USULU SALASA A TAKAICE
بسم الله
الرحمن الرحيم
Idan aka ce maka: Menene ginshikai uku, wadanda ya zama
wajibi Mutum ya sansu? Ka ce: Bawa, ya san UbangijinSa, da addininSa, da AnnabinSa; Muhammadu –S.A.W-.
[ASALI NA FARKO: SANIN UBANGIJI]:
Idan aka ce maka: Wanene Ubangijinka? Ka ce: Ubangijina, shine Allah, wanda ya rene ni, kuma ya
reni dukkan talikai da ni'imominSa, kuma shine abin bautata, bani da wani abin
bauta wanda ba shi ba.
Idan aka ce maka: Da me ka san
Ubangijinka? Ka ce: Da ayoyinSa da halittunSa. Ubangiji shine
abin bauta. Kuma nau'ukan ibada
wadanda Allah ya yi umarni da su,
dukkansu ana yinsu ga Allah Ta'alah
ne. Wanda ya aiwatar da wani abu na ibada ga wanin Allah shi
mushriki ne kafiri.
ASALI NA FARKO: SANIN ADDININ MUSULUNCI DA DALILAI:
Shine, Mika
wuya ga Allah, da tauhidi, da jawuwa gare shi da da'a, da barranta daga shirka
da ma'abutansa. Kuma martabobi uku ne, Musulunci, da Imani, da Ihsani. Kuma
kowace martaba tana da rukunnai.
ASALI NA FARKO: SANIN ANNABINKU MUHAMMADU S.A.W:
Shine annabi: Muhammadu dan Abdullahi dan
Abdulmuddalib, dan Hashim. Ya rasu, yana da shekaru sittin da uku. Allah ya
turo shi domin yin gargadi kan shirka, kuma domin ya yi kira zuwa ga Tauhidi.
Annabi -S.A.W- ya yi wafati, Saidai addininsa mai wanzuwa ne. Wannan shine
addininsa, babu wani alkhairi face ya nusar da shi ga al'umma, kuma babu wani
sharri face ya tsawatar da su akansa. Allah ya aike shi da Manzanci zuwa ga
mutane gaba daya, kuma ya farlanta yin da'a a gare shi, akan dukkan Aljanu da Mutane.
Kuma Allah ya cika addininsa, da shi.
No comments:
Post a Comment