HATSARIN
"MINAH" A HAJJIN BANA QADDARA TA RIGA FATA
(KUMA TAKA-TSAN-TSAN
BAYA IYA TUNKUXE SHI)
A ranar
alamis 10 ga zulhijjah, na shekarar hijira ta 1436, wanda tayi daidai da 24 ga
satumba 2015 na miladiyya, a yinin layya, wanda kuma shine mafi girman yini a
warin Allah (ranar hajji da tafi girma), a kuma gari mai girma (Makkah), Lallai hatsari
mai munin gaske ya auku wa mahajjata xakin Allah; bayan fitowansu daga
Muzdalifah, a hanyarsu ta zuwa jifan Shexan, a qarshen Minah, wanda
lamarin yayi sanadiyyar mutuwan fiye da
mutane xari bakwai, kamar yadda alqaluman da hukumomi suka bayar suka nuna. Kuma
hukumomi sun tsayu wajen binciko musabbabinta ta hanyar kama komiti na musamman
akan haka, da fatan magance aukuwar irinta a gaba, tare kuma da yin hukunci ga
wanda yayi sakaci a cikinta, gwargwadon yadda binciken ya nuna. Amma ya zuwa
yanzu kamar yadda bayanan farko suka fara nunawa kan musabbabin wannai musibar
shine: Savawa tsare-tsaren gudanar da wannan aikin wanda sashin mahajjata suka
tafka, da kuma yadda wassu mahajjatan bayan sun yi jifa suka dawo ta hanyar
masu tafiya, wanda hakan ya haifar da cunkoso, da turarreniyar da ya haifar da
rasuwan mahajjata da dama; nan take, wassun kuma bayan an kaisu wuraren basu
kula na musamman. Saidai kuma wani abun lura a nan, shine wannan musibar lallai
bata taqaita da iyalan waxanda abin ya shafa kaxai ba; a, a ! wannan musiba ce ta
dukkan musulmai gabaxayansu, a ko-ina
suke, a duniya. Kuma a wannan gaxar akwai abubuwan day a kamata a xauka na
darasi, kamar haka:
(1)
Lallai
waxannan mahajjatan da suka fito daga muzdalifa, suka nufi wurin jifa, suna
xauke da burace-burace dayawa, a wannan yini, sun kuma shirya yin aiyuka
dadama, faraway das hi jifan, sai soke rakuman hadaya ko yanka shanu da awaki
ko tumaki, sannan sai aski, daga bisani kuma su shiga garin Makkah domin yin
xawafi, da sa'ayi, Sai kuma su dawo birnin Minah don su kwana biyu, ko uku,
domin yin jifa, sai kuma xawafin bankwana, kana su koma garurrukansu, waxannan bayin Allan babu wanda ya san cewa
mutuwarsa za ta dufafe shi a gurbin da ta haxu da shi, kuma babu wanda ya san
cewa za su yi irin wannan mutuwar a wannan wurin, saboda "Rai bata san
a wani gari zata mutu ba" [Luqman:]. Wannan shi yake nuna muhimmancin
kowani musulmi ya kasance cikin tanadi da jiran mutuwa, a safiya da maraice, da kuma a kowani hali.
(2)
Lallai
mahajjatan nan basu yi hasarar rayuwarsu ba, idan muka duba nassoshin da suke
nuna cewa: wanda ya rasu a cikin wani yanayi za a tayar das hi akan halin day a
rasu a cikinsa. Wannan yasa wani hadisin ya bayyana cewa kada a lulluve kan
sahabin day a rasu a cikin haramarsa, haka kada a lulluve masa fiska; saboda
"Za a tayar das hi a ranar qiyama yana TALBIYYAH". Haka wassu
hadisan sun nuna cewa: Shahidai guda biyar ne, Sai kuma ya ambace su;
Wanda ciyon ciki ya kashe, da wanda aka soke shi, da wanda Katanga ta ruso
masa, da wanda ruwa ya shanye, sai kuma wanda ya yi shahada fisabillahi. Kuma lallai
wani hadisin ya nuna cewa aikin hajji shima yana shiga cikin "fisabilillah",
saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya tambayi matar da mijinta ya rasu, kan
taje hajji sai tace: mijinta ya bar abun hawa, saidai kuma ya sanya shi waqafi
fiysabilillah, don haka bata da abin hawa zuwa hajji, sai Annabi yace mata ta
hau wannan raqumin zuwa hajji domin shima fiysabillahi ne.
(3)
Wannan
musibar ta auku ne a ranar farin cikin mai girma a wajen dukkan musulmai, sai ta cakuxa musu
farin cikin da baqin ciki mai girma, wannan kuma shi yake nuna cewar rayuwar
duniya bata zama garaua 100/100 ga mutane, akan haka baya
dacewa musulmi ya ruxu da farin cikin duniya, saboda baqin ciki da hawaye za su
iya gaurayuwa das hi a cikin kowani hali. Gidan daxi na shi ne kaxai aljannah,
Allah ya shigar da waxannan mahajjatan, da mu gabaxaya cikinta, amin.
(4)
Farin
cikin musulmai guda xaya ne, haka baqin cikinsu, saboda wannan musibar ta
jijjiga musulman duniya gabaxayansu, Wannan kuma yana qara tabbatar da maganar
Manzon Allah (لى الله عليه وسلم) da yake cewa:
"Musulmi ga musulmi kamar gini ne; sashinsa yana qarfafa
sashi". Da hadisin da yake cewa: "Misalin muminai cikin
soyayyarsu da tausasawarsu da yin rahama wa junansu kamar misalin jiki ne guda
xaya, Idan sashi ya tavu sai sauran
jikin ya taya shi jin zogi, da rashin barci".
(5)
Hadisin
da Alhakim da wassunsa suka ruwaito, kuma malamai suka ce hadisi ne mai kyau
"hasan", wanda yake bayyana cewa:
"لا يغني حذر من قدر".
Ma'ana: "Taka-tsantsan baya tunkuxe qaddara".
Saboda kayi mamakin irin abinda hukumomin qasar Makkah suke kashewa gabanin
hajji, da lokacinsa, da kuma bayansa don ganin mahajjata sun huta, ba tare da
sun sha wahala ba, Amma tak-tsantsan
xinsu, ba zai tava tunkuxe abinda Allah ya qaddara ba. Musulmi kuma dole ne akansa
yayi imani da haka.
Bayan haka;
Zai kyautu na
kawo tarjamar huxubar Madina ta wannan satin, wacce tayi magana kan karkasuwan
mutane dangane da hukunci akan irin abubuwan da ka iya aukuwa zuwa kashi uku,
sai kuma in biyo bayanta da huxubar garin Makkah ta Juma'a, wacce itama tayi Magana
akan wannan lamari, kamar haka:
HUXUBAR
MASALLACIN ANNABI (r), JUMA'A, 11/ZULHIJJAH/1436H,
wacce LIMAMI MAI HUXUBA SHEHI ALIYU XAN
ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY ya gabatar,
Limamin a cikin huxubarsa ta biyu yace:
Mutane dangane da hukunci akan abubuwan da
suke aukuwa da annoba da musibu sun kasu kasha-kashi
Wani kason su kan yi magana akan
abinda ya auku ba tare da ilimi ba,
sai suyi ta kukkutsawa a cikin labarin ta hanyar yayata jita-jita,
waxanda basu inganta ba, sai suyi ta
ambaton duk abinda suka ji a majalisosi, suna faxa suna nanatawa, wai da nufin rage ciyon musibar, Kuma lallai Allah ya hana bin wannan
turbar, a inda yake cewa:
(وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ
وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا) [إسراء: 36].
"Kada
ka bibiyi abinda baka da ilimi
akansa, Lallai ji da gani da
zuciya za a tambaye su akan haka", [Isra'i: 36].
Akwai
wani kason Waxanda suke kukkutsawa cikin labarun abinda ya wakana da
niyyoyi munana, da kuma manufofi maqasqanta, suna sanyawa abinda ya auku
rigunan qarya, da gyara zance; da
nufin isa zuwa ga wani abinda suke nufi; ko Na tuhumar kuvutattaun mutanen da
basu ji ko suka gani ba, ko kuma
qoqarin bunne kyawawan aiyukansu,
Irin waxannan su kan yi iya qoqarinsu wajen mayar da kyawawan aiyuka
munana, ko kuma alheri zuwa sharri, lafiya kuma su mayar da shi bala'i, Kuma irin wannan kason a cikin mutane basu
san adalci ko kunya ba; saboda sun
riga sun saba yin qarya da qirqiran zance,
ba tare da sun damu ba.
Wannan
kason saboda dai karyarsu ta bayyana,
da yadda suke aukawa cikin walaqanci, da raini daga mutane, sakamakon
yadda suke jiran su ji musiba ta aukawa bayin Allah don su yi farin ciki =
Allah ta'alah (a cikin alqur'ani) ya bayyana mana siffofinsu domin mu nisance
su, a inda yake cewa:
(إِن تُصِبْكَ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ وَإِن تُصِبْكَ مُصِيبَةٌ
يَقُولُوا قَدْ أَخَذْنَا أَمْرَنَا مِن قَبْلُ وَيَتَوَلَّوا وَّهُمْ فَرِحُونَ *
قُل لَّن يُصِيبَنَا إِلَّا مَا كَتَبَ اللَّهُ
لَنَا هُوَ مَوْلَانَا وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ) [التوبة: 50-51].
Ma'ana: "Idan kyakkyawa ya same ka sai
ya baqanta musu rai, Idan kuma musiba
ta same ka sai su ce: HAQIQA MU TUN GABANIN HAKA MUN XAUKE AL'AMARINMU, Sai
su juya alhalin suna farin ciki. Kace: Babu abinda zai same mu sai abinda Allah
ya rubuta mana, kuma shine masoyinmu (mai jivintar lamarinmu), Kuma ga Allah ne
muminai suke dogara" [Taubah: 50-51].
Kuma Allah ta'alah yace:
(لَقَدِ ابْتَغَوُا الْفِتْنَةَ مِن قَبْلُ وَقَلَّبُوا لَكَ
الْأُمُورَ حَتَّىٰ جَاءَ الْحَقُّ وَظَهَرَ أَمْرُ اللَّهِ وَهُمْ كَارِهُونَ) [التوبة: 48].
"Kuma
haqiqa sun nemi fitina gabanin haka, kuma suka yi ta jujjuya maka lamura, har
gaskiya ta zo, al'amarin Allah ya bayyana alhalin suna qi" [Taubah:
48].
Sai
kaso na uku, Waxanda suka yi aiki da sabbuban da Allah ya shar'anta don
kare kansu daga aukawa cikin musiba,
Amma sai abinda Allah ya qaddara yayi rinjaye (sai musibar ta auku), daga nan; sai suka
miqa wuya ga Allah kan abinda ya qaddara sannan ya hukunta, kaga a nan; sai suka tunkuxe su SABBUBAN
da ALLAH, sannan kuma da SABBUBAN DA ALLAH YA SHAR'ANTA. To waxannan za a basu lada kan miqa wuya
da suka yi akan abinda aka qaddara,
kuma waxannan sune ma'abota hankali da shiriya da tunani, Allah ta'alah
yana cewa:
(وَلَنَبْلُوَنَّكُم بِشَيْءٍ مِّنَ الْخَوْفِ وَالْجُوعِ
وَنَقْصٍ مِّنَ الْأَمْوَالِ وَالْأَنفُسِ وَالثَّمَرَاتِ وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ
* الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوا
إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ) [البقرة:
155-156].
Ma'ana: "Tabbas zamu jarrabe ku da
wani abu na tsoro, da yunwa, da tauyewar dukiya da rayuka da 'ya'yan itatuwa,
Kayi bushara ga masu haquri Sune waxanda idan musiba ta same su sai
suce: LALLAI MU DAGA ALLAH MUKE, KUMA LALLAI MU ZUWA GARE SHI MASU KOMAWA NE"
[Baqarah: 155-156].
Lallai
a qarshen hajjin wannan shekarar MUNA YABAWA ALLAH kuma MUNA YIN GODIYA A GARE
SHI, akan tsayuwan rukunin aikin hajji da kuma dawwamarsa.
Kuma
lallai duniya sun shaida kan abinda wannan qasar shiryayyiya take yi; na bada
kula na musamman ga mahajjatan xakin Allah mai alfarma, da hidimomi manya-manya, ta kowace
fiska, tare da haxe duk wani qarfi
wuri guda don sauqaqe al'amuran
hajji, tare da bada jagoranci mai
hikima cikin kowani hali daga cikin halayyar aikin hajji.
Kuma
duk wanda ya musanta kasancewar haka, to yayi daidai da wanda yake musanta
samuwar rana, Sai ya zama; abin a
tuhumi hankalinsa ne !
Al'amari
kuma duka na Allah ne; yana aikata
abinda ya nufa. Kuma shi Allah ma'abocin rahama ne, da hikima.
Kuma
qarfin qasa –a duniya- ba zai iya tsara lamarin wannan taro na hajji ba, Saidai kuma –da musulunci- Allah ya bada
iko a wannan qasar, tana iya tsara shi koyaushe.
Wannan
kuma shine karshen hudubar limamin.
Kuma lallai limamin a cikinta ya tunatar da
Mutane ne, akan karkasuwan Mutane, idan WANI ABU YA AUKU, KO MUSIBA TA FARU, ta
yadda suke kasuwa kashi uku, biyu daga
cikinsu abun zargi ne, duk da cewa dayansu ya fi muni. Yayin da kaso na uku shine abinda ake
neman DUKKAN MUSULMAI SU KASANCE AKANSA A IRIN WANNAN HALIN KO MAKAMANCINSA.
Da
fatan Allah ya amfanar da mu da abinda ya zo a cikinta.
Daga nan sai mu garzaya garin Makkah
don mu saurari me shi kuma limamin a cikin hudubarsa ta biyu yake cewa:
HUXUBAR
MASALLACIN KA'ABAH, JUMA'A, 11/ZULHIJJAH/1436H, wacce LIMAMI MAI HUXUBA SHEHI
SALIH BN MUHAMMADU ALU XALIB ya gabatar, Yace:
Bayan haka:
Lallai masarautar larabawa ta Saudia da
mazajenta da na'urorinta, da dukkan hukumominta = suna aikata aiyuka
manya-manya, domin su zamto hidima ga mahajjata da masu umrah da ziyara.
Kuma tun gomannin shekarun da suka wuce ita wannan
qasar (ta Saudia) tana jagorantar gudanar da aikin hajji, cikin iyawa da
gwanancewa, da bada kulawa na alfahari. Kuma ba zai tava cutar da hakan ba, ko
ya tauye shi MAI AUKUWA DA KA IYA BIJIROWA wanda kuma (a wannan karon) ya faru
sakamakon cunkoson da ya auku ga wassu mahajjatan da kuma abinda hakan ya
haifar na tunkuxar junansu, ko kuma don sava wa wassu tsare-tsaren gudanar da
wannan aiki.
Kuma idan a qaddarar Allah, ya zavi ya riqi
wassu daga cikin bayinSa a matsayin shahidai; a mafi kyan halin da suka samu
kansu a cikinsa, sa'annan a wurin da yafi xaukaka (Makkah), Wassun kuma
Ubangiji ya qaddara jarrabarsu da samun raunukan da za a basu lada akansa = to
lallai yana daga cikin abinda har abada ba zai samu karvuwa ba, A QARYATA
SAMUWAR QOQARI, KO MUSANTA NASARORI DA AKA CIMMA, ko hakan ya zama SABABIN CIN
MUTUNCI, DA QIRQIRE-QIRQIRE (KO QARIN GISHIRI). Kuma yana daga cikin mugunta da
qaranta: Yin tafi idan musiba ta shafi wani musulmi, da kuma ribatar musibar
musulmi don samun wassu buqatu na duniya, ko cimma manufofi na siyasa. Kuma
wannan MASARAUTA (ta Saudia) cikin godiyar Allah, tana da cikakken ikon
jagorantan lamuran hajji, ba tare da wani qarin qishiri ba. Kuma lallai hukumar tana da kyakkyawan
shugabanci akan abinda Allah ya xaukakata da shi na hidimar harami guda biyu
maxaukaka, babu mai jayayya akan haka. Kuma lallai kundin wannan qasar, da
tsarin mulkinta na farko; na asali yayi magana akan wannan hidimar. Kuma kulawar da aka yi ko ake yi ga haramin
nan guda biyu, ko ga mutanen da suke nufansu abu ne da idanu suke gani (ba a
voye ba). Kuma haqiqa Allah ta'alah ya kewaye xakinSa, da baqinSa, da basu
aminci da nitsuwa, a lokutan da duniya suke cikin firgici da rashin tsaro,
wanda wutan fitinu da yaquka ke kunnuwa. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya
hore wa garinSa mai alfarma masu bashi kariya ma'abota gaskiya, waxanda Allah
ya kiyaye addini da su, ya kuma kiyaye garurruka da bayi da shugabancinsu,
(أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا حَرَمًا آمِنًا
وَيُتَخَطَّفُ النَّاسُ مِنْ حَوْلِهِمْ) [العنكبوت:
67].
Ma'ana: "SHIN BASU
GANI BA NE, LALLAI MUNE MUKA SANYA HARAMI YA ZAMA MAI AMINCI, ALHALIN ANA WAFCE
MUTANE A KEWAYENSU…" [Ankabuut: 67].
Kuma lallai mu, a lokacin da muke
godewa Allah akan ni'imominSa; wajen sauqaqe hajji ga xarurrukan dubban
mahajjata, da kiyaye su, to lallai mu
muna juyayin baqin ciki akan abinda ya auku, wanda Allah ya qaddara shi ga
wassu daga cikin mahajjata, a ranar jiya (10/zulhijjah/1436h), har su ka haxu
da ajalinsu, a turerreniyar da ba a ji daxinsa ba a MINAH, Saidai babu wani
abinda zamu ce: Sai abinda zai yardar da Ubangijinmu, ba tare da fushi ko yin
musu da abubuwan da Allah ya qaddara ba. Kuma ya dace a lokacin da ake bincike
kan musabbabin faruwar wannan musibar domin daqile aukuwar irinsa a gaba, ko
kuma hukunta wanda yayi sakaci a yanzu = ya dace kada ayi watsi da qoqarin
gomannin dubban masu tsara wannan aiki, da masu hidima wa baqin Allah; waxanda
suke rakiya ga mahajjata a dukkan matakansu da matsayansu, wajen tsara aikin ko
bibiyarsa, suna kuma qoqarin kawo aminci a dukkan hanyoyi, kuma suna tsara
tawagogi, da bada kula ga marasa lafiya, da xora vatacce kan hanya, da nusar da
mahajjata ko karantar da su, da ciyar da mayunwaci, da shayar da masu qishi, da
taimakawa gajiyayye, Ga waxanda suke bada rayuwarsu da dukkan qoqarinsu don
hutun mahajjata da walwalarsu muke miqa yabo da godiya, da kuma yin addu'a, da
qanqan da kai ga Allah kan ya sakanta musu da alheri. Kuma lallai abinda yake
vuya na aikinsu yafi yawa, akan abinda yake bayyana wa mutane. Saidai kawai
muce: Allah ya biya su lada, ya kuma ninninka sakayyarsu.
Saidai
kuma yana cikin fajircin husuma: Wassu mutane su yi amfani da abinda ya faru
don sanya shakka wa jama'a kan qoqarin da ake yi, ko don yin suka kan kyautuka…
. Bayan kuma duniya gabaxayanta ta shaida kan girman kyauta, da manya-manyan
abinda ake qaddamar da shi ga waxanda suka nufo xakin Allah, daga wajen mazauna
Makkah da Madina, xaixaikunsu ne, ko hukumomi. Kuma saboda idan aka rasa kunsa
sai mutumin da ya rasa shi ya iya faxa ko aikata duk abinda yaga dama.
Kuma
lallai yana cikin izgilanci mai xaci: Yayi qoqarin qaqalo kukan rashin SHAHIDAN
MINAH Waxanda a tarihance suka karkashe mutane ko mahajjata, tare da aikata ilhadi
a HARAMI, ta hanyar karkashewa, ko
qone-qone, da shigar da munanan makamai, tare da tsoratar da mahajjata, da
alqawarta azabtar da su, tare da yin qoqarin hana mutane zuwa haramin.
Kuma
yana daga cikin abin mamakin ('yan shi'a) waxanda suke qaqalo kuka ga rayukan
musulmai, waxanda a waiwai suke bayyanar da kwaxayinsu kan kiyaye zuban jinin
musulmai: Lallai su sune suke tuttura gomannin sojojin gona a qasar Iraqi da
Yemen da Siria, don kashe dubban xarurrukan musulmai (sunnah), da qauratar da
miliyoyi daga mahallansu, kuma domin su samu damar taskance manya-manyan siton
makamai a dayawa daga garurrukan musulmai,
kuma sune suke dasa qiyayya a zukatan waxanda suka yaudaru da su, da
kuma laqqana musu faxin kalmomin da ake neman maimaita su, waxanda kuma suke
cike da alqawarin yayyaka uku bisa huxun (3/4) musulmai.
Da fatan Allah ya kare musulmai daga sharrinsu, ya kuma shiryar da waxanda aka
vatar ko kuma waxanda suka ruxar da su. To zuwa ga waxanda suke tiqa rawa akan
ciyo ko raunin da aka samu, waxanda kuma sune suka fi tsananin farin ciki kan
samuwar haka = muke cewa: Lallai maganar "taqiyyah" ta faxi babu
nauyi, kuma wanda yake shakkar cewa ku maqiya ne ya samu tabbaci kan lamarinsa,
kuma gari ya riga ya waye ga duk mai idanu guda biyu, kuma Allah ya sanya
dayawa daga cikin mutane yanzu suna iya tantance gaskiya daga varna, da kuma
wanene maqiyi ko aboki. Kuma duk abinda kuke yi, ihu ne na wanda ya xebe
tsammanin nasara, da gurnanin wanda ya kunyata, saboda babu abinda yau-da-gobe
ya qara muku sai qara kunyata, abubuwan da suke aukuwa –a nan da can- basa qara
muku komai sai ciyo da rauni, Albishirinku da abinda zai faranta wa musulmai,
ku kuma ya baqanta muku, wanda kuma zai yaye baqin ciki wa larabawa da
musulmai, ku kuma ya qasqantar da ku. ….
….
Daga nan sai mai huxubar yayi
Magana akan MASALLACIN QUDUS DA IRIN WALAQANCIN DA YAKE GANI A KWANAKIN NAN A
HANNUN YAHUDAWA, Sannan yace:
Ya
ku mahajjatan xakin Allah mai alfarma …
Ku sani
lallai wannan qasar (masarautar larabawa ta Saudia) da mazajenta, da
na'urorinta da hukumominta, suna yin gagaruman aiyuka don yin hidima a gare ku,
da kuma sauqaqe hajjinku, kuma dukkan tsare-tsare an sanya su ne don
maslaharku, faxi-tashi kuma gabaxayansa don ku ake yi, SAI KU YI AIKI DA
FAXAKARWA, KUMA BI DUKKAN DOKOKI, KU RIKA JINCEWA KU ALHAZAI NE, SAI KU KASANCE
AKAN MAFI ALHERIN HALI CIKIN AIYUKA DA HALAYYA, KUMA KU LAZIMCI NITSUWA DA BI
SANNU-SANNU, DA TSAKAITAWA, Sannan kuma albishirinku; kasancewar ku masu tafiya
ne zuwa ga Ubangiji mai karamci. Allah
ya sanya hajjinku ya zama kuvutacce, aikinku kuma abun godiya, zunubinku kuma
abun gafartawa, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR
WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
Wannn
shine qarshen abinda limamin ya faxa akan wannan lamari. Sai yayi addu'oi.
Wannan shine abinda na so na tunatar da
'yan'uwana akansa, kan wannan lamari mai girma, da fatan Allah ta'alah ya karvi
waxannan bayin a matsayin shahidai a wurinsa, majinyata kuma ya gaggauta basu
lafiya. Sannan ina roqonsa da
sunayensa masu kyau da sifofinsa maxaukaka yak are bayinsa daga aukuwar makamancin
haka, a garin Makkah ko a waninta. Amin.
Abubakar
Hamza Zakariyya,
Madinah, 13/zulhijjah /1436h
Daidai
da 27/ satumba/ 2015m.