HUKUNCE-HUKUNCEN LAYYAH
A ISLAMA
A nan akwai mas'aloli biyar kamar haka:
Mas'alar farko: Bayani kan
"layyah", hukuncinta da dalilan shar'anta ta, tare da sharuxanta:
1-
Bayani akan layyah: Layyah
–a harshen larabci-
Shine: Yanka abun layya a lokacin walaha. A shari'ar Musulunci kuma
Itace: Abun da ake yankawa na raquma
da shanu, awaki da tumaki, don neman kusantar Allah maxaukakin
sarki a ranar idi.
2-
Hukuncin layyah da kuma dalilan shar'antata:
Hukuncinta sunna ne mai qarfi;
saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﮊ ﮋ ﮌ ﭼ الكوثر: ٢
Ma'ana: (Ka yi sallah ga Ubangijinka, ka kuma soke raqumi ga
Ubangiji) [Kausar: 2]. Da kuma saboda hadisin Anas -t-:
"أنَّ النَّبِيّ r ضَحَّى بِكَبْشَيْنِ أَمْلَحَيْنِ أَقْـرَنَيْنِ،
ذَبَـحَـهُمَا بِـيَدِهِ، وَسَـمَّى وَكَـبَّـرَ، وَوَضَعَ رِجْلَهُ
Ma'ana: (Lallai Annabi –r-
ya yi layyah da raguna guda biyu masu roxin
fari da baqi, madaidaita qaho guda biyu, ya
yanka su da hannayensa, yana mai anbaton sunnan Allah, da yin kabbara, ya kuma xora
qafarsa
a gefen wuyansu).
3-
Sharuxan shar'anta layyah:
An sunnata layyah ga bawan da sharruxa
dake tafe suka samu a wajensa:
1)
Musulunci: Layyah
ba ta inganta idan wanda ba musulmi ba ya aikata ta.
2)
Balaga da hankali: Duk mutumin da
bai kasance baligi mai hankali ba, ba a kallafa masa yin layyah.
3)
Samun iko da dama: Wannan ikon na
tabbatuwa idan mutum ya mallaki qimar
da zai sayi abun layyah da shi, bayan ya mallaki abincinsa da na iyalansa, na
tsawon ranar idi, da kuma kwanakin sallah guda uku bayan yinin idi (ayyamu at-tashriq).
Mas'ala ta biyu: Da waxanne dabbobi ake layyah?
Layyah
ba ta inganta sai in an yi ta da nau'ukan dabbobi masu zuwa:
1-
Raquma. 2- Shanu 3- Awaki
da tumaki.
Wannan
kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ الحج:
٣٤
Ma'ana:
(Kuma ga kowace al'umma mun sanya ibadar yanka; domin su ambaci sunan Allah
akan abinda ya azurta su da shi daga dabbobin ni'imah) [Hajj: 34]. Su kuma
"dabbobin al-an'aam" basa fita daga nauo'i guda uku da suka
gabata. Wani dalilin kuma shine: saboda
ba a ruwaito cewa Annabi (r)
ko kuma sahabbansa ba, cewa sun yi layyah da wata dabbar da ba su ba (kamar
kaza ga misali), in banda waxancan nau'uka na
dabbobin ni'imah.
Akuya da tinkiya na isa ga mutum xaya
da kuma iyalan gidansa; saboda ya zo a cikin hadisin Abu-ayyub -t- cewa:
"كَانَ الرَّجُلُ فِي عَهْدِ رسول الله r يُضَحِّي بِالشَّاةِ عَنْهُ، وَعَنْ
أَهْلِ بَيْتِهِ، فَيَأْكُلُونَ وَيُطْعِمُون"([2]).
Ma'ana:
(Mutum ya kasance a zamanin manzon Allah –r-
ya kan yi layyah da akuya -ko tinkiya-, wa kansa, da kuma iyalan gidansa, sai
su ci, su kuma ciyar).
Ya kuma halatta a yi layyah da
"raqumi ko saniya guda xaya" a
madadin mutane guda bakwai; wannan kuma saboda hadisin Jabir -t-, ya ce:
"نَحَرْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ r عَامَ الْحُدَيْبِيَةِ الْبَدَنَةَ
عَنْ سَبْعَةٍ، وَالْبَقَرَةَ عَنْ سَبْعَة"([3]).
Ma'ana:
(Mun yi layyah tare da manzon Allah –r- a
shekarar sulhun hudaibiyyah, mutane bakwai ga raqumi xaya,
itama saniya xaya mutane bakwai).
Mas'ala ta uku: Sharuxan da ake kula da su kan dabbar layyah:
1-
Shekaru:
a)
Raqumi: An
sharxanta
ya zama ya kammala shekaru biyar.
b)
Shanu: An sharxanta
su cika shekaru biyu.
c)
Akuya: An sharxanta
ta cika shekara xaya.
Wannan kuma duka saboda hadisin Jabir -t- cewa lallai Manzon Allah (r), ya ce:
"لا تَذْبَحُوا إِلا مُسِنَّةً إِلا أَنْ يُعْسِرَ عَلَيْكُمْ، فَتَذْبَحُوا
جَذَعَةً مِنَ الضَّأْن"([4]).
Ma'ana: (Kada ku yi yankar layyah sai dabbar da ake mata laqabi
da "musinnah", sai dai in kun rasa wannan, sai ku yanka
"jaza'ah" daga cikin tumaki).
"Musinnah" daga cikin raquma
itace: wanda ta cika shekaru biyar. Daga cikin "shanu" kuma itace:
wanda ta cika shekaru biyu. Daga cikin "awaki" kuma: wacce ta cika
shekara xaya. Kuma ana kiranta "Saniyyah".
d)
Tinkiya: An
sharxanta
ta zamo "jaza'ah"; wacce kuma itace: ta ke da watanni guda shida;
wannan kuma saboda hadisin Uqbah xan Aamir -t- yace a lokacin
da Annabi (r)
ya bani dabbobin layyah don na raba wa sahabbansa, ya ce:
Ma'ana: (Ni na samu "jaza'ah –tinkiya 'yar wata
shida" ne, Sai Annabi –r-
yace: To sai ka yi layyah da ita). Da kuma saboda wani faxin
na Uqbah
xan Aamir -t-:
Ma'ana: (Mun yi layyah tare da manzon Allah –r- da
"jaza'ah daga cikin tumaki –wato: 'yar watanni shida-).
2-
Kuvutuwa daga aibuka:
An
sharxanta
ga raquma
da shanu, awaki da tumakin da za yi layyah da su; cewa su kasance sun kuvuta
daga aibukan da za su sanya naman dabbobin ya qaranta;
don haka; yankwananniyar dabba ba ta isarwa, haka kuma karyayyiya, da mai ido xaya,
da maras lafiya; waxannan kuma saboda hadisin
Al-bara'u xan Aazibin -t- daga Annabi (r) ya ce:
"أَرْبَعٌ لا تُجْزِئُ فِي الأَضَاحِيِّ: الْعَوْرَاءُ الْبَيِّنُ عَوَرُهَا،
وَالْمَرِيضَةُ، الْبَيِّنُ مَرَضُهَا، وَالْعَرْجَاءُ الْبَيِّنُ عَرَجُهَا، وَالْعَجْفَاء
الَّتِي لا تُنْقِي"([7]).
Ma'ana:
(Dabbobi guda huxu basa isarwa a "layyah": Dabba mai harari-garke
wacce matsalan idonta ya bayyana, da maras lafiyan da cutarta ta bayyana, da
gurguwar da gurguntakanta ya bayyana, da kuma ramammiyar da bata da kitse).
Kuma
ana "qiyasi" ga waxannan aibuka guda huxu,
duk wani aibin da ke da irin ma'anarsu; kamar dabbar da haqoranta
na gaba suka faxi, da wacce mafi yawan kunnenta ko qahonta
ya yanke, da makamancin haka na daga aibuka.
Mas'ala ta huxu: Lokacin yanka abun layyah:
Lokacin
yanka layyah na farawa ne daga bayan sallar idi ga mutumin da ya sallace ta, ga
mutumin da bai sallace ta ba kuma (saboda uzuri): bayan fudowar rana na yinin
idi da gwargwadon lokacin da za a iya yin raka'oi guda biyu, da hudubobi biyu;
wannan kuma saboda hadisin Al-bara'u xan Aazib -t-, yace: Manzon
Allah (r)
ya ce:
"مَنْ صَلَّى صَلاَتَنَا، وَنَسَكَ نُسْكَنَا فَقَدْ أَصَابَ النُّسُكَ، وَمَنْ
ذَبَح قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ فَلْيُعِدْ مَكَانَهَا أُخْرَى"([8]).
Ma'ana:
(Duk wanda ya yi sallah irin tamu, ya kuma yi yanka irin namu to lallai ya dace
da yankan layyah akan tafarki, Amma mutumin da ya yi yanka kuma gabanin ya yi
sallar idi to sai ya sake yanka wata a madadinta). Lokacin yankan dabbobin na
cigaba har zuwa faxuwar ranar yinin qarshe daga cikin
kwanakin "attashriq" (wato: 13/ ga watan:
12); saboda hadisin Jubair xan Muxim -t- daga Annabi (r) yace:
Ma'ana:
(Dukkanin ranakun "tashriq" lokacin yanka ne).
Abin da ya fi falala shine a yanka
abun laiyan bayan an idar da sallar idi; saboda hadisin Al-bara'u xan
Aazib -t-, lallai Annabi (r) yace:
"أَوَّل مَا نَبْدَأُ بِهِ يَوْمنَا هَذَا نُصَلِّي، ثُمَّ نَرْجِعُ فَنَنْحَرُ،
فَمَنْ فَعَلَ ذَلِكَ فَقَدْ أَصَابَ سُنَّتَنَا، وَمَنْ ذَبَحَ قَبْلَ ذَلِك فَإِنَّمَا
هُوَ لَحْمٌ قَدَّمَهُ لأَهْلِهِ؛ لَيْسَ مِنَ النُّسُكِ فِي شَيْءٍ"([10]).
Ma'ana:
(Abun da zamu fara yininmu wannan da shi, shine mu yi sallar idi, sa'annan sai
mu dawo don mu soke abun layyarmu. Duk wanda ya aikata haka to ya dace da
sunnarmu, Duk kuma mutumin da ya yanka abun layyansa gabanin haka to ya sani
cewa: nama ne ya gabatar da shi ga iyalansa, ba layyah ba).
Mas'ala ta biyar: Yaya ake yi da naman
layyah? Kuma meke lazimtar mutumin da zai yi layyah idan goman farkon wata suka
shigo:
1-
Me ake yi da naman layyah?
Lallai an sunnata ga mai layyah ya ci daga layyarsa, ya kuma
bada kyauta ga dangi da makwabta da abokai, haka kuma ya yi sadaka ga faqirai,
wannan kuma saboda faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﭼ الحج: ٢٨
Ma'ana: (Sai ku ci daga layyarku, kuma ku ciyar da faqiri
mai tsananin talauci) [Hajj: 28].
Kuma mustahabbi ne mutum ya kasa naman layyarsa kashi uku: xaya
ga iyalan gidansa, xaya kuma ya ciyar da makwabtansa talakawa, ya kuma bada kyautan
kaso na qarshen; wannan kuma saboda hadisin Abdullahi xan
Abbas -t-
yana siffanta layyar Annabi (r),
ya ce:
"ويُطْعِمُ أَهْلَ بَيْتِهِ الثُّلُثَ، وَيُطْعِمُ فُقَرَاءَ
جِيرَانِهِ الثُّلُثَ، وَيَـتَصَدَّقُ عَلَى السُّؤَّالِ بِالثُّلُثِ"([11]).
Ma'ana: (Zai ciyar da iyalan gidansa xaya-bisa-uku
1/3, ya ciyar da faqirai
makwabtansa xaya-bisa-uku 1/3, kuma ya yi sadaka wa
masu roqo da xaya-bisa-uku 1/3).
Yana halatta ya ijiye naman layyah fiye da kwanaki uku;
wannan kuma saboda hadisin Buraidah -t-,
Lallai Annabi (r)
yace:
"كُنْت نَهَيْتُكُمْ عَنْ ادخار لُحُومِ الأَضْاحَى بَعْدَ ثَلاَثٍ فَكُلُوا،
فَأَمْـسِكُوا مَا بَـدَا لَكُم"([12]).
Ma'ana: (Na kasance na hana ku ijiye naman layyah fiye da
kwanaki uku, to ku ijiye na tsawon yadda ya yi muku).
2-
Abun da ke lazimtar mutumin da yake da
niyyar layyah idan kwanaki goman zul-hijjah suka shiga:
Idan kwanaki goman zulhijjah suka shiga ya haramta ga mutumin
da ya nufi yin layyah ya cire gashin jikinsa, ko wani abu daga faratunsa, i
zuwa ya yanka layyansa; wannan kuma saboda hadisin Ummu-salamah –رضي
الله عنها-, daga Annabi (r)
"إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ وَعِنْدَهُ أُضْحِيَّةٌ يُرِيدُ أَنْ يُضَحِّيَ فَلا
يَأْخُذَنَّ شَعْرًا، وَلا يَقْلِمَنَّ ظُفُرًا"([13]).
Ma'ana: (Idan kwanaki goma suka shiga, a wajen xayanku
ya zama akwai abun layyah da zai yi layya da shi to kada ya cire wani gashi, ko
ya yanke wani farce). A wata riwayar kuma cewa ya yi:
Ma'ana: (kada ya tava wani abu
daga gashinsa da fatarsa).
Jazakallahu khaira
ReplyDeleteJazakallahu khaira
ReplyDeleteجزاك الله خير
ReplyDelete