HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/RAJAB/1440H
daidai da 15/MARIS/2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
KIYAYE SALLOLIN FARILLAI
(المحافظة على الصلوات المفروضات)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Al-Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KIYAYE
SALLOLIN FARILLAI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya
ta tabbata ga Allah wanda yake cewa: "Kuma
ka tsai da sallah a gefe biyu na yini da wani yanki daga dare" [Hud:
114].
Kuma
ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da
abokin tarayya, irin shaidawar da take tseratar daga yin shirka da sabo da
karkata.
Kuma
ina shaidawa lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawanSa ne, manzonSa, Allah
ka yi dadin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, salati mai dawwama, mai tsarki, wanda ake
ninka lada da ita, kuma a tunkude mana bakin-ciki da bala'i da azaba.
Bayan haka
Ya ku Musulmai
Ku
yi takawar Allah, saboda tsoron Allah shine mafi karfin abin taimako, kuma mai bada
nasarar da yafi cikawa, "Ya ku wadanda suka yi
imani ku ji tsoron Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya" [Taubah:
119].
Ya ku Musulmai
Allah
ya bayyana wa Mutane alamomin addininsu, kuma karara a fili ya fito musu da
abinda shari'arsa ta shar'anta, ya kuma farlanta wa BayinSa kiyaye da dawwama
akan salloli biyar da aka farlanta, aka wajabta, wadanda aka saba yinsu cikin
yini da dare, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma
ku tsare lokatan salloli da salla mafificiya, kuma ku tsayu ga Allah kuna masu
kankan da kai" [Bakara: 238].
Wanda ya
bar sallah da ganganci, yana mai kin yinta, haka ramukonta, da tsayar da
ita, to bashi da rabo a cikin Musulunci.
Wanda kuma
ya yi sallah, kuma yake dogewa akan yinta, sai a masa shaida da Musulunci.
An ruwaito
daga Jabir dan Abdullahi (Allah ya yarda da shi) ya ce: Na ji Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- yana
cewa: "Tsakanin
Mutum da shirka da kafirci shine barin sallah", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma an
ruwaito daga Abdullahi dan Shakik, Tabi'iy -Allah ya yi masa rahama- ya ce: "Sahabban Annabi
Muhammadu SAW sun kasance babu wani aikin da suke ganin barinsa kafirci ne, in
banda sallah" Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga AbudDarda'i
-رضي
الله عنه- ya ce: "Masoyina badadina -صلى الله عليه وسلم- ya min wasiyya da cewa: Kada ka yi
shirka da komai ga Allah, koda za a sassara ka, a kokkona ka. Kuma kada ka bar
sallar farilla, da gangani, saboda idan Mutum ya barta da gangan, to lallai
zimmar Musulunci ta barranta daga gare shi. Kuma kada ka sha giya, domin giya
mabudin dukkan sharri ce", Ibnu-Majah ya ruwaito shi.
Ya yi
hasara, wanda ya bar sallah kuma ya tabe
Kuma ya
ki makoma tagari da zai koma!
idan ya
kasance yana musun wajabcinta, to lallai wannan
Ya yi
yammaci yana wanda ya kafirta da Ubangijinka, yana cikin shakka
Idan
kuma ya bar sallar saboda wata kasala ce
to,
lallai ya lullube gaskiya da wani shamaki
Ya ku Musulmai
Malamai
sun yi ijma'i akan kasantuwar salloli biyar an sanya musu lokatai iyakantattu,
kuma lokacin sallah yana da farko da kuma karshe, baya halatta ga Musulmi ya yi
sallar farillah gabanin lokacinta, kuma baya halatta ya fitar da ita ko ya
jinkirta ta daga lokacinta, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne sallah ta
kasance akan muminai farilla ce mai kayyadaddun lokuta", [Nisa'i: 103].
Abdullahi dan Mas'ud -Allah ya
yarda da shi- ya ce: "Lallai sallah tana da kayyadadden lokaci,
kamar hajji".
Kamar yadda baya halatta ayi
hajji ba a cikin watanninsa ba, ko Mutum ya tsaya a filin Arfah bayan
lokacinsa, ko ya yi juma'a a ranar asabat, to haka baya halatta ya yi sakaci a
al'amarin lokatan sallolin farillah.
Kuma lallai Allah ya yi narko ga
masu sallah wadanda suke fitar da sallar farilla daga lokacinta wanda shari'a
ta kaddara mata; har ya zama basu yinta sai bayan fitan lokacinta, a inda Allah
Mabuwayi da daukaka yake cewa: "To,
bone ya tabbata ga Masallata * wadanda suke masu shagalta daga sallarsu"
[Ma'una: 4-5].
Kuma wannan
shine halin munafikai da fasikan Musulmai, wadanda suke yin sallar yini a cikin
dare, suke yin sallar dare a cikin yini, suke yin sallah yadda suka ga dama, ba
yadda ya dace da sharadin ingancin ibadarsu ba, suna aikata hakan, suna masu
sakaci da lamarin sallah, da fasikci, da fitsaranci, da kuma sakaci da hakkinta.
An
ruwaito daga Naufal dan Mu'awuyah -رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda sallah ta kubuce
masa, to kamar an wawashe masa iyalansa da dukiyarsa", Ibnu-Hibbana ya ruwaito
shi.
Wawasasshen Mutum shine wanda aka
kashe masa makusanci, ko aka debe dukiyarsa, sai bai riski hakkinsa ko ya samu
damar daukar fansa ba.
Fiskar da suka yi kamantacceniyar
(da wanda sallah ta kubuce masa), itace lallai wanda sallah ta kubuce masa,
hakika bakin cikin sabo, da bakin cikin rashin samun lada sun hadu akansa,
kamar yadda mutumin da aka wawashe iyalansa da dukiyarsa bakin cikin dauke masa
su, da bakin cikin wahalar sake nemansu sun hadu akansa.
Kuma abinda ake nufi da "kubucewar sallah",
shine jinkirta ta da fitar da ita daga lokacinta na halacci, ba tare da wani
uzuri ba.
An tambayi
Sheikhul Islam Ibnu-Taimiyyah -رحمه الله تعالى- akan
Mutumin da ya bar sallah guda daya, da ganganci, da niyyar zai sallace ta bayan
fitar lokacinta, a matsayin ramuko, Shin wannan aikin laifi ne babba daga cikin
alkaba'irai?
Sai ya amsa: Jinkirta sallah da fitar da ita
daga lokacinta da ya wajaba a aikata ta a cikinsa da ganganci yana daga manyan
laifuka na alkaba'irai. Kuma ya ce: Duk
wanda ya bar sallah guda daya da ganganci, to hakika ya aikata laifi mai girma
na kaba'ira. Sai ya yi kokarin gyarawa, da
abinda ya samu iko; na tuba, da kuma ayyuka na-kwarai. Kuma koda ya yi
ramukonta, to wannan ramukon kawai, ba zai dauke masa zunubin abinda ya aikta
ba, da ijma'in Musulmai.
Ya ku Musulmai!
Wanda kuma ya bar sallah da
mantuwa, ko barci, To wajibi ne ya rama sallar; Sai mai barci ya yi ramuko idan
ya farka, wanda kuma ya yi mantuwa, idan ya tuna, saboda hadisin Anas -رضي الله عنه- ya ce:
Manzon Allah -صلى
الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya manta
wata sallah, ko kuma ya yi barci bai sallace ta ba, to kaffararta shine ya
sallace ta idan ya tuna ta, bata da wani kaffarar in banda haka (KUMA KA TSAYAR
DA SALLAH DOMIN AMBATONA) [Daha: 14]", Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi.
Kuma an ruwaito daga Abu-Katadah
-رضي
الله عنه- lallai sun ambata wa Annabi
-صلى
الله عليه وسلم- lamarin barcinsu basu yi
sallah ba, sai ya ce: "Babu sakaci a al'amarin
barci, sakaci yana nan ne ga wanda yake farke, Idan dayanku ya manta wata
sallah, ko ya yi barci bai yi ta ba, to ya sallace ta idan ya tuna ta".
Ibnu-Abdulbarri -رحمه الله تعالى- ya ce: "Kebance mai
barci da wanda ya manta sallah da aka yi da ambato (a hadisin), a al'amarin
ramukon sallah, babu abinda ya dauke lamarin biyan sallar ga wanda ya yi
gangancin barinta har lokacinta ya fita. Bal, a cikin lamarin akwai dalilai
masu karfi, cewa lallai wanda ya bar sallah da ganganci (ya yi zunubi), shine wanda
yafi cancantar a umurce shi da yin ramukonta, fiye da wanda yayi mantuwa wanda
aka masa rangwame, da mai barci mai uzuri. Shi wanda ya yi gangancin barinta
babu makawa, yana tune da ita, sai ya zama wajibi akansa ya rama wannan sallar,
ya kuma yi ta neman gafara, akan jinkirta yinta".
Wasu Ma'abuta ilimi kuma
suka ce: Wanda ya bar sallah da ganganci, to, ba a shar'anta masa
ramukonta ba, kuma ko ya yi ta, bata inganta daga gare shi. Kuma wajibi ne
akansa ya yi ta yawaita tuba.
Ya ku
Musulmai!
Yana
daga cikin sakaci, yin barci bayan shigan lokacin sallah, ga wanda yake
rinjayar da zaton cewa zai makara, ko barcin zai cinye lokacin sallar farillar,
har lokacin ya fita, ko kuma zababben lokacinta zai fita. Saidai idan ya aminta
cewa wani zai tayar da shi, ko kuma ya rinjaya a zatonsa cewa, zai iya tashi da
agoganni masu fadakarwa.
Kuma
(Musulmi) ba zai jinkirta sallar la'asar -ba tare da uzuri ba- zuwa lokacin da
rana take yin fatsi-fatsi, idan kuma ya aikata hakan, to lallai shi mai laifi
ne, a daya daga cikin zantukan Maluma guda biyu, saboda fadin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Lokacin sallar
la'asar, shine matukar rana bata yi fatsi ba", Muslim ya ruwaito shi.
Da kuma saboda abinda aka ruwaito
daga Anas dan Malik -رضي
الله عنه- ya ce: Na ji Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- yana cewa:
"Wannan
itace sallar Munafikai, Wannan itace sallar Munafikai, Wannan itace sallar
Munafikai! Dayansu zai zauna har sai rana ta zama fatsi, kuma ta kasance
tsakanin kaho biyu na Shaidan, ko akan kahon Shedan, to sai ya tashi ya dungura
sau hudu, baya ambaton Allah a cikinsu face kadan", Muslim ya
ruwaito shi.
To, da
halal ne jinkirta sallar la'asar zuwa rana ta zama fatsi, da Annabi bai zargi mai
aikata hakan ba, kuma da bai sanya hakan ya zama alamar Munafikai ba.
Kuma (Musulmi)
ba zai jinkirta sallar Isha ta wuce rabin dare ba, saboda fadin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Lokacin sallar isha
zuwa rabin dare ne", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ba zai jinkirta sallar asuba
zuwa fudowar rana ba, saboda fadin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Lokacin sallar
asuba shine daga fudowar alfijir, matukar rana ba bata fudo ba ",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma duk wanda ya riski raka'a
daya cikakkiya daga sallah, da ruku'inta da sujjadarta, a cikin lokacinta, to
hakika ya riski wannan sallar, saboda fadin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Wanda ya riski
raka'a daya daga sallah, to hakika ya riski sallar", Bukhariy
daMuslim suka ruwaito shi.
Wanda ya yi gangancin seta agogon
fadakarwa bayan fudowar rana, ko ya saba aikata hakan, baya damuwa da sallar
asuba, kuma bai yi riko da wani abu daga sabubban farkawa ba, kuma bai yi
sammako zuwa ga yin barci ba, kuma bai yi wasici ga wanda zai tashe shi ba, To
lallai ya auka cikin zunubin sakaci, kuma za a iya kidaya shi ya dauki hukunci
mai gangancin jinkirta sallah.
Amma wanda kansa da barcinsa suka
yi nauyi, bayan nuna kiyayewarsa da kwadayinsa, da kyakkyawan aikinsa, da yadda
ya yi riko da sabubban da aka saba tashi daga barci da su, To lallai babu laifi
akansa, saboda bai yi sakaci ba.
Kuma wajibi ne a rika tayar da
mai barci, domin riskar sallar farillah;
Almardawiy ya ce: "Kuma yana wajaba a sanar da shi, idan lokacinta ya yi
kunci".
Nawawiy ya ce:
"Saboda
aikata hakan, yana cikin taimakakkeniya akan biyayya da takawa".
Alkurdubiy ya ce: "Saboda mai barci
abinda yake hana shi riskar sallar yana da saurin gushewa, don haka, shi (mai barci)
kamar wanda ya rafkana ne, kuma fadakar da gafalalle wajibi ne".
Wanda salloli masu yawa suka wuce
shi, wajibi ne akansa ya rama su, a jejjere.
Kuma idan ya sallaci sallar da
ake cikin lokacinta, alhalin ya manta da wanda ta wuce shi, To sai ya cigaba da
sallarsa, ba sai ya sake ramukonta ba (don kawai bai jeranta su ba).
Idan lokacin sallar da ake ciki,
ya zama ya yi kunci, To a nan ba wajibi ne sai ya jeranta su ba, sai ya yi
wanda ake cikin lokacinta a cikin lokacin, sa'annan ya sallaci wanda lokacinta
ya fita.
Kuma Mutum ya rika bibiyar
Mutanen gidansa dana wurin zamansa, yana umurtarsu da yin sallar farilla, kuma
ya rika tayar da su sallar asuba, a lokacin da za su iya yin tsarki da alwala
da sallar gabadayanta, gabanin fudowar rana.
Kuma ana umurtar yaro karami da
yin sallar farilla, koda kuwa bata wajaba akansa ba, domin ya saba da sallar, saboda
fadin Annabi -صلى
الله عليه وسلم-: "Ku umurci 'ya'yanku da yin sallah, alhalin suna da
shekaru bakwai, kuma ku doke su akanta alhalin suna da shekaru goma, kuma ku
rarrabe tsakaninsu a wuraren kwanciya", Abu-Dawud ya ruwaito
shi.
Kuma kananan yara, da matasa da
samari wadanda suke wargi da wasa akan hanyoyi da wuraren wasanni, da kuma
makwabtan Masallatai dakunan Allah, sai kuma ya zama basu halartar jam'i, kuma
basu damuwa idan suka ji kiran sallah, kuma basu girmama wannan alama mai girma
ta addini, yana wajaba akan majibintan lamuransu su rika bibiyan al'amuransu,
kuma wajibi ne ga wanda ya shige ta wurin da suke ya musu nasiha, yana fadakar
da su.
Ya ku Musulmai!
Kada dukiyoyinku
da 'ya'yanku su shagaltar da ku,
kuma
kada kasuwancinku da saye-da-sayarwarku su mantar da ku,
kuma
kada kasuwanninku da kantunanku su shagaltar da ku ga barin halartar sallah, da
kiyaye lokutanta, da kula da abinda Allah ya baku kulawa da shi na al'amarin
sallah, An ruwaito daga Abdullahi dan Mas'ud -رضي الله عنه- yana cewa: "Wanda yake faranta
masa ya hadu da Allah a gobe yana Musulmi, to ya kiyaye wadannan sallolin a
lokacin da ake kiransu, saboda Allah ya shar'anta wa Annabinku -صلى الله عليه وسلم- hanyoyin shiriya, kuma sallolin
suna daga hanyoyin shiriya. Kuma da, za ku yi salla a cikin gidajenku, kamar
yadda mai kin halartar Masallaci yake yin salla a cikin gidansa, da kun bar
sunnar Annabinku, da kuma za ku bar sunnar Annabinku da kun bace. Kuma babu
Mutumin da zai yi tsarki sai ya kyautata alwalarsa, sa'annan ya nufi masallaci
daga cikin wadannan Masallatan, face Allah ya rubuta masa lada akan dukkan
takun da ya yi, kuma ya daga darajarsa da hakan, kuma ya kankare masa mummunansa
da wannan takun. Kuma hakika na ganmu (a zamanin Sahabbai), babu mai kin
halartar sallar jam'i face Munafiki wanda aka sanshi da munafirci. Kuma hakika
Mutum ya kasance ana zuwa da shi ana rike da shi a tsakanin Mutane biyu, har a
tsayar da shi a cikin sahu", Muslim ya ruwaito shi.
Wane kira ne yafi zaki kuma yafi
dadi
kuma wane sauti yafi kara kuma
yafi kyau
Fiye da sautin mai kururuwa da kiran
sallah
Sai ka jiyar da zukata, ya kai Mai
kiran sallah
Lallai ne zuciya, da sallah take
samun natsuwa
Sai ka farkar da masu barci, da
kiran sallah
Ya kai Mai kiran
Mutane izuwaga Mai jinkai
Ina
fadan abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa,
lallai shi ya kasance ga masu komawa gare shi, Mai yawan gafara ne.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah wanda a cikin
tausasawarSa yake bada mafaka ga mai neman mafakarsa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda cikin ni'imarSa
yake bada waraka ga wanda ya debe tsammanin waraka daga cutukansa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonSa, wanda ya bi shi ya samu shiriya,
wanda kuma ya saba masa ya bace hanya,
Allah ka yi dadin salati a gare shi da
iyalansa da sahabbansa, salatin da yake wanzuwa, da sallama mai ninkuwa.
Bayan haka
Ya ku Musulmai
Ku ji
tsoron Allah, kuma ku kiyaye shi, kuma ku masa biyayya kada ku saba masa, "Ya
wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, iyakar jin tsoronsa, kuma kada ku
mutu face kuna Musulmai" [Ali-imrana: 102].
Ya kai karamin 'Dan'uwana!
Ya kai karamin
'Dan'uwana!!
Ya wanda yake jin kiran sallah,
amma baya amsawa,
Ya wanda yake sako-sako, yake yin
nawa, yake yin jinkiri,
Ya wanda yake nauyin jiki, yake
shagaltuwa, yake yin sakaci,
Wadannan lada ne ake rabiya,
alhalin kai kuma kana cikin warginka, da nauyi jiki da zunubi!
Wadannan sune wuraren kusanci, da
karramawa, da bayar da lada, alhalin kai kana nesa, korarre, kana wuraren
juyawa da sharrace-sharrace da rudi, "Duk wanda ya yi sammako zuwa ga
Masallaci, ko ya je da yamma, -
Wato ya fita domin ziyartar wa?
Shi bakon wanene?
Shi wurin wa ya je?
Lallai shi yana
karkasin bakuncin Allah Mai kyauta, da karramarSa, da ni'imarSa, da baiwarSa.
An ruwaito daga
Abu-hurairah -رضي الله عنه-
daga Annabi -صلى الله عليه وسلم-
lallai ya ce: " Duk wanda ya yi sammako zuwa ga Masallaci, ko ya je da yamma,
Allah ya masa tanadin liyafa, a duk lokacin da yaje da jijjifi, ko ya je da
maraicen", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Wato, Allah zai tanada masa wata
(kasaitacciyar) liyafa a gidan Aljannah, duk lokacin da yaje Masallacin da
sammako, ko da yammaci.
ALLAHU AKBAR
Wane irin liyafa ce!
kuma wace karama ce! kuma wace kyauta ce! kuma wane arziki ne! wane abinci ne!
wace gara ce! kuma wani irin abin tarban
bako ne, Allah yake tanadarsa ga Bakonsa!
Ka yi mamakin girman
wannan ladan, kuma ka yi mamakin girman wannan karramawar!
Don haka, Babu mai
kin halartar Masallatai, bayan wannan ladan da tarin kyauta, face shakiyyi
maras rabo.
Kuma Mutane ba za su
gushe suna jinkiri ba, face Allah ya jinkirta su!
Ku saurara! Lallai a
cikin sallah alheri da falala suke gaba daya
saboda a cikinta,
wato sallah gabbai suke kankan da kansu ga Allah
Kuma (sallah) ita ce
farkon farilla a cikin shari'ar addininmu
Kuma itace karshen
abinda zai wanzu, idan aka daga addini
Duk wanda ya tsayu
domin yin kabbara, sai wata rahama ta sadu da shi
Sai ya kasance, kamar
Bawan da yake kwankwasa kofar Shugabansa
Sai ya zama da
UbangijinSa a lokacin sallarsa yake ganawa,
UbangijinSa a lokacin sallarsa yake ganawa,
Ya jin dadinsa! Da
zai kasance mai tawali'u (mai kankan da kai).
No comments:
Post a Comment