HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/SHA'ABAN/1440H
daidai da 12/AFRILU/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. HUSAINDAN ABDUL'AZI ALUS-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
WATAN SHA'ABAN
FALALARSA DA HUKUNCE-HUKUNCENSA
(شهر شعبان
فضائل وأحكام)
Shehin Malami
wato: Husain dan Abdul'aziz Alus-sheikh–Allah ya kiyaye shi- ya yi
hudubar juma'a mai taken: WATAN SHA'ABAN FALALARSA DA
HUKUNCE-HUKUNCENSA,Wanda kuma a cikinta ya tattauna,
akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Bayan
haka:
Watan
Sha'aban kamar sauran watannin ne, waxanda ya wajaba Mutum Musulmi ya riqa sauke
farillan Allah Mabuwayi da xaukaka a cikinsu, ya kuma tabbatar da aikata xa'arsa
Subhanah, kuma Musulmi ya katange rai daga dukkan haramun da savo.
Kuma
watan Sha'aban haqiqa ya kevantu da wasu falaloli, don haka ne ya dace Mumini
ya kasance mai sauri wajen nemansu, yana gaggawar ribatarsu, Bukhariy da Muslim
sun ruwaito, daga uwar Muminai; A'ishah -رضي الله
عنها-, lallai ta ce: Ban ga Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya kammala azumin wani wata in banda Ramadhana
ba, kuma ban ga ya yawaita yin azumi a cikin wani watan fiye da na Sha'aban ba".
A
wata riwaya ta Bukhariy da Muslim, cewa ta yi: Annabi -صلى الله عليه وسلم- bai kasance yana azumin wani
wata fiye da watan Sha'abana ba, saboda ya kasance yana azumtarsa gaba xayansa".
Saidai
riwayar azumtar Sha'abana gaba xayansa, ana fassara ta da azumtar mafi yawan
kwanakinsa, kamar yadda Abdullahi bn Almubarak ya bayyana shi, da Ibnu-Hajar da
wasunsu, saboda abinda ya zo na riwayar
Muslim mai cewa: "Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana azumtar watan
Sha'abana, in ban da kaxan daga cikinsa".
Ibnu-Rajab
-رحمه الله- ya ce: "Lallai azumtar watan
Sha'aban shine yafi falala akan sauran watannin".
San'aniy
-رحمه الله- ya ce: "A cikin hadisin akwai
dalilin dake nuna cewa lallai Annabi -صلى
الله عليه وسلم-
ya kasance yana kevance watan Sha'abana da yin azumi, fiye da wani watan wanda
ba shi ba".
Sha'aban
ya kasance, ana kiransa a wajen wasu magabatan na kwarai, da watan Mahaddata;
saboda yawaita muraja'ar Alkur'ani da suke yi, da yadda suke yanke komai izuwa
ga tilawarsa, da lazimtarsu ga sabunta alkawarinsa, da yawaita karatunsa, domin
shiri ga tsayuwan dare a cikin watan azumi, na Ramadhana.
Sai
a yi gaggawa, a yi sauri, sai a yi gaggawa a yi sauri, wajen raya wannan watan
(na Sha'abana) da dangogin ibadodi domin kusantar Allah, da sauran nafilfili da
xa'oi, Imam Ahmad ya ruwaito, da Nasa'iy, daga Usamah ɗan
Zaid -Allah ya ƙara yarda a gare su- ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ban ga kana azumi a cikin wani wata irin abinda kake yi a cikin
watan Sha'abana ba? Sai Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: Wannan wata ne da Mutane
suke gafala da shi, a tsakanin watan Rajab da Ramadhana, kuma wata ne da ake xaukaka
ayyuka (na shekara) a cikinsa ga Ubangijin talikai, sai nake son a ɗaukaka
aikina alhalin ina azumi. Ahmad ya fitar da shi da
Nasa'iy, kuma Ma'abuta ilimi sun ce: hadisi ne hasan.
Ibnu-Rajab
-رحمه الله- ya faxa dangane da ma'anar: "wata ne da Mutane suke gafala da shi, a tsakanin watan
Rajab da Ramadhana, cewa hakan ya nuna cewa,
yayin da watanni biyu masu girma suka kewaye Sha'aban, wato, Wata mai alfarma,
da watan azumi, sai Mutane suka shagaltu da su, suka kyale shi, har ya zama an
gafala an bar shi -har zuwa faxinsa-:
Sai Mutane su shagaltu da watannin da suka fi falala su kyale shi, ko su
sarayar da samun falalar abinda ba shahararre ba a wurinsu".
Amma
abinda ya zo a cikin Musnad (Ahmad) da Sunan na Abi-Dawud da Nasa'iy da waninsu
na hadisin: "Idan watan
Sha'aban ya kai rabi, to kada ku yi azumi" to mafi
yawan Ma'abuta ilimi suna raunata wannan hadisin, domin isnadinsa da mataninsa
munkari ne, a wajen jiga-jigan Maluma. Wanda kuma ya inganta isnadinsa, to ya
fassara mataninsa akan wanda bashi da wata al'ada ta yin azumi, to shi kam
makruhi ne ya yi azumi bayan watan Sha'aban ya raba biyu, matuqar ya yi nufin
tsantseni ga Ramadhana, saboda hakan bidi'a ne.
'Yan'uwana
Musulmai!
Yana
daga abubuwan da sunnah ta tabbatar, Lallai baya halatta ga Musulmi, matukar
bashi da al'adar azumtar yini da shan ruwa a wani yinin, ko ta azumtar litinin
da alamis, to bai halatta ya rigayi watan azumi da yin azumi xaya ko biyu ba,
da nufin yin tsantseni ga watan Ramadhana, saboda Annabi -صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Kada ku rigayi shigan Ramadhana da azumtar yini xaya ko
biyu, sai ga Mutumin da yake yin wani azumi, to ya azumce shi",
Bukhariy da Muslim.
Kuma Ammar
xan Yasir -رضي الله عنه- ya
ce: "Wanda ya yi azumin ranar da
ake shakku a cikinta, to haqiqa ya sava wa Baban Qasimu -صلى الله عليه وسلم-" Abu-dawud
ya ruwaito shi da Tirmiziy da isnadi ingantacce.
Ya
ku bayin Allah!
Ku rayar
da lokutanku a cikin wannan watan da sauran watanni da dukkan abinda zai
kusantar da ku zuwa ga Majivincinku Mabuwayi da xaukaka, kuma ku yi tsere wajen
aikata ayyukan alherori, kuna masu ribatar kyawaywan ayyuka, Allah Ta'alah ya
ce: "Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga
Ubangijinku, da wata Aljannah wanda faxinta shine da faxin sammai da qasa, an yi
tattalinta ga masu taqawa" [Ali-imrana: 132].
Kuma Allah
Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Ya ku waxanda suka yi
imani ku ji tsoron Allah, kuma rai ta yi dubi ga abinda ta gabatar saboda gobe
(qiyamah), kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai bada labari ne ga
abinda kuke aikatawa".
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Bayan
haka
Keve daren
rabin watan Sha'aban da sallar dare, yininta kuma da azumi, to wannan al'amari
ne da bai zo a cikin dalili ingantacce daga wanda baya kuskure -صلى الله عليه وسلم- ba.
Hasalima
dayawa daga cikin jiga-jigan Maluma sun yi inkarinsa, kuma sun bayyanar da
kasancewarsa bidi'a ne.
No comments:
Post a Comment