2015/10/01

HUDUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN ANNABI saw 19 zulhijjah 1436h Ta Shehi Husain Alush-sheikh








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
 JUMA'A, 19/ZULHIJJAH/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI HUSAINI XAN ABDUL'AZIZ ALUSH-SHEIKH







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya tabbata ga Allah wanda cikin ni'imominsa kyawawan abubuwa suke cika. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Ubangijin qassai da sammai,  kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, fiyayyen dukkan halittu, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, ma'abota biyayya da kuma aikin kusanci.
Bayanbhaka;
Ya ku musulmai…
Ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa, kuma ku yi riqo –a musulunci- da igiya mai qarfi. Kuma ku sani lallai rabauta da tsira da moriya yana nan ne cikin biyayya wa Mahalicci.

Ya ku taron musulmai
Muna godiya wa Allah akan baiwar da yayi  na kammalawar aikin hajji wa mahajjata,         da kuma datarwar da yayi wa salihan bayi na raya yini goman (10 zulhijjah) da nau'ukan bauta mabanbanta,        Wannan kuma yana daga falalar Allah da datarwarSa,       Yabo nasa ne, kuma godiya itama tasa ce,       Muna kuma roqonsa dacewa, da karvar aiyuka.
Mahajjata xakin Allah mai alfarma…
Taya ku murnar kammala aikin hajji, Allah ya karva muku, kuma ya kiyaye ku, kuma ya mayar da ku zuwa ga iyalanku lafiya a halin cin riba.
Yanzu kuma ga ku nan kun iso Madinar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)  Allah ta'alah ya faranta muku, kuma marabanku lale da zuwa, zamanku a wannan gari Allah yasa yayi daxi, kuma ya girmama rabonku a cikin dare da yini.
Lallai hajji da kwanakin nan guda goma, da abinda ke cikinsu na aiyuka kyawawa; waxanda mahajjata suka cike su da aiyukan bauta, Haka waxanda aka datar da su daga cikin  sauran mutane wajen aikata dangogin aiyukan biyayya, = lallai ni'ima ne mai girma, wacce take hukunta qarin godiya wa Allah mabuwayi da xaukaka, irin godiyar da yake farlanta wa bawa dawwama kan aiyukan taqawa, tare da juriya kan yi masa xa'a, da tsere kan aikata aiuykan alkhairi da shiriya, da tabbatuwa akan tauhidin Allah (سبحانه), da bin sunnar ManzonSa zavavve.
An tambayi ALHASANUL BASARIY cewa: Menene "hajji mabrur?" Yace:
"Shine: Ka dawo, kana mai guje wa DUNIYA, kana mai kwaxayin LAHIRA".
Kuma Ibnu-rajab ya ambaci qissar wani mutum cewa bayan yayi hajji sai ransa ta kira shi zuwa ga sava wa Allah, Sai yaji wani sauti daga sama yana cewa:
"Ya kai wannan mutum, shin baka yi hajji ba ne?".

            Lallai bayi abinda yake wajibi akansu shine: Tsayuwa kan miqaqqiyar hanya, da yin aikin xa'ar mahalicci mai girma, a cikin kowani lokaci da zamani,
"Kuma ka tsayu kamar yadda aka umurce ka, da wanda ya tuba tare da kai, kuma kada kuyi xagawa, Lallai shi akan abinda kuke aikatawa mai gani ne" [Hudu: ].
"Kuma ku daidaita zuwa gare shi, ku nemi gafararSa"  [Shura: ].
Don haka;           Musulmi rayuwarsa gabaxayanta wajibi ne ta zama lokaci ne na yin dangogin xa'a, da kuma saurin neman samun yardar Ubangijin qassai da sammai,
"Lallai sallata da yanke-yankena, da rayuwata da mutuwata ga Allah ne, Ubangijin talikai  **   Bashi da abokin tarayya. Da haka aka umurce ni, Kuma nine farkon musulmai" [An'aam: ].  Kuma Allah (سبحانه) yana cewa:   
"Kuma ka bautawa Ubangijinka har sai mutuwa ta zo maka" [Hijir: ].
Kuma ya zo cikin faxakarwar Annabi wanda duk mutumin da yayi riqo da su zai tsira kuma ya rabauta,      Ya zo cewa lallai wani mutum yazo wajen Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai yace:
"Ya ma'aikin Allah ka gaya min wata Magana a cikin musulunci wacce ba zan tambayi wani akansa ba a bayanka? Sai yace: Ka ce: Nayi imani da Allah, sannan ka tsayu".

            Ya ku 'yan'uwa musulmai…
Lallai babbar manufa daga cikin manufofin aikin hajji itace: Tarbiyyar zukata akan babbar manufa, da kuma qara tabbatar da itako jaddada ta a cikin zukata, Wanda kuma shine tabbatar da tauhidi ga Allah mabuwayi da xaukaka, Wannan kuma saboda musulmi ya zama mai kaxaita Allah a zahirance da a voye, a cikin zance da aiki da halayya, ta yadda (musulmi) ba zai karaya ba, ba zai qasqantar da kansa ba sai ga Allah, haka nan ba zai bayyanar da qasqancinsa ko miqa wuya ba sai ga Allah wanda sha'aninSa ya xaukaka.
Ibadar aikin hajji makaranta ce, wacce take rayar da zuciya, da kuma gavvai da kaxaita Allah (سبحانه) da bauta, ta fiskar jin tsoronsa da girmama shi, da kwar-jini, da roqo, da soyayya da fata, tawakkali da dogara, mayar da lamari da sallamawa, Tauhidi tatacce da yake fitar da zukata daga "wahami ko tatsuniya", sannan su xage rayuka daga matsalar qasqanta ga kowani halitta.
Kuma aikin hajji shine mafi girman darasin da yake tarbiyyantar da mutane kan girmama mahalicci, da tabbatar da cikakken qasqanci a gare shi, da soyayya cikakkiya, domin bawa ya kuvuta daga tushen shirka da hanyoyin da suke kaiwa zuwa gare shi, da kuma sabbubansa, Allah ta'alah ya ambata a tsakiyan ayoyin da suke bayanin hukunce-hukuncen aikin hajji:
"Kuma wanda yayi shirka wa Allah, to kamar ya faxo ne daga sama, sai tsuntsu ya wafce shi, ko kuma iska ta gangarar da shi a wuri mai nisa"[Hajji: ].
Shi mai tauhidi mumini baya neman taimako a lokacin  tsanani sai daga Allah, kuma a lokacin qunci baya neman mafaka sai zuwa ga Allah;       wannan kuma saboda yaqinin da yake da shi cewa: Babu mai tunkuxe cuta, ko ya jawo wani amfani idan ba wanda sha'aninsa ya xaukaka ba, Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma wanene ya ke amsawa mabuqaci idan ya roqe shi, kuma ya ke yaye mummuna, yake sanya ku, ku zama masu mayewa a bayan qasa,  Akwai wani abin bautan ne, tare da Allah? Kaxan ne kuke wa'aztuwa" [?????].
            Kuma yana cikin shirka mai girma: Roqon wanin Allah; kamar neman agajin matattu, da kuma rataya zuciya da waliyyai da salihai, da roqonsu, da yin bakance a gare su, ko kuma yin bauta a gare su ta hanyar yin xawafi a qabarinsu, ko kuma qudurce cewa sun san gaibu, ko suna iya yaye cuta,ko jawo amfani, daga cikin dangogin da babu wanda ke iya mallakarsu sai mahalicci mai iko.
            Kuma yana daga cikin babban shirka: Gaskata masu sihiri da qulunboto, da bokaye da masu ilimin taurari. Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma idan Allah ya shafe ka da wata to babu mai yayewa masa sai shi. Idan kuma ya shafe ka da wani alkhairi to lallai shi mai iko ne akan komai" [An'aam: ].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:  
"Duk wanda ya mutu alhalin yana roqon wata kishiya koma bayan Allah to ya shiga wuta", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Ya ku taron musulmai…
            Lallai ya yi matuqar raxaxi ga kowani musulmi hatsarin da turarreniya da turmutsutsi ya jawo shi a yankin Minah, Saidai kuma muna yin godiya wa Allah akan hukuncnsa da qaddararsa. Kuma muna roqon Allah da cewa yayi gafara ga waxanda suka rasu daga cikinsu, ya sanya su daga sahun shahidai a wurinSa,  domin ya qaddara yin shahada a gare su, kuma duk wanda ya mutu akan wani abu to za a tayar da shi akansa, kuma muna roqon Allah da ya kyautata haqurin iyalansu da makusantansu, ya kuma yi musu canjin alkhairi, ya kyautata ladanSa a gare su. Sannan ya gaggauta warakar majinyata daga cikinsu.
Kuma hidimar haramin Makkah da Madina guda biyu –Allah yayi masa sakayyar alkhairi- ya baiwa wannan lamari matuqar kulawarsa, kuma yayi umurnin cewa a yi binceke na adalci, domin sanin idan akwai wani sababi, domin kuma ayi hisabi ga wanda yayi sakaci, a kuma yi uquba ga wanda ya sabbaba hakan; idan akwai wanda ya zama musabbabin.
Kuma wannan abinda ya bijiro, ko ya auku, ba zai tava gurvata irin manya-manyan qoqari, da aiyuka masu girma, da hidimomi mabanbanta masu yawa da girma; waxanda hukumar mai hidimar harami guda biyu take aiwatar da su, don su zama hidima ga mahajjata da masu umrah ba. Kai, da aiki tuquru don gabatar da dukkan abinda zai iya yiwuwa, cikin aiyuka mabanbanta, da suke raya masallatan harami guda biyu, da sauran wuraren ibada masu tsarki (Minah, Arfah, da Muzdalifah), waxanda a tarihi ba a tava ganin irin waxannan aiyukan ba.
            Kuma mai hidiman maramai guda biyu, da mutane biyu da suke na'ibtarsa sune da karan-kansu suke kula da dukkan aiyukan da ake (masu alaqa da haramin Makkah dana Madina, basa wakilta wassu akan haka), wanda kuma aiyukan saboda yawansu basu da iyaka, suna kuma yin muraja'ar aiyukan, suna kuma sake bada wassu qare-qare, cikin duk abinda zai yi wata hidima ga wannan lamari.
            Daula ko kuma qasar Saudia a qarqashin shugabancin mai hidimar haramai guda biyu ta kan shugabanci gudanar hajji, da aiyukan umrah a lokuta mabanbanta a tsawon kwanakin shekara, da dukkan kwarewa ko iko (babu gazawa), kuma waqi'in da ake ji, da gani yana yin shaida akan haka, kuma babu mai yin musun hakan sai wanda aka shafe basirarsa, daga cikin waxanda suka sanya qulli a zukatansu, da masu yin hassada kan wannan ni'imar; wacce Allah yayi baiwarta ga shugabanin wannan qasar. Kuma lallai kamala (da rashin naqasa) na Allah ne shi kaxai. Saidai kuma duk wanda yake qoqarin sanya shakka, ko sukan hukumar mai hidimar haramai guda biyu maxaukaka da cewa wai bata bayyanar da kwaxayinta wajen ganin mahajjata sun yi akinsu lafiya ba, ko cikin hutu, ko ya tuhume ta da cewa: Wai bata wani qoqari wajen bunqasa wuraren ibadodi masu tsarki, ko yace: Wai sun gaza wajen samar da damammakin ka-iya samuwa, na mutane, da dukiya, da aminci, da kayan aikin zamani dana likitanci, Waxanda kuma miqiyin da zai yi adalci shima ya san an samar da su, gabanin masoyi adali. Duk wanda ya ke qoqarin sanya shakka cikin waxannan to lallai mutum ne mai qin gaskiya da girman kai, wanda kuma zai iya musanta samuwar rana a lokacin tsakiyar yini.
Kuma daga nan (minbarin Manzon Allah saw) muna Magana da harshen kowani musulmi cewa: Allah yayi maka sakayyar alkhairi ya mai yin hidima wa harami guda biyu masu daraja, kuma Allah yayi sakayya wa mai jiran gadonsa, da mai jiran mai jiran gado, kuma Allah ya karva muku, kuma ku ci gaba da tafiyarku cikin albarkar Allah, kuma Allah ya gwavava ladanku, ya kuma yi albarka cikin aiyukanku. Kuma maqiyinku ba zai samu komai ba sai asara da kuma nadama.
Kuma shi wannan godiyan shugaban hajji; wato: gwamnan yankin Makkah mai karamci, akan aiyukansa waxanda sashinsu ke bin sashi, da fatan Allah ya kyautata sakayyarsa, sannan ya datar da shi wajen qara wassu aiyukan.
Haka kuma muna roqon Allah yayi sakayya ga dukkan vangarorin hukuma waxanda suka hana idanunsu barci, kuma suke hana su, don yin hidima wa baqin mai rahama (mahajjata), musamman dakarunmu aminai, masu kula da aminci, akan aiyukansu na yau da kullum na kiyaye aminci da tsaro, da nitsuwa da kwanciyar hankali.
Da kuma dukkan gwanayen vangaren lafiya, waxanda suka yi aiki mai kyau,  Da fatan Allah yayi sakayya a gare su da mafi alherin sakamako, yayi musu albarka, ya kiyaye su, sannan ya jiyar da su daxi a duniya da lahira.

'Yan'uwa musulmai…    
Lallai shugabanmu –a lokacin da yake aiki tukuru don sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, wajen tabbatar da maslahohin hajji masu yawa- tare kuma da yawan masu ziyarar xakin Allah ta fiskar adadi daga sauran yankunan duniya, to lallai maslahar shari'a ta hukunta a kawo tsare-tsare, waxanda lalurar tunkuxe varna da sharri take hukunta ayi aiki da su, wannan kuma sabili da mummunan cunkoso, wanda xinbin adadi ke jawo shi.
Kuma yana daga waxancan tsare-tsaren da zasu kawo hutu ga mahajjata, don su samu sauqin sauke faralinsu, su kuma aikata wajibinsu; Kuma yana daga abubuwan da ba za su dace da musulmi ba, yayi wayo wa waxannan tsarin, ko kuma yayi jifa da su ta bayan Katanga, wai saboda nufin aikata alkhairi; wanda kuma shine sauke hajjin nafila, kuma lallai manufofin shari'ar musulunci da qa'idodinta masu gamewa, da tushenta manya-manya suna wajabta wa musulmi taimakakkeniya kan biyayyar Allah da taqawa, Wanda yana daga cikin hakan: Bubbuxe damammaki ga mutane masu yawa, daga cikin waxanda basu tava aikin hajji na farilla ba, yin hakan kuma haqqi ne daga cikin haqqoqin 'yan'uwantakar imani, kuma wajibi ne daga cikin wajiban soyayya ta aqida, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai muminai 'yan'uwa ne" [Hujuraat: ].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"'Xayanku ba zai zama mai cikakken imani ba, har sai ya so wa xan'uwansa abinda yake so wa kansa".
A kan haka; Ba zai dace wassu su xau hanyar sava wa ijma'in maluman wannan zamanin; wanda ya nuna lalurar iyakance yawan masu hajji ko umrah, tare da kawo tsare-tsaren da za a iya tabbatar da maslaha da tunkuxe matsaloli ko varna tare da su. Ta yaya zai dace da musulmi ya sava wa gangogin umurnin da shugaba ya bayar a cikin lamarin da babu barin wajibi, ko kuma sava wa umurnin shari'a na wajibi, wanda kuma shugaban ya bada umurninsa ne, saboda babbar maslahar da duba na musulmai gabaxaya,     Kuma ta yaya zai dace da musulmi ya sava wa shari'a cikin hukunce-hukuncen hajji, kamar barin yin  harama daga miqaati; wai saboda ya zo da hajjin nafila; wanda shari'a bata lazimta masa shi ba, kai, lallai mutumin da Allah ya san niyyar gaskiya tare da shi, na neman yin nafilar hajji, sai kuma tsare-tsare ba su bashi damar aiwatar da hakan ba, to falalar Allah tana da yalwa, kuma zai samu lada da sakayya mai kyau akan niyyar da yayi, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Lallai a garin Madina akwai wassu mazaje; baza ku yi wata tafiya ba, kuma ba za ku yanka ta wani kwari ba, face sun kasance tare da ku, rashin lafiya ne ya katange shu", A wata riwayar kuma:
"Face sun yi tarayya da ku cikin lada", Muslim ya ruwaito shi.   A cikinhadisin Anas kuma yace:
"Mun dawo daga yaqin tabuka, da Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai yace: Lallai wassu mutanen da muka barsu a garin Madina, bamu bi wata hanyar da take tsakanin duwatsu ba, ko kuma wani kwari, face su suna tare da mu, uzuri ne ya riqe su", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ibnu-qayyim yace: ((Zancen wanda ya faxa daga cikin maluman fiqihu cewa: WAI BAYA HALATTA A FIFITA WANI AKAN KAI, A CIKIN AIYUKAN IBADA, wannan zancen bai inganta ba; saboda A'ishah ta fifita Umar alfaruq akan kanta, da cewa a bunne shi a xakinta, yana makwabtaka da Annabi –صلى الله عليه وسلم-  …. –Har zuwa inda ya ke cewa:- Shin wannan ba karamci ba ne da kyauta, da kuma fifita wani akan kanta, ga abinda take matuqar sonsa –wato: bunneta kusa da mijinta da mahaifinta- don taga ta kwaranye baqin ciki ga xan'uwanta musulmi –Umar-, da kuma girmama matsayinsa,       …-har zuwa faxinsa: Sai wanda ya fifita waninsa akan kansa ya zama daga cikin waxanda suka yi kasuwanci da ransu, ta hanyar bayar da wani abu, tare da xaukar ninkin baninkiyansa.   Sa'annan sai ya hakaito daga sahabbai cewa su sahabbai basa ganin cewa hakan makruhi ne.    Sannan yace: kuma littafin Allah da sunnar Manzon Allah –saw-, da kyawawan halayya basa hana aikata haka)). Maganarsa ta qare.
A kan wannan, Yaya ga mutumin da ya fifita hanuwa daga    yin aikin hajjin nafila da nufin yalwatwa waxanda suke son yin hajjin farilla, musamman a wannan zamanin wanda cunkuso ya kan yi yawa a cikinsu, to a nan fifitawar; lura da maslahar al'umma ta gabaxaya, wacce ta game dukkan al'umma, kuma za ta sauqaqe mata sauke wannan farilla na wajibi (shine yafi muhimmanci).
            Wanda aka datar da shi, shine kaxai wanda Allah ya datar da shi.
            Ina faxan wannan maganar, kuma ina neman gafarar Allah wa Ni da Ku da kuma dukkan  musulmai daga kowani zunubi, ku  nemi gafararsa lallai shi mai gafara ne mai rahama.
  
HUXUBA TA BIYU
            Ina yin yabo wa Ubangijina kuma ina yi masa godiya, Kuma ina shaidawa babu abin  bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,  Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa,
            Bayan haka:
            Ina yi muku  wasici da taqawar Allah mabuwayi da xaukaka, saboda duk wanda ya kiyaye dokokinsa sai Allah ya bashi daddaxar rayuwa, kuma ya kare shi, sannan sai ya ci nasara ya kuma rabauta a duniya da lahira.
            Ya ku musulmai…   
            Lallai bayyanar da qiyayya wa al'ummar musulmai da garrurukansu wani al'amari ne wanda tsananinsa ya fi qarfin tunani, kuma ba zai yiwu a zance na gaggawa a game Magana akansa ba, musamman qasar harami guda biyu maxaukaka, lallai ana shirya mata makirce-makirce, da zaman lafiyanta, daga masu qullin qiyayya a zuci, abinda harshe a irin wannan wurin ba zai iya siffanta shi ba.
            Ya ku samarin musulmai…
            Lallai yana daga cikin abubuwan da suke gargaxin cewa hatsari na fiskantowa: Irin abinda hanyoyin sadarwa suke watsawa na bayanai, waxanda basa banbance daidai daga varna, da kuma gaskiya daga qarya,     Bayanai ne ake tultulowa, tsare-tsare ne da ake tsananta kai hari da su, ga wannan qasa, da abinda ta mallaka, da shugabanninta da jama'arta. Kuma lallai mai hankali shine wanda  
Addu'a ….
……………….
……………….


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...