AMFANI
DA DUKKAN DAMAMMAKI, DOMIN HIDIMAR BAKIN ALLAH; MAHAJJATA, DON SU YI TAFIYARSU
TA HAJJI CIKIN SAUKI DA NATSUWA
(تسخير
كافة الإمكانات لضيوف الرحمن لتأدية رحلة الحج بيسر وطمأنينة)
Mai girma
ministan hajji da umrah;
Dr.
Muhammadu Salih bn Dahir Bintin
معالي وزير الحج
والعمرة د. محمد صالح بن طاهر بنتن
Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya
Ministirin hajji da umrah ta kasar Saudia
|
MA'AIKATA
|
Bayani ga 'yan jarida
|
SASHEN SADARWA
|
Amfani da dukkan damammaki domin
hidimar bakin Allah; Mahajjata, don su yi tafiyarsu ta hajji cikin sauki da
natsuwa
|
MAUDU'I
|
Cikin kasar Saudia da wajenta
|
YADAWA
|
06/ Zul-hijjah/1439h
|
RANA
|
Mai girma ministan hajji da umrah; Dr. Muhammadu Salih bn Dahir
Bintin
|
MASU MAGANA
|
Mai girma
Ministan hajji da umrah
YIN
AMFANI DA DUKKAN DAMAMMAKI, DOMIN HIDIMAR BAKIN ALLAH; MAHAJJATA, DON SU YI
TAFIYARSU TA HAJJI CIKIN SAUKI DA NATSUWA
Mai girma
ministan hajji da umrah; wato Dr. Muhammadu bn Salih bn Dahir Bintin, ya
bayyana cewa lallai bin yadda ayyukan suke gudana ko-da yaushe, da umurnin Mai
hidimar harami biyu masu girma; Sarki Salman bn Abdul'aziz, da kuma Mai girma
Na'ibin sarki, wato Yarima Muhammadu bn Salman bn Abdul'aziz, wanda shine
Na'ibin shugaban majalisar ministoci, kuma ministan tsaro –Allah ya kiyaye su-,
sun nuna cewa: A yi amfani da dukkan damammaki da kafatanin ma'aikata, domin
hidima ga Bakin Allah, wadanda suka zo domin hajjin dakin Allah mai alfarma.
Kuma Mai
girman ministan ya tabbatar cewa hukumarsa da sauran hukumomi sun yi
cikakken shiri domin tarbar Bayin Mai rahama, wadanda suka fito daga sako
daban-daban na Duniya, wadanda suke shiri a ranar lahdi mai zuwa (wato, ranar
takwas ga watan zul hijjah) cewa za su sauka a mahada ta farko daga cikin wuraren
bauta masu tsarki, domin su kwana a wurin da ake kira Minah, (Ministan)
yana mai fatan su samu tafiyarsu ta imani, cike da natsuwa, don su sauke
hajjinsu da ibadodinsu cikin dukkan sauki da natsuwa.
Kuma minister
Dr. Bintin ya ce: "Lallai ministirin hajji da umrah, da dukkan
bangarorinta, suna yin aiki tukuru, tare da samun taimakon dukkan hukumomin da
aka hada na hajji da umrah, wajen gabatar wa bakin Allah mafi kyan hidimomi, a
lokacin tarbarsu a wuraren ibada masu tsarki (Minah, Muzdalifah, da Arfah), har
zuwa lokacin da za su koma gidajensu suna masu riba da samun babbar ganima".
Kuma Mai
girma ministan hajji da umrah Dr. Bintin ya yi nuni cewa lallai hukumar
hadimin harami guda biyu madaukaka, ta yi aiki dayawa daga mafi girman ayyukan
fadada Masallatai wanda garurruka biyu masu tsarki suka taba samu a tarihin
Musulunci, wanda kuma hakan shine ya kara yawan abinda Masallatan biyu zasu
dauka na masu ibada, kuma ya baiwa Musulmai daga ko-ina suke a Duniya, damar
yin ayyukansu na ibada cikin sauki da natsuwa.
Kamar yadda
masarautar Saudia ta yi manyan ayyukan raya kasa, a garin Makkah da Madina da
wuraren bauta na Mina da Muzdalifa da Arfah, wanda suka zama cibiyoyin ayyukan
hidimtawa masu tarin yawa, wanda kuma sun kunshi:
1.
Ayyukan fadada harami biyu masu daraja.
2.
Da kuma wuraren da aka ware, sannan aka gina mazaunan
Mahajjata, a wuraren da suka fi muhimmanci (da ake kira mandika markaziyya), na
garurrukan Makkah da Madinatul
munawwarah.
3.
Da samar da jirgin kasa a wuraren ibada masu
daraja (Mina, Arfah, da Muzdalifah).
4.
Da kammala gadodi na wurin jifan shedan.
5.
Da hidimomi ta bangaren ababen daukan
Mahajjata (kamar motoci), da hidimomin lafiya, da tsafta, da wasu makamantan
haka, daga cikin hidimomi na wajibi ga masu hajji da umrah da masu ziyara.
6.
Da assasa ko samar da yanayin tarbar baki na
zamani, wanda ke karfafa hidimomi da tsare-tsaren tattali ga ayyukan hajji da
umrah.
Kuma Mai
girma ministan hajji, Dr. Bintin ya bayyana cewa, lallai manufar
bunkasa Saudia mai taken shekarar 2030 ta shigar wa aikin hajji da umrah
tsare-tsare na cigaba, wadanda babu irinsu a baya, ta yadda hukumar hajji ke
yin aiki da sabon tsari, wanda ya ginu a kan barin tsarin nan na baya; mai yin
aiki a wasu lokuta, zuwa ga aiki tukuru a tsawon shekara, da kuma aiki da
takanoloji domin bunkasa ayyuka, da tabbatar da yin aikin da bai san rufa-rufa
ba, da amfani da tsare-tsare don samar da ayyuka ingantattu, da aiki da
ma'aunan gwada ci-gaban da ake samu, domin kara bunkasa damammaki ko kara
adadinsu, da bunkasa gwanancewar ma'aikata, da kara kawo tsari ga hukumomin da
suke ayyukan hajji da umrah, da irin tsare-tsaren da insha Allahu za su taimaka
wajen tabbatuwan manufofin da ake son cin musu, zuwa shekarar 2030, tare da
tafiya da tsarin kawo canji ga kasar gaba daya.
Kuma lallai Mai
girma ministan hajji da umrah, Dr. Muhammadu bn Salih bn Dahir Bintin ya
kwadaitar da dukkanin Ma'aikatan hukumar hajji da umrah cewa su kara aiki da
kwazo, domin cimma abinda hukumar Mai hidimar harami guda biyu madaukaka –حفظه الله- ta ke fatan gani.
## Labarin ya kare##
No comments:
Post a Comment