BULAGURO ZUWA HAJJI
(رحلة ملبي)
TANADAR
(زاد)
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
Allah ya umarci annabi Ibrahima (alaihis salam) da cewar
ya daga ginin Masallaci mai alfarma, sa'annan ya kira mutane zuwa ga tafiya hajji,
sai wannan wurin ya kasance mai albarka, kuma shiriya ga talikai, kuma zuwa
gare shi, rayukansu su ke shauki, kuma zukatansu su ke karkata.
Kuma a shekara ta tara (9) ta hijira ayar
da ba a soke hukuncinta ba, ta sauka ga Annabi (sallal lahu alaihi wa sallama),
wanda take wajabta wa mutane hajjin dakin Allah, ga wanda ya samu hanyar zuwa
gare shi, Sai hajjin ya kasance farilla daga farillan Musulunci, da rukuni daga
cikin rukunnansa, Allah Ta'alah ya ce:
"ولله على
الناس حج البيت من استطاع إليه سبيلا ومن كفر فإن الله غني عن العالمين"
[آل عمران: 97].
Ma'ana: (Kuma Allah ya wajabta wa mutane, ziyartar
wannan dakin, ga wanda ya samu hanyar tafiya gare shi, kuma duk wanda ya
kafirce to lallai ne Allah Mawadaci ne ga barin halittu) [Ali-imraana: 97].
Don haka,
Ya zama wajibi ga Musulmi, ya yi gaggawan
sauke farillar hajji, duk lokacin da ya kasance yana da iko, saboda bai san mai
zai kasance tare da shi ba, idan ya jinkirta shi, saboda ya zo cikin hadisi
daga Annabi (sallal lahu alaihi wa sallama) lallai shi ya ce:
"تعجلو إلى الحج
–يعني الفريضة-، فإن أحدكم لا يدري ما يعرض له"، رواه أحمد.
Ma'ana: (ku yi gaggawan yin hajji –yana nufin na
farilla- saboda dayanku bai san abinda ka-iya bijiro masa ba), [Ahmad ya ruwaito shi, 1/314, kuma Albaniy ya ce
hadisi ne hasan [a cikin littafin Irwa'ul galil, 990].
Kuma wajibi ne ga wanda ya yi azamar
aiwatar da wannan farillar mai girma.
1- SHIRI A GARE TA, ta hanyar
gangariyar tuba.
2- DA IKHLASIN niyya ga Allah
shi kaxai, sai ya nemi ganin fiskar Allah, da hajjinsa, da kuma gidan lahira.
3- Sai kuma YA YI QOQARIN SAUKE
HAQQOQI, DA BASUKA, DA KAYAN MUTANE DA SU KE HANNUNSA.
4- Sai kuma ya yi WASIYYA GA
IYALANSA DA BIN DOKOKIN ALLAH da taqawa.
5- Sai kuma ya rubuta wasiyyarsa,
idan akwai abinda zai yi wasiyyar da shi, na haqqoqi da wasunsu.
6- Ya kuma TANADI GUZURI daga dukiya
ta halal.
7- Ya kuma nemi abokan tafiya nagari
8- Ya kuma KOYI FIKIHUN HAJJI da
SIFAR HAJJI
9- YANA MAI YIN GUZURI DA LITTAFAN
MA'ABUTA ILIMI da suke magana akan haka.
Manzon Allah (sallal lahu alaihi wa
sallama) ya ce:
"العمرة إلى
العمرة كفارة لما بينهما، والحج المبرور ليس له جزاء إلا الجنة".
"UMRAH ZUWA UMRAH YANA KANKARE ABINDA YA AUKU
TSAKANINSU, SHI KUMA HAJJI GANGARIYA BASHI DA WANI SAKAMAKO FACE ALJANNAH", [Bukhariy da Muslim].
No comments:
Post a Comment