HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 22/Rajab/1440H
daidai da 29/Maris/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
HIKIMA
(الحكمة)
Shehin Malami
wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi
hudubar juma'a mai taken: HIKIMA,Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya
ta tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan baiwa,
Mai gafarar zunubai, Mai karbar tuba, Mai tsananin ukuba, Ma'abucin
ni'imah, Babu abin bautawa face shi, zuwa gare shi makoma take.
Ina
yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa, wadanda muka sani,
da wadanda bamu sani ba. Godiya tasa ce, da yabo mai kyau, a gare shi nake
dogaro kuma zuwa gare shi tuba take.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, Mai jin kai Mai yawan tuba.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa,
wanda ya zo da hasken sunnah da kuma Alkur'ani.
Ya
Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka
Muhammadu da iyalansa da sahabbansa, wadanda suka taimaki Musulunci, kuma suka
kaskantar da kafirci, har ya kasance a cikin hasara.
Bayan
haka
Ku
ji tsoron Allah Ta'alah kuma ku yi masa da'a, domin babu wanda zai samu rabo
sai ta hanyar yin biyayya a gare shi, kuma babu wanda zai tabe face mai sabon
Allah. Allah Subhanahu ya ce: "Kuma
wadanda suka yi da'a ga Allah da Manzonsa, to wadannan suna tare da wadanda
Allah ya yi ni'ima a gare su, daga Annabawa da masu yawan gaskatawa, da masu
shahada, da salihai, kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya" [Nisa'i:
69].
Kuma Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to
lallai yana da Jahannama, yana mai dawwama a cikinta har abada" [Jin:
23].
Ya
ku Bayin Allah
Kowane
Mutum yana son, kuma yana fatan kuma yana kokarin ya kasance a mafi kyan hali, kuma
akan mafi girman sifofi, kuma ya kasance da'iman akan hanya mafi mikewa, kuma
da'iman ya kasance tabbatacce akan tafarki madaidaici, wanda Allah ya hada masa
alkhairin rayuwa, da alkhairin mutuwa.
Kuma
kowane Mutum yana kin tabewa da hasara da kaskanci da karanta da munanan sifofi
da dabi'u ababen ki, da hanyoyin wulakanci da tabewa da bata, kuma yana kin mummunan
karshe cikin dukkan halaye,.
Kuma
kowane Mutum yana son ya tunkude wa kansa sharrori da abubuwa masu halakarwa,
kuma yana yin kokarin haka, da dukkan abinda yake da iko akansa na sabubba masu
tseratarwa.
To, shin
akwai hanyar samun wadannan ababen neman madaukaka? Kuma shin rabauta da
wadannan alherorin, da tsira daga sharrace-sharracen rayuwa, da fitinoni masu
batarwa, da munanan karshe cikin al'amura, shin wannan abu ne mai yiwuwa?
E, abu ne
mai yiwuwa, ga wanda Allah ya saukake masa.
Lallai
hanyar samun wadancan alkhairorin, da tunkude karshe na sharri, a cikin wannan
rayuwar da bayan mutuwa, hanya ce guda daya, kuma hanya ne mikakke, wanda babu
na biyunsa, Wannan kuma ita ce, HIKIMA, da ma'anarta faffada mai gamewa, Allah
Ta'alah ya ce: "Yana
bayar da hikima ga wanda ya so, kuma duk wanda aka bashi hikima to lallai an
bashi alkhairi mai yawa, Amma babu mai wa'azantuwa face ma'abuta hankula" [Bakara:
269].
Amma
hanyoyin kaucewa hikima da nisantarta, to lallai suna da yawa, babu mai
kididdige iyakarsu in banda Allah Ta'alah, Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa:
"Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin
Shedan, domin duk wanda ya bi, hanyoyin Shedan, to lallai yana yin umurni da
alfasha da munkari" [Nur: 21].
Kuma
hanyoyin Shedan dukansu wauta ne da bata, saboda wanda ya fara binsu shine
Iblisu wanda yafi dukkan wawaye wauta, Allah Ta'alah ya fada a cikin suratul
jin ya fada: "Kuma lallai wawanmu (Iblisu) ya kasance
yana fadar abinda ya ketare haddi ga Allah" [Jin: 4]. Maluman
tafsiri suka ce, abinda ake nufi da Wawa a cikin wannan ayar, shine Iblisu.
Kuma Allah
ya kira, mabiyansa da suna wawaye, ainda ya ce: "Kuma
wawaye daga cikin Mutane za su ce: Menene ya juyar da su daga alkiblarsu wadda
suka kasance akanta? Ka ce: Allah ne yake da gabas da yamma, yana shiryar da
wanda ya so zuwa ga tafarki madaidaci" [Bakara: 142].
Kuma ya
sifanta masu yin shirka ga Allah da dabi'ar wauta, wanda ita ce rashin basira,
da karancin hankali, Allah Ta'alah: "Kuma babu mai gudu
daga akidar annabi Ibrahimu face wanda ya wautar da kansa, kuma hakika mun zabe
shi a cikin duniya, kuma lallai shi a lahira hakika yana daga cikin salihai * A
lokacin da Ubangijinsa ya ce masa: Ka sallama, ya ce: Na sallama ga Ubangijin
talikai" [Bakara: 130-131].
Don haka, hanyoyin
wauta suna da yawa, kuma dukkansu suna komawa zuwa ga nau'ukan kafirci da
munafurci da manyan zunubai na kaba'ira da sabo.
Kuma
daidaikun hanyoyin wauta suna yin daura da daidaikun hikima.
Kuma
maganganun Maluman tafsiri sun kasance nau'i-nau'i, wajen bayanin menene
hikima, Imamul Bagawiy ya fada a tafsirin fadin Allah Ta'alah: "Wannan
yana daga abinda Ubangijinka ya maka wahayi na" [Isra'i:
39].
Ya ce: "Dukkan abinda Allah ya yi umurni da shi (yinsa), ko ya yi
hani akansa (barinsa) hikima ne".
Kuma Bagawin
ya ce dangane da fadinsa madaukakin sarki: "Sai
Allah ya bashi mulki da hikima" [Bakara:]. Ya ce: Shine
ilimi da aiki da shi.
Kuma ya
ce, a tafsirin: "Yana bayar da hikima ga wanda ya so" [Bakara]. Mujahid ya ce: "Alkur'ani
da ilimi da fikihu",
Ibnu-kasir
-Allah ya yi masa rahama- a tafsirinsa na fadin Allah: "Kuma
muka bashi hikima" [:] ya ce: Katadah ya ce: "Littafin Allah, da bibiyar abinda yake cikinsa".
Mujahid kuma ya ce: Dacewa da daidai.
Don haka,
HIKIMA, ma'anoni masu yawa, sune ILIMIN SHARI'A DA AIKI DA SHI, DA YIN DACE DA
DAIDAI A CIKIN ZANTUKA, DA YIN HUKUNCI DA NASSOSIN SHARI'A AKAN AYYUKA, DA
AMFANAR DA HALITTU DA DUKKAN NAU'UKAN AMFANIN DA AKE DA IKO AKANSA, cikin
gaskiya da tsarkin kirji, da tsarkake niyya ga Allah Ta'alah, domin neman ladansa,
da guje wa ukubarsa,.
Kuma mafi
girman hikima shine abinda Allah ya yi mana wasici da shi a cikin littatafinsa,
kamar yadda ya zo a cikin suratul An'aam, a cikin fadinsa: "Ka
ce; ku zo in karanta abinda Ubangijinku ya haramta akanku, (wajibi ne) kada ku
yi shirkar komai da shi, kuma ga mahaifa biyu ku kyautata musu kyautatawa, kuma
kada ku kashe diyanku saboda talauci, mune muke azurta ku da da su, kuma kada
ku kusanci abubuwan alfasha, abinda ya bayyana daga gare ta, da abinda ya boyu
kuma kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta, face da hakki, Wannan ne Allah
ya muku wasiyya da shi, tsammaninku za ku hankalta * Kada ku kusanci dukiyar
maraya, face ta hanyar da take itace
mafi kyau, har ya kai ga karfinsa, kuma ku cika mudu da sikeli da
adalci, ba mu kallafa wa rai face iyawarta, kuma idan za ku fadi magana to ku
yi adalci, koda ya kasance ma'abucin zumunci ne, kuma da alwarin Allah ku cika,
Wannan ne ya muku wasiyya da shi, tsammaninku za ku wa'aztu * Kuma lallai
wannan ne tafrkina madaidaici, sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi sai
su rarraba da ku daga barin hanyata, Wannan ne Allah yake muku wasiyya da shi,
tsammaninku za ku yi takawa" [An'am: 151-153]. Wannan ayar, da ayoyi
biyu bayanta.
Sa'annan
sai wasiyyoyin Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- kamar fadinsa, alokacin hajjin bankwana: "Ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku yi sallolinku biyar,
kuma ku rika yin azumin watanku, kuma ku rika biyayya ga ma'abucin lamarinku
(shugaba), sai ku shiga Aljannar Ubangijinku", Ahmad ya ruwaito
shi daga hadisin Abu-umamah -رضي الله عنه-.
Sa'annan
sai wasiyyoyin ma'abuta hikima Muminai.
Kuma yana
daga cikin wasiyyoyin da suka fi tattara alkhairi, wasiyyar Mutum salihi, wato
Lukman -عليه السلام-wanda Allah
Ta'alah ya bashi hikima, sai yake fada akansa: "Kuma
a lokacin da Lukman yace wa dansa, alhalin yana masa wa'azi, Ya karamin dana!
Kada ka yi shirka ga Allah, lallai shirka zalunci ne mai girma",
[Lukman: 13]. Sai ya yi wasiyya ga Mutumin da yafi so, da yin Tauhidi ga
Ubangiji Mabuwayi da daukaka, kuma ya hane shi yin shirka ga Allah a cikin
nau'ukan ibada. Wannan kuma shine samun rabo a Duniya, da sababin tsira a
Lahira, kuma shine matattarar alheri gabadayansa.
Sai ya
kwadaitar da shi kan aikata alheri, koda ya kasance kadan ne. Ya kuma tsawatar
wa dansa dangane da aikata sharri, koda kuwa daidai da kwayar zarra ne, domin
Allah zai halarto da shi, kuma ya yi sakayya akansa.
Sai ya yi
wasici ga dansa da ya rika tsayar da sallah, yana mai cika ta, yana kyautata
ta.
Kuma ya
masa wasiyya da riko da dabi'ar umurni da kyakkyawa da hani kan mummuna, saboda
yin hakan lamari ne mai karfi, kuma farilla ne daga Ubangiji Madaukaki. Kuma
sai ya masa wasici da yin hakuri akan wannan, saboda Mutane suna cutar da wanda
yake kishiyantarsu cikin hana su abinda suke so, kuma saboda ibadar hakuri tana
da mafi girman sakamako.
Kuma sai
ya masa wasiyya da kyawawan dabi'u da tawali'u, da kuma ya lazimci natsuwa a
cikin tafiyarsa da maganarsa.
Kuma
lallai mun sani muna masu tabbaci cewa lallai Lukmanu ya yi wasiyya ga dansa
kan biyayyar iyaye, saidai Allah Ta'alah da kansa ya jibinci al'amarin wasici
da iyaye biyu, saboda girman lamarin biyayya a gare su, sai Allah ya kawata
wasiyyoyin Lukman da wasiyyarsa Mabuwayi da daukaka akan biyayya ga iyaye biyu,
a bayan wasiyyar Lukman cewa a kula da hakkin Allah.
Wadannan
wasiyyoyin sune hikimar da tafi kyau, kuma yin aiki da su yana tabbatar da
hikima a cikin rayuwa.
Kuma yana
daga cikin asiran wannan surar mai girma, yadda Allah Mabuwayi da daukaka a
farkon surar ya sifanta Alkur'ani da cewa shi Mai hikima ne. Kuma Allah ya
sifanta kansa a wannan surar da cewar shi: Mabuwayi ne Mai hikima, da kuma
"Lallai ne Allah Mabuwayi ne Mai hikima".
Wadannan
wasiyyoyi masu hikima daga Lukman, sun dace da abinda ya zo a farkon suratul
Isra'i na umurce-umurce da hani. Kuma ita hikima dukkan nau'ukanta suna komawa
ne zuwa ga yin aiki daga umurni da hanuwa da hani.
Allah Mai
hikima ne cikin zancensa, Mai hikima ne cikin shari'arsa, Mai hikima cikin
hukuncinsa da kaddarawarsa, Mai hikima cikin halittarsa. Kuma hikimar sifarsa
ce, kuma mulkinsa ne da yake bai wa wanda yake so.
Kuma
Ma'abuta hikima sune Annabawa -عليهم الصلاة والسلام- da kuma mabiyansu, gwargwadon koyinsu da Annabawa, kuma sune
ma'abuta kyautatawa wadanda Allah ya musu tanadin sakamakon da ya dace da
baiwarsa Mabuwayi da daukaka, a cikin alkawalinsa na gaskiya, kamar fadinsa: "Lallai
wadannan da suka yi imani suka yi aiki na kwarai, lallai ne Mu bamu tozarta
ladan wanda ya kyautata aiki * Wadannan suna da gidajen aljannar zama, koramu
na gudana daga karkashinsu, ana sanya musu kawa a cikinsu daga mundaye na
zinariya, kuma suna sanya wasu tufafi kore, na alhariri sirara da alhariri mai
kauri, suna kishingide a acikinsu, akan karagogi, Madalla da sakamakonsu, kuma
Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutawa" [Kahf: 30-31].
hikima
matsayi ne madaukaki, kuma aiki ne yardadde, kuma alheri ne mai dadi. Bawa yana
samun hikima da baiwar Allah da karramawarsa da falalarsa, Sa'annan da sabubban
da Bawan yake aikata su, yana mai neman taimakon Allah Ta'alah:
YANA DAGA
CIKIN SABUBBAN DA AKE SAMUN HIKIMA DA SU, TAUHIDI GA ALLAH TA'ALAH DA KIN YIN
SHIRKA MA ALLAH Mabuwayi da daukaka, Allah Ta'alah yana cewa:
"Wadanda suka yi imani, sai basu gauraya imaninsu da
wani zalunci ba, wadannan lallai suna da aminci, kuma sune shiryayyu" [An'am:
82]. don haka, tsaftar akida haske ne dake karuwa akan hasken fidira, kuma
karin fahimta ne akan fahimtar hankali, kuma karfi ne ga gangar jiki da ruhi,
wanda Mutum zai rika riskar abubuwa da shi, a bisa hakikanin yadda suke, Allah
Ta'alah ya ce: "Wanda Allah bai sanya masa haske ba, to
bashi da wani haske" [Nur: 40].
YANA DAGA
CIKIN SABUBBAN SAMUN HIKIMA: GODIYAR ALLAH TA'ALAH AKAN NI'IMOMINSA, da zance
da kuma aiki, Allah Ta'alah ya ce, dangane da Annabi Sulaiman -عليه السلام-: "Ya Ubangijina, ka cusa mini in gode wa
ni'imarka wadda ka ni'imtata a gare ni, da kuma ga mahaifana biyu" [Naml:
19]. Kuma Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin
ba zan kasance Bawa mai yawan godiya ba!".
YAN DAGA
CIKIN SABUBBAN: KIYAYE GABBAI DAGA BARIN SABO, DA KIYAYE ZUCIYA DAGA MUNANAN
ABABEN DA SUKE DARSUWA, DA KUMA BAWA YA BAR DUKKAN ABINDA BAI DAME SHI BA, Maluman
Tarihi sun ambata, a cikin labarun wadanda suka shude, lallai wani Mutum ya
tsaya akan Lukman sai ya ce: Kai mai kiyon dabbobi ne? Ya ce: E, Ya ce: Kai
bakin Mutum ne? Ya ce: Lamarin bakin launina a fili yake, to me yake burge ka
daga al'amarina? Sai ya ce: Yadda Mutane dayawa suke zama a shumfudarka, suke
cika kofar gidanka, suke yarda da maganarka! Sai ya ce: Ya kai dan' dan'uwana,
idan ka karkatu zuwa ga abinda zan gaya maka, kai ma za ka kasance kamar haka.
Sai Lukman ya ce: "Runtse idanuna, da kame harshena, da
tsarkin abincina (halal), da kiyaye farjina, da yadda nake fadin gaskiya, da
cika alkawalina, da girmama wanda ya bakunce ni, da kiyaye hakkin makwabcina,
da barin dukkan abinda bai dame ni ba, Wadannan sune suka kai ni zuwa ga abinda
kake ga ni".
KUMA YANA
DAGA CIKIN SABUBBAN SAMUN HIKIMA: FADIN ZUCIYA DA KYAUTARTA, DA SHUMFUDA
HANNUWA, DA AMFANAR DA HALITTU, DA KAMEWA DAGA CUTAR DA SU, DA KUBUTAR ZUCIYA
DAGA KYASHI DA HASSADA, saboda wadannan sifofin suna da wani sirri na
janyo wa Mutum yin dace.
Kuma
wadannan sabubban duka sun tattaru cikin, TSORON ALLAH A ASIRCE DA KUMA A
BAYYANE, DA DAWWAMAR DA ADDU'A, wanda kuma shine mafificin ayyuka bayan
farillai, tare da yawaita zikirin Allah Ta'alah, Allah -سبحانه- ya ce: "Lallai Ubangijinku ya
bayar da shela, cewa: Idan kuka yi godiya tabbas zan kara muku, idan kuma kuka
kafirce to lallai azabata mai tsanani ce" [Ibrahim: 7].
Allah
ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Ma'abucin girma da karramawa, Majibincin kyautatawa da bada
ni'imomi, Ma'abucin buwayar da ba a iya cimmata, da mulkin da ba a iya samunsa.
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin
tarayya Mai mulki da tsarki.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Ya Allah
ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa masu karamci.
Bayan
haka
Ku ji
tsoron Allah wanda ya halitta ku, kuma yake ciyar da ku da ni'imomi, kuma ku
tuna abinda Allah ya muku baiwa na Alkur'ani da hikima (hadisai), da yadda ya
sanya su suka zama hasken da kuke tafiya da shi.
saboda Mumini
idan ya dawwama akan hisabi ga ransa, to sai hisabinsa ya yi sauki a Lahira. Kuma
dawwamar da hisabinsa ga kansa zai shi zuwa ga yau dinsa yafi alheri fiye da
jiyansa, Allah ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi
imani ku ji tsoron Allah, kuma Rai ta yi dubi kan abinda ta gabatar domin gobe,
kuma ku yi takawar Allah, domin Allah Mai bada labari akan abinda kuke aikatawa" [Hashr:
18].
Kuma rigaggeniya
mai amfani, mai wanzuwa kuma mai gadar da samun ni'ima tabbatacciya yana nan
ne, cikin kokarin samun HIKIMA CIKAKKIYA MAI GAMEWA, Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu hassada sai cikin abu
guda biyu; Mutumin da Allah ya bashi hikima, sai yake hukunci da ita, kuma yake
karantar da Mutane ita. Da Mutumin da Allah ya bashi dukiya, sai ya dora shi
akan hallaka ta, a al'amuran gaskiya" Bukhariy da Muslim, daga
hadisin Abu-hurairah -رضي الله عنه-.
An ruwaito
da Suwaid dan Alharis Al'azdiy, ya ce: Na zo wurin Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- daya daga cikin bakwai, yayin da muka shiga wurinsa muka yi
magana da shi, sai abinda ya gani na natsuwarmu da tufafinmu ya burge shi, sai ya ce, Ku su
wanene? Sai muka ce: Muminai. Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya yi
murmushi, sa'annan ya ce: "Lallai kowane zance yana
da hakika, to menene hakikanin zancenku da imaninku?" Sai
muka ce: Halaye ne guda goma sha biyar (15); Biyar daga cikinsu Manzanninka
suka umurce mu da mu yi imani da su, Biyar kuma suka umurce mu muyi aiki da su,
Biyar kuma mun dabi'antu da su tun a jahiliyya, don haka muna kan wadannan
dabi'un, saidai idan ka kiye mana wani abu daga cikinsu! Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Menene biyar din da 'yan aikana suka umurce ku da ku yi
imani da su?" Sai muka ce: Sun
umurce mu da muyi imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littatafansa, da
Manzanninsa, da tayarwa bayan mutuwa, Sai ya ce: "Menene biyar din da suka umurce ku da ku yi aiki da su?" Sai muka ce: Sun umurce mu da mu tsayar da
sallah, mu bada zakkah, mu yi azumin watan Ramadhana, mu yi hajjin dakin Allah,
ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, Sai ya ce: "To, Menene biyar din da kuka dabi'antu da su tun a Jahiliyya?" Sai suka ce: Godiya a yayin wadaci, da hakuri a
lokacin bala'i, da yarda da kaddara mai daci, da gaskiya a lokacin gwabzawa, da
barin dariyar keta ga makiya, Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسل- ya ce:
"Masu hikima, Maluma, sun yi kusa saboda zurfin fahimtarsu
su kasance Annabawa" Sa'annan yace:
"Ni kuma zan kara muku abubuwa biyar sai su zama ashirin: Idan
kun kasance kamar yadda kuke fadi, to, kada ku tara abinda ba za ku cinye ba, kada
ku gina abinda ba za ku zauna ba, kuma kada ku yi tsere akan abinda ku a gobe za
ku barshi, kuma ku ji tsoron Allah wanda zuwa gare shi za a mayar da ku, kuma za
a bijiro da ku a gare shi, kuma ku yi kwadayin ga abinda zaku tafi gare shi, kuma
a dawwamar da ku a cikins" Sai suka
tafi daga wurin Manzon Allah -صلى
الله عليه وسلم-,
kuma suka kiyaye wasiyyarsa, suka yi aiki da ita.
Ibnu-Asakir
ya ruwaito shi, da Abu-Sa'id Annaisaburiy.
Ya ku
Bayin Allah!
"Lallai
ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi
imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci"
[Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment