بسم الله الرحمن الرحيم
HARAMCIN SAKE TUFAFI (ISBALI)
Dan'uwana Mai
girma: Tsawaita tufafi zuwa ƙasan
idon sawu biyu abu ne wanda Annabi -sallal Lahu alaihi wa sallama- ya yi hani a
kansa, a cikin fadinsa: "Abinda ya zama ƙasa da idon sawu biyu na tufafi,
to yana cikin Wuta", don haka, sake tufafi haramun ne, kuma
Malamai sun ƙidaya shi daga cikin manyan zunubai,
kuma hakan ya game riga da wando d.s. Kuma haramcin yana ƙara
muni, kuma ukubar tana tsananta idan jiji-da-kai ya hadu da shi, Annabi sallal
Lahu alaihi wa sallama ya ce: "Mutane uku Allah
ba zai yi magana da su ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai
radadi", Sai Annabi ya ambaci, Mai sake tufafinsa daga cikinsu.
Kuma ka sani, lallai dukkaninmu ma'abuta
kuskure ne, kuma dogewa akan saɓo wani laifi ne na-daban, Annabi -sallal Lahu alaihi wa
sallam- ya ce: "Dukkan ƴan adam masu kuskure ne, saidai
mafi alkhairin masu kuskure, sune masu yawaita tuba".
To, Me ya sa ba zaka maida tufarka kamar yadda aka shar'anta ba; domin
tsoron fushin Allah da ukubarsa?!
Kuma Allah yana karɓar
tuban Mutumin da ya tuba, yana gafarta wa wanda ya nemi gafararSa kuma yake
mayar da al'amarinsa izuwa gare shi!
MAI MAKA ADDU'AR ALKHAIRI
No comments:
Post a Comment