ARFAH SHINE WANNAN YININ DA AKE
HALARTA
(عرفة ذلك اليوم المشهود)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Idan rana ta fudo a yini na tara (9)
a watan ZUL-HIJJAH, Mahajjata su kan nufi filin Arfah, domin sauke babban
rukunin hajji, a cikin wani yini daga cikin jerin yinin da ake halarta, kamar
yadda Allah Ta'alah ya ce:
"واليوم الموعود * وشاهد ومشهود".
Ma'ana: "Kuma ina rantsuwa da yinin da
aka yialkawarin zuwansa * da yini mai shaidu, da yini da ake halartan Arfa a
cikinsa".
Kuma abinda ake nufi da yini mash-hud shine yinin Arfah, kamar yadda
hakan ya tabbata daga Annabi –Sallal Lahu alaihi wa sallama-.
Kuma yana daga falalar wannan yinin akan sauran kawanaki, lallai shine
yinin da Allah ya dauki alkawari da 'yan-adam. Kuma shine yinin da Allah ya
cika addini a cikinsa, kuma ya cika ni'imarsa ga Annabi –sallal Lahu alaihi wa
sallama-, da Al'ummarSa. Kuma rana ne na gafarta zunubai, da 'yanta bayi daga
fadawa wuta. Kuma ranar idi ne ga wadanda suka tsayu a filin Arfah.
Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya shar'anta azumtar wannan yinin
ga wanda ba Mahajjaci ba, a cikin fadinSa:
"صيام يوم عرفة أحتسب على الله أن يكفر السنة التي قبله والسنة التي
بعده"،
مسلم.
"Azumin yinin Arfah ina fatan
Allah zai kankare shekarar da ta gab ace shi da shekarar da take bayansa",
Muslim.
Kuma a farfajiyar Arfah Mahajjata ke tsayawa, suna masu ambaton Allah Ta'alah,
suna masu fiskantarsa da addu'oi, suna masu tsoro masu Kankan-da-kai, har zuwa
faduwar rana.
Allah yana alfahari da su ga Mala'ikunsa a wannan yammacin wannan yinin,
sai ya ce:
"انظروا إلى عبادي أتوني شعثًا غبرًا، من كل فجّ عميق، أُشهدكم أني قد
غفرت لهم".
"Ku yi dubi ga bayina, sun zo
min da gizo da kura, daga kowani lungu mai nisa, Ina shaida muku lallai ni na
gafarta musu".
Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"خير الدعاء دعاء يوم عرفة، وخير ما قلت أنا والنبيون من قبلي: لا إله
إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير"
"Mafi alherin addu'a shine
addu'ar yinin Arfah, kuma mafi alherin abinda na fada Ni da annabawan da suka
zo gabanina shine: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL
HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR".
No comments:
Post a Comment