HAJJI … RUKUNNANSA DA WAJIBANSA
(الحج .. أركان وواجبات)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Shin ka yi azamar hajji a wannan
shekarar?
Shin kana son hajjinka ya zama
mabrur?
To, sai ka koyi hukunce-hukuncen
hajjinka, sai ka yi aiki da su da-kyau, kuma tsarkake Allah da ikhlasi cikin
hajjinka.
Hajji yana da RUKUNNAI guda hudu.
Da ayyukan WAJIBI guda bakwai.
Kuma banbanci tsakaninsu shine
lallai WAJIBI idan ya kubuce, ana cike gibinsa da yanka dabba. Amma shi kuma
RUKUNI to lallai hajjin baya inganta sai in aikata shi.
RUKUNNAN HAJJI sune:
1. YIN HARAMA: Kuma shine niyyar
shiga cikin aikin.
2. TSAYUWA GA ARFAH.
3. DAWAFUL IFADHA: Kuma shine ake
aikata shi ranar idi ko bayansa.
4. YIN SA'AYI tsakanin Safah da
Marwah.
Su kuma WAJIBAN HAJJI: Sune:
1. YIN HARAMA daga Mikati.
2. WANZUWA A FILIN ARFAH, har zuwa
faduwar rana, ga wanda yay i tsayuwarsa da rana.
3. KWANA A MUZDALIFA.
4. KWANA A MINAH.
5. JEFA JAKWANKWANI.
6. ASKE GASHIN KAI GABA DAYA, KO
RAGE SHI, Saidai askewan shine yafi falala.
7. DAWAFIN BANKWANA ga wand aba mai
haila ko jinin biki ba.
Duk kuma abin da ba wadannan ba,
sunnoni ne abin so, kamar kwana a Minah a dare tara.
Sai ka yi kokarin hajjinka ya
cika, ta hanyar aiki da RUKUNNANSA DA WAJIBANSA DA SUNNONINSA, domin ya kasance
hajji gangariya karbabbe. Kuma ka sani! Lallai sakamakon haka shine Aljannah,
saboda ya zo cikin hadisi cewa:
"والحج المبرور ليس له جزاء إلا الجنة"، متفق عليه.
Ma'ana: "Kuma hajji gangariya bashi da
wani sakamako face Aljannah", Bukhariy da Muslim.
No comments:
Post a Comment