2015/09/25

HUDUBAR MASALLACIN MANZO JUMA'A 12 Zulhijjah 1436h ta Alhuzaifiy








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
 JUMA'A, 12/ZULHIJJAH/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah;     muna gode maSa, muna neman taimakonSa,    muna neman shiriyarSa,   kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu da kuma munanan aiyukanmu,      Duk wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi,      Wanda kuma ya vatar to babbu mai shiryar da shi.
  Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokan tarayya,    maxaukaki mai girma,  
Ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa,    Yana albishir kuma yana gargaxi,   
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa waxanda suka kasance ga addinin Allah mafiya  alherin masu taimako.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah kamar yadda yayi umurni, kuma ku hanu daga abinda yayi hani; ya tsawatar,    Lallai masu taqawa sun rabauta,    Su kuma waxanda suka rafkana suka yi sakaci sun tave.
Ya ku bayin Allah!
Lallai waxannan kwanakin da kuke cikinsu kwanaki ne masu falala,    waxanda a cikinsu ake ninnika aiyukan bayi masu kyau,   Kuma wannan ninkin ya kan qaru idan aka yi IKHLASI wanda kuma kamar ruhi ko rai yake ga ibada, Kuma lallai su waxannan kwanakin da suke biye ga yinin layyah yana daga cikin abubuwan da suka yi fice da shi: Kasancewar mustahabbi ne a yawaito ambaton Allah  ta'alah Ambato mai lokaci qayyadadde, da wanda ake yinsa a lokacin da ba                                                                                                                    kevantacce ba.     
Shi kuma kevantaccen zikiri qayyadadde ana yinsa ne bayan kowace sallar farilla,      Wanda mutum zai fara  shi tun daga lokacin sallar asuba na yinin arfah,     har zuwa sallar la'asar na yinin goma sha uku (13) wanda shine yinin qarshe daga cikin yinin da ake busar da naman layya a cikinsu.   Saboda abinda Ibnu-Abiyshaibah da Addaraquxniy suka ruwaito na daga hadisin Jabir (رضي الله عنه) yace: Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance idan  yayi sallar asuba, a yinin arfah ya kan yi kabbara, zai yi ta yin haka, har zuwa sallar la'asar ta qarshen kwanakin busar da nama, ya kan yi haka lokacin da ya ke yi sallama daga sallolin farilla.
A wani lafazin kuma Ya kasance    idan yayi sallar asuba a yinin arfah sai ya fiskanto sahabbansa sai yace: Ku zauna a wurarenku, Sai yace: ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
            Kuma yana daga cikin zikiri mai qayyadajjen lokaci: Addu'ar buxe sallah,   Wanda kuma nau'uka ne masu yawa da suka tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) .      Kuma mustahabbi ne ya buxe sallarsa a wannan karon da wannan, a wancan kuma da wancan    domin ya samu ladan koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم) kuma domin ya samu albarkar kowani addu'ar buxewan.     Kuma domin ya maimaita nau'ukan addu'ar buxe sallah; don ya haddace su;    domin ya riqa  aiki da su.         Kuma nau'ukan wannan zikirin an rubuta su a cikin LITTATAFAN ZIKIRORI.  
Kuma yana daga cikin zikirori masu qayyadajjen lokaci bayan Tahiyar qarshe: Faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"ALLAHUMMA A'INNIY ALA ZIKRIKA WA SHUKRIKA WA HUSNI IBADATIKA", Abu-dawud da Annasa'iy suka ruwaito shi, daga hadisin Mu'az (رضي الله عنه).
            Da kuma faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"ALLAHUMMA INNIY ZALAMTU NAFSIY ZULMAN KASIYRAN WALA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA FAGFIRLIY MAGFIRATAN MIN INDIKA WAR HAMNIY INNA ANTAL GAFURUR RAHIM", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin Abubakar (رضي الله عنه).
            Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya qarfafa                         lamarin yin addu'a da waxannan kalmomi guda huxu, bayan tahiya, Yace:
"ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MIN AZABI JAHANNAMA, WA MIN AZABIL QABRI, WA MIN FITNATIL MAHYAH WAL MAMAATI, WA MIN FITNATIL MASIHID DAJJAAL". Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Kuma lallai zikirori da addu'oin bayan TAHIYAR QARSHE suna dayawa kuma suna da albarka.
            Annabi (صلى الله عليه وسلم) dangane da addu'oin bayan tahiya yake cewa:
"Sa'annan sai ya zavi abinda yafi burge shi daga cikin addu'oi".
            Kuma yana daga cikin addu'oin da suke da gamewa:
"RABBANA ATINA FID DUNYA HASANATAN WA FIL AKHIRATI HASANATAN WA QINA AZABAN NAARI", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin Anas (رضي الله عنه).
            Kuma irin wannan zikirin ta hanyar yin addu'a bayan tahiya, yana cike irin givin da aka samu a cikin sallah, kuma yana tsarkake ta.
            Kuma musulmi ya kan xaga buqatunsa zuwa ga Ubangijinsa a qarshen sallar farillah, domin fatan ya samu amsa daga Ubangiji mai karamci,   bayan yayi tawassuli da wannan xa'ar mai girma (wato: sallah).
            Sai musulmi yayi kwaxayin kiyaye ko hardace  addu'oin da suka tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) a bayan  tahiya,  saboda duk wanda ya dawwama kan yin addu'a to zai rabauta kuma ya tsira. Sai kuma atunkuxe masa munanan abubuwa.
            Kuma yin zikiri bayan idar da sallah: qari ne ga ladanta, sannan kuma xaukaka ne ga bawa a wajen UbangijinSa;    Yazo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Wanda yayi SUBHANAL LAHI bayan kowace sallah sau 33, Yace: ALHAMDU LILLAHI sau 33, yace: ALLAHU AKBAR sau 33, To wannan sun zama 99 kenan,     Sai kuma ya faxi cikon 100, LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR. Za a gafarta zunubansa koda ya kasance kamar kumfan teku ne", Muslim ya ruwaito shi.
            An karvo daga Abu-umamah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya karanta AYATUL KURSIYYU bayan kowace sallar farillah Babu abinda zai hana shi shiga gidan aljannah  Face mutuwa". A wata riwayar: "Da qul huwal lahu ahad", Axxabaraniy a cikin [Alkabiir, da Al'ausax] ya ruwaito shi. Almunziri yace: Ibnu-hibbana ya inganta shi.
           
            Kuma zikiri yinsa mustahabbi ne, kuma shari'a a kowani lokaci ba tare da wani qaidi ba,     Kuma haqiqa Allah yayi umurnin a riqa yinsa dayawa, a inda yace:
"Ya ku waxanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa,     kuma ku tsarkake shi (da tasbihi) safiya da maraice" [Ahzaab: 41-42]. Kuma Allah yayi alqawarin samun lada mai yawa akan zikiri; Yace:
"Da masu ambaton Allah dayawa maza, da masu ambaton Allah mata Allah ya tanada musu gafara da lada mai girma", [Ahzaab: 35].
Kuma lallai ladan zikiri ya kan banbanta wajen yawa gwargwadon lokacin da aka yi zikirin, Allah yana cewa:
"Kuma kayi tasbihi da gode wa Ubangijinka gabanin fudowar  rana da gabanin faxuwarta" [Xaha: 130]. 
Allah ta'alah yana cewa:
"Da masu neman gafara a lokacin sahuur" [Aali-imran: 17].
Allah ta'lah yana cewa:
"Kuma ka ambaci sunan Ubangijinka safiya da maraice" [Insaan: 25].
Kuma lallai yin zikiri yana haskaka zuciya, kuma yana qara imani,  Allah ta'alah  yana cewa:
"Lallai muminai sune waxanda idan aka ambaci Allah sai zukatansu su karkaxa, kuma idan aka yi tilawar ayoyinsa akansu sai su qara musu imani,     kuma akan Ubangijinsu suke dogara" [Anfaal: 2].
            Ya zo cikin hadisi cewa: "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda baya ambaton Ubangijnsa misalin rayayye ne da matacce".
            Kuma lallai yin zikiri yana kare mutum daga Shexanu; saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Sai naga wani mutum daga cikin al'ummata Shexanu sun kewaye shi, Sai ambaton Allah ya zo masa ya kore masa Shexanu".
            Kuma lallai zikiri yana kankare munana,   yana kuma ninninka kyawawa,    saboda hadisin         "Duk wanda ya faxa a lokacin da ya wayi gari da lokaci da yayi yammaci: SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI sau xari Babu wani mutum a ranar tashin qiyama wanda zai zo da fiye da abinda ya faxa sai mutumin da ya zo da irin abinda ya zo da shi, ko kuma yayi qari akan nasa". Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Da kuma saboda hadisin "Duk wanda yace: LA ILA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR a cikin yini xaya sau xari, To yana da ladan bayi goma da aka'yanta, Za a rubuta masa kyawawa guda xari, a kuma kankare masa munana guda xari, Kuma za su zame masa kariya daga Shexan na tsawon yininsa wannan har yayi yammaci, Kuma babu wani da zai zo da fiye da abinda ya zo da shi saidai mutumin da ya aikata fiye da nasa",   Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
            Kuma lallai shi zikiri yana cike givi ko sakacin da bawa yayi;    wannan kuma saboda hadisin:
"Duk wanda yace a lokacin da yayi yammaci da lokacin da ya wayi gari:  FA SUBHANALLAHI HIYNA TUMSUNA WA HINA TUSBIHUNA WA LAHUL HAMDU FIS SAMAWATI WAL ARDHI WA ASHIYYAN WA HINA TUZHIRUNA, YUKHRIJUL HAYYA MINAL MAIYYITI WA YUKHRIJUL MAYYITA MINAL HAYYI WA YUHYIL ARDHA BA'ADA MAUTIHA WA KAZALIKA TUKHRAJUN. Wanda ya faxi haka Lallai ya riski duk abinda ya wuce   masa a cikin yininsa da darensa", Tirmiziy ne ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi xan Abbas.
            Kuma lallai shi zikiri yana tsamar da bawa daga cikin tsanani, yana kuma fitar da shi daga cikin baqin ciki, Allah ta'alah yana cewa (Dangane da Annabi Yunus):
"Ba don ya kasance yana cikin masu yin tasbihi ba, to da ya zauna a cikinsa (kifi) har zuwa yinin da za a tayar da su" [Assaafaat: 143-144].
Ya zo kuma a cikin hadisi cewa:
"LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZIMI, LA MALJA'A WALA MANJAH MINAL LAHI ILLA ILAIHI faxinsa yana tunkuxe wa bawa qofofi saba'in na bala'oi,     Kuma mafi qaranci daga cikinsu shine: BAQIN CIKI".
            Kuma AMFANIN ZIKIRI a duniya da lahira da FALALOLINSA abu ne da baza su qididdigu ba, sai da matsanancin wahala da xaukar dogon lokaci.
            Kuma musulunci ya shar'anta yin zikiri ga musulmi a cikin awannin darensa dana yininsa, da kuma sauyin yanayinsa a halin yana farke ko yana barci, da kuma cikin zamansa a gari ko tafiyarsa,       Don haka;     Duk wanda yayi aiki da ZIKIRORI (ambaton Allah) a cikin dukkan halayyarsa, to lallai Allah ya sauqaqe masa dalilin tsira a gidajen nan guda biyu (duniya da lahira).     Wanda kuma yayi sakaci kan wassu zikirorin to lallai alheri dadama ya suvuce masa gwargwadon abinda ya kyale na ZIKIRORI,        Yazo daga Abdullahi xan Busur yace: Lallai shari'oin musulunci sun yi yawa, Sai ka bamu wata qofa gamammiya da za mu yi riqo da ita? Sai yace:     Kada harshenka ya gushe yana xanye shatab da ambaton Allah". Tirmiziy ya ruwaito shi.

            Allah ta'alah yana cewa:
"KUMA KA AMBACI UBANGIJINKA A CIKIN RANKA, KANA MAI QANQAN-DA KAI A GARE SHI, DA KUMA A VOYE, DA KUMA QASA DA BAYYANAWA CIKIN ZANCE, DA SAFIYA DA KUMA MARAICE, KADA  KA KASANCE DAGA CIKIN RAFKANANNU" [A'araaf: 205].

            Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma!


HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah wanda yayi halitta kuma ya daidaita ta,      Wanda yayi qaddara sai ya shiryar,     Ina yin yabo wa Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominsa da baza su lissafu ba,
Ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,     Yana da sunaye mafiya kyawu.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa; zavavve.
            Ya Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa;  ma'abota ilimi da hankali.
            Bayan haka!
            Ku kiyaye dokokin Allah iyakar kiyayewa,     kuma ku yi riqo –a musulunci- da igiya mai qarfi..
           
            Ya ku musulmai…    
Mutane dangane da hukunci akan abubuwan da suke aukuwa da   annoba  da musibu sun kasu kasha-kashi

Wani kason su kan yi Magana akan abinda ya auku ba tare da ilimi ba,      sai suyi ta kukkutsawa a cikin labarin ta hanyar yayata jita-jita, waxanda basu inganta ba,   sai suyi ta ambaton duk abinda suka ji a majalisosi, suna faxa suna nanatawa,    wai da nufin rage ciyon musibar,     Kuma lallai Allah ya hana bin wannan turbar, a inda yake cewa:
"Kada ka bibiyi abinda baka da ilimi  akansa,    Lallai ji da gani da zuciya za a tambaye su akan haka", [Isra'i: 36].

            Akwai wani kason Waxanda suke kukkutsawa cikin labarun abinda ya wakana da niyyoyi munana, da kuma manufofi maqasqanta, suna sanyawa abinda ya auku rigunan qarya, da gyara zance;        da nufin isa zuwa ga wani abinda suke nufi; ko Na tuhumar kuvutattaun mutanen da basu ji ko suka gani ba,   ko kuma qoqarin bunne kyawawan aiyukansu,     Irin waxannan su kan yi iya qoqarinsu wajen mayar da kyawawan aiyuka munana,  ko kuma alheri zuwa sharri,    lafiya kuma su mayar da shi bala'i,   Kuma irin wannan kason a cikin mutane basu san adalci ko kunya ba;      saboda sun riga sun saba yin qarya da qirqiran zance,    ba tare da sun damu ba.
            Wannan kason saboda dai karyarsu ta bayyana,     da yadda suke aukawa cikin walaqanci, da raini daga mutane, sakamakon yadda suke jiran su ji musiba ta aukawa bayin Allah don su yi farin ciki   =  Allah ta'alah (a cikin alqur'ani) ya bayyana mana siffofinsu domin mu nisance su, a inda yake cewa:
"Idan kyakkyawa ya same ka sai ya baqanta musu rai,   Idan kuma musiba ta same ka sai su ce: HAQIQA MU TUN GABANIN HAKA MUN XAUKE AL'AMARINMU, Sai su juya alhalin suna farin ciki. Kace: Babu abinda zai same mu sai abinda Allah ya rubuta mana, kuma shine masoyinmu (mai jivintar lamarinmu), Kuma ga Allah ne muminai suke dogara" [Taubah: 50-51].
Kuma Allah ta'alah yace:
"Kuma haqiqa sun nemi fitina gabanin haka, kuma suka yi ta jujjuya maka lamura, har gaskiya ta zo, al'amarin Allah ya bayyana alhalin suna qi" [Taubah: 48].

            Sai kaso na uku, Waxanda suka yi aiki da sabbuban da Allah ya shar'anta don kare kansu daga aukawa cikin musiba,    Amma sai abinda Allah ya qaddara yayi rinjaye   (sai musibar ta auku), daga nan; sai suka miqa wuya ga Allah kan abinda ya qaddara sannan ya hukunta,       kaga a nan; sai suka tunkuxe su SABBUBAN da ALLAH, sannan kuma da SABBUBAN DA ALLAH YA SHAR'ANTA.     To waxannan za a basu lada kan miqa wuya da suka yi akan abinda aka qaddara,     kuma waxannan sune ma'abota hankali da shiriya da tunani, Allah ta'alah yana cewa:
"Tabbas zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro, da yunwa, da tauyewar dukiya da rayuka da 'ya'yan  itatuwa,    Kayi bushara ga masu haquri Sune waxanda idan musiba ta same su sai suce: LALLAI MU DAGA ALLAH MUKE, KUMA LALLAI MU ZUWA GARE SHI MASU KOMAWA NE" [Baqarah: 155-156].
            Lallai a qarshen hajjin wannan shekarar MUNA YABAWA ALLAH kuma MUNA YIN GODIYA A GARE SHI, akan tsayuwan rukunin aikin hajji da kuma dawwamarsa.
            Kuma lallai duniya sun shaida kan abinda wannan qasar shiryayyiya take yi; na bada kula na musamman ga mahajjatan xakin Allah mai alfarma,    da hidimomi manya-manya, ta kowace fiska,    tare da haxe duk wani qarfi wuri guda don    sauqaqe al'amuran hajji,    tare da bada jagoranci mai hikima cikin kowani hali daga cikin halayyar aikin hajji.

            Kuma duk wanda ya musanta kasancewar haka, to yayi daidai da wanda yake musanta samuwar rana,     Sai ya zama; abin a tuhumi hankalinsa ne   !

            Al'amari kuma duka na Allah ne;  yana aikata abinda ya nufa.   Kuma shi Allah          ma'abocin rahama ne, da hikima.

            Kuma qarfin qasa –a duniya- ba zai iya tsara lamarin wannan taro na hajji ba,    Saidai kuma –da musulunci- Allah ya bada iko a wannan qasar, tana iya tsara shi koyaushe.

            Ya ku Bayin  Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin…" [Ahzab: 56].

Addu'a ….
……………….

……………….

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...