2018/08/30

HIMMATUWAR MASARAUTAR SAUDIYA DA KULAWANTA GA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA (اهتمام المملكة وعنايتها بضيوف الرحمن)









HIMMATUWAR MASARAUTAR SAUDIYA DA KULAWANTA GA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA
(اهتمام المملكة وعنايتها بضيوف الرحمن)




Mai girma Na'ibin ministan hajji da umrah;
Dr. Abdulfattah bn Sulaiman Mash-shad
معالي نائب وزير الحج والعمرة د. عبد الفتاح بن سليمان مشاط











Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya


Ministirin hajji da umrah
MA'AIKATA
Bayani ga 'yan jaridu
SASHEN SADARWA
Tsarin yanar gizo da ke dora bus din jigilar daukar Mahajjata hanya/ Bus dubu sha takwas (18,000) domin jigilar Mahajjata zuwa wuraren bauta tsarkaka (Minah, Arfah, da Muzdalifah)
MAUDU'I
Cikin kasar Saudia da wajenta
YADAWA
09/ Zul-hijjah/1439h
RANA
>Mai girma Na'ibin Ministan hajji da umrah; Dr. Abdulfattah bn Sulaiman Mash-shad
MASU MAGANA
HIMMATUWAR MASARAUTAR SAUDIYA DA KULAWANTA GA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA
SAKON AIKIN

Mai girma Na'ibin Ministan hajji da umrah
HIMMATUWAR MASARAUTAR SAUDIYA DA KULAWANTA GA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA

Mai girma Na'ibin Ministan hajji da umrah; Dr. Abdulfattah bn Sulaiman Mushad ya bayyana cewa lallai bada kulawa ga Mahajjatan 'dakin Allah mai alfarma, yana tsayawa wajen fito da alhaki mai girma da ya doru a wuyan Masarautar larabawa ta Saudia, wanda ta ke samun murni na kai-tsaye daga hadimin Masallatan harami biyu, wato sarki Salman bn Abdul'aziz Alu-sa'ud, da mai jiran gado ma'abucin girma mai mulki Yarima Muhammadu bn Salman bn Abdul'aziz, wanda shine Na'ibin shugaban majalisar ministoci, kuma ministan tsaro –Allah ya kiyaye su-.

Kuma Dr. Mushad ya ce: "Lallai manyan ayyuka, wanda suka kasance, daga cikin jeringiyar hidimomin hajj da umrah, da aikin fadada Masallaci mai alfarma a karo na uku, kari a kan manyan ayyuka a wuraren ibada masu tsarki (Minah, Arfah, Muzdalifah), suna zuwa ne domin su iya daukan adadin Mahajjata, wanda ke kakkaruwa a kullum, kuma wadannan ayyukan sun fada cikin tarin ayyukan wannan kasa mai albarka ga bayin Allah; Mahajjata".

Kuma Mai girma Na'ibin ministan hajji da umrah ya karfafa cewa lallai umurnin mai hidimar harami biyu madaukaka da wanda mai girma mai jiran gadonsa yake bayarwa sun tsananta ga dukka hukumomi da ofisoshin da suke tarayya da hukumar hajji da umrah, a hajjin shekarar hijira ta 1439 kan muhimmancin bada cikakkiyar kulawa ga Mahajjata dakin Allah mai alfarma; ba tare da rarrabewa ba.

Kuma Dr. Mushad ya ce: "Lallai hidimomin intanet wadanda ministirin hajji suka samar da su, sun saukake wa bakin Allah; Mahajjata sauke ayyukansu, kuma sun tabbatar da sanin makamar aiki wanda ya zama dole, da mataki mai girma na yin ayyuka a fili, cikin dukkan ayyukan gudanarwa, wannan kuma tun lokacin shigan bakin Allah kasa mai tsarki, har lokacin da za su bar wannan kasa zuwa ga kasashensu suna cikin aminci, da samu ganima (riba) da izinin Allah".  
Kuma Dr. Mushad ya kara da cewa: "Lallai bada himma ga sha'anonin hajji da kula da Mahajjata yana zuwa daga manyan abinda wannan daular take basu muhimmanci, ta yadda take bada kulawa ta musamman da muhimmantarwa mai girma ga dukkan bangarorin hidimomi da tsare-tsare wadanda suke da alaka da samar tare da bunkasa dukkan bangarorinsa.
Kuma babban tsarin da ke hukunci ga wannan Masarautar ya yi bayani cewa lallai alhaki ne da ya rataya a wuyar hukumar yin hidimar harami biyu, da kulawa da Mahajjata, da ayyukan raya harami biyu madaukaka, da samar da aminci (tsaro) da kulawa ga wadanda suke nufo su, ta yadda hakan zai bada damar sauke ibadodin hajji da umrah da ziyara cikin sauki da rangwame".
            Kuma shugaban ya karfafa cewa hukumar tana cikin cikakken shiri na tarbar bakin Allah; Mahajjata, wadanda suke a yau litinin suke shirin tsayuwa a filin Arfah mai tsarki, ta yadda hukumar hajji da umrah ta sanya dukkan bangarorinta da Ma'aikatanta tsayuwa da wasu ayyukan domin jin dadin  Mahajjata dakin Allah, har su sauke ibadodinsu cikin dukkan sauki da walwala.

            Kuma a cikin jerin maganganunsa, lallai Mai girma Na'ibin shugaban hukumar hajji da umrah; Dr. Abdulfattah bn Sulaiman Mushad, ya bayyana cewa, lallai dukkan wakilan hukumar hajji masu yin aiki a wurare za su kasance a halarce a dukkan wurare, domin tabbatar da gabatar hidimomi ga Mahajjata, da tabbatar da kasancewar hidimar sun dace da sharruda da kuma sifofin da aka bayar'

            Kuma gwargwadon abinda ya zo daga Dr. Mushad lallai hidimar Bakin Allah daya ne daga cikin shirye-shirye na tabbatar da manufar wannan kasa mai taken shekarar 2030, wadanda "majalisar sha'anoni tattalin arziki da bunkasa kasa" suke aikin kula da zartar da shi, zuwa shekara ta 2020.
Kuma manufar wannan shirin na farko wanda a yanzu haka ya kama aiki, yana karfafa lamarin/ Saukake tarbar karin adadin Masu umrah, da saukake isowarsu harami biyu masu girma.
ita kuma manufa ta biyu an kebe ta ne wajen gabatar da hidimomi ma'abuta madaukakin kyau ga Mahajjata da masu umrah.
Ita kuma manufa ta uku tana bada muhimmanci ne, kan zurfafa wayewar addini da zamani a tsakankanin Mahajjata da masu umrah.

Kuma Dr. Mushad ya ce: "Tsarin shirin (hidimar bakin Alla; Mahajjata) yana bada dama wa adadi dayawa na Musulmai su sauke farillarsu ta hajji da umrah da ziyara, ta mafificiyar fiska, tare da yin aiki kan zurfafa wayewar addini da zamani a tsakankanin Mahajjata da masu umrah, ta hanyar shirya harami guda biyu madaukaka, da tabbatar sakon Musulunci; addinin Duniya, da shirya wuraren yawon bude-ido, da samun wayewa, da bayar da gabatar da mafi kololuwar hidimomi gabanin da lokacin da bayan ziyarar Mahajjata garin Makkatul mukarrama da Madinatul munawwara, da wuraren bauta masu tsarki (Mina, Arfah, Muzdalifah). Da kuma karfafa alakar kamfanoni masu cin gashin kansu, da yadda za su bada gudummawa mai girma wajen kyautata tattalin kamfanoninsu".

Kuma shirin "Hidimar bakin Allah; Mahajjata" an sanya masa manufofi guda takwas, wadanda ba su ne na asali ba, wadanda ake samunsu a cikin wasu tsare-tsaren na-daban, daga cikinsu akwai: Kyautata tsarin ginin biranen Saudia, bunkasa bangaren buda-ido, kiyaye ababen da aka gada a wannan masarauta ta Saudia na Musulunci, da Larabawa, da Kasa, da aikin sanar da Mutane wadannan kayayyakin.
Kuma Dr. Mushad ya gama ta'alikinsa ne, da cewa: lallai ministirin hajji da umrah ta kirkiri ofishin ganin tabbatuwar manufar kasar Saudia (2030) mai alaka da bangaren hajji da umrah, domin ya zama window ne wanda ta nan Duniya za ta tsinkayi aikin bunkasa wannan kasar, kuma shine zai kulle tsakaninta da tsakanin abokan tarayyarta, domin abubuwan da wannan hukumar ta hajji zata fito da su, domin tabbatar da wannan manufa ta kasa.
Kuma shima tsarin kawo canje-canje na kasa wanda ke da manufar bayar da dama ga adadi mai yawa na Musulmai, damar sauke faralin ayyukan hajji da umrah, da zartar da tsare-tsare masu dogon zango masu kuma tasiri, tare da gamayyar kamfanoni. Da bunkasa wayewa ko karuwar ilimin Mahajjata da masu umrah, da bunkasa wayewar ma'aikatan hukumar hajji da umrah. Da samar da hanyoyin bunkasa tsari tsakanin dukkan Ma'aikatun da alhakin yin dokoki da gudanar na lokaci hajji da umrah ya doru a wuyansu.

Kuma Mai girma Na'ibin ministan hajji da umrah ya ce: "Ofishin tabbatar da manufofin kasa 2030 ya gabatar da ayyuka dayawa ta wannan  bangaren, daga cikin misalinsu akwai: Tanadar cikakken tsari na wuraren ibada masu tsarki (Minah, Arfa, Muzdalifah), kuma wannan aikin ya kebantu, da yin nazarin hakin da wuraren suke a yanzu, a cikin ckakken tsarin nan na bunkasa Makkatul mukarrama da Madinatul munawwara, ta yadda za su iya zama cikin shirin tarbar Karin adadi mai yawa nab akin Allah; Mahajjata, domin tabbatar da manufar 2030, da samar saukin aiki da jin dadi da kula da lamuran tsaro da aminci, da tsare-tsaren kula da muhalli, da kauce wa ababen da suke bata gari, da kula da tsafta, da tabbatar da samar da birane masu bishiyoyi korra, da kawo cigaba ta bangaren takanoloji, da tsarin da zai tabbatar da gabatar da hidimomi, musamman a lokutan cunkoso, wajen yawatawan Mahajjata, a lokacin zamansu a Makka da Madina da wuraren bauta na Mina da Arfa da Muzdalifa, da lura da kai-komon masu umrah da mahajjatan cikin kasa, da yadda za a gudanar da ayyukan taron jama'a. kuma lallai yiwuwar amfana da dukkan wurare abu ne da ake nazari akansa, a lokacin ayyukan hajji da umrah da ziyara, da kara bunkasa abinda za a samu ta bangaren tattalin arzikin kasa, tare da shiga da kamfanoni a cikin lamarin. Haka lamarin samar da tare da shirya nazari kan menene amfanuwa da za a iya samu, da rubuta sharudda da sifofin ayyuka, domin a iya zartar da abinda zai haifu na ayyukan da za a zartar da su a gaba, bayan an gudanar da wadancan bincike-binciken"

## Labarin ya kare##



No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...