HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/Zulki'ida/1439H
daidai da 03/Ogosdos/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
YI MA KAI HISABI
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YI MA KAI HISABI, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah
Wanda ya ke karbar tuban bayinSa, yake yafe munanan ayyuka. Ya yalwaci dukkan
komai da jin-kai da ilimi. Kuma cikin falalarSa yake ninninka kyawawan ayyuka,
yake daga darajojin ma'abutansu.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Babu
abinda ke gagaransa a cikin kassai, ko a cikin sammai.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, wanda Allah ya karfafe
shi da nasara daga wurinSa da kuma mu'ujizozi.
Ya Allah ka yi dadin
salati da sallama da albarka, ga bawanka
kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu gaggawar aikata
alkhairori.
Bayan haka:
Ku bi Allah Ta'alah da takawa; ta hanyar kusantarSa da abinda ke yardar
da shi, da kuma nisantar abinda ke fusata shi, kuma yake kinsa.
kuma Lallai ne, wanda yayi takawa ya samu babban rabo kuma ya tsira,
Wanda kuma ya bi son zuciyarsa, to ya tabe, ya yi hasara.
Ya ku, Bayin Allah…
!!!
Ku sani Lallai ne, samun rabon
dan-adam da tsiransa ya rataya ne kan iya fin karfin ransa, da yin hisabi a
gare ta, da sa mata ido; cikin dukkan kanana da manyan zantuka da
ayyukansa, saboda duk wanda ya yi hisabi ga ransa, kuma ya yi dabaibayi ga
zantukansa da ayyukansa, har da irin ababen da suke darsuwa a cikin zuciyarsa,
sai ga abinda Allah yake so ya yarda, to lallai ya rabauta rabo mai girma,
Allah Ta'alah yana cewa: "Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaba ga UbangijinSa, sai ya kange kansa daga son rai *
To lallai ne, Aljannah ita ce makomarsa" [Nazi'at: 40-41].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya ji
tsoron tsayawa a gaba ga UbamgijinSa yana da Aljanna guda biyu" [Rahman: 46].
Kuma Allah Mabuwayi da
daukaka ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah, kuma rai ta yi
dubin abinda ta gabatar domin gobe (kiyama), kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne
Allah Mai bada labari ne akan abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].
Kuma Allah Mabuwayi da
daukaka ya ce: "Lallai ne wadanda suka yi takawa, idan waswasi daga Shedan ya shafe
su; har suka aikata zunubi, sai su tuna girman Allah, sai su komo cikin basira" [A'araf: 202].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ba sai nayi
rantsuwa da Rai mai yawan zargin kanta ba" [Kiyamah: 2].
Maluman tafsiri suka ce:
Allah ya yi rantsuwa ne da ran da take zargin kanta akan sakaci, wajen aikata
wajibai, take kuma zargin kanta akan aukawa cikin wasu ayyuka na haramun, sai
ta yawaita zargin kanta, har zuwa lokacin da lamarinta zai daidaita.
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah
(صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya yi imani da Allah da ranar karshe,
to ya fadi alkhairi ko ya yi shiru", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Wannan kuma ba zai kasance
ba, sai ta hanyar yin hisabi ga rai.
Kuma an ruwaito daga Shaddad bn Aus, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai hankali shine
wanda ya yi hisabi ga kansa, kuma ya yi aiki domin abinda ke tafe bayan mutuwa.
Gajiyayye kuma shine wanda ya biye wa son zuciyarsa, Sai yake kwallafa buri ga
Allah",
Hadisi ne hasan.
Umar bn Alkhaddabi (رضي الله عنه) ya ce: "Ku yi hisabi ga
kayukanku, gabanin a muku hisabi, kuma ku auna kayunanku gabanin a dora ku akan
sikelin awu, kuma ku yi shiri domin babban hisabi".
Kuma Maimun bn Mihran ya ce: "Mutum mai takawa,
ya fi tsananta hisabi ga kansa, fiye da marowacin abokin gamayyar kasuwanci, ga
abokin hadakar kasuwancinsa".
Kuma Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Lallai ne mumini
yana ganin zunubansa, kamar akan kololuwar dutse ne, wanda yake tsoron ya
rikito akansa. Shi kuma fajiri yana ganin zunubansa ne, kamar wani kuda, wanda
ya hau karan hancinsa, sai ya yi haka da hannunsa, wato ya kore shi da tafin
hannunsa",
Bukhariy ya ruwaito shi.
Shi mumini –a har kullum- ya kan yi hisabi ga kansa, yana
kuma kula da ransa, domin ya iya daidaituwa akan mafi kyan halaye; sai ya yi
hisabi wa kansa akan ayyukansa, yana mujahadar kansa wajen ganin ya aikata
ibadodi da da'oi; har ya iya aikata su da cikakken ikhlasi, suna tsaftatattu
lafiyayyu daga abinda ka iya shiga cikinsu na bidi'oi, da riya, da jiji-da-kai
da ganin aiki, yana neman dacewa ta hanyar aikinsa da ganin fiskar Allah, da
samun rabon gidan lahira.
Kuma yana hisabi ga kansa
domin ganin ya yi aiki na kwarai, kuma ya aikata shi yana mai dacewa da sunnar
Annabi (صلى
الله عليه وسلم), tare da lazimtar dawwama kan aikata aiki, ba tare da yin
ridda ko dena aikin ba, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma wadannan da
suka yi kokari ga neman yardarmu, to lallai za mu shiryar da su ga hanyoyinmu,
kuma lallai Allah tabbas yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma duk wanda ya
yi jihadi, to lallai yana yin jihadin ne ga kansa, Kuma lallai Allah Wadatacce
ne ga barin talikai"
[Ankabut: 6].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Lallai Mu, mun saukar da littafi zuwa gare ka, da gaskiya, sai ka
bauta wa Allah, kana mai tsarkake addini a gare shi * Kuma addini tsarkakakke
na Allah ne"
[Zumar: 2-3].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Ka ce, idan kun kasance kuna son Allah, sai ku bi ni, Sai Allah ya
so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku, saboda Allah Mai gafara ne Mai jin kai" [Ali-imraana: 31].
Kuma Sufyanus Sauri ya ce:
"Babu abinda na wahala masa wajen gyaransa, wanda yafi wahalar da ni,
fiye da niyyata, saboda tana kokarin caccanzawa".
Kuma Fadl bn Ziyad ya ce:
"Na tambayi Imam Ahmad kan niyyah, a cikin aiki; Na ce: Yaya niyyar
zata kasance? Sai yace: Ya yi ta fama da ransa, idan ya so yin aiki, har ya
zama baya nufin mutane da wannan aikin".
Kuma an ruwaito daga
Shaddad bn Aus, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Duk wanda ya yi
sallah da niyyar riya, to lallai ya yi shirka. Wanda ya yi azumi da niyyar
riya, to lallai ya yi shirka. Wanda ya yi sadaka da niyyar riya, to lallai ya
yi shirka".
Ahmad a cikin littafin
Musnad ya ruwaito shi, da Alhakim, da Dabaraniy a cikin littafin mu'ujamul
kabir.
Kuma mutum ya rika hisabi
ga ransa akan furucinsa da maganarsa; ta yadda ba zai rika sakan harshensa
wajen fadin yasassun maganganu ba, da kuma laffuza na haram. Kuma ya rika tuna
cewa, lallai Shi an wakilta Mala'iku biyu suna rubuta dukkan abinda harshensa
ke furtawa, da dukkan abinda ya aikata na ayyuka; sai kuma a masa sakayya akan
haka, ko a masa ukuba, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma lallai akanku
akwai Mala'iku masu kiyayewa, * masu karamci, marubuta * suna sanin duk abinda
kuke aikatawa"
[Imfidar:10-12].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Ba zai furta wata magana ba, face a tattare da shi, akwai mai tsaro,
halartacce"
[Kaaf: 18].
An ruwaito daga Abdullahi
bn Abbas (رضي
الله عنهما) lallai ya ce: "Lallai akan rubuta dukkan abinda mutum ya
yi magana da shi; na alheri da na sharri; har a rubuta fadinsa cewa; Na ci
kaza, na sha, na tafi, na zo, na ga".
Kuma an ruwaito daga
Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Mutum ya kan
fadi ko furta kalma, wanda Allah ya yarda da ita, ba tare da ya kai tunaninsa
ba, sai Allah ya daga darajojinsa da ita. Kuma lallai bawa, ka iya fadin wata
kalma, wanda take fusata Allah, ba tare da ya kai tunaninsa ba, sai ta gangarar
da shi cikin wutar Jahannama" , Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Abdullahi bn Mas'ud ya
ce: "Na rantse da Allah wanda babu abin bautawa face shi! A bayan kasa,
babu wanda yafi cancantar a tsawaita dabaibayi a gare shi, fiye da harshe".
Kuma Abubakar (رضي الله عنه) ya kasance yana
kama harshensa sai ya ce: "Wannan shine ya aukar da ni wuraren halaka".
Kamar yadda ya wajaba ga
Musulmi ya rika hisabi ga ransa, yana kuma yakarta, akan ababen da
suke darsuwa, da wadanda suke-kaiwa suna komowa a cikin zuciyarsa, da ababen da
suke masa waswasi, domin mafarin alheri da sharri; dukkansu daga ababen da
suke darsuwa ne a cikin zukata, suna kaiwa-suna komowa;
Don haka, idan musulmi ya
iya sanya wa ababen da suke kaiwa suna komowa a cikin zuciyarsa dabaibayi, har
ya zama yana farin ciki da abin alkhairin da suke kai-komo, yana natsuwa da su,
yana kuma zartar da su cikin aiki, to sai ya tsira; ya kuma rabauta.
Haka idan ya kori waswasin Shedanu,
da abinda shedan ke sanya masa, kuma ya nemi tsarin Allah daga waswasinsa, to
sai ya tsira daga sharrinsa ya kubuta ya samu salama daga aikata munanan ayyuka
da sabo.
Idan kuma ya gafala daga
waswasin ransa, ya karbe su –hannu bibbiyu-, to sai su kai shi zuwa ga aikin
haramun; Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan wata fizga daga Shedan ta fizge
ka, sai ka nemi tsarin Allah, lallai ne shi Mai ji ne Masani" [Fussilat: 36].
Kuma Allah a cikin suratun
Naas, ya bada umarnin a rika neman tsarinsa daga wannan makiyin mabayyani (wato
Shedan); Abdullahi bn Abbas ya ce: "Lallai Shedan yana lazimtar zuciyar kowane
dan-adam, idan ya yi mantuwa ya gafala, sai ya sanya masa waswasi, idan kuma ya
ambaci Allah, sai ya buya".
Kuma an ruwaito daga Anas (رضي الله عنه), ya ce: Manzon
Allah (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Shedan ya kan sanya mummunan
hancinsa, akan zuciyar dan-adam; amma idan mutum ya ambaci Allah, to sai shedan
ya buya, idan kuma ya manta da Allah, sai ya lankwame zuciyarsa, to wannan
shine mai sanya waswasi a boye a cikin kirazan mutane", Abu-Ya'alah
Almusily ya ruwaito shi.
Kiyaye aukawa cikin zunubai
yana kasancewa, a matakin farko, ta hanyar kididdige waswasin da Shedan ke sanyawa,
da kare kai daga fizgar shedanu, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma kada ku
kusanci alfasha; abinda ya bayyana daga cikinta, da wanda ya buya, kuma kada ku
kashe rai wanda Allah ya haramta kasha ta, face da hakki, Wannan ne Allah yake
muku wasiyya da shi, tsammaninku ku hankalta" [An'aam: 151]. Rashin kusantan
alfasha yana kasancewa ne, ta hanyar yin hisabi ga rai, a lokacin faruwan
sabubansu.
Don haka, duk wanda ya ke
hisabi ga kansa, ya ke yakarta, sai kyawawan ayyukansa su yawaita, munanan
ayyukansa su karanta, sai kuma ya fita daga duniya yana abin yabo, a tayar da
shi bayan mutuwa yana mai rabauta, sai ya kasance tare da Annabi (عليه الصلاة والسلام) wanda aka turo shi
domin ya zama mai bada shaida.
Wanda kuma ya rika biye wa
son zuciyarsa, ya juya baya ga Kur'ani, sai yake aikata dukkan abinda ransa ta
yi sha'awa, har yake jin dadin ababen sha'awa, yake dulmuya cikin laifukan
kaba'irai, ya kuma baiwa Shedan akalar jagorancin zuciyarsa, to sai Shedan ya
aukar da shi cikin dukkan zunubi mai girma, sai kuma a dawwamar da shi tare da
Shedan cikin azaba mai radadi, Allah Ta'alah yace: "Kuma kada ka bi wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga
ambatonmu, sai ya bi son zuciyarsa, alhalin al'amarinsa yana a watse" [Kahf: 28].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na fadi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Wanda ke rayar da zukata da wahayin
Alkur'ani, yana karbar kyawawan ayyuka, kuma yana yin afuwa ga munanan ayyuka.
Ina yin yabo ga Ubangijina,
kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masanin
ababen da suka buya,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai kira zuwa ga
aikata alkhairori,
Ya Allah ka yi dadin salati
da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa;
jagororin shiriya, kuma fitilun haskaka dufu.
Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah,
iyakar takawa, saboda tsoron Allah shine mafi alherin tanadi a duniya da
lahira,
Ya ku Bayin Allah …
!!
Lallai rayayyar zuciya,
Itace, wanda kyakkayawan aikinta ke faranta mata, mummunansa kuma ke bakanta
mata.
Matacciyar zuciya kuma, itace wanda bata jin
radadin aikata zunubi, kuma bata damuwa kan haka, kuma bata yin farin ciki kan
aikata kyakkayawan aiki, ko biyayya; kuma bata damuwa da ukobobin da aka rataya
ga zunuban; Sai ni'imar lafiyar jiki, da yadda duniya take fiskanto masa, ta
rude shi. Har ya rika zaton ni'imar da aka bashi, wata karama ce a gare shi
daga Allah, Allah Ta'alah yana cewa: "Shin zato, suke yi, cewa lallai
abinda muke karfafarsu da ita na dukiya da 'ya'ya, * muna gaugawan basu alheri
ne? Kai dai basu sani ba" [Mu'uminuna: 55-56].
Kuma ya zo cikin hadisi
cewa, "Lallai ana bijirar da fitintinu ga zukata, kamar yadda ake bijiro da
tabarma; tsinke-tsinke. Kuma duk zuciyar da ta kyamaci fitina, sai a sanya mata
farar alama. Duk kuma zuciyar da ta kwankwadeta, sai a zana mata bakar alama;
har zukatan su wayi gari, kamar zuciya guda biyu; zuciya fara kal, kamar
falalen dutse; wanda wata fitina ba ta cutar da ita, tsawon dawwamar sammai da
kassai. Da zuciyar da tayi baki; launinta ya caccanza, kamar kofin da aka kife
shi, wato aka mayar da kansa kasa; wanda bata sanin aiki mai kyau, kuma bata
iya kyamatar mummuna, in banda wanda ta
kwankwada na bin son zuciyarta".
Kuma dukkan cutukan zukata,
suna sanya zuciyar jinya, ko su kashe ta kurmus gabadaya, matukar mutum bai
rika yin hisabi ga zuciyarsa ba.
Kuma yana daga cikin azama
da alheri ga mutum, ya rika yin hisabi ga ransa a cikin yini da dare, da sati,
da wata, da shekara, domin ya rika gano ta ina Shedan ya kutso masa, sai ya
tuba, kuma domin ya iya risko abinda yayi sakaci a cikinsa, da fatan a yaba wa
ayyukansa, a kuma datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe.
Shi Mumini; zuciyarsa
rayayya ce, mai zurfin basira, Idan aka bashi; sai ya yi godiya, idan kuma ya
aikata zunubi, sai ya tuba, idan kuma aka jarrabe da wani ibtila'i, sai ya
dangana ya yi hakuri; saboda a cikin zuciyar mumini akwai mai masa wa'azi, da
ke farkar da shi daga gafala, mai tsoratar da shi daga aukawa halaka, saboda ya
zo cikin wani hadisi cewa:
"Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-
ya zana mana mikakken zane,
sai ya zana wasu
zanen ta geffansa,
kuma akan wannan
zanen, akwai wani mai yin da'awa,
A samansa kuma
akwai mai wa'azi;
SHI WANNAN
MIKAKKEN ZANEN, SHINE: HANYAR ALLAH,
MAI YIN KIRA KUMA
AKAN WANNAN HANYAR SHINE LITTAFIN ALLAH,
WANDA KUMA YAKE
WA'AZA A SAMAN WANNAN HANYAR, SHINE MAI WA'AZI ZUWA GA ALLAH WANDA KE CIKIN
ZUCIYAR KOWANE MUMINI,
SU KUMA HANYOYIN
DA SUKE TA DAMA DA HAGUN DINSA, SUNE HANYOYIN BATA".
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama ta aminci"
[Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, ……………………………
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment