HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 28/ZUL-KA'ADAH/1439H
Daidai da 10 /OGOSDOS / 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
DR. ABDULMUHSIN DAN MUHAMMADU DAN ABDURRAHMAN
ALKASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
HAJJ
تزكية النفوس وإصلاحها
Shehin Malami wato:
Abdulmuhsin bn Muhammadu bn Abdurrahman Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya
yi hudubar juma'a mai taken: AIKIN HAJJ, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke
tafe, Ya ce:
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da
kuma a bayyane (a lokacin ganawa).
Ya ku musulmai …
LOKATAN ALKHAIRAI SUNA
SABUNTUWA GA BAYI,
falala
daga Allah da karamci, saboda wata ibada bata shudewa face lokacin yin wata yam
aye gurbinta, to yanzu ga Mahajjatan farko-farko sun nufi dakin Allah mai
tarihi, suna masu amsa kiran da badin Allah annabi Ibrahim –عليه السلام- ya yi: "Kuma ka yi shelar
aikin hajji ga Mutane, za su zo maka da kafa, da kuma akan dawakai, za su zo
daga dukkan lungu mai nisa", [].
Nufato dakin Allah da hajji
farilla ne, kuma ibada, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ya ku Mutane! lallai ne Allah ya farlanta
hajji akanku; sai ku yi hajji", Muslim ya ruwaito shi.
Hajji ibada ce mai girma a
Musulunci, domin shine rukuninsa na biyar, kuma yana cikin manyan da'oi,
wadanda Allah yafi sonsu, saboda an tambayi Annabi –صلى الله عليه وسلم- cewa: "Wane aiki ne a
cikin ayyuka yafi falala? Sai ya ce: Imani da Allah, sai ya ce: sa'annan sai
me? Ya ce: sai jihadi fiy sabil Lahi, sai ya ce: sa'annan sai me? Ya ce: sai
hajji lafiyayye",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma da aikata hajji ake
shafe zunubai da kura-kurai, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kuma hajji yana rushe abinda ya kasance
gabaninsa",
Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, hajji tsarkaka ne
ga ma'abutansa kuma dauraya, saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda yay i hajji bai yi kwarkwasa ba, bai
yi fasikci ba, zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi", Bukhariy da Muslim.
Mahajjata ne kawai Allah ke
alfahari da su ga ma'abutan sammanSa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu wani yinin da Allah yafi 'yanta bayi a
cikinsa daga wuta fiye da ranar Arfah, saboda Allah yak an kusanto, sai ya yi
alfahari da su ga Mala'ikunSa, ya ce: Me wadannan suke nema?", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma babu wani sakamako ga
wanda ya tsarkake niyya cikin hajjinsa face Aljannah, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Umrah zuwa umrah
suna kankare abinda ya auku tsakaninsu, shi kuma hajji lafiyayye bashi da wani
sakamako face Aljanna",
Bukhariy da Muslim.
Hajji shine taron Musulunci
mafi girma, wanda ke kulla tsakanin Musulman yau da wadanda suka shude, domin
bayi su rayu a matsayin al'umma daya, suna masu riko da addininsu. Kuma babu
hanyar tabbatuwan hakan sai sun yi riko da littafin Allah da sunnah, sun kuma
tafi akan turbar magabatan al'umma na kwarai.
Kuma a cikin hajji fifikon
jinsi da harshe da launi suke tafiya kuma su bace. Sai ma'aunin fifiko dake
wanzuwa ya kasance shine takawa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai wanda yafi
matsayi a cikinku shine wanda yafi ku takawa", [Hujurat: ].
Kuma mafi alherin guzurin
da mahajjata ke tafiya da shi a cikin aikinsu shine takawa, Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma ku yi guzuri,
kuma lallai mafi alherin guzuri shine tsoron Allah, kuma ku yi takawata ya
Ma'abuta hankali",
[Bakara: ].
Kuma duk wanda ya nufi
dakin Allah, to ya dace da shi ya lazimci tsantsenin da zai kange shi daga
aikin sabo, da hakurin da zai hana shi yin fushi, da kyakkyawar mu'amala ga
wadanda zai yi abota da su.
Kuma mafi girman abinda
bayi suke kusantar Ubangijinsu da shi a cikin hajjinsu shine TAUHIDI, da
TSARKAKE AYYUKA GA ALLAH cikin dukkan bautansu, Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma ku cika hajji
da umrah domin Allah",
[Bakara:].
Kuma lallai shelanta
kadaitakar Allah a cikin hajji shine tambarin mahajjata, kuma da shi suke samun
daukaka "LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIK, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIK, INNAL
HAMDA WANNI'IMATA LAKA WALA WAL MULKA LA SHARIKA LAK".
Kuma duk wanda yayi hajji
yana mai yakinin haduwa da Ubangijinsa, to ya yi riko da lamarin tauhidin Allah
da kadaita shi da ibada har zuwan mutuwansa, Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma duk wanda ya
kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa, to ya aikata aiki na kwarai, kuma
kada yay i shirki da wani cikin ibadar UbangijinSa", [Kahf: ].
Kuma yin KABBARORI GA ALLAH
DA GIRMAMA SHI shine ke debe wa Mahajjata kewa a cikin dawafinsu, da sa'ayinsu,
da lokacin jifan Shedan da yayin yanka, da cikin darensu da yininsu, domin
zukata su wanzu suna rataye da Allah, kuma tsarkakakku daga dukkan wand aba shi
ba.
Hajji makaranta ce ta
tabbatuwa kan bi da koyi da shugaban halittu –صلى الله عليه وسلم-; saboda babu hajji, haka babu wata ibada da zata cika ta samu
kamala, sai irin abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya aikata, kuma wanda ta kasance akan shiriyarsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Domin ku koyi
aikinku na hajji, saboda lallai ni, ban sani ba, la'alla b azan yi hajji ba,
bayan wannan hajjin nawa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma koyi da Annabi SAW
dalili ne kan gaskiyar imani da kuma sonsa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Idan kun
kasance kuna son Allah, sai ku bi ni, Allah zai so ku, kuma ya gafarta
zunubanku, domin Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Ali-imrana: ].
Kuma duk ibadar da ta saba
wa shiriyar Annabi –صلى
الله عليه وسلم- Allah ba zai karbe ta ba, saboda rugujejjiya ce, Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda ya aikata
wani aiki wanda babu umurninmu, to an mayar masa", Muslim ya ruwaito.
Kuma yana daga MANUFOFIN
HAJJI MASU GIRMA: Tsayar da ambaton Allah, da yawaita zikirinsa, A'isha –رضي الله عنها- ta ce: "Lallai an shar'anta
dawafin dakin Allah ne, da sa'ayi tsakanin Safah da Marwah, da jifan tsakuwa,
domin tsayar da ambaton Allah".
Saboda haka, Ambaton Allah
Ta'alah yake kasancewa da Mahajjata, duk lokacin da suka taso, ko suka sauka,
ko suka gangaro, ko suke hawa, kuma ba zai gushe yana tare da su ba, har
lokacin gama aikinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka cika
aikinku, sai ku yi zikirin Allah, kamar ambaton Ubanninku, ko ambaton da ya fi
haka",
[Bakara: ].
Kuma Mahajjacin da yafi
kusanci da Allah, shine wanda yafi su yawaita ambaton Allah.
Hajji aikin da'a ne, wanda
ayyukan da'a suke tattare da shi, a cike yake da tarin amfani da guraben daukar
izina da ayoyi. Kuma a cikinsa akwai tsarkake zuciya ga Allah Ta'alah, da
sallama rai a gare shi da nuna cikar bauta, Shekhul Islam –رحمه الله- ya ce: "Hajji yana ginuwa
ne akan mika wuya da Kankan-da-kai ga Allah, shi ya sa ya kebanta da sunan:
NUSUK".
A hajji Musulmai ke samun
haduwar zukata, sai igiyoyin soyayya su kara karfi a tsakaninsu. Sai girman
Musulunci da falalarsa ta bayyana ga halitta, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ya daidaita
tsakanin zukatanku, da zaka ciyar da abinda ke bayan kasa gaba daya, gaba daya,
da ba za ka iya daidaita tsakanin zukatansu ba, Saidai Allah shine ya daidaita
tsakaninsu",
[Anfal: ].
Kuma cikin haduwar
Mahajjata a bagire daya akwai nuna ko tunatarwa kan falalar wannan al'ummar, da
daukakar sha'aninta.
Kuma mafi alherin Mahajjata
shine wanda ya fi su kyan hali, kuma da haka bawa ke koyan sifofi da halaye
ababen yabo, Allah Ta'alah ya ce: "Duk wanda ya niyyaci hajji a cikinsu, to
babu kwarkwasa, kuma babu fasikci, kuma babu jayayya a cikin hajji", [Bakara: ].
Kuma cikinsa akwai horas da
rai kan juriya da hakuri, A'ishah –رضي الله عنها- ta ce: "Muna ganin yin jihadi shine aikin da yafi
fifiko, shin mata ba za mu je jihadi ba? Sai Annabi SAW ya ce: A'a! ku kuna da
jihadin da yafi falala; shine yin hajji gangariya", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Musulmi yana jin daukaka da
addininsa, kuma yana nisatar da kansa daga ayyukan jahiliyya da halayensu. Kuma
a cikin hajji akwai karfafa hakan gaya, Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: "Shari'a ta tabbatu
wajen nufin saba wa mushirkai, musamman a cikin ayyukan hajji".
Kuma duk lokaci a cikin
rayuwar bawa idan bai kusantar da shi ga Ubangijinsa ba, to sai ya nisantar da
shi. Kuma lallai bayi suna cikin tafiya ne mai sauri zuwa ga Allah, kuma hakan
yana fitowa fili ga Mutum a cikin ibadodin hajji da ayyukansa, idan y agama
wata ibadar sai ya yi gaggawar fara wata, to haka sha'anin yake a cikin dukkan
rayuwarsa, Allah Ta'alah ya ce: "Idan ka gama ibada, sai ka kafu wurin
addu'a * kuma zuwa ga Ubangijinka, ka nuna kwadayi", [: ].
Aikin biyayya yana kara wa
ma'abucinsa bukatuwa ga UbangijinSa, da Kankan-da-kai, sai bawa ya shaidi
falalar Allah akansa da ya bashi damar aiwatar da ita, sai kuma ya rika neman
gafararSa akan sakaci da gajartawa a cikin ibadar, "Sannan ku gangaro
ta wurin da Mutane ke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai Allah Mai
gafara ne Mai jin kai",
[Bakara: ].
Kuma duk wanda ya kange
kansa daga aukawa cikin Mahzuraat a hajjinsa, to lallai ya dace ya hana kansa
aikata sabo, a kowani zamani da kowane wuri.
BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
Fa'idar hajji shine gyaran rai da tsarkake ta, da rabauta da
yardarm Allah Ta'alah, da tsira da Aljannonin ni'ima.
Wanda aka masa katarin
samun haka, shine wanda yay i hajjinsa da niyya tagari tsarkakakkiya, cikin
ilimi da basira, da guzuri mai dadi na halal, sai ya raya zuciyarsa da
harshensa da ambaton Allah. Kuma ya cike ibadarsa da kyautatawa halittu da
amfanar da su.
Kuma wanda ya kyautata
hajjinsa, ya nisanci abinda suke masa miki, to sai ya koma bayan hajjinsa da
mafi kyan hali, kuma ya samu daddadan makoma.
Kuma alamar karbuwar aiki
ita ce yin kyakkyawan aiki bayanta, da barin alfahari da girman kai da ibada.
A UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR
RAJIM:
"Kuma Allah ya
wajabta wa Mutane ziyartar dakinsa, ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, kuma
wanda ya butulce, to lallai Allah ya wadatu ga barin Talikai", [Ali-imrana: ].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. Kuma
ya amfanar da ni da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima.
Ina fadan abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da sauran
Musulmai daga kowane zunubi, sai ku nemi gafararSa, lallai shi Mai yawan gafara
ne, Mai jin kai
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa, kuma godiya tasa ce, akan datarwarSa da ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya; ina mai
girmama sha'aninSa,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa,
Ya Allah, ka yi dadin
salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai
ninninkuwa
Ya ku Musulmai…
Fifikon da ke tsakanin darare da yini yana kira don ribatar
alherin da ke cikinsu.
Kuma kusa-kusa mafi falalan yini a wurin Allah za su sauko a
cikinmu, Annabi –صلى الله
عليه وسلم- ya ce: "Mafi falalan kwanakin Duniya sune kwanaki
goman farkon watan hajji", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi.
Kuma ranar LAYYAH a
cikinsu shine ranar ayyukan hajji da yafi girma, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai mafi girman
kwanaki a wurin Allah Tabaraka Wa Ta'alah shine ranar soke layyah", Abu-dawud ya
ruwaito shi.
Wadannan kwanakin goma Allah yay i rantsuwa da dararensu a
inda ya ce: "Ina rantsuwa da Alfijir * da kuma darare guda goma" [Fajr: 1-2].
Kuma kowane aiki nagari idan aka yi shi a cikin wadannan
kwanakin yafi soyuwa a wurin Allah, fiye da a yi shi a cikin kwanakin da ba su ba,
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce "Babu wasu yini
wanda aiki nagari yafi soyuwa a cikinsu a wurin Allah, fiye da wadannan yinin
guda goma. Sai suka ce: Ya Ma'aikin Allah! Koda jihadi ne fiysabilil Lahi?! Sai
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: koda jihadi ne fiysabillahi, sai ga mutumin da ya fita
da ransa da dukiyarsa, sai bai koma da komai ba", Abu-dawud ya
ruwaito shi, Amma tushen hadisin yana wurin Imam Albukhariy.
Don haka, sai ku yawaita ambaton Allah a cikinsu, da tilawar
littafinSa mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Sais u ambaci sunan
Allah a cikin kwanaki sanannu", [Hajji: ].
Kuma yana daga cikin ayyuka na mustahabbi a cikin kwanakin
nan guda goma: Yin azumin yini tara na farko daga cikinsu, kuma a cikinsu an
kebance yinin Arfah, ga wand aba Mahajjaci ba, da Karin falala, saboda azuminsa
yana kankare shekarar da ta shude da wanda ake ciki.
Kuma yana daga cikin ayyuka na kwarai da suke cikin kwanakin
nan goma: Karin biyayya da kyautata wa iyaye biyu, da sadar da zumunci, da
sadaka, da yawaita nafilfilin ibadodi.
Mai rabo shine wanda ya ribaci lokutan alherori gabanin
wucewansu, kuma yay i rige wajen aikata kyawawan ayyuka, kuma ya yi rigaggeniya
da masu gaggawan aikin kwarai a cikinsu.
Kuma rayuwa ganima ce ga masu takawar Allah.
Wanda kuma yay i dace,
shine wanda aka kidanya shi daga cikin bayin Allah muhsinai.
Wanda ya yi nufin YIN
LAYYAH, to kada ya aske wani abu na gashinsa ko yanke farce ko cire fata, har
sai ya yi layyah.
Amma wanda aka bashi
wakilcin layya, ko wanda za a musu layya, idan suka kasance rayayyu, to wannan
hukuncin bai hau kansu ba.
>>>
Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da
sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana
yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani
akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu
tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment