FIKIHUN AZUMI
(فقهُ الصيام)
NA
SHEHIN MALAMI
HAISAM BN MUHAMMADU JAMIL
SARHAN
Tsohon Malami a Sakandaren
Masallacin Annabi -SAW-,
kuma shugaban shafin
intanet
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Bismillahir RahmanirRahim
AZUMI wato, SIYAAM a harshen larabci, shine: Kamewa.
A shari'akuma, Bauta wa Allah, ta hanyar kamewa daga cin abinci, da
abin sha, da sauran ababen da suke karya azumi, daga ketowar alfijir
na-gaskiya, zuwa faduwar rana.
RUKUNNAN AZUMI
1- Niyyah.
2- Kamewa daga
ababen da suke karya azumi.
KARKASUWAR NIYYAR AZUMI
1- Niyyar azumin farilla: Babu makawa dole ne, sai an kwana da
niyyar, ga azumin farillai, tun cikin dare, wato gabanin ketowar alfijir. Kuma yana
wadatarwa a kulla niyyar daga shigan watan azumi. Kuma mahallin niyya zuciya
ne, furta ta kuma da harshe bidi'a ne.
2- Niyyar azumin nafila: Kuma
niyyar tana inganta idan aka yi ta cikin kowace dakika ko lokaci na yini,
matukar bai kusanci abinda suke karya azumin ba. Saidai zai fara samun lada ne,
daga lokacin da ya kulla niyyar.
KARKASUWAR AZUMI
1- Azumi na
wajibi: (Ramadana, kaffara, da bakance).
2- Na nafila.
SHARRUDAN WAJABCIN
AZUMIN RAMADANA
1. Musulunci.
2. Hankali.
3. Balaga (Shi kuma Yaron da ya kai shekarun tantancewa,
za a rika kwadaitar da shi kan azumi, waliyyinsa ya rika umartarsa).
4. Zaman
gari (Saboda azumi baya wajaba akan matafiyi,
kuma abinda ya fi a gare shi, shine ya yi azumin, matukar azumin ba zai yi tsanani
a gare shi ba; saboda hakan shine aikin Annabi –S.A.W-, kuma saboda hakan shi ya fi saurin sauke nauyin
da ya doru a wuyansa, kuma ya fi sauki ga Mutum, kuma domin ya riski falalar
yin azumi a cikin wannan watan).
5. Lafiya.
6. Kubuta
daga jinin haila da na haihuwa.
JINYA KASHI BIYU NE
DANGANE DA AZUMI:
1-
Jinyar da ba a tsammanin gushewarta.
Ana yin kiyasin
tsofon da ya gajiya; wanda kwata-kwata ba zai iya azumi ba, da majinyacin da ba
zai iya azumin ba; sai azumin ya sauka akansa, sai dai kuma zai ciyar da
miskini guda daya a madadin kowane azumi; ko ta hanyar ya hada miskinai
gwargwadon yawan kwanakin da bai yi azuminsu ba, sai ya ciyar da su. Ko kuma ya
rarraba abinci ga miskinan, na tsawon wadannan kwanakin; ta hanyar baiwa kowane
miskini rubu'i wato daya bisa hudun sa'iy irin sa'in Annabi SAW; (1/4),
(Ma'ana: ya bayar da gwargwadon awun rabin kilo, da giram goma, na shinkafa ko
alkama mai kyau).
Kuma abu ne mai
kyau ya hada da abinda zai zama, kamar miya a gare shi, na mai, ko nama.
2-
Jinyar da ake tsammanin za ta gushe; sai dai yin azumi zai tsananta ga
mai ita, Wannan kuma ana kiyasin Mace mai haila da jinin biki (haihuwa), da Mai
shayarwa, da Matafiyi, da wannan nau'i na jinya, Sai Majinyacin ya biya adadin
kwanakin da ya karya azumi a cikinsu; idan har ya warke. In kuma ya rasu
gabanin ya samu damar biya, to azumin ya fadi daga wuyansa.
Kuma shigowan watan
Ramadana yana tabbatuwa, ta hanyar ganin jinjirin wata, ko kuma watan Sha'abana
ya cika kwanaki talatin (30).
ABABEN DA SUKE LALATA
AZUMI
(amma ana yin uzuri ga
Jahili, da Mai mantuwa, da wanda aka masa tilasci)
1-
Ci, ko sha da ganganci, Amma wanda ya yi da mantuwa to
azuminsa ingantacce ne.
2-
Jima'i, Idan har ya auku a cikin yinin Ramadana, alhali yin
azumin wajibi ne akansa, To dole ne ya yi kaffara mai tsanani, wanda itace,
'yanta baiwa, idan kuma bai samu ba, sai ya yi azumin watanni biyu a jere, idan
kuma ba zai iya ba, sai ya ciyar da miskinai sittin (60).
3-
Fitar maniyyi, ta hanyar runguma, ko sumba, ko
hada jiki, ko makamancinsu.
4-
Abinda ke daukar ma'anar ci da sha, Misalin allurar abinci. Ita kuma allurar da ba a sanya mata abinci a cikinta ba,
ita kam bata karya azumi.
5-
Fitar da jini ta hanyar kaho. Amma fitar da jini kadan, domin awu, ko makamancin haka, shi kam baya
karya azumi.
6-
Yin amai da ganganci.
7-
Fitar jinin haila da na biki (haihuwa).
MUSTAHABBAN AZUMI
1-
Yin sahur.
2-
Jinkirta yin sahur.
3-
Gaggauta buda-baki.
4-
Yin buda-baki da dabinon da bai bushe ba (rudab). Idan
kuma bai samu ba, sai ya yi da busasshen dabino, kuma dabinon su kasance
wutiri, Idan kuma bai samu ba, sai ya sha ruwa, Idan kuma bai samu wani abu ba,
sai ya yi niyyar karya azumin a zuciyarsa.
5-
Yin addu'a a lokacin buda-baki, da a halin azumi.
6-
Yawaita yin sadaka.
7-
Dagewa wajen yin sallolin dare.
8-
Karatun Alkur'ani.
9-
Yin umrah.
10-
Fadin: Ni mai
azumi ne, ga wanda ya zage shi.
11-
Kokarin neman Lailatul kadr.
12-
I'itikafi a goman karshen watan azumi.
MUKRUHAN AZUMI
1-
Kaiwa makura cikin kurkuran baki.
2-
'Dandana abinci, ba tare da bukatar hakan ba.
YANA HALATTA GA MAI AZUMI
Hadiye yawu, 'dan'dana abinci yayin bukata, yin wankan ibada, Yin asiwaki,
shafa turare, da yin wanka domin jin sanyi.
HARAMUN
NE GA MAI AZUMI
Hadiye kaki (sai dai baya karya azumi), Da yin sumba, ga wanda yake tsoron
lalacewar azuminsa, da fadin zancen zur ko shaidar karya (da aikata kowane
haramun), da aikin jahilci (wauta, da rashin hakuri), da yin wucel (ma'ana yin
kwanaki biyu bai yi buda-baki ba).
AZUMIN NAFILA
1-
Yin azumin ranaku shida a watan
Shawwal, ga wanda ya cika azuminsa na Ramadana. Kuma abinda ya fi, shine, a
fara yinsu daga yini na biyu, kuma a jeranta su.
2-
Azumin yinin Arafah, ga wanda ba Mahajjaci ba.
3-
Azumin yinin Ashura, da kuma ranar
tara, da ranar goma sha daya (9, 10, 11, na watan Muharram).
4-
Azumin ranar Litinin da Alamis, kuma na ranar
litinin sunnarsa tafi karfi.
5-
Azumtar kwanaki uku, a kowane wata,
kuma abinda yafi shine azumtarsu ya
kasance a
kwanakin da wata yake cika haskensa wato, 13, 14, da
15.
6-
Azumtar yini, da shan ruwan yini.
7-
Yin azumi a cikin watan Allah na
Muharram.
8-
Azumtar yini tara na farkon watan
Zul-hijjah.
9-
Yin azumin watan Sha'aban, amma kada
ya kammala shi gaba dayansa.
AZUMI NA MAKRUHI
Yinin Juma'a, da Asabat, da Lahdi, makruhi ne a kebance kowanne da azumi,
sai dai idan kebe shin ya zamo sakamakon wani sababi ne, to ba makruhi ba ne,
kamar yinin Arafah.
AZUMI NA HARAM
1-
Kebe watan Rajab da azumi.
2-
Azumtar yinin shakku, Amma wanda ya
saba da wani azumi, to babu komai akansa.
3-
Azumtar yinin idi guda biyu.
4-
Azumtar kwanaki uku na bayan idin
layya (Tashrik), sai ga Mahajjacin da bai mallaki hadaya ba.
5-
Azumtar zamani (kullum-kullum).
Mustahabbi ne, a jeranta azumin ramuko, kuma ya dace, Mutum ya yi gaggawan
yinsu, daga bayan idi, kuma bai halatta ya jinkirta ramukon da yake kansa har
wani Ramadanan ya sake shigowa ba, Idan kuma ya jinkirta shin, ba tare da wani
uzuri ba, to dai wadancan azumin da suka wucen sune zai rama (babu kari), sai
dai kuma ya yi zunubi.
ZAKKAR
FID-DA-KAI (FIDR)
Tana wajaba ne ga
wanda yinin Ramadana na karshe ta fadi masa alhalin yana Musulmi, sai (aka yi
dacen) sa'in abinci guda 'daya ya doru akan abincinsa da na iyalan gidansa da
bukatunsa na asali.
Kuma mustahabbi ne a cire ta ga 'Dan tayi (da yake cikin mahaifa).
HIKIMAR
FITAR DA ZAKKAR FID-DA-KAI:
1-
Domin ta tsarkake Mai azumi daga wargi da kwarkwasa.
2-
Domin a wadatar da Miskinai; kada su yi roko a ranar idi (yinin farin ciki).
LOKACIN
FITAR DA ZAKATUL FIDR
1-
Lokaci na halacci, shine gabanin
ranar idi da yini daya ko biyu.
2-
Lokaci na mustahabbi, shine,
gabanin ayi sallar idi, bayan ketowan alfijir.
3-
Lokaci na haramci wannan kuma
shine, Bayan yin sallar idi.
GWARGWADON
ZAKATUL FIDR
Sa'iy daya ne na dangogin abincin da Mutane suka rika a matsayin abinci,
don haka, bata isarwa idan aka fitar da ita daga cikin kudi.
(Gwargwadon sa'iy shine,
kilo biyu, da giram arba'in na alkama mai kyau).
SALLAR
IDI
Farilla ce akan kowane Mutum.
Kuma ana sallatar ta ne, bayan dagowar rana daidai da kibiya, har zuwa
lokacin gotawar rana (zawali).
Kuma ba a yin ramukonta, idan ta wuce.
Sunnah shine a yi ta a sahara ko fili, ba cikin gini ba.
Kuma ya halatta a yi ta a cikin Masallaci.
Mustahabbi ne Mutum ya ci dabino wutiri gabanin sallar idi, kuma ya yi
tsafta, ya fesa turare, ya sanya mafi kyan tufafinsa, ya tafi ta wata hanya, ya
komo ta wata hanya.
Babu laifi kan gaishe-gaishen idi, ta hanyar fadin: TAKABBAL LAHU MINNAH WA
MINKUM (Allah ya karba mana; mu da ku).
Kuma sunnah ne, yin kabbarori mudlakai, a daren idi, da bayan salloli, har
zuwa faduwar ranar yinin idi. Kuma SIFAR KABBARAR ITACE:
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,
LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
Kuma SIFAR SALLAR IDI ita ce Raka'oi biyu gabanin yin huduba, zai yi
kabbarori shida a raka'ar farko, bayan kabbarar harama.
No comments:
Post a Comment