بسم الله الرحمن الرحيم
HARAMCIN ASKE GEMU
Dan'uwana
Mai girma: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATUL LAHI WA BARAKATUHU.
Ina gabatar maka da kyautar wadannan
kalmomin, kuma ina fatan su samu gurbi a cikin zuciyarka.
Dan'uwana
Masoyi: Ka san lallai Annabi SAW shine abin koyinmu, kuma wajibi ne
akanmu mu bishi ta hanyar aiki da umurninsa da nisantar haninsa, kuma hakika
annabi SAW ya ce: "Ku sabawa mushrikai ku cike
gemu ku rage gashin baki", saboda haka; aske gemu haramun ne da
ijma'in mazhabobi guda hudu, kuma ya saba wa shiriyar Manzanni, kuma yin
kwaikwayo ne ga kafirai, kuma ya zo a
cikin hadisi: "Wanda ya kwaikwayi wasu mutane
to yana daga cikinsu", Kuma babu wani Musulmin da yake aikata
hakan a zamanunnukan da suka gabata.
Sai ka yi da'a ga Annabinka, kuma ka rika
kwaikwayonsa; domin a tayar da kai karkashin tutarsa, kuma ka sha daga
dausayinsa.
Kuma ka rika saba wa son zuciyarka; domin
ka rabauta da shiga Aljannonin ni'ima.
No comments:
Post a Comment