WAJABCIN
HALARTAR JAM'I MASALLATAI
An
ruwaito daga Abdullahi dan Mas'ud -رضي الله عنه- yana cewa: "Wanda yake faranta
masa, ya hadu da Allah a gobe (kiyamah) yana
Musulmi, to ya kiyaye wadannan sallolin a lokacin da ake kiransu, saboda Allah
ya shar'anta wa Annabinku -صلى الله عليه وسلم- hanyoyin shiriya, kuma sallolin
suna daga hanyoyin shiriya. Kuma da, za ku yi salla a cikin gidajenku, kamar
yadda mai kin halartar Masallaci yake yin salla a cikin gidansa, da kun bar
sunnar Annabinku, da kuma za ku bar sunnar Annabinku da kun bace. Kuma babu
Mutumin da zai yi tsarki sai ya kyautata alwalarsa, sa'annan ya nufi masallaci
daga cikin wadannan Masallatan, face Allah ya rubuta masa lada akan dukkan
takun da ya yi, kuma ya daga darajarsa da hakan, kuma ya kankare masa mummunansa
da wannan takun. Kuma hakika na ganmu (a zamanin Sahabbai), babu mai kin
halartar sallar jam'i face Munafiki wanda aka sanshi da munafirci. Kuma hakika
Mutum ya kasance ana zuwa da shi ana rike da shi a tsakanin Mutane biyu, har a
tsayar da shi a cikin sahu", Muslim ya ruwaito shi.
No comments:
Post a Comment