2018/08/30

TSARIN KULA DA MOTOCIN JIGILAR MAHAJJATA (النقابة العامة للسيارات)









TSARIN KULA DA MOTOCIN JIGILAR MAHAJJATA
(النقابة العامة للسيارات)













Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya


Ma'aikatar kula da motocin daukan Mahajjata
MA'AIKATA
Rahoro ga jaridu
SASHEN SADARWA
Tsarin yanar gizo da ke dora bus din jigilar daukar Mahajjata hanya/ Bus dubu sha takwas (18,000) domin jigilar Mahajjata zuwa wuraren bauta tsarkaka (Minah, Arfah, da Muzdalifah)
MAUDU'I
Cikin kasar Saudia da wajenta
YADAWA
06/ Zul-hijjah/1439h
RANA
>Shugaban ofishin kulawa da motocin jigilar Mahajjata.
>Daraktan kula da aikin motocin a wuraren aikinsu.
>Bayanan tsarin aikin motocin, na hajjin shekara ta 1439h
MASU MAGANA
Hada hannu domin gabatar da hidima ga Bakin Allah; Mahajjata
SAKON AIKIN

Map a yanar gizo domin bibiya da nusar da bus na daukar Mahajjata
BUS DUBU SHA TAKWAS (18.000) SUNA JIGILAR MAHAJJATA MILIYAN 1.82 ZUWA WURAREN BAUTA MASU TSARKI (MINAH, ARFAH, DA MUZDALIFA)

Shugaban ofishin kula da motocin jigilar Mahajjata; Wato Abdurrahman bn Ma'ayuf Alharbiy ya bayyana cewa bus 18,415 sune za su yi jigilar bakin Allah Mahajjata zuwa wuraren bauta masu tsarki, domin su yi ayyukan hajjinsu na shekara ta 1439H.
            Kuma ofishin kulawa da motoci yana jiran samun karuwan Mahajjata, idan an kula da yadda hajjin baya ya gabata (1438h), Karin da zai iya kaiwa goma cikin dari (10/100) wato kimani Mahajjata (195,965). Kuma shugaban ya ce:
"Lallai kamfanoni masu yin jigilar Mahajjata, wadanda suke yin aiki karkashin inuwar kulawar hukumar kula da motoci, suna burin kawo motocin jigila wadanda suka dace da bakin Allah; Mahajjata, domin jidon su, daga kafafen shigowa kasar Saudia, zuwa inda suka nufa a garin Makkah, ko Madinatul munawwarah, ko tafiya cikin wuraren bauta masu tsarki –Minah, Arfah, Muzdalifa-, domin su yi ibadodinsu".
            Kamar yadda hukumar ta yi doka ga kamfanonin jigilar Mahajjata (wato kamfani 35) cewa lallai shekarun sana'anta motocin jigilar Mahajjata, kada ya fice daga tsakanin 2013 zuwa 2018 (shekaru biyar da suka shude), wannan kuma domin bayin Allah; Mahajjata, su samu cikakken hutu da moriya.

            --------- Tallafin ministirin hajji
Kuma shugaban hukumar kulawa da motocin ya yi nuni cewa, lallai tallafi ne mai girma hukumomin da suke tarayya cikin aikin hidimar Mahajjata daga wannan kasar (ta Saudia), da samun bibiya da umurni daga Mai girma ministan hajji da umrah; wato Dr. Muhammadu Salih bn Dahir Bintin, da Mai girma Na'ibinsa; Dr. Abdulfattah bn Sulaiman Mushad. Yana mai kirga hakan a matsayin sababi mai girma kuma karfafa guiwa domin dorewa wajen bunkasa aiki, da kara kyautata kayan aikin tsare-tsare da na gudanarwa. Da kokarin ficewa daga tsarin da aka masa taken: Khidmar Mahajjaci (خدمة الحاج) zuwa ga tsari mai taken: Shirya garar bako (صناعة الضيافة) tare da gina sarkar hidima Mahajjata mai tasiri, daga hidimomi da tattali domin hajji da umrah, wanda za su ka ga cimma tsarin kawo canji ga kasar mai taken 2020, da manufar bunkasa ta da aka masa lakabi da 2030.
Shugaba Abdurrahman Ma'ayuf Alharbiy ya karfafa cewa lallai hukumar kulawa da motocin jigilar Mahajjata ta tsayu wajen yin jerin ayyuka kuma cikakku, wadanda aka hada karfi domin hidimar Mahajjata, da kauracewa barci domin samun hutunsu, da yin hidimomi a gare su, tun lokacin shigowansu wannan kasa (Saudia), ta dukkan hanyoyin shiganta, domin sauke ayyukansu na hajji, har zuwa lokacin ficewarsu daga kasar ta Saudia.

Tsarin aikin kula da motocin jigilar mahajjata na shekarar 1439h ya yi nunin cewa, lallai jimillar kujerun bus din jigilar hajji, wadanda suke aiki akan tsarin jigilar kai-komo (النقل الترددي) sun kai kujeru 849,019, wanda hakan ke nuna cewa, matsakaicin abinda kowace bus take da sun a wuraren zama shine gurbi 47.

---------- Map na intanet
A karon farko, ofishin kula da motocin jigilar Mahajjata, sun sake wani tsari mai suna "daif" a intanet, domin tsattsara hidimomin jigilar jeka-ka-dawo, a wuraren ibada masu tsarki (Minah, Arfah, Muzdalifah), domin bude hidimar jigilar, ko cike bayanan neman jigilar, da tsara ayyukan gudanar da jigilar motocin, da bin inda suke; ta hanyar map da yake cikin intanet, wanda hakan zai bada damar bin-diddigin fiye da bus dubu goma sha takwas (18), a lokaci guda.

Gwargwadon abinda ya zo cikin maganar Daraktan kula da aikin motoci a wuraren aikinsu; wato injiniya Ahmad Kariy, to lallai wannan matakin ya zo cikin matakan yin amfani da dukkan damammaki, domin hidima ga bakin Allah; Mahajjata, ta hanyar bibiyar yadda bus take tafiya a lokacin tafiyarta, wanda hakan zai samar da kulolon aminci kan motocin jigila da sadarwa".
A nan sai Dr. Kariy ya kara bayani cewa: "Shi tsari mai suna daif, zai baiwa hukumar kula da jigilar motoci damar bibiyar motsawan dukkan bus na jigila mallakin kamfanonin da suka yi tarayya wajen hidimar hajjin wannan shekarar, da yadda motocin nasu suke bin layukan da aka tsara musu, kuma za su samu tabbacin lokatan lodin kai-komo wanda yake cikin tsari ko jadawali, ta hanyar linkin da aka tanadar na intanet". 
Kuma ya kara da cewa: "Lallai map na intanet yana bayyanar da layukan motocin bus, akan wata komfuta, a wani daki ko ofishi na musamman na ma'aikatan kula da wadannan motocin. Kuma wannan tsarin yay i fice ta hanyar bayyanar da gurbin da kowace mota ta ke, kuma yana sane da dukkan motsawanta, ta yadda yake bayyanar da lambar motar, da wuraren da duk ta je, gwargwadon layukansu iyakantattu. Kamar yadda yake bayyanar da kwanan watan duk wani motsi, da lokaci, ta hanyar fadin awoyi da mintoci da sekon din dakikoki, tare da bayanin irin saurin da motar ta ke yi (a dukkan wurare).
Amfani da taknoloji na zamani yana zuwa ne cikin kokarin da baya yankewa na ofishin kula wa da motoci, da nufin su samar da mataki mafi girma aminci da jin amintuwa, ga hanyoyin daukar mutane da sadar da su ga bukatunsu. Da kuma kara kyautata irin hidimar da ake gabatarwa gab akin Allah; Mahajjata.

Kuma ofishin kulawa da motocin hidimar Mahajjata suna da manufofi guda bakwai (07) domin dora motocin bus na jigilar akan hanyar da tafi, daga cikinsu:
1-     Amfani da fasahar map da take cikin intanet.
2-     Shigar da fasahar zamani domin bunkasa ayyukan dora motocin bus na jigilar Mahajjata akan turba.
3-     Bada damar yin hidimomi masu tarin yawa, wadanda suke da alaka da bibiyar motocin jigilar, bayan kulla kowace mota da mai nuna mata hanya, kuma an kasa su kashi-kashi.
4-     Baiwa shugannin kowane kamfani damar gudanar da ko bibiyar dukkan dukkan motocin da mallakinsu ne.
5-     Magance matsalar bacewar motocin jigilar, ko jinkirin dawowansu.
6-     Saurin bada sanarwan bacin motocin da ka iya aukuwa, ta hanyar mai nuna wa Direba hanya.
7-     Gano wurin da motar ta caskare, ta hanyan wannan sabon tsari.
8-     Kari akan, tabbatar wa Mahajjata hutunsu.

An mika lamarin tirenin don iya aiki da tsarin "daif" na intanet, ga ofishin samar da tsare-tsare na kula da motocin jidon Mahajjata, ta yadda su kuma suka sanar da wadanda za su amfana, ko su rika amfani da shi da ma'aikatan a mu'assasosin bayar da hemomi da kula da jigila, tare da nuna wannan tsarin ga masu aikin nuna wa direbobi wurare, da wasu daga cikin direbobin motocin bus wadanda suke jigila ta kai-komo.

·        Adadin Mahajjatan da aka yi jigilarsu da motocin bus, a shekarun da suka gabata:
§  Hajjin 1435H: 1,324,000
§  Hajjin 1436H: 1,364,000     
§  Hajjin 1437H: 1,334,000
§  Hajjin 1438H: 1,644,000
§  Hajjin 1439H: 1,820,000

·        Manufofin aikin bibiyarmotocin jigilar Mahajjata ta tsarin kafar intanet
1)     Amfani da fasahar map da take cikin intanet.
2)     Shigar da fasahar zamani domin bunkasa ayyukan dora motocin bus na jigilar Mahajjata akan turba.
3)     Bada damar yin hidimomi masu tarin yawa, wadanda suke da alaka da bibiyar motocin jigilar, bayan kulla kowace mota da mai nuna mata hanya, kuma an kasa su kashi-kashi.
4)     Baiwa shugannin kowane kamfani damar gudanar da ko bibiyar dukkan dukkan motocin da mallakinsu ne.
5)     Magance matsalar bacewar motocin jigilar, ko jinkirin dawowansu.
6)     Saurin bada sanarwan bacin motocin da ka iya aukuwa, ta hanyar mai nuna wa Direba hanya.
7)     Gano wurin da motar ta caskare, ta hanyan wannan sabon tsari.
8)     Kari akan, tabbatar wa Mahajjata hutunsu.

## Labarin ya kare##  


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...