لَا يَمُوتُ، وَالْجِنُّ وَالْإِنْسُ يَمُوتُونَ».
ALLAHUMMA LAKA ASLAMTU, WA
BIKA AMANTU, WA ALAIKA TAWAKKALTU, WA ILAIKA ANABTU, WA BIKA KHASAMTU,
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BI IZZATIKA, LA ILAHA ILLA ANTA, AN TUDILLANIY, ANTAL HAYYU
ALLAZIY LA YAMUTU ,
WAL JINNU WAL INSU YAMUUTUUNA.
Ma'ana: "Ya Allah a gare ka kawai na miqa wuya,
kuma da kai ne kawai na yi imani, akanka kaxai na
dogara, zuwa gare ka na mayar da lamarina, don kai kawai na ke husuma, Ya Allah
lallai ina neman tsarinka da buwayarka, babu abin bautawa da gaskiya sai kai;
kada ka vatar da ni, kai ne rayayyen da baya mutuwa, da mutane da aljanu duk suna
mutuwa".
«اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ
عِلْمٍ لَا يَنْفَعُ، وَمِنْ قَلْبٍ لَا يَخْشَعُ، وَمِنْ نَفْسٍ لَا تَشْبَعُ،
وَمِنْ دَعْوَةٍ لَا يُسْتَجَابُ لَهَا».
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA
MIN ILMIN LA YANFA'U ,
WA MIN QALBIN LA
YAKH'SHA 'U, WA MIN NAFSIN LA TASHBA'U , WA MIN
DA'AWATIN LA
YUSTAJAABU LAHA.
Ma'ana: "Ya Allah lallai ina neman
tsarinka daga samun ilimin da bashi da amfani, da kuma zuciya da bata samun
kushu'i (tsoron Allah), da rai da ba ta koshi, da kuma addu'ar da ba a amsa
mata".
«اللَّهُمَّ جَنِّبْنِي مُنْكَرَاتِ
الْأَخْلَاقِ، وَالْأَهْوَاءِ، وَالْأَدْوَاءِ».
ALLAHUMMA JANNIBNIY
MUNKARATIL AKHLAQI, WAL AHWA'I, WAL ADWA'I.
Ma'ana: "Ya Allah ka nisantar da ni da
munanan halayya, da son zuciya, da cutuka".
«اللَّهُمَّ أَلْهِمْنِي رُشْدِي،
وَأَعِذْنِي مِنْ شَرِّ نَفْسِي».
ALLAHUMMA AL-HIMNIY RUSHDIY,
WA A'IZNIY MIN SHARRI NAFSIY.
Ma'ana: "Ya Allah ka min ilhamar
shiriyata, ka kuma kare ni daga sharrin kaina".
«اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلَالِكَ عَنْ
حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ».
ALLAHUMMA IKFINIY BI HALALIKA
AN HARAMIKA, WA AGNINIY BI FADLIKA AN MAN SIWAKA.
Ma'ana: "Ya Allah ka wadatar da ni da
halal xinka, ga barin haramiyarka, ka kuma wadatar da ni da
falalarka daga wanda ba kai ba".
«اللهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى
وَالتُّقَى وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL
HUDAH, WAT TUQAH, WAL AFAFA, WAL GINAH.
Ma'ana: "Ya Allah lallai ina roqonka
shiriya, da taqawa, da kamewa, da kuma wadaci".
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْهُدَى
وَالسَّدَاد».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL
HUDAH WAS SADAD.
Ma'ana: "Ya Allah ina roqonka da
ka bani shiriya da dacewa".
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنَ
الْخَيْرِ كُلِّهِ؛ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ
أَعْلَمْ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الشَّرِّ كُلِّهِ؛ عَاجِلِهِ وَآَجِلِهِ، مَا
عَلِمْتُ مِنْهُ، وَمَا لَمْ أَعْلَمْ. اللَّهُمَّ
إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنْ خَيْرِ مَا سَأَلَكَ عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ مُحَمَّدٌ صَلَّى
اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا استعَاذَ مِنْهُ
عَبْدُكَ وَنَبِيُّكَ مُحَمَّدٌ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَمَا
قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ النَّارِ وَمَا
قَرَّبَ إِلَيْهَا مِنْ قَوْلٍ أَوْ عَمَلٍ، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ
قَضَاءٍ تَقْضِيهِ لِي خَيْرًا».
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA
MINAL KHAIRI KULLIHI AJILIHI WA AJILIHI, MA ALIMTU MINHU WAMA LAM A'ALAM, WA
A'UZU BIKA MINASH SHARRI KULLIHI; AJILIHI WA AJILIHI, MA ALIMTU MINHU WAMA LAM
A'ALAM.
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA MIN
KHAIRI MA SA'ALAKA ABDUKA WA NABIYYUKA MUHAMMADUN (r), WA
A'UZU BIKA MIN SHARRI MA ISTA'AZA MINHU ABDUKA WA NABIYYUKA MUHAMMADUN (r).
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKAL
JANNATA WAMA QARRABA ILAIHA MIN QAULIN
AU AMALIN , WA A'UZU BIKA MINAN NAARI WAMA QARRABA
ILAIHA MIN QAULIN AU AMALIN. WA AS'ALUKA AN TAJ'ALA KULLA QADA'IN
QADAITAHU LIY KHAIRAH.
Ma'ana: "Ya Allah ina roqonka
alkhairi dukkansa; na gaggawa daga cikinsa da na nesa, wanda na sani daga ciki
da wanda ban sani ba. Ina kuma neman tsarinka sharri dukkansa; na gaggawa daga
cikinsa, da na nesa, wanda na sani daga ciki da wanda ban sani ba.
Ya Allah ina roqonka duk
abinda bawanka kuma annabinka Muhammadu (r) ya tava roqonka, Ina
kuma neman tsarinka daga abinda bawanka kuma annabinka Muhammadu (r) ya tava neman
tsarinka.
Ya Allah ina roqon
aljannah da duk abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko aiki, Ina kuma
neman tsarinka daga wuta da duk abinda yake kusantarwa zuwa gare ta na zance ko
aiki. Kuma ina roqon da ka sanya dukkan abinda ka qaddara
min ya zamto alkhairi a gare ni.
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ
لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ
حَيٌّ لَا يَمُوتُ، بِيَدِهِ الْخَيْرُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِير. سُبْحَانَ
اللَّهِ، والْحَمْدُ لِلَّهِ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ، وَلَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ
إِلَّا بِاللَّهِ العلي العظيم».
SUBHANAL LAHI, WAL HAMDU LILLAHI, WAL LAHU AKBAR, WALA HAULA WALA QUWWATA
ILLA BIL LAHIL AL' ALIYYUL AZIIM.
Ma'ana:
"Babu wanda ya cancanci ayi masa bauta sai Allah; shi kaxai ya
ke; bashi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya itama tasa ce, yana rayarwa
kuma yana kashewa, shi kuma rayayye ne da baya mutuwa, a hannunsa alheri ya ke,
kuma lallai shi mai iko ne akan komai. Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya itama
ta Allah ce, Allah
shine mafi girma, babu dabara babu qarfi (ga bawa), sai in ya haxa da Allah".
«اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ
وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وعَلَى آلِ
إِبْرَاهِيمَ، فِي الْعَالَمِين إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَـارِكْ
عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وعَلَى
آلِ إِبْرَاهِيمَ، فِي الْعَالَمِين إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيد».
"ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WA ALA ALI MUHAMMADIN, KAMA
SALLAITA ALA AALI IBRAHIMA WA ALA AALI IBRAHIMA FIL AALAMINA INNAKA HAMIDUN
MAJIID.
ALLAHUMMA BARIK ALA
MUHAMMADIN WA ALA AALI MUHAMMADIN, KAMA BARAKTA ALA IBRAHIMA WA ALA AALI
IBRAHIMA FIL AALAMINA INNAKA HAMIDUN MAJIID".
Ma'ana: "Ya Allah ka yi qarin
salati ga annabi Muhammad, da iyalan annabi Muhammad, kamar yadda ka yi salati
ga annabi Ibrahima da kuma iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin halittu Abun
yabo ne Mai girma. Ya Allah ka yi qarin
albarka ga annabi Muhammadu, da iyalan annabi Muhammad, kamar yadda ka yi
albarka wa annabi Ibrahima da kuma iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin
halittu Abun yabo ne Mai girma".
ﭽ ﯜ
ﯝ ﯞ ﯟ
ﯠ ﯡ ﯢ
ﯣ ﯤ ﯥ
ﯦ ﭼ البقرة: ٢٠١
RABBANA ATINA FID DUNYAH HASANATAN , WA FIL
AKHIRATI HASANATAN , WA QINA
AZABAN NAAR.
Ma'ana: "Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a
duniya, a lahirama mai kyau, ka kuma kare mu daga azabar wuta".
Kuma mustahabbi ne a wannan matsaya mai girma (filin arafah)
mahajjaci ya yi ta maimaita abinda ya gabata na zikirori da addu'oi, da kuma
makamantan haka waxanda su ke xauke da
irin ma'anoninsu, tare da yawaita yin salati ga Annabin rahama (r), kuma an
so mahajjaci ya yi ta naci wajen addu'a da dogewa akan naciyar, yana mai roqon
Ubangijinsa alherin duniya da kuma na lahira.
Kuma Annabi (r)
ya kasance idan yana roqon Allah
ya kan
maimaita buqatarsa har sau uku, don haka; ya dace a yi koyi da shi akan
haka.
Ana so musulmi a wannan matsaya (filin arafah) ya qanqantar
da kansa ga Ubangijinsa, yana mai yi masa tawali'u, tare da nuna karayar zuci a
gaba gare shi, da kuma qaunar
samun rahamar Allah da gafararsa, tare da jin tsoron faxawa
cikin azabar Allah da fushinsa, yana mai yin hisabi wa kansa, tare da jaddada
tubansa lafiyayya, saboda wannan yini (na arafah) yini ne mai girma, cikin kuma
taro babba, wanda Allah yake yin kyauta
a cikinsa ga bayinsa, ya kuma yi alfahari da su ga mala'ikunsa, tare da yawaita
'yanta su a cikinsa daga wuta, kuma ba a tava
ganin shexan a cikin wani yini da aka fi nisantar da shi daga rahamar
Allah, yana kuma wanda ya fi qaranci
da qanqanta fiye da yinin arafah, in banda yinin da aka yi yaqin
badar a cikinsa, wannan kuma ya kan kasance ne saboda abinda shexan
ya ke gani na kyautayin Allah ga bayinsa da kyautatawarsa
a gare su, da yadda ya ke yawaita 'yanta su daga wuta a cikinsa yana mai gafarta
musu.
Ya zo a cikin littafin sahihu Muslim, daga A'ishah (رضي الله عنها) lallai Annabi (r) ya ce:
«مَا مِنْ يَوْمٍ أَكْثَرَ مِنْ أَنْ
يُعْتِقَ اللَّهُ فِيهِ عَبْدًا مِنَ النَّارِ مِنْ يَوْمِ عَرَفَةَ، وَإِنَّهُ
لَيَدْنُو ثُمَّ يُبَاهِى بِهِمُ الْمَلاَئِكَةَ فَيَقُولُ: مَا أَرَادَ هَؤُلاَءِ؟».
Ma'ana: "Babu
wani yini wanda Allah ya fi 'yanta bayi a cikinsa daga wuta fiye da yinin
arafah, kuma lallai Allah yana kusantowa, sannan sai ya yi alfahari da su ga Mala'ikunsa,
sai ya ce: Me waxannan su ka nufa?"
([4]).
Akan haka; ya dace ga
musulmai su nuna wa Allah alherin da yake cikin zukatansu, su kuma wulaqanta
maqiyinsa shexan, suna
masu baqanta masa rai; ta hanyar yawaita ambaton Allah da kuma
yawaita addu'oi, da tuba zuwa gare shi, tare da neman gafararsa daga dukkan
zunubai.
Kuma mahajjata ba za su gushe
ba a wannan matsaya suna masu shagaltuwa da zikiri da addu'a tare da qanqan
da-kai, har zuwa lokacin da rana za ta faxi,
idan kuma ta riga ta faxin to sai
su tafi zuwa ga filin muzdalifah cikin nitsuwa da kwanciyar hankali, tare da
yawaita yin talbiyyah, da kuma yin sauri in an samu sararin yin hakan, saboda Annabi
(r)
ya aikata hakan.
Kuma baya halatta a tafi a
bar filin arafah gabanin faxuwar rana,
saboda Annabi (r)
ya tsaya ne, har zuwa faxuwarta, sannan kuma yace, na yi
haka ne:
«لتأخُذُوا مَنَاسِكَكُمْ».
Idan mahajjata suka sauka a filin muzdalifah sai su yi sallar
magriba a wannan wurin; raka'oi uku, ishah kuma raka'oi biyu (wato: qasaru),
suna masu aikata su a tare (jam'i), bayan yi musu kiran sallah guda xaya,
da kuma iqamah biyu, za su yi haka daga zarar isowarsu, saboda haka Annabi
(r)
ya aikata, kuma wannan hukuncin haka ya ke ba banbanci; sawa'un isowar tasu ta
kasance ne a lokacin sallar magriba, ko kuma a lokacin yin sallar ishah.
Kuma abinda wassu daga cikin gama-garin mutane (marasa ilimi)
suke aikatawa na tsintar tsakwankwani daga zarar isowarsu filin muzdalifah
gabanin su yi sallolinsu, da yadda da-dama daga cikinsu suke qudurta
cewa hakan shari'a ne = wannan aikin kuskure ne da bashi da wani asali ko
madogara a cikin addini, kuma Annabi (r) bai yi
umurni da a tsinta masa duwatsun da ya yi jifansa da su ba, har sai bayan ya
bar wurin da ya yi tsayuwarsa (mash'arul haraam), ya kuma xau
hanyarsa ta tafiya minah (wurin yin jifa, a safiyar yinin goma), kuma lallai
daga kowanni wuri mahajjaci ya tsunci duwatsunsa hakan ya isar masa; saboda ba
dole ne a tsince su daga filin muzdalifah ba, hasalima ya halatta a tsince su a
filin minah, kuma sunnah a wannan yinin itace a tsinci tsakwankwani guda bakwai
waxanda za a jefi "jamratul aqabah"
da su, saboda koyi da Annabi (r),
amma a sauran kwanaki ukun qarshe; su
kuma sunnah dangane da su ita ce mahajjaci ya tsunci duwatsu guda ashirin da xaya
(21), waxanda zai jefi wuraren jifa guda uku, a kullum da su.
Kuma baya cikin mustahabbai wanke duwatsun da za a yi jifa da
su, hasalima zai yi jifan da su ba tare da ya wanke su ba, saboda aikata hakan
(wankewar) ba a ruwaito shi daga Annabi (r) ko
sahabbansa ba, kuma ba zai yi jifa da dutsen da aka riga aka yi jifa da shi ba.
Kuma a daren goma (10) mahajjaci zai kwana ne a filin
muzdalifah, saidai kuma ya halatta ga masu rauni daga cikin mata da yara da
kuma makamantansu, su garzaya zuwa minah a qarshen
wannan daren, saboda hadisin A'ishah da ummu-salamah (رضي الله عنهما) da wassu sahabban na daban. Amma duk mutumin da ba waxannan
da aka ambata ba to dole ne a kansu su ci gaba da zama a muzdalifah har sai sun
yi sallar asubahi, sannan bayan haka sai su yi tsayuwan da ake yi a mash'arul
haraam, su fiskanci alqiblah suna masu ambaton Allah da girmama shi, da yawaita roqonsa,
har sai gari ya yi haske sosai (ya washe).
Kuma yana cikin mustahabbai mahajjaci ya xaga
hannayensa a wannan wuri yayin addu'arsa, kuma a duk wurin da mahajjata suka yi
tsayuwansu na muzdalifah (matuqar dai a cikin
kewayensa mutum ya tsaya) to hakan ya isar musu. Wannan kuma saboda ba wajibi
ba ne akansu kusantar masallacin mash'arul haraam, haka kuma hawa kan dutse a wurin,
saboda fadin Annabi (r):
«وَقَفْتُ هَاهُنَا _ يعني: على المشعر _، وَجَمْعٌ كُلُّهَا مَوْقِفٌ».
Ma'ana: "Ni na yi
tsayuwata a nan –yana nufin: akan mash'arul haraam- ita kuma muzdalifah
dukkanta wurin tsayawa ce" ([6]). Muslim ya ruwaito shi a cikin
littafinsa mai suna sahihi. Lafazin "jam'un" a cikin hadisin shine:
muzdalifah.
Idan gari ya waye duniya kuma ta washe; haske ya yi yawa
sosai, sai mahajjata su tafi zuwa ga minah, amma gabanin fudowar rana, suna
masu yawaita talbiyyah a cikin tafiyat ta su. Idan a hanyarsu suka iso wurin da
ake kiransa: muhassar to mustahabbi ne su qara
yin sauri kaxan.
Idan kuma suka iso minah to sai su yanke faxin
talbiyyah a jikin "jamratul aqabah",
sannan kuma sai su yi jifansu daga lokacin da suka iso da tsakwankwani guda
bakwai; xaya bayan xaya,
mahajjaci zai kuma daga hannunsa a lokacin jefa kowanne dutse yana mai yin
kabbara (Allahu akbar), kuma mustahabbi ne ya yi jifan daga wurin da ake
kiransa BAXANUL WADIY; sai ya sanya xakin
ka'abah ta hannunsa na hagu, minah kuma ta dama, saboda haka Annabi (r) ya
aikata, idan kuma da zai yi jifan ta sauran geffanta hakan ya isar masa matuqar
dutsen ya faxa cikin wurin da ake jefa su. Kuma ba a sharxanta
wanzuwan duwatsun a wurin da aka jefa su ba, kawai dai sharaxin
shine aukuwan kowannensu a ciki, don haka; da ace dutsen zai faxa
a wurin da aka jefa shi, sannan sai ya zame ya fita daga cikinsa, to lallai ya
isar masa a zahirin zancen ma'abota ilimi, daga cikin waxanda
suka faxi wannan magana qarara
akwai: Imam An-nawawiy (رحمه الله) a cikin littafinsa Sharhul muhazzab
(da ake ce da shi: Almajmu'u).
Su kuma duwatsun da ake ibadar jifa da su (a jamraat)
girmansu ya kan kasance ne kamar girman dutsen
da ake harbawa akan farcen babbar yatsa, wato: su kan fi gujiya girma da xan
kaxan.
Sannan bayan mahajjaci ya gama jifa, to sai ya soke raqumarsa
(ko yanka rago, saniya), kuma mustahabbi ne a lokacin soke dabba ko yanka ta ya
ce: "BISMILLAHI, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA HAZA MINKA WA LAKA", yana
mai fiskantar da ita alqiblah.
Sunnah shi ne: a soke raqumi:
alhali yana tsaye, hannunsa na hagu kuma yana lankwashe a kuma xaure,
saniya kuma da awaki suna kwance akan kuivinsu
na hagu. Da kuma bawa zai yanka dabbarsa ba ta fiskar alqibla
ba, to lallai ya bar sunnar Annabi (r) cikin
yanka, amma yankarsa ta yi, wannan kuma saboda fiskantar da dabba a lokacin
yanka zuwa ga alqiblah sunnah ne ba wajibi ba. Kuma mustahabbi ne mahajjaci ya
ci wani abu daga naman hadayarsa, ya kuma bada kyauta, ya yi sadaka, saboda faxin
Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﭼ الحج:
٢٨
Ma'ana: "Sai ku ci
daga ciki, kuma ku ciyar da marashi faqiri", [Hajj: 28].
Lokacin yankan yana faxaxa
har zuwa faxuwar rana, na yinin goma sha uku (13), daga cikin kwanakin da
ake busar da nama a cikinsu (waxanda
ake kira da: ayyamut tashriqi), a mafi
inganci daga cikin zantukan maluma, don haka; sai lokacin yanka ya zama ranar
layyah, da kuma kwanaki uku da suke bayansa.
Sa'annan bayan mahajjaci ya soke raquminsa,
daga nan zai aske gashin kansa gabaxaya
ko ya rage, saidai kuma askewa gabaxayan
shi ne ya fi falala, kasancewar Annabi (r) ya yi
addu'ar neman rahamar Allah da gafararsa ga waxanda
su ka aske gashinsu gabaxaya har
sau uku, su kuma waxanda suka rage sashin gashinsu ya musu sau xaya
kacal, kuma rage wani abu na gashin kai baya isarwa, kasancewar dole ne a rage
shi gabaxaya, kamar inda aske shi za a yi.
Ita kuma mahajjaciya mace za ta rage gashin kanta ne daidai
da kamar kan
yatsa; daga kowanni yawo guda xaya,
ko qasa da haka.
Bayan jifa da aka yi na "jamratul aqabah"
da aske gashi ko rage shi, an halatta wa mai harama dukkan abubuwan da
ihraminsa ya haramta masa aikata su, in banda saduwa da mata, wannan halaccin
kuma ana kiransa: halaccin farko (attahallulul auwal), kuma sunnah ne a gare
shi bayan samun wannan halaccin ya shafa turare, sannan kuma ya tafi cikin
garin Makkah, domin aikata xawafin ifadha,
saboda hadisin A'ishah (رضي الله عنها), lallai ta ce:
«كُنْتُ أُطَيِّبُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِإِحْرَامِهِ قَبْلَ أَنْ يُحْرِمَ، وَلِحِلِّهِ قَبْلَ
أَنْ يَطُوفَ بِالْبَيْتِ».
Ma'ana: "Na sanya
turare wa Manzon Allah (r) saboda
yin haramarsa, gabanin ya yi haramar, da kuma lokacin da ya warware aikinsa
gabanin ya yi xawafin xakin
ka'abah"([7]), Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Shi kuma wannan xawafin ana kiransa da: xawaful
ifadha, ko xawafin ziyara, kuma rukuni ne daga cikin rukunnan hajji;
wanda aikin hajjin mutum baya cika sai ya aikata shi, kuma shine abin nufi a
cikin faxin Allah maxaukakin
sarki:
ﭽ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﭼ الحج:
٢٩
Ma'ana: "Sannan su
fice daga dauxarsu, su cika bakancensu, suna masu xawafin xaki 'yantacce",
[Hajj: 29].
Sannan bayan mahajjaci ya yi xawafi
da sallatar raka'oi guda biyu, a ta bayan "maqaamu
Ibrahima" daga nan sai ya yi sa'ayinsa tsakanin safah da marwah in
tamattu'i ya ke yi, wannan sa'ayin kuma na hajjinsa ne, yayin da sa'ayin da ya
aikata daga farko shi kuma shi ne na umrarsa.
Kuma yin sa'ayi guda xaya
tsakanin safah da marwah baya isarwa (ga mai tamattu'i) a abinda ya fi inganci
daga maganganun maluma, saboda hadisin A'ishah (رضي الله عنها) ta ce: Mun fita tare da Manzon Allah (r), sai ta
ambaci hadisin, wanda a cikinsa kuma akwai faxinsa:
«مَنْ كَانَ مَعَهُ هَدْيٌ فَلْيُهْلِلْ
بِالْحَجِّ مَعَ الْعُمْرَةِ، ثُمَّ لاَ يَحِلُّ حَتَّى يَحِلَّ مِنْهُمَا جَمِيعًا».
Ma'ana: "Wanda ya
ke da hadaya a tare da shi to ya yi haramar aikin hajji tare da umrah, sannan
ba zai warware a matsayin ya gama aikinsa ba sai a tare; su biyun",
har zuwa faxinta:
«فَطَافَ الَّذِينَ أَهَلُّوا
بِالْعُمْرَةِ، بِالْبَيْتِ وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ، ثُمَّ حَلُّوا، ثُمَّ
طَافُوا طَوَافًا آخَرَ، بَعْدَ أَنْ رَجَعُوا مِنْ مِنًى لِحَجِّهِمْ».
Ma'ana: "Sai waxanda
suke aikin umrah suka yi xawafin xakin
Allah, da kuma sa'ayi tsakanin safah da marwah, sa'annan suka warware, daga
bisani sai suka sake yin wani xawafin
na daban bayan sun dawo daga minah; na hajjinsu"([8]). Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Maganar A'ishah (رضي الله عنها) dangane da waxanda
suka yi umrah cewa "Sai waxanda
suke aikin umrah suka yi wani xawafin
na daban bayan sun dawo daga minah; na hajjinsu" = tana nufin: xawafin
da shi ne SA'AYIY TSAKANIN DUTSEN SAFAH DA MARWAH, a mafi ingancin magana daga
cikin maganganun maluma. Amma (malamin) da ya ce A'ishah (رضي الله عنها) na nufin: xawafin
ifadha ne, da maganarta da ta gabata to maganarsa ba ingantacciya ba ce; saboda
yin xawafin ifadha rukuni ne kana kuma wajibi; wanda baya sauka
akan kowa (mai hajjin tamattu'i, ifradi, dana qiraani),
kenan abinda ake nufi da faxinta shi
ne, abinda ya kevanci mai aikin hajjin tamattu'i; wanda kuma shi ne: xawafin
da zai yi tsakanin safah da marwah a karo na biyu, bayan dawowarsa daga minah;
don ya cika hajjinsa, wannan kuma zance ne da ya ke a fili, walhamdu lillah,
kuma shine maganar mafi yawan maluma.
Daga cikin dalilai da suke qara
nuna wannar ma'anar, akwai hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito shi, (hadisi
mu'allaq, ba da sigar shakka ba) daga Abdullahi xan
Abbas (رضي الله عنها), lallai cewa an tambaye shi dangane da
aikin hajjin tamattu'i, sai ya ce:
«أَهَلَّ الْمُهَاجِرُونَ وَالأَنْصَارُ
وَأَزْوَاجُ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم فِي حَجَّةِ الْوَدَاعِ وَأَهْلَلْنَا،
فَلَمَّا قَدِمْنَا مَكَّةَ قَالَ رَسُولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم: اجْعَلُوا
إِهْلاَلَكُمْ بِالْحَجِّ عُمْرَةً إِلاَّ مَنْ قَلَّدَ الْهَدْيَ، فَطُفْنَا
بِالْبَيْتِ، وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ، وَأَتَيْنَا النِّسَاءَ، وَلَبِسْنَا
الثِّيَابَ، وَقَالَ: مَنْ قَلَّدَ الْهَدْيَ فَإِنَّهُ لاَ يَحِلُّ لَهُ حَتَّى
يَبْلُغَ الْهَدْيُ مَحِلَّهُ. ثُمَّ أَمَرَنَا عَشِيَّةَ التَّرْوِيَةِ أَنْ
نُهِلَّ بِالْحَجِّ، فَإِذَا فَرَغْنَا مِنَ الْمَنَاسِكِ جِئْنَا فَطُفْنَا
بِالْبَيْتِ، وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ».
Ma'ana: "Waxanda
suka yi hijira (daga garin Makkah) da mataimaka (ga waxanda
suka yi hijira) tare da matan Annabi (r);
dukkansu sun yi niyyar aikin hajji, a shekarar hajjin bankwana, muma duk muka
yi niyyah, A yayin da muka iso garin Makkah, Sai Annabi (r) ya ce: Ku
mayar da niyyarku na hajji ta zamto ta umrah, sai ga wanda kawai ya koro dabbar
hadayarsa, Sai mu ka yi xawafin xakin
Allah, da kuma na safah da marwah, muka kuma sadu da mata, muka sanya tufafi,
Sai Annabi ya sake cewa: Duk mutumin da ya jawo dabbar hadayarsa to lallai ba
zai warware haramarsa ba, har sai hadayar ta riga ta kai ga wurin yanka ta
(10/12). Sannan sai ya umurce mu a yinin da ake ce da shi: ranar tarwiyah
(08/12) cewa mu qulla niyyar aikin hajji, idan kuma muka kammala aiyukanmu sai
mu zo; don yin xawafin xakin
ka'abah, da kuma a tsakanin safah da marwah"([9]). Makasudinmu na koro wannan hadisin a
wannan wuri ya qare. Kuma yana bayani ne qarara
cewa mai aikin hajjin tamattu'i ya kan
yi sa'ayi tsakanin safah da marwah sau biyu, Allah ne mafi sani!
Amma abinda Imam Muslim ya ruwaito daga Jabir xan
Abdullahi (t)
cewa lallai Annabi (r)
da sahabbansa ba su yi xawafin
safah da marwah ba sai sau xaya; wanda
kuma shine sa'ayinsu na farko, to lallai wannan za a fahimce shi ne kawai ga waxanda
suka kora hadayarsu zuwa garin Makkah daga cikin sahabbai, saboda su waxannan
sun ci gaba da wanzuwa cikin haramarsu tare da Annabi (r), har
zuwa lokacin da suka warware daga aikin hajji da umrarsu a tare (wato ranar 10
ga wata), kuma Annabi (r)
ya niyyaci hajji da umrah ne a tare (mai suna qiraani),
da haka ne kuma ya umurci duk wanda ya ja dabbar hadayarsa zuwa garin Makkah;
cewa suma su yi niyyar hajji tare da umrah (qiraani),
da kuma cewa kada su warware har sai lokacin warwarewa daga gare su; su biyun ,
gabaxaya ya zo (wato ranar 10). Shi kuma mai aikin hajjin qiraani
sa'ayi tsakanin safah da marwah guda xaya
ne akansa kawai, kamar yadda hadisin Jabir (t) da
sauran hadisai ingantattu suka yi nuni akai.
Haka shima mutumin da ya ke yin aikin hajji kaxai;
wanda ba umrah a cikinsa (mai suna ifraadi) sa'ayiy tsakanin safah da marwah
guda xaya ne akansa.
Don haka; idan mai hajjin qiraani
da ifraadi suka yi sa'ayinsu bayan sun aiwatar da xawafinsu
na quudum, to aikata hakan ya isar musu ba sai sun sake yin wani
sa'ayin na daban ba bayan yin xawafin
ifadha.
Wannan kuma ita ce hanyar da
za a haxe tsakanin hadisin A'ishah da na Abdullahi xan
Abbas, tare da kuma hadisin Jabir da muka ambata, (Allah ya qara
yardarsa a gare su gabaxaya), kuma
da haka ne cin karon da yake tsakaninsu (na zahiri) zai gushe, a kuma iya aiki
da hadisan gabaxayansu.
Yana daga abinda
zai qarfafa irin wannan magana, na cewa kan waxannan
hadisan ya haxe wuri guda ba savani
= kasancewar hadisan A'ishah da na Abdullahi xan
Abbas hadisai ne ingantattu da suke tabbatar da qarin
hukunci ko aiki, wanda shi ne sa'ayiy na biyu ga mai aikin hajjin tamattu'i,
Shi kuma zahirin hadisin Jabir yana kore shi, qa'idah
kuma tana cewa DALILI DA YAKE TABBATAR DA HUKUNCI SHINE ABIN GABATARWA AKAN
WANDA YAKE KORE SHI, kamar yadda maluma suka tabbatar da bayanin wannan qa'idar
a cikin ilimomi guda biyu; USULUL FIQ-H,
DA ULUMUL HADIS, Allah shi kaxai
shine mai datarwa ga daidai, babu kuma wani qarfi
babu dabara sai daga wajensa.
No comments:
Post a Comment