USULUS SALASA DA
DALILANSU
الأصول الثلاثة
Na
Sheikhul
Islam Muhammadu dan Abdulwahhab
-Allah Ta'alah ya yi
masa rahama-
(1115-1206h)
AMSOSHI
ne tare da DALILANSU ga TAMBAYOYIN KABARI:
Wanene
Ubangijinka?
Menene
Addininka?
Wanene
Annabinka?
Tarjamar
Abubakar Hamza
Bismil Lahir
Rahmanir Rahim
Ka
sani –Allah ya yi maka rahama- Lallai yana wajaba akanmu mu koyi mas'aloli guda
hudu:
Mas'alar farko: ILIMI, Shine sanin Allah, da sanin AnnbinSa S.A.W da sanin addinin Musulunci, tare da dalilai.
Mas'ala ta biyu: AIKI DA
ILIMIN.
Mas'ala ta Uku: YIN
DA'AWA ZUWA GA ILIMI DA AIKI.
Mas'ala ta hudu: Hakuri kan
cutarwa a cikinsa.
Dalilin hakan
shine fadinsa Madaukaki: Bismil Lahir Rahmanir Rahim: "INA RANTSUWA DA
ZAMANI * LALLAI MUTUM YANA CIKIN HASARA * FACE WADANDA SUKA YI IMANI, KUMA SUKA
AIKATA AYYUKAN KWARAI, KUMA SUKA YI WA JUNA WASIYYA DA BIN GASKIYA, KUMA SUKA
YI WASIYYA DA YIN HAKURI" [Asr: 1-3].
Shafi'iy –Allah Ta'alah ya yi masa rahama-
ya ce: Da Allah bai saukar da wata hujja ga halittunsa ba, sai wannan sura, to
da ta isar musu.
Kuma
Bukhariy –Allah Ta'alah ya yi masa rahama- ya ce: Babin da yake bayani akan: Ilimi
shine gabanin zance da aiki. Dalili akan haka shine fadin Allah
Ta'alah: "KA SANI, LALLAI BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA, FACE ALLAH, KUMA
KA NEMI GAFARAR ZUNUBANKA" [Muhammadu: 19]. Sai Allah ya fara ambaton
ilimi, gabanin zance da aiki.
Ka sani, Allah ya yi maka rahama; Lallai yana wajaba akan
kowane Musulmi
namiji da mace, su koyi mas'aloli guda uku, kuma su yi aiki da su.
NA FARKO: Lallai Allah ya halitta mu, kuma ya azurta
mu, kuma bai bar mu kara zube ba, sai ya aiko mana da wani Manzo; wanda ya masa
biyayya ya shiga Aljannah, wanda kuma ya saba masa ya shiga wuta.
Dalili akan haka,
shine fadinSa Madaukaki: "Lallai ne Mu,
mun aiko wani Manzo gare ku, Mai shaida akanku, kamar yadda muka aike da Manzo zuwa ga Fir'auna * Sai Fir'auna ya saba wa Manzon, saboda haka Muka
kama shi, kamu mai tsanani" [Muzammil:
15-16].
MAS'ALA TA BIYU: Lallai ne Allah, baya yarda a hada shi da
wani, a cikin bautarSa; Mala'ika ne makusanci, ko kuma Annabi Manzo.
Dalili akan haka
kuma shine fadinSa Madaukaki: "KUMA LALLAI
WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH" [Jin: 18].
MAS'ALA TA UKU: Lallai duk wanda ya yi da'a ga Manzo, kuma ya
yi tauhidi ga Allah, to baya halatta a gare shi, ya jibinci wanda ya saba wa
Allah da ManzonSa, koda kuwa dangin da yafi kusanci ne.
Dalili kan haka shine fadinSa madaukaki: "BAZA KA SAMU MUTANEN DA SUKA YI IMANI DA
ALLAH, DA RANAR KARSHE SUNA YIN SOYAYYA DA WANDA YA SABA WA ALLAH DA MANZONSA
BA; KODA KUWA SUN KASANCE UBANNINSU NE, KO 'YA'YANSU, KO 'YAN'UWANSU, KO
DANGINSU, WADANNAN ALLAH YA RUBUTA IMANI A CIKIN ZUKATANSU, KUMA YA KARFAFA SU
DA WANI RUHI DAGA WURINSU, KUMA ZAI SHIGAR DA SU ALJANNONI WADANDA KORAMU SUKE
GUDANA KARKASHINSU, SUNA MASU DAWWAMA A CIKINSU, ALLAH YA YARDA DA SU, KUMA SUN
YARDA DA SHI, WADANNAN SUNE KUNGIYAR ALLAH, KUMA LALLAI KUNGIYAR ALLAH SUNE
MASU BABBAN RABO" [Mujadalah: 22].
Ka sani –Allah ya shiryad da kai zuwa ga biyayya a gare shi-,
Lallai mikakken addini; tafarkin annabi Ibrahima, shine: Ka bauta wa Allah, shi kadai, kana mai tsantsanta addini a gare shi, kuma
da aikata haka, Allah ya umarci dukkan Mutane, kuma ya halitta su domin haka,
kamar yadda Allah Ta'alah ya ce: "KUMA BAMU HALITTA MUTUM DA ALJANI BA,
FACE SU BAUTA MIN" [Zariyaat: 56].
Ma'anar:
"SU BAUTA
MIN", shine su min tauhidi (kadaita Allah).
Mafi girman abinda Allah ya yi umarni da shi, shine, Tauhidi, wanda kuma shine: kadaita Allah a cikin bauta.
Kuma mafi girman abinda Allah ya yi hani akansa, shine shirka, wanda kuma ita ce: Rokon wanin Allah tare da Allah.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "KU BAUTA WA ALLAH, KADA KU HADA SHI DA KOWA"
[Nisa'i: 36].
Idan aka ce maka: Menene ginshikai uku, wadanda ya zama wajibi mutum ya
sansu?
Sai ka ce: Bawa,
ya san UbangijinSa, da addininSa, da AnnabinSa; Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-.
[GINSHIKI NA FARKO]:
Idan aka ce maka: Wanene Ubangijinka?
Sai ka ce: Ubangijina,
shine Allah, wanda ya rene ni, kuma ya reni dukkan talikai, da ni'imominSa,
kuma shine abin bautata, bani da wani abin bauta, wanda ba shi ba.
Dalilin haka shine
fadinSa Madaukaki:"GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI" [Fatiha:
2]. Kuma dukkan abinda ba Allah ba halitta ne, Ni kuma daya ne daga
cikin wadannan halittun.
Idan
aka ce maka: Da me ka san Ubangijinka?
Ka ce: Da ayoyinSa da halittunSa.
Daga cikin
ayoyinsa, akwai dare da yini, da rana da wata.
Daga cikin
halittunsa, akwai sammai bakwai da abinda
suke cikinsu, da kassai bakwai, da abinda suke cikinsu da
kuma abinda
yake a tsakaninsu.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "DAGA AYOYINSA AKWAI DARE DA YINI DA RANA DA
WATA, KADA KU YI SUJJADA GA WATA KO RANA, KU YI SUJJADA GA ALLAN DA YA HALITTA
SU, IDAN KUN KASANCE GA SHI KADAI KUKE YIN BAUTA" [Fussilat: 37].
Da fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE UBANGIJINKU SHINE ALLAN DA YA
HALITTA SAMMAI DA KASA, A CIKIN YINI SHIDA, SA'ANNAN YA DAIDAITA A AL'ARSHI,
YANA SHIGAR DA DARE YA RUFA YINI, YANA NEMANSA DA GAGGAWA, KUMA RANA DA WATA DA
TAURARI HORARRU NE DA UMARNINSA, LALLAI HALITTA TASA CE, UMARNI NASA NE,
ALBARKAR ALLAH UBANGIJIN HALITTU TA BAYYANA" [A'araf: 54].
Kuma
Ubangiji shine abin bauta, dalili shine fadinSa Madaukaki: "YA
KU MUTANE! KU BAUTA WA
UBANGIJINKU DA YA HALITTA KU, DA WADANDA SUKE GABANINKU, DOMIN KU SAMU KARIYA *
WANDA YA SANYA MUKU KASA SHIMFIDA, SAMA KUMA GINI, YA SAUKAR DA RUWA DAGA SAMA,
SA'ANNAN YA FITAR DA ABINCI DAGA 'YA'YAN ITACE, DA SHI, SABODA KU, DON HAKA,
KADA KU SANYA WA ALLAH KISHIYOYI, ALHALI KUNA SANE" [Bakara: 21-22].
Ibnu-kasir –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce:
"Wanda ya halicci wadannan ababen shine mai cancantar bauta".
Nau'ukan ibada wadanda Allah ya yi umarni da su, Misalinsu shine: Musulunci, da Imani, da Ihsani, kuma
daga cikin ibada akwai, addu'a, tsoro, fata, tawakkali, bayyana kwadayi, da
tsoro, da khushu'i, da khashyah, da maida lamari ga Allah, da neman taimako, da
neman tsari, da neman agaji, da yanka, da bakance, da abinda ba wannan ba cikin
na'ukan ibada, wadanda Allah ya yi umarni da su, dukkansu
ana yinsu ga Allah Ta'alah.
Dalili
kuma shine: FadinSa Madaukaki: "KUMA
LALLAI WURAREN SUJJADA NA ALLAH NE; SABODA HAKA, KADA KU ROKI WANI TARE DA ALLAH"
[Jin: 18].
Duk wanda
ya aiwatar da wani abu na ibada ga wanin Allah shi mushriki kafiri.
Dalili
shine fadinSa Madaukaki: "KUMA
DUK WANDA YA ROKI WANI ABIN BAUTA TARE DA ALLAH, BASHI DA HUJJA AKAN HAKA, TO
LALLAI HISABINSA YANA WURIN UBANGIJINSA, KUMA LALLAI SHA'ANIN, KAFIRAI BASA
SAMUN RABO" [Mu'uminuna: 117].
Ya
zo a cikin hadisi, "Addu'a itace ibada".
Dalili shine fadinSa
Madaukaki: "UBANGIJINKU YACE, KU ROKE NI, ZAN AMSA MUKU, LALLAI WADANDA
SUKE GIRMAN KAI, BASU MIN BAUTA ZASU SHIGA JANNAMA, SUNA KASKANTATTU" [Gafir: 60].
Dalilin ibadar tsoro shine, fadinSa Madaukaki: "KUMA KADA KU JI
TSORONSU, KU JI TSORONA IDAN KUN KASANCE MUMINAI"
[Ali-imarana: 175].
Dalilin ibadar fata kuma
shine fadinSa Madaukaki: "WANDA YA KASANCE YANA FATAN HADUWAR UBANGIJINSA,
TO YA AIKATA AIKI NAGARI, KUMA KADA YA HADA WANI CIKIN BAUTAR UBANGIJINSA"
[Kahf: 110].
Dalilin Tawakkali shine
fadinSa Madaukaki: "GA ALLAH NE, ZA KU DOGARA, IDAN KUN KASANCE MUMINAI"
[Ma'idah: 23]. Da fadinSa: "DUK WANDA YA DOGARA GA ALLAH, TO YA
ISAR MASA" [Dalak: 3].
Dalilin ibadar kwadayi da fargaba da khushu'i, shine
fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE, SU, SUN KASANCE SUNA YIN SAURIN AIKATA
ALHERORI, KUMA SUNA ROKONMU CIKIN KWADAYI DA FARGABA, KUMA SUN KASANCE A GARE
MU MASU KHUSHU'I" [Anbiya'i: 90].
Dalilin ibadar tsoro: shine fadinSa Madaukaki: "KADA KU JI TSORONSU, KU JI TSORONA" [Ma'idah: 3].
Dalilin ibadar maida lamari ga Allah: shine fadinSa Madaukaki: "KUMA KU MAYAR DA AL'AMARI ZUWA GA ALLAH, KU MIKA WUYA A GARE SHI" [Zumar: 54].
Dalilin ibadar neman taimako: shine fadinSa Madaukaki: "A GARE KA MUKE YIN
BAUTA, KUMA DAGA GARE KA MUKE NEMAN TAIMAKO"
[Fatiha: 5]. Ya zo cikin hadisi:
"Idan zaka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah".
Dalilin ibadar neman tsari: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: INA NEMAN
TSARIN UBANGIJIN SAFIYA" [Falak: 1]. Da "KA CE: INA NEMAN TSARIN UBANGIJIN MUTANE"
[Nas: 1].
Dalilin ibadar neman agaji: shine fadinSa Madaukaki: "A YAYIN DA KUKE NEMAN
AGAJIN UBANGIJINKU, SAI YA AMSA MUKU" [Anfaal: 9].
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "KA CE: LALLAI NE SALLATA DA YANKANA,
DA RAYUWATA, DA MUTUWATA, NA ALLAH NE UBANGIJIN TALIKAI * BASHI DA ABOKIN
TARAYYA" [An'am: 162-163].
Ya zo cikin sunnah: "Allah ya tsine wa wanda ya yi yanka,
ga wanin Allah".
Dalilin ibadar bakance: shine fadinSa Madaukaki: "SUNA CIKA BAKANCE,
KUMA SUNA TSORON YININ DA SHARRINSA YAKE YADUWA"
[Insaan: 7].
ASALI NA
BIYU: SANIN ADDININ MUSULUNCI, DA DALILAI.
SHINE, Mika wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa
gare shi da da'a, da barranta daga shirka da Ma'abutansa.
Kuma addini martabobi uku ne, Musulunci, da
Imani, da Ihsani. Kuma kowace martaba tana da
rukunnai.
Martabar farko: Musulunci.
Rukunnan Musulunci guda biyar ne: Shaidawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne,
da tsayar da sallah, da bayar da zakkah, da azumin Ramadhana, da Hajjin dakin
Allah mai alfarma.
Dalilin Kalmar shahada shine
fadinSa Madaukaki: "ALLAH YA SHAIDA: LALLAI BABU ABIN BAUTAWA DA
CANCANTA FACE SHI, KUMA MALA'IKU DA MA'ABUTA ILIMI SUN SHAIDA, YANA TSAYE DA
ADALCI, BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA FACE SHI, MABUWAYI MAI HIKIMA"
[Ali-imrana: 18].
Ma'anar kalmar (LA ILA
ILLAL LAHU) shine babu abin bautawa da cancanta, face Allah, saboda "LA
ILAHA" tana kore cancanta ne ga dukkan ababen da ake musu bauta, koma
bayan Allah. "ILLAL LAHU" kuma, yana tabbatar da cancantar
bautan ne ga Allah shi kadai; bashi da abokin tarayya cikin bautarsa, kamar
yadda bashi da abokin tarayya cikin mulkinsa.
Kuma tafsirin (LA ILAHA ILLAL
LAHU) wanda yake fitar da ma'anarta a sarari shine, fadinSa Madaukaki: "KA
AMBATA, LOKACIN DA IBRAHIMU YA CE GA BABANSA DA MUTANENSA, LALLAI NE NI NA
BARRANTA DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA * FACE WANDA YA KAGE NI" [Zukruf:
26-27]. Da fadinSa: "KA CE, YA KU MA'ABUTA LITTAFI, KU TAFO, ZUWA GA
KALMA MAI DAIDAITAWA, A TSAKANINMU DA KU, KADA MU BAUTA WA KOWA, FACE ALLAH,
KUMA KADA MU HADA KOME DA SHI, KUMA KADA SASHENMU YA RIKI SASHE, UBANGIJI,
BAICIN ALLAH, IDAN KUMA SUKA BIJIRE, SAI KACE: KU YI SHAIDA, LALLAI NE MU MASU
SALLAMAWA NE" [Ali-imrana: 64].
Dalili akan shaidawa lallai
annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine fadinSa Madaukaki: "HAKIKA
WANI MANZO DAGA KAYUKANKU YA ZO MUKU, ABINDA YAKE WAHALAR DA KU YANA BUWAYARSA,
MAI KWADAYI NE A GARE KU, GA MUMINAI KUMA MAI TAUSHI NE, MAI JIN KAI"
[Tauba: 128].
Ma'anar
shaidawa lallai annabi Muhammadu manzon Allah ne, shine:
Yin da'a a gare shi cikin abinda yayi umarni, da gaskata shi cikin abinda ya
bada labari, da nisantar abinda ya yi hani akansa; ya tsawatar, da kuma kada a
bauta wa Allah sai da abinda ya shar'anta.
Kuma dalilin sallah da zakkah, da
bayani kan fassarar tauhidi shine fadinSa Madaukaki: "BA A
UMARCE SU DA KOMAI BA, FACE BAUTA WA ALLAH SUNA TSARKAKE ADDININSU A GARE SHI, SUNA
KARKATA ZUWA ADDININ GASKIYA, KUMA SU TSAYAR DA SALLAH, SU BADA ZAKKAH, KUMA
WANNAN SHINE ADDINI MIKAKKE" [Bayyinah: 5].
Kuma dalilin azumi shine
fadinSa Madaukaki: "YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, AN WAJABTA MUKU AZUMI
KAMAR YADDA AKA WAJABTA SHI GA WADANDA SUKE GABANINKU, LA'ALLA KO ZA KU SAMU
TAKAWA" [Bakara: 5].
Kuma
dalilin hajji shine fadinSa Madaukaki: "KUMA ALLAH YA WAJABTA WA MUTANE
HAJJIN DAKINSA GA WANDA YA SAMU HANYAR ZUWA, KUMA WANDA YA KAFIRCE, TO LALLAI
ALLAH YA WADATA GA BARIN TALIKAI" [Ali-imrana: 97].
MARTABA TA BIYU: ITACE; IMANI;
Kuma imani rassa
saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu shine, fadin LA ILAHA ILLAL LAHU, Kuma
mafi kankantarsu itace, kautar da abu mai cutarwa daga hanya, Kuma kunya reshe
ne na imani.
Rukunnan imani guda shida ne, Ka yi
imani da Allah, da Mala'ikunSa, da LittatafanSa, da ManzanninSa, da ranar
karshe, da kaddarar alheri da ta sharri.
Dalili
akan wadannan rukunnan guda shida, fadinSa Madaukaki: "BA KAWAI
ADDINI SHINE KU JUYAR DA FISKOKINKU, WAJEN MAFUDAR RANA, KO MAFADARTA, AMMA ADDINI
SHINE GA WANDA YA YI IMANI DA ALLAH, DA RANAR KARSHE, DA MALA'IKU, DA
LITTATAFAI, DA ANNABAWA" [Bakarah: 177].
Dalilin kaddara kuma shine, FadinSa Madaukaki: "LALLAI NE
MU, KOWANE ABU MUN HALICCE SHI DA KADDARA" [Kamar: 49].
MARTABA
TA UKU: IHSANI (KYAUTATA BAUTA)
Rukuni ne guda daya, kuma shine: Ka bauta wa Allah (da
kyautatawa), kamar kana ganinsa, don idan kai baka ganinsa, shi yana ganinka.
dalili
kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI NE ALLAH YANA TARE DA MASU
TAKAWA, WADANNAN DA SUKE MASU KYAUTATA" [Nahl: 128].
Da fadinSa Madaukaki: "KA DOGARA GA
MABUWAYI MAI RAHAMA * WANDA YAKE GANINKA A LOKACIN DA KAKE TSAYUWA (A SALLAH) *
DA JUJJUYAWARKA A CIKIN MASU SUJJADA * LALLAI, SHINE MAI JI, MASANI" [Shu'ara'i:
219].
Da fadinSa
Madaukaki: "BA ZA KA KASANCE CIKIN WANI SHA'ANI BA, KO KARANTA ALKUR'ANI,
KUMA BAZA KU AIKATA WANI AIKI BA, FACE MUN KASANCE MUNA HALARCE, A LOKACIN DA
KUKE KUKKUTSAWA A CIKINSA" [Yunus: 61].
Dalili
daga cikin sunnah, shine shahararren hadisin mala'ika Jibrilu, wanda aka ruwaito
shi daga Umar –Allah ya yarda da shi- ya ce: Wata rana muna zaune
a wurin Manzon Allah –S.A.W-, Sai wani Mutum ya bullo mana, mai tsananin farin
tufafi, mai tsananin bakin gashi, babu wata alamar tafiya a gare shi, kuma babu
wani daga cikinmu da ya sanshi, har ya zauna kusa da Annabi –S.A.W-; Sai ya
jingina guiwoyinsa zuwa guiwoyinsa, ya kuma dora tafukansa akan cinyoyinsa,
yace: Ya Muhammadu! Bani labari akan Musulunci? Ya ce: Shaidawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzon Allah ne,
kuma ka tsayar da salla, ka bada zakka, ka yi azumin watan Ramadhana, ka yi
hajjin daki; idan ka samu hanyar zuwa gare shi. Sai
yace: ka yi gaskiya, Sai muka yi mamakinsa; yana tambayarsa kuma yana gaskata
shi.
Sai
yace: Ba ni labari akan imani? Yace: Ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da
littatafansa, da Manzanninsa, kuma ka yi imani da kaddara; na alkhairinsa dana
sharrinsa.
Yace:
To ba ni labari akan "ihsani"? Sai
yace: Ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, domin idan baka ganinsa, to shi
yana ganinka.
Yace:
To ba ni labari akan kiyamah? Sai yace: Wanda
ake tambayarsa akanta bai fi wanda yayi tambayar sanin lokacinta ba.
Sai
yace: To ba ni labari akan alamominta? Sai yace: Baiwa zata haifi uwar gijiyarta, kuma zaku ga
marasa takalma, tsirara, masu kiyon dabbobi suna yin gini masu tsayi.
Yace:
Sannan sai ya tafi, sai na zauna na wani lokaci, Sa'annan sai yace: Ya
kai Umar, shin ka san wanene mai yin wannan tambayar? Sai
yace: Allah ne da Manzonsa suka sani. Yace: Lallai
shi mala'ika Jibrilu ne, ya zo muku, domin ya karantar da ku addininku".
ASALI NA UKU: SANIN ANNABINKU
MUHAMMADU –S.A.W-:
Shine annabi:
Muhammadu dan Abdullahi dan Abdulmuddalib, dan Hashim. Hashim kuma daga kabilar
Kuraishawa ne, su kuma Kuraishawa daga al'ummar Larabawa suke, Larabawa kuma
daga zurriyar annabi Isma'il dan Ibrahimul Khalil, Allah ya yi karin mafificin
salati da sallama akansa, da kuma Annabinmu.
Ya rasu, yana da shekaru sittin
da uku, shekaru arba'in gabanin annabta, shekaru ashirin da uku yana
annabi manzo.
An bashi annabta da saukar
"Ikra'a", an kuma turo shi da manzanci da saukar "Ya, ayyuhal
muddasir".
Garinsa
shine Makkah. ya kuma yi hijira zuwa ga Madinah.
Allah ya turo shi
da gargadi daga shirka, kuma domin ya yi kira zuwa ga Tauhidi;
Dalili shine, fadinSa Madaukaki: "YA
WANDA YA LULLUBA DA MAYAFI * KA TASHI DOMIN YIN GARGADI * KUMA UBANGIJINKA KA
GIRMAMA SHI * KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU * GUMAKA KUMA KA KAURACE MUSU *
KADA KA YI KYAUTA KANA NEMAN KARI * KUMA
SABODA UBANGIJINKA, SAI KA YI HAKURI" [Mudassir: 1-7].
Ma'anar: "KA
TASHI DOMIN KA YI GARGADI" wato yayi gargadi akan shirka, ya kuma kira
zuwa ga Tauhidi. "KUMA UBANGIJINKA KA GIRMAMA SHI", Ma'ana: ka
girmama shi da tauhidi. "KUMA TUFAFINKA KA TSARKAKE SU",
ma'ana: ka tsarkake ayyukanka daga shirka. "GUMAKA KUMA KA KAURACE MUSU",
Rujz: gumaka, kwaurace musu: shine barinsu da barranta daga gare su, da
ma'abutansu.
Ya dauki shekaru goma yana yin da'awa akan Tauhidi.
Kuma bayan shekaru goma sai aka yi mi'iraji da shi zuwa sama, sai aka farlanta
masa salloli biyar, kuma ya yi sallah a garin Makkah tsawon shekaru uku, bayansu kuma aka umarce shi da yin hijira, zuwa garin Madina.
Hijira: ita ce:
kaura daga garin shirka, zuwa garin Musulunci.
Kuma hijira farilla ne, ga wannan
al'ummar, daga garin shirka, zuwa garin Musulunci, kuma aiki da ita yana
nan, har zuwa tashin kiyama.
Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "LALLAI
WADANNAN DA MALA'IKU SUKA KARBI RAYUKANSU, ALHALIN SUNA MASU ZALUNTAR KANSU, SU
KA CE: A CIKIN ME KUKE? SAI SUKA CE: MUN KASANCE WADANDA AKA RAUNANA A CIKIN
KASA, SUKA CE: ASHE KASAR ALLAH BATA KASANCE MAYALWACIYA BA? DOMIN KU YI HIJIRA
GARE TA, TO WADANNAN MAKOMARSU JAHANNAMA CE, KUMA TA MUNANA TA ZAMA MAKOMA * IN
BANDA MASU RAUNI DAGA MAZA DA MATA DA YARA, WADANDA BASU IYA YIN WATA DABARA,
KUMA BASU SHIRYUWA GA HANYA * TO WADANNAN AKWAI TSAMMANIN ALLAH YA YAFE LAIFI
DAGA GARE SU, KUMA ALLAH YA KASANCE MAI YAFEWA NE MAI GAFARA" [Nisa'i:
97-99].
Da fadinSa Madaukaki: "YA KU BAYINA,
WADANDA SUKA YI IMANI, LALLAI NE KASATA MAI YALWA CE, SABODA HAKA KU BAUTA MINI"
[Ankabut: 56].
Bagawiy –Allah ya yi masa rahama- ya ce:
"Sababin saukar wannan ayar akan Musulman da suke garin Makkah ne, wadanda
basu yi hijira ba, sai Allah ya kira su da sunan imani".
Dalili
akan hijira daga cikin hadisai, akwai fadinSa –S.A.W-: "Hijira bata
yankewa har sai karban tuba ta yanke, kuma tuba bata yankewa har sai rana ta
fudo daga mafadarta".
Yayin da ya zauna a garin Madina sai aka
umarce shi da yin aiki da sauran shari'oi, misalin zakkah, da azumi, da hajji,
da jihadi, da kiran salla, da umarni da kyakkyawa, da hani ga mummuna, da wasun
wadannan daga cikin shari'oin Musulunci. Ya dauki shekaru goma akan haka.
Sa'annan ya rasu, salatin
Allah da sallamarsa su kara tabbata a gare shi. Addininsa kuma mai wanzuwa ne.
Wannan shine addininsa, babu wani
alkhairi face ya nusar da al'ummarsa akansa, kuma babu wani sharri face ya
tsawatar mata akansa.
Kuma alkhairin da ya nuna wa al'umma, shine Tauhidi da dukkan
abinda Allah yake sonsa, kuma ya yarda da shi.
Sharrin da ya tsawatar akansa, shine:
Shirka da dukkan abinda Allah baya sonsa, kuma ya ke ki.
Allah ya aike shi da manzanci
zuwa ga Mutane gaba daya, kuma ya farlanta yin da'a a gare shi,
akan dukkan Aljanu da Mutane; Dalili kuma shine FadinSa Madaukaki: "KA
CE: YA KU MUTANE, LALLAI NE NI 'DAN AIKAN ALLAH NE ZUWA GARE KU GABA DAYA"
[A'araf: 158].
Allah ya cika addininsa, da shi, Dalili kuma
shine fadinSa Madaukaki: "A YAU NA CIKA MUKU ADDININKU, KUMA NA CIKE
NI'IMOMINA AKANKU, KUMA NA YARJE MUKU MUSULUNCI A MATSAYIN ADDINI"
[Ma'idah: 3].
Kuma
dalili akan mutuwarsa –S.A.W-: "LALLAI, KAI MAI MUTUWA NE, KUMA
LALLAI SU MASU MUTUWA NE * SA'ANNAN KU, A RANAR KIYAMA, A WURIN UBANGIJINKU,
MASU YIN HUSUMA NE" [Zumar: 31].
Kuma Mutane idan suka mutu za a
tayar su, dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "DAGA KASA MUKA
HALITTA KU, KUMA ZUWA CIKINTA ZA MU MAYAR DA KU, KUMA DAGA GARE TA ZA MU FITAR
DA KU, A KARO NA GABA" [Daha: 55]. Da fadinSa Madaukaki: "ALLAH
YA TSIRAR DA KU DAGA KASA TSIRARWA, SA'ANNAN YA MAYAR DA KU CIKINTA, YA KUMA
SAKE FITAR DA KU FITARWA" [Nuh: 17-18].
Kuma bayan an tayar da su za a
musu hisabi, kuma za a sakanta musu da ayyukansu, Dalili
akan haka shine fadinSa Madaukaki: "ZAI YI SAKAYYA GA WADANDA SUKA
MUNANA AIKI DA ABINDA SUKA AIKATA, KUMA ZAI YI SAKAYYA GA WADANDA SUKA KYAUTATA
DA ALJANNAH" [Najm: 31].
Wanda ya karyata lamarin sake
tayar da Mutane, to ya kafirta, Dalili kuwa shine fadinSa Madaukaki:
"WADANDA SUKA KAFIRTA SUN RIYA CEWA, BA ZA A TAYAR DA SU BA, KA CE,
A'A, INA RANTSUWA DA UBANGIJINA, LALLAI ZA A TAYAR DA KU, SA'ANNAN A BAKU
LABARIN ABINDA KUKE AIKATAWA, WANNAN KUMA GA ALLAH ABU NE MAI SAUKI"
[Tagabun: 7].
Kuma Allah ya turo Manzanni gaba
dayansu, suna yin albishir, suna gargadi, Dalili akan haka, shine fadinSa
Madaukaki: "MANZANNI MASU ALBISHIR DA GARGADI, DOMIN KADA
MUTANE YA KASANCE SUNA DA HUJJA, BAYAN MANZANNI" [Nisa'i: 156].
Na farkonsu shine annabi Nuhu –عليه السلام-.
Na karshensu kuma, annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-, kuma shine
cika-makon Annabawa.
Dalili akan
farkon Manzanni shine annabi Nuhu –عليه السلام- shine fadinSa
Madaukaki: "LALLAI NE MUN YI WAHAYI ZUWA GARE KA, KAMAR YADDA MUKA YI
WAHAYI GA NUHU DA ANNABAWAN DA SUKE BAYANSA" [Nisa'i: 163].
Kowace al'ummar da Allah ya aike
mata Manzo - tun daga annabi Nuhu har zuwa annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- yana umartarsu ne da
ibadar Allah; shi kadai, kuma yana hana su bauta wa dagutu.
Dalili shine fadinSa Madaukaki: "KUMA
HAKIKA MUN TAYAR DA MANZO GA KOWACE AL'UMMA; (SUNA CEWAR); KU BAUTA WA ALLAH,
KUMA KU NISANCI DAGUTU" [Nahli: 36].
Kuma Allah ya farlanta wa dukkan
bayi (cewa) su kafirce wa dagutu, su yi imani da Allah.
Ibnul-kayyim –Allah ya yi masa rahama- ya
ce: Ma'anar Dagutu: Shine duk wanda Bayi suka wuce iyaka akansa, na abin bauta,
ko wadanda ake bi, ko wadanda ake musu da'a.
Dagutu suna da yawa, amma
manyansu guda biyar ne; Iblisu –Allah ya la'ance shi-, da wanda aka masa bauta
alhalin ya yarda, da wanda ya kira Mutane zuwa ga bauta a gare shi, da wanda ya
riya sanin wani abu na ilimin gaibu, da wanda ya yi hukunci ba da abinda Allah
ya saukar ba, Dalili kuma shine fadinSa Madaukaki: "BABU TILASTAWA A
CIKIN ADDINI, HAKIKA SHIRIYA TA BAYYANA DAGA BATA, DON HAKA, WANDA YA KAFIRTA
DA 'DAGUTU, KUMA YA YI IMANI DA ALLAH, TO HAKIKA, YA YI RIKO DA IGAYA
AMINTACCIYA" [Bakara: 256].
Wannan kuma shine ma'anar (LA ILAHA ILLAL
LAHU).
Kuma ya zo
a cikin hadisi "Kan lamarin nan, shine Musulunci, kuma kashin bayansa shine
salla, kuma tozon kololuwarsa shine jihadi fiysabillahi". Allah ne Masani.
No comments:
Post a Comment