ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'DAH
(خصائص شهر ذي القعدة)
Tarjamar
Abubakar Hamza
Allah ya fifita sashen watanni
akan sashe,
"وربك يخلق ما يشاء ويختار".
Ma'ana: "Kuma Ubangijinka yana halitta
abinda ya so, sai kuma ya yi zabi".
Kuma yana daga cikin watannin da Allah Ta'alah ya fifita su, WATAN
ZULKA'ADAH, wanda kuma shine wata na goma sha daya (11) daga cikin watannin
shekarar hijira.
Kuma an sanya masa wannan suna na zul-ka'ada ne, saboda labara a cikin
wannan watan su kan zauna su bar yaki, saboda girmama wannan watan, kuma domin
su shirya domin yin hajji a watan zul-hijjah.
Kuma yana daga ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WANNAN WATAN, Shine farkon
watanni masu alfarma guda hudu, wadanda Allah Ta'alah yake cewa a kansu:
"إن عدة الشهور عند الله اثنا عشر شهرا في كتاب الله يوم خلق السموات
والأرض منها أربعة حرمٌ، ذلك الدين القيم فلا تظلموا فيهن أنفسكم".
"Lallai kidayar watanni a wurin
Allah wata goma sha biyu ne, a cikin littafin Allah, tun ranar da ya halitta
sammai da kasa, a cikinsu akwai guda hudu masu masu alfarma, wannan shine
addinin mikakke, don haka kada ku zalunci kayukanku a cikinsu".
Kuma larabawa sun kasance suna daukar wadannan watannin (hudu) masu
alfarma ne, saboda Mutane su samu aminci, a hanyarsu ta tafiya zuwa ga hajji,
Sai musulunci ya zo, ya kara basu alfarma, kuma ya haramta fara yin yaki a
cikinsu, kuma yay i hani kan zalunci a cikinsu, domin kara girmama lamarinsu, da
kausasa lamarin yin zunubi a cikinsu, duk da cewa, yin zalunci lamari ne da aka
yi hani akansa a cikin sauran watannin wadanda ba hudun nan ba.
Kuma yana daga ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'ADAH, Lallai
shi yana daga watannin hajji, wanda niyyar hajji bata kulluwa sai a cikinsu,
kamar yadda Allah Ta'alah yake cewa:
"الحج أشهر معلومات فمن فرض فيهن الحج فلا رفث ولا فسوق ولا جدال في
الحج".
"Hajji watanni ne sanannu, kuma
duk wanda yay i niyyar hajji a cikinsu, to babu kwarkwasa, babu fasikci, kuma
babu jayayya a cikin hajji".
Kuma yana daga ABUBUWAN DA SUKA KEBANCI WATAN ZUL-KA'ADAH, Lallai
Annabi صلى
الله عليه وسلم ya yi umrarsa guda hudu ne, a cikin
wannan watan, saboda an ruwaito daga Anas –Allah yakara yarda a gare shi-, "Lallai Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya yi umrah
guda hudu, kuma dukkansu a watan zul-ka'adah ne, in banda wanda take tare da
hajjinsa".
Nawawiy ya ce:
"Lallai Annabi –sallal Lahu alaihi wa
sallama- yay i wadannan umran ne gabadayansu a watan zul-ka'adah, saboda
falalar wannan watan, kuma domin ya saba wa mutanen jahiliyya cikin haka, domin
su sun kasance suna ganin yin umrah a cikin watanni masu alfarma guda hudu,
daga cikin mafi girman fajirci".
No comments:
Post a Comment