SIFFAR
SALLAR ANNABI (S.A.W)
صفة صلاة النبي صلى الله عليه وسلم
Na
Babban Malami
Abdul'aziz dan
Abdullahi Ibnu-Baaz
Tarjamar
Abubakar Hamza
Bismil Lahir
Rahmanir Rahim
Yabo da godiya
sun tabbata ga Allah shi kaxai. Salati da
sallama su qara
tabbata ga bawansa kuma manzonsa; annabinmu Muhammad da Iyalansa da Sahabbansa.
Bayan haka:
Waxannan
kalmomi ne taqaitattu da suke bayanin siffar sallar Annabi (S.A.W) mun yi nufin gabatar da su ga xaukacin Musulmai maza da mata; domin wanda ya leqa
abinda yake cikin takardun ya yi iya qoqarinsa
wajen koyi da Annabi (S.A.W) cikin haka;
saboda faxinsa (S.A.W):
«صَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِي أُصَلِّي».
GA BAYANINTA GA MAKARANCI:
(1)
Musulmi dole ya cika
alwalarsa: Wannan kuma shi ne ya yi
alwala kamar yadda Allah ya umurce shi; yana mai aiki da faxinsa maxaukakin sarki:
ﭽﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙ ﭚﭛﭜﭝﭞﭟﭠ ﭡﭼالمائدة: ٦
Ma'ana: "Ya ku waxanda suka
yi imani idan kuka tashi izuwa ga sallah sai ku wanke fiskokinku da hannayenku
zuwa guiwoyin hannu, ku shafi kayukanku, kafofinku kuma ku wanke su zuwa idon
sawu biyu", [Ma'idah: 6].
Da kuma aiki da faxin Annabi
(S.A.W):
«لا يَقْبَلُ اللَّه صَلاةً بِغَيْرِ طُهُورٍ».
Da kuma faxinsa ga Mutumin da ya munana sallarsa:
«إِذَا قُمْتَ إِلَى الصَّلاَةِ فَأَسْبِغِ الوُضُوءَ».
(2) Sai Mai sallah ya fiskanci alqiblah; -Wacce: ita ce ka'abah- Zai fiskance ta a ko-ina yake a cikin Duniya, da xaukacin jikinsa, yana mai nufan sallar da ya ke
nufi; ta nafila ce ko ta farilla da zuciyarsa, amma ba zai furta niyyarsa ba da
harshensa; saboda furta niyyah ba shari'a ba ne; dalili kuwa shine Annabi (S.A.W)
da sahabbansa (R.A) basu furta ta ba. Sai kuma ya sanya "SITRAH" a
gaba gare shi; ya yi sallah zuwa gare ta; in ya kasance liman ne ko kuma Mutumin
da yake sallarsa shi kaxai. Shi kuma fiskantar alqiblah a cikin sallah yana daga cikin sarruxanta (ma'ana: idan ba a aikata shi ba sallar bata inganta), Sai dai a
wassu halaye sanannu da aka togace, waxanda aka yi bayaninsu a cikin littatafan Ma'abota ilimi.
(3) Sai kuma ya yi kabbarar harama; Yana mai cewa: "ALLAHU AKBAR", yana mai dubin gurbin sujjadarsa
da ganinsa.
(4) Yana mai xago hannayensa guda biyu a lokacin kabbararsa
daidai da (setin) kafaxunsa guda biyu, ko kuma daura da kunnuwansu guda biyu.
(5) Zai kuma xora hannayensa guda biyu akan qirjinsa; tafin hannun dama kuma akan tafin hagu;
saboda tabbatan hakan daga Annabi (S.A.W).
(6) Sunna ne ya karanta addu'ar buxe sallah (istiftah); Wacce kuma ita ce:
«اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ
بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبِ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنَ الخَطَايَا كَـمَا
يُنَقَّى الثَّوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ، اللَّهُمَّ اغْسِلْ خَطَايَايَ
بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالبَرَد»([5]).
ALLAHUMMA BA'ID BAINIY WA BAINA KHAXAAYAYA KAMA
BAA'ADTA BAINAL MASHRIQI WALMAGRIBI, ALLAHUMMA NAQQINIY MINAL KHAXAYA KAMA
YUNAQQAS SAUBUL ABYADU MINAD DANASI, ALLAHUMMA IGSIL KHAXAAYAYA BIL MA'I WAS
SALJI WAL BARADI.
In kuma yaso sai ya ce:
«سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ،
وَتَعَالَى جَدُّكَ، وَلَا إِلَهَ غَيْرُك»([6]).
SUBHANAKAL LAHUMMA WA BI HAMDIKA, WA TABARAKA ISMUKA, WA TA'ALAH JADDUKA,
WA LA'ILAHA GAIRUKA.
Idan kuma ya karanta wanin addu'oin nan guda biyu
daga cikin addu'oin buxe sallah,
da suka tabbata daga Annabi (S.A.W) to hakan ya yi kyau. Saidai kuma mafificin abu shine ya aikata
wannan addu'ar a wannan lokacin, wancan kuma a wani lokacin na daban; saboda
yin hakan shi ke nuna "cikakken koyi da Manzon Allah".
Sa'annan sai ya ce: "A'UZU BILLAHI MINASH SHAIXAN AR-RAJIIM, BISMILLAHIR RAHMAN
AR- RAHIIM.
Sanannan sai ya karanta "FATIHAH" gabaxayanta, saboda faxinsa (S.A.W):
«لا صَلاةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ الْكِتَاب».
Sai kuma ya ce: "Aamin" bayan ya gama
karanta ta; a bayyane a sallar da ake bayyana karatu a cikinta.
Sa'annan sai ya karanta duk abin da ya sauwaqa na daga ayoyi ko surorin alqur'ani.
(7)
Daga nan sai ya yi ruku'i
yana mai yin kabbara, tare da xago hannayensa daidai da kafaxunsa, ko
kunnuwansa guda biyu; yana mai sanya
kansa daidai da bayansa, hannayensa guda biyu kuma akan guiwowinsa, tare da
bubbuxe tsakanin
yatsunsa. Dole ne kuma ya nitsu a cikin ruku'insa.
Yana mai cewa: "SUBHANA RABBIYAL AZIIM", Anso ya maimaita haka
sau uku ko fiye da haka. kuma mustahabbi ne ya qara akan haka da faxinsa: "SUBHANAKAL LAHUMMA RABBANA WA BIHAMDIKA ALLAHUMMA IGFIR
LIY".
(8) Sai ya xago kansa daga ruku'i, yana mai xago
hannayensa guda biyu daidai da kafaxunsa guda biyu ko kunnuwansa, yana
mai faxin: "Sami'al lahu liman hamidah"; Idan
liman ne ko kuma mai sallah shi kaxai. Bayan kuma ya riga ya gama tsayuwa sai ya ce: " RABBANA WA LAKAL
HAMD, HAMDAN KASIRAN XAYYIBAN MUBARAKAN FIYHI, MIL'AS SAMAWAATI WA MIL'AL ARDI
WA MIL'A MA BAINAHUMA WA MIL'A MA SHI'TA MIN SHAI'IN BA'ADU".
Amma idan kuma mamu ne to shi a lokacin xagowarsa daga ruku'i zai ce: "RABBANA WA LAKAL
HAMD; HAMDAN KASIRAN XAYYIBAN
MUBARAKAN FIYHI, MIL'AS SAMAWAATI WA MIL'AL ARDI WA MIL'A MA BAINAHUMA WA MIL'A
MA SHI'TA MIN SHAI'IN BA'ADU".
Kuma mustahabbi ne ga kowanne daga cikin liman da mamu su sanya
hannayensu akan qirazansu, kamar yadda
suka aikata hakan a cikin tsayuwarsu; gabanin su yi ruku'i; saboda tabbatan
abin da ke nuna hakan daga Annabi (r); a hadisin Wa'il xan Hujr, da Sahl xan Sa'ad (رضي الله عنهما).
(9) Sai kuma ya yi sujjada, yana mai fara ajiye guiwowin qafofinsa
akan qasa gabanin
hannayensa; idan hakan ya sauqaqa masa; in kuma aikata hakan ya wahalar da shi to sai ya fara gabatar da
hannayensa gabanin guiwowinsa, yana mai fiskantar alqiblah da kan yatsun qafofinsa da hannayensa, tare da haxe tsakanin yatsun hannayensa.
Kuma mutum zai yi sujjada ne akan gabbai guda bakwai; goshinsa tare da
hanci, hannaye guda biyu, da guiwowi biyu, da cikin 'yan yatsun qafofi guda biyu.
Sai kuma ya ce: "SUBHANA RABBIYAL A'ALAH", zai maimaita hakan
har sau uku ko fiye da haka.
Kuma mustahabbi ne ya qara da
cewa: "SUBHANAKAL LAHUMMA RABBANA WA BI HAMDIKA, ALLAHUMMA IGFIR
LIY". Sai ya yawaita addu'oi; saboda faxinsa (r):
«فَأَمَّا الرُّكُوعُ فَعَظِّمُوا فِيهِ الرَّبَّ عَزَّ وَجَلَّ،
وَأَمَّا السُّجُودُ فَاجْتَهِدُوا فِي الدُّعَاءِ، فَقَمِنٌ أَنْ يُسْتَجَابَ
لَكُمْ».
Ma'ana: "Amma shi
ruku'i to sai ku girmama ubangiji a cikinsa, Shi kuma sujjada ku yi qoqarin addu'oi
a cikinsa; ya cancanci a amsa muku"([8]). Sai mutum ya
roqi ubangijinsa
alkhairin duniya dana lahira, sawa'un sallar ta farilla ce ko ta nafila.
Sannan ya kuma nisantar da damatsunsa daga kuivinsa, ya nisanta cikinsa ga
cinyoyinsa, suma cinyoyin sai ya nisanta su daga kwabrin qafofinsa guda biyu, yana mai xage zira'ansa guda biyu daga qasa; saboda faxin Annabi (r):
«اعْتَدِلُوا فِي السُّجُودِ، وَلا يَبْسُط أَحَدُكُمْ ذِرَاعَيْهِ
انْبِسَاطَ الْكَلْبِ».
Ma'ana: "Ku daidaita
a cikin sujjadarku, kada xayanku ya
shumfuxa
zira'insa kamar yadda kare ke shumfuxawa"([9]).
(10)
Sai kuma ya xago kansa
daga sujjada, tare da faxin "ALLAHU AKBAR" yana mai shumfuxa dugadugin qafarsa ta hagun tare
da zaunawa akanta, ya kuma kafe qafarsa ta dama, sai kuma ya xora tafukansa guda biyu akan cinyoyinsa guda biyu da guiwarsu, yana mai
cewa:
RABBI IGFIR LIY, WARHAMNIY, WARZUQNIY, WA AFINIY, WAJBURNIY.
Wajibi ne mutum ya nitsu a cikin wannan zaman.
(11)
Sa'annan sai ya yi sujjada ta
biyu, tare da faxin "ALLAHU AKBAR", Zai aikata kwatankwacin abin da ya aikata a cikin sujjadarsa ta farko.
(12)
Sa'annan sai ya xago kansa
yana mai yin kabbara, Sai kuma ya yi
zama takaitacce kamar irin zaman da ke kasancewa tsakanin sujjadai biyu, ana
kiran wannan zama "JILSATUL ISTIRAHA", hukuncin aikata hakan kuma
mustahabbi ne, ta yadda idan da bawa zai bar aikatata to da babu komai akansa,
kuma ba a yin wani"zikiri ko addu'a a cikin wannan zama".
Daga nan sai mutum ya zabura izuwa ga raka'a ta biyu, yana mai dogara -a
lokacin tashinsa- akan guiwowinsa guda biyu, idan hakan ya yi masa sauqi, in kuma da wahala to sai ya
dogara akan qasa. Sa'annan sai ya
karanta "FATIHA" da kuma abin da ya sauwaka na alqur'ani bayan fatihar.
(13)
Sa'annan
sai ya aikata kwatankwacin abubuwan da ya aikata a raka'arsa ta farko.
Idan sallar
mai raka'oi biyu ce, kamar sallar asuba
da juma'a da idin azumi ko layya To sai ya zauna bayan xagowarsa daga sujjada ta biyu, yana mai kafe kafarsa
ta dama, tare da shumfuxa kafarsa ta hagu, yana mai xora hannunsa na dama akan cinyarsa ta dama, da dunkule 'yan yatsunsa gabaxayansu in banda manuniyar yatsa;
yana mai nuni da ita zuwa ga tauhidi, idan kuma da zai damqeqaramar yatsa da wacce ta ke biye da ita, sai kuma ya lankwashe babbar yatsarsa
tare da ta tsakiya, sai kuma ya yi nuni da manuniya to hakan ya yi kyau; saboda dukkan sifofin guda biyu sun tabbata
daga Annabi (r). Amma mafificin abu shi ne ya
aikata wannan a wannan lokaci, xayan kuma a wani lokacin na daban. Sai kuma ya
sanya hannunsa na hagu akan cinyarsa ta hagu da guiwarsa, Sa'annan ya yi
"TAHIYA" a wannan zaman, wanda kuma shi ne: "ATTAHIYYATU LIL LAHI WAS-SALAWATU WAX-XAYYIBATU,
ASSALAMU ALAIKA AYYUHAN NABIYYU WA RAHMATUL LAHI WA BARAKATUHU, ASSALAMU ALAINA
WA ALA IBADIL LAHIS SALIHINA, ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, WA ASH-HADU ANNA
MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUH"([11]).
Sa'annan sai mutum ya ce: "ALLAHUMMA
SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMA SALLAITA ALA IBRAHIMA WA ALI
IBRAHIMA; INNAKA HAMIDUN MAJID, WA BARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMADIN
KAMA BARAKTA ALA IBRAHIMA WA ALI IBRAHIMA; INNAKA HAMIDUN MAJID"([12]).
Sa'annan sai ya nemi tsarin Allah daga munanan abubuwa guda huxu; ya ce:
«اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ
عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَـرِّ
الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ».
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MIN AZABI JAHANNAM, WA MIN AZABIL QABRI, WA
MIN FITNATIL MAHYA WAL MAMATI, WA MIN SHARRIL MASIHID DAJJAAL.
Ma'ana: "Allah ina
neman tsarinka daga azabar jahannama, da kuma azabar kabari, da kuma fitinar
rayuwa da ta mutuwa, da kuma fitinar mai shararren ido; dujjal".
Sa'annan sai ya yi duk addu'ar da ya ga dama; na
alherorin duniya da lahira. Kuma idan da zai yi addu'a ga iyayensa ko kuma ga
waninsu daga cikin musulmai to da haka ya yi kyau; sawa'un sallar ta farilla ce ko ta nafila; saboda gamewar faxinsa (r) a cikin hadisin Abdullahi xan Mas'ud a yayin da ya koyar da shi "TAHIYA":
«ثُمَّ لِيَتَخَيَّرْ مِنَ الدُّعَاءِ أَعْجَبَهُ إِلَيْهِ
فَيَدْعُو به».
Ma'ana: "Sannan sai
ya zavi
abinda ya burge shi na addu'a; sai yaroqi a bashi"([13]). A wani
lafazin kuwa:
«ثُمَّ يَتَخَيَّرُ مِنَ
الْمَسْأَلَةِ مَا شَاءَ».
Wannan kuma ya game dukkan abinda zai amfanar da bawa a rayuwarsa ta
duniya, da kuma ta lahira.
Daga nan sai ya yi sallama, ta bangarensa na dama,
dana hagu, yana mai cewa: AS-SALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAHI, AS-SALAMU ALAIKUM
WA RAHMATUL LAH,
(14)
In
kuma sallar tasa mai raka'oi uku ce, kamar sallar magriba, ko hudu kamar sallar
azahar da la'asar da ishah, To a nan zai karanta TAHIYAR da ta gabata,
sannan ya yi SALATI ga Manzon Allah (r). Daga nan
sai ya miqe a tsaye, yana dogara akan guiwowinsa, tare da xaga
hannayensa daidai da kafaxunsa yana mai cewa: ALLAHU AKBAR, Sai kuma ya xora su akan qirjinsa,
kamar yadda ya gabata. Sai ya karanta surar FATIHA kawai. In kuma a wassu
lokuta ya karanta wassu sashin surori bayan fatihar, to babu laifi; saboda ya
tabbata cewa wani lokaci Annabi (r) yana
karanta "sura" a waxannan raka'oin bayan fatiha, kamar yadda hakan
ya tabbata a hadisin Abu-sa'id (t) ([15]).
Kuma idan da mutum zai bar yin salati ga Annabi a cikin tahiyar
farko to babu komai; saboda yinsa a tahiyar farko mustahabbi ne ba wajibi ba.
Sa'annan sai ya yi tahiya bayan raka'a ta uku, a sallar magriba,
da kuma bayan ta huxu a sallar azahar da la'asar da isha'i, kamar yadda hakan
ya gabata a sallah mai raka'oi guda biyu.
Sa'annan ya yi sallama ta dama da shi da kuma ta hagu.
Sannan sai ya ce: ASTAGFIRULLAH, sau uku.
Sai kuma ya ce:
«اللهُمَّ أَنْتَ السَّلاَمُ،
وَمِنْكَ السَّلاَمُ، تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالإِكْرَامِ».
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ
لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ».
"LA ILAHA ILLAL
LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI
SHAI'IN QADIIR"([17]).
«اللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا
أَعْطَيْتَ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ
الْجَدّ».
"ALHUMMA LA MANI'A
LIMA A'AXAITA, WALA MU'UXIYA LIMA MANA'ATA, WALA YANFA'U ZAL JADDI MINKAL
JADDU"([18]).
«لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ
لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ
قَدِيرٌ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللَّهِ، وَلَا نَعْبُدُ إِلَّا
إِيَّاهُ، لَهُ النِّعْمَةُ، وَلَهُ الْفَضْلُ، وَلَهُ الثَّنَاءُ الْحَسَنُ، لَا
إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ».
"LA ILAHA
ILLAL LAHU; WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA
KULLI SHAI'IN QADIIR. LA HAULA WALA QUWWATA
ILLA BILLAH, WALA NA'ABUDU ILLA IYYAH, LAHUN NI'IMATU WA LAHUL FADL, WA LAHUS
SANA'UL HASAN, LA ILAHA ILLAL LAHU, MUKHLISIYNA LAHUD DINA, WA LAU KARIHAL
KAFIRUUNA"([19]).
Sannan ka yi SUBHANAL LAHI sau talatin da uku (33).
Ka ce ALHAMDU LIL LAHI sau talatin da uku (33).
Sai ka ce: ALLAHU AKBAR sau talatin da uku (33).
Sannan sai ka faxi cikon xarin: LA ILAHA ILLAL LAHU; WAHDAHU LA
SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIIR.
Sai kuma ya karanta "ayatul kursiyyi", da QUL HUWAL
LAHU AHAD, da QUL A'UZU BI RABBIL FALAQ, da
QUL A'UZU BI RABBIN NAAS. Bayan kowace sallah.
Kuma mustahabbi ne ya maimaita surorin nan guda uku, sau uku,
bayan sallar asuba da magriba, saboda hadisi ingantacce da ya zo akan haka,
daga Manzon Allah (r) ([20]).
Kamar yadda kuma mustahabbi ne, ya yi qari
akan zikirin da ya gabata, bayan sallar magriba da asuba, ta hanyar faxin:
LA ILAHA ILLAL LAHU; WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WA
LAHUL HAMDU, YUHYI WA YUMIYTU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIIR. Saboda
tabbatan hakan daga Manzon Allah (r).
Idan liman ne an so bayan ya yi ASTAGFIRULLAHI sau uku, ya kuma
faxi "ALLAHUMMA ANTAS SALAMU WA MINKAS…"([21]) mustahabbi ne a gare shi ya juya zuwa ga mutane, yana mai
fiskantarsu Sa'annan sai ya zo da sauran zikirorin da su ka gabata, kamar yadda
hadisai da yawa daga Annabi (r) su ka yi
nuni akan haka, Daga cikinsu akwai hadisin A'ishah (t) a cikin
sahihu Muslim([22]).
Su kuma waxannan zikirorin
dukkansu sunnoni ne; babu na farilla.
Kuma an shar'anta wa kowani musulmi namiji da mace da su yi
raka'oi guda huxu gabanin sallar la'asar, da raka'oi biyu bayanta, bayan sallar
magriba kuma raka'oi biyu, bayan isha'i raka'oi biyu, haka kuma gabanin sallar
asuba raka'oi biyu, gabaxaya za su zama
raka'oi guda goma sha biyu (12), waxannan
raka'oin kuma ana kiransu sallolin RAWATIB, saboda Annabi (r) ya kasance
yana aikata su a halin zaman gari, amma a halin kasancewarsa matafiyi kuma ya
kan bar aikata su, in banda raka'oi guda biyu na sunnar alfijir (da ake yinsu
bayan ketowarsa) da kuma witiri, waxannan
biyun kam Annabi (r) ya kasance
yana kiyaye su a halin zaman gida da kuma yanayi na tafiya.
Kuma abinda ya fi falala shine a yi sallolin rawatib da witiri a
cikin gidaje, amma idan da mutum zai yi su a cikin masallaci to babu laifi akan
haka, saboda faxin Annabi (r):
«أَفْضَل الصَّلاَة صَلاَة الْمَرْءِ
فِى بَيْتِهِ إِلاَّ الْمَكْتُوبَةَ».
Kiyaye yin aiki da waxannan nafilfilin yana daga sabbuban shiga
aljannah, saboda faxin Annabi (r):
«مَنْ صَلَّى اثنْتَيْ عَشْرَةَ
رَكْعَةً فِي يَوْمه وَلَيْلَته تَطَوُّعًا، بنى الله لَهُ بَيْتًا فِي الْجَنَّة».
Ma'ana:
"Duk wanda ya kiyaye raka'oi guda goma sha biyu (12) cikin yininsa da
darensa na nafila, Allah zai gina masa gida a cikin gidan aljannah"([24]). Muslim ya ruwaito shi a cikin "sahihinsa".
Idan da kuma mutum zai yi raka'oi
guda huxu gabanin yin sallar la'asar, da raka'oi biyu gabanin magriba, da wassu
biyun bayan isha to hakan ya yi kyau, saboda abinda yake nuni akan hakan ya
tabbata daga Annabi (r).
Haka kuma da zai sallaci raka'oi
guda huxu bayan azahar, da wassu huxun gabaninta to wannan shima ya yi kyau, saboda faxinsa
(r):
«مَنْ حَافَظَ عَلَى أَرْبَعِ
رَكَعَاتٍ قَبْلَ الظُّهْرِ، وَأَرْبَعٍ بَعْدَهَا، حَرُمَ عَلَى النَّارِ».
Ma'ana:
"Duk wanda ya kiyaye raka'oi guda huxu gabanin azahar, da guda huxu
bayanta, to ya haramta ga wuta"([25]). Imam Ahmad ne da ma'abuta littatafan "sunan"; (wato:
Abu-dawud, Tirmiziy, Nasa'iy da Ibnu-majah) su ka ruwaito shi da isnadi
ingantacce, daga Ummu-Habibah (رضي الله عنها). Ma'ana a nan shi ne: Bawa zai yi qarin
raka'oi guda biyu bayan "sunna ratiba" da ake yinta raka'oi biyu
bayan azahar, domin sunna ratibar ita ce a yi raka'oi huxu gabanin azahar da
kuma biyu bayanta; don haka idan ya qara biyu akan haka sai abinda aka ambata
cikin wannan hadisin da Ummu-habibah (رضي الله عنها) ta ruwaito ya samu.
Allah shine majivincin dacewa!
Salati da
sallama su qara tabbata ga annabinmu
Muhammadu xan Abdullahi, da kuma iyalansa,
da sahabbansa, da waxanda su ka bi su da kyautatawahar zuwa ranar sakamako.
([6]) Wannan lafazi ya zo daga maganar Annabi (S.A.W, da ake masa laqabi da: marfu'i), ta
hanyar Abu-sa'id da A'ishah (رضي الله عنهما), a
wajen Abu-dawud, (lamba: 775, 776), Shi kuma Imam Muslim ya fitar da shi daga
maganar Umar bn Alkhaxxab
–t- (wato: Mauqufi, da lamba: 399) daga
hadisin Abu-hurairah (R.A).
No comments:
Post a Comment