2019/03/14

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI Dr Salah Albudair kan KIYAYE SALLOLIN FARILLAI المحافظة على الصلوات المفروضة










HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/RAJAB/1440H
daidai da 15/MARIS/2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR

TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
KIYAYE SALLOLIN FARILLAH
(المحافظة على الصلوات المفروضات)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Al-Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KIYAYE SALLOLIN FARILLAH, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
A
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Allah ya bayyana wa Mutane alamomin addininsu, kuma ya fito musu da abinda shari'arsa ta shar'anta a fili, kuma ya farlanta wa Bayinsa kiyaye da dawwama akan salloli biyar da aka farlanta, aka wajabta, wadanda aka saba yinsu cikin yini da dare, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku tsare lokatan salloli da salla mafificiya, kuma ku tsayu ga Allah kuna masu kankan da kai a gare shi" [Bakara: 238].
Kuma wanda ya bar sallah da ganganci, yana mai kin yinta, da ramukonta, da tsayar da ita, to bashi da rabo a Musulunci. Wanda kuma ya yi sallah, kuma yake dogewa akan yinta, sai a masa shaida da Musulunci.
An ruwaito daga Jabir dan Abdullahi (Allah ya yarda da shi) ya ce: Na ji Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- yana cewa:  "Tsakanin Mutum da shirka da kafirci shine barin sallah", Muslim ya ruwaito.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi dan Shakik, Tabi'iy -Allah ya yi masa rahama- ya ce: "Sahabban Annabi Muhammadu SAW sun kasance babu wani aikin da suke ganin barinsa kafirci ne, in banda sallah" Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga AbudDarda'i -رضي الله عنه- ya ce: "Badadina -صلى الله عليه وسلم- ya min wasiyya da cewa: Kada ka yi shirka da komai ga Allah, koda za a sassara ka, a kona. Kuma kada ka bar sallar farilla, da gangani, saboda idan Mutum ya barta da gangan, to lallai zimma ta barranta daga gare shi. Kuma kada ka sha giya, domin giya mabudin dukkan sharri ce", Ibnu-Majah ya ruwaito shi.
Ya yi hasara, wanda ya bar sallah kuma ya tabe
Kuma ya ki makoma tagari da zai koma!

idan ya kasance yana musun wajabcinta, to lallai shi
Ya yi yammaci yana wanda ya kafirce da Ubangijinka, mai shakka

Idan kuma ya bar salla saboda wata kasala ce
to lallai ya lullube gaskiya da wani shamaki

Ya ku Musulmai
Malamai sun yi ijma'i akan kasancewar salloli biyar an sanya musu lokatai iyakantattu, kuma lokacin sallah yana da farko da karshe, baya halatta ga Musulmi ya yi sallar farillah gabanin lokacinta, kuma baya halatta ya fitar da ita ko ya jinkirta daga lokacinta, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne sallah ta kasance akan muminai farilla ce mai kayyadaddun lokuta", [Nisa'i: 103].
Abdullahi dan Mas'ud -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Lallai sallah tana da kayyadadden lokaci, kamar hajji".
Kamar yadda baya halatta ayi hajji ba a watanninsa ba, ko ya tsaya a filin Arfah bayan lokacinsa, ko ya yi juma'a a ranar asabat, to haka kuma baya halatta ya yi sakaci a al'amarin lokatan sallolin farillah.
Kuma lallai Allah ya yi narko ga masu sallah wadanda suke fitar da sallar farilla daga lokacinta da shari'a ta kaddara mata; har ya zama basu yinta sai bayan fitan lokacinta, a inda Allah Mabuwayi da daukaka yake cewa:  "To, bone ya tabbata ga masallata * wadanda suke masu shagalta daga sallarsu" [Ma'una: 4-5].
Kuma wannan shine halin munafikai da fasikan Musulmai, wadanda suke yin sallar yini a cikin dare, suke yin sallar dare a cikin yini, suke yin sallah yadda suka ga dama, ba yadda ya dace da sharadin ingancin ibadarsu ba, suna aikata haka suna masu sakaci da lamarin sallah, da fasikci, da fitsaranci, da kuma sakaci da hakkinta.
An ruwaito daga Naufal dan Mu'awuyah -رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda sallah ta kufce masa, to kamar an wawashe masa iyalansa da dukiyarsa", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi.
Wawasasshe shine wanda aka kashe masa makusanci, ko aka debe dukiyarsa, sai bai riski hakkinsa ko ya samu damar daukar fansa ba.
Fiskar da suka yi kamantacceniyar, itace lallai wanda sallah ta kufce masa, hakika bakin cikin sabo da bakin cikin rashin samun lada sun hadu akansa, kamar yadda mutumin da aka wawashe shi bakin cikin dauke masa abu, da bakin cikin nema sun hadu akansa.
Kuma abinda ake nufi da "kubucewar sallah", shine jinkirta ta da fitar da ita daga lokacinta na halacci, ba tare da wani uzuri ba.
An tambayi Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah -رحمه الله تعالى- ga Mutumin da ya bar sallah guda daya, da ganganci, da niyyar zai sallace ta bayan fitan lokacinta, a matsayin ramuko, Shin wannan aikin laifi ne babba daga cikin alkaba'irai?
Sai ya amsa: Jinkirta sallah da fitar da ita daga lokacinta da ya wajaba a aikata ta a cikinsa da ganganci yana daga manyan laifuka (Kaba'irai). Kuma ya ce: Duk wanda ya bar sallah guda daya da ganganci, to hakika ya aikata laifi mai girma na kaba'ira. Sai ya yi kokarin gyarawa, da abinda ya samu iko; na tuba, da kuma ayyuka na-kwarai. Kuma koda ya yi ramukonta, to wannan ramukon kawai, ba zai dauke masa zunubin abinda ya aikta ba, da ijma'in Musulmai.

Ya ku Musulmai!
Wanda kuma ya bar sallah da mantuwa, ko barci, to wajibi ne ya ramata; Sai mai barci ya yi ramuko idan ya farka, wanda kuma ya yi mantuwa, idan ya tuna, saboda hadisin Anas -رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, ko kuma ya yi barci bai sallace ta ba, to kaffararta shine ya sallace ta idan ya tuna ta, bata da wani kaffarar in banda haka (KUMA KA TSAYAR DA SALLAH DOMIN AMBATONA) [Daha: 14]", Bukhariy da Muslim.
Kuma an ruwaito daga Abu-Katadah -رضي الله عنه- lallai sun ambata wa Annabi -صلى الله عليه وسلم- lamarin barcinsu basu yi sallah ba, sai ya ce: "Sai ya ce, Babu sakaci a al'amarin barci, sakaci yana nan ne ga wanda yake farke, Idan dayanku ya manta wata sallah, ko ya yi barci bai yi ba, to ya sallace ta idan ya tuna ta".
Ibnu-Abdulbarri -رحمه الله تعالى- ya ce: "Kebance mai barci da wanda ya manta sallah da aka yi da ambato, a al'amarin ramukonta, babu abinda ya sauke lamarin biyanta ga wanda ya yi gangancin barinta har lokacinta ya fita. Bal, a cikin lamarin akwai dalilai masu karfi, cewa lallai wanda ya barta da ganganci (mai zunubi) shine yafi cancantar a umurce shi da yin ramuko, fiye da wanda yayi mantuwa wanda aka masa rangwame, da mai barci mai uzuri. Shi wanda ya yi gangancin barinta babu makawa, yana tune da ita, sai ya zama wajibi akansa ya rama wannan sallar, sai kuma ya yi ta neman gafara, akan jinkirta yinta".
Wasu Ma'abuta ilimi kuma suka ce: Wanda ya bar sallah da ganganci, ba a shar'anta masa ramukonta ba, kuma ko ya yi bata inganta daga gare shi. Kuma wajibi ne akansa ya yi ta tuba.

Ya ku Musulmai!
Yana daga cikin sakaci, yin barci bayan shigan lokacin sallah, ga wanda yake rinjayar da zaton cewa barcinsa zai cinye lokacin sallar farillah, har lokacinta ya fita, ko kuma zababben lokacinta, Saidai idan ya aminta cewa wani zai tayar da shi, ko kuma ya rinjaya a zatonsa cewa, zai iya tashi da agoganni masu fadakarwa.
Kuma (Mutum) ba zai jinkirta sallar la'asar ba tare da uzuri ba, zuwa lokacin da rana take yin fatsi-fatsi, idan kuma ya aikata haka, to lallai shi mai laifi ne, a daya daga cikin zantukan Maluma guda biyu, saboda fadin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Lokacin sallar la'asar, shine matukar rana bata yi fatsi ba", Muslim ya ruwaito shi.
Da kuma saboda abinda aka ruwaito daga Anas dan Malik -رضي الله عنه-

Ina fadan abinda kuke ji, kuma ina gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance ga masu komawa gare shi, Mai yawan gafara ne.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah wanda a cikin tausasawarSa yake bada mafaka ga mai neman mafakarsa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda cikin ni'imarSa yake bada waraka ga wanda ya debe tsammanin waraka daga cutukansa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonSa, wanda ya bi shi ya samu shiriya, wanda kuma ya saba masa ya bace hanya,
Allah ka yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, salatin da ke wanzuwa, da sallama mai ninkuwa.

Ya ku Musulmai
Yana daga sifofin Ma'abuta imani, kasancewarsu masu fadakakken zukata, masu hankali mai fahimta, suna kiyaye wa Allah umurninSa da haninSa, da alwalinSa da narkonSa, Idan aka karanta musu ayoyinsa, sai su karkata gare su, suna masu ji, masu kiyayewa, masu kula, da kunnuwan da suke jin ayoyin, da kuma zukatan da suke kiyaye su, ba su gafala daga wa'azinsa, kuma ba su girman kai kan ibadarSa, kamar yadda yasassun Mutane suke yi, masu nuna girman kai, kurame wadanda ba su jin gaskiya, makafi wadanda ba su ganin gaskiya, Ubangijinmu ya ce:   "Sune wadanda idan aka tunatar da su ayoyin Ubangijinsu, basu faduwa akansu kuramai, makafi" [Furkan: ].
 Alhasan Albasariy ya ce: "Sau nawa, Mutum yake karanta aya, sai kuma ya fadi akanta kurma kuma makaho".

Ya ku Musulmai
Lallai samun girma da daukaka, da matsayi da fifiko da mukami yana nan, cikin SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI
Ya Allah ka sanya mu daga cikin ma'abuta basira a cikin addini, masu yin sujjada domin kai, masu yin tasbihi da gode maka, masu kankan da kai ga umurninka, masu girmama shari'arka! Ya Ubangijin Talikai
Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad, Mai shiryatarwa, mai ceton Mutane gaba daya
Domin idan Mutum ya masa salati guda daya, Allah Ta'alah zai masa guda goma da shi
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,
            Kuma –Ya Allah- ka yarda da iyalansa da sahabbai, ka hada da mu tare da su, Ya Mai karimci ya Mai baiwa!
            Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai, kuma ka kaskantar da shirka da mushirkai, ka ruguza makiya addini,
Kuma ka game kasashen Musulmai da aminci da wadaci, kuma ka kiyaye kasar harami biyu madaukaka, daga kaidin masu kaidi, da makircin masu masu makirci, da hassadar masu hassada, da kyashin masu kyashi, Ya Ubangijin Talikai!
            Ya Allah ka datar da shugabanmu majibincin lamarinmu mai hidimar harami biyu ga abinda kake so, ka yarda da shi, kuma ka rike makyamkyamarsa da ayyukan da'a da takawa. Ya Allah ka datar da shi da na'ibinsa ga abinda akwai daukakar Musulunci a cikinsa, Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah ka taimaki rundunoninmu masu kiyaye iaykokinmu, Ya Allah ka kiyaye jami'an tsaronmu, kuma ka saka musu da mafi alherin sakamako, Ya Ubangijin Talikai!
            Ya Allah ka gafarta mana kuskurenmu da gangancinmu, da warginmu da kuma gaskenmu, kuma dukkan hakan akwai shi a wurinmu.
            Ya Allah lallai ne muna neman tsarinka daga mummuniyar rana, da mummunan dare, da lokaci mummuna,
            Ya Allah, lallai muna neman tsarinka daga annoba, da zuwan bala'i Ya Ubangijin Talikai
            Ya Allah ka warkar da marasa lafiyanmu, kuma ka bada lafiya wadanda aka jarrabe su daga cikinmu, ka yi rahama ga mamatanmu, ka taimake mu akan mai gaba da mu, Ya Ubangijin Talikai!
            Ya Allah! Ka sanya addu'armu ta zama abar ji, ka daga kiraye-kirayenmu, Ya Mai karramawa, Ya Mai girma, Ya Mai jin kai.




No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...